Showing 12001 words to 15000 words out of 81932 words

Chapter 5 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

rawa ta karba sannan ta kafa kai ta rinqa zugan shi a hankali shiko sai zuba mata ido da
yayi har ta shanye.

A take sai ga zufa ta keto mata tako ina lokaci d'aya kuma ta fara damqe cikin ta.

Ganin haka yasa ya fito da kofin kai tsaye kitchen ya nufa yana zuwa ya sake had'a mata tea
mai kauri sannan ya dawo ya same ta sai riqe cikin take tana murqususu
cup d'in ya kuma miqa mata,
a wahal ce ta rinqa juya kai hawaye na bin fuskar ta cikin wahala tace.
"Cikina zan mutu."

Bai kula taba sai murtuqe fuska daya kuma yi dole ta karb'i cup d'in ta k'afa kai tana sha tana
kallon yadda ya tsuke fuska kamar d'an zai mareta dole sai data shanye sannan ta ajiye .

aiko sai zufa take ta karyo mata dole ta zaune tana yiwa kanta fifita da hannun ta duk da A.C
dake fesa sanyi.

Ido ya tsura mata tare da tab'e fuska murya a daqile yace.
"Ke ba'a wonka a garin kune?."

Murya na rawa tace .
"Anayi."

"Qazan tace ta hanaki yi ?."

"Nayi ."

"Toh wanna buhun zanin naki kuma na gadone ko?."

Zuwa yanzu hawaye ya jiqa mata gaban riga cikin tsoron yadda yake mata mgnan murya na
rawa tace.
"Banida wani kayan."

Mitsss yaja d'an gajeren tsaki sannan ya juya gun y'ar madaidai ciyar durowar ya bud'e cikin
durowar ya tsura ido har zuwa wani lokaci sannan ya zaroh wani 3qtr enshi wanda kuma kamar
skin teit ne sannan ya zaro riga mai dogon hannu rigar farace qal wondon kuma read ne mai
ratsin fari-fari, gaban ta ya dawo cikin tsuke fuska ya miqa mata,
ita kuwa hannu tasa ta karba tana mamaki ya zatayi tasa wannan kayan ,

ganin ya tsare ta da ido yasa ta shiga toilet ta zare kayan jikin ta tasa wanda ya batan sannan
ta fitoh tana ta d'aga hannu tana gyara hannun rigar don ya mata tsawo har yatsun ta hanna
yen suka rufe sai fama take da rigar ga wuyan rigar ma ya mata yawa wondon ne dai ta samu
yayi kib da qugun ta, yana ganin ta fito shima ya fice kai tsaye masallaci suka wuce shida Sani dan maggariba tayi.

banya sunyi harda ishah Sani ya wuce Restaurant ya samo musu abinci sannan ya dawo,
a parlon suka ci tare da d'an yin kallo har zuwa 8:15 Pm Captain Sani ya kalli ogan nashi cikin
sanyi yace,
" Oga bari inje in kwana a d'akin Abdul,
tunda yanzu nan kam ba fili."

bai kulashi ba har ya fita sannan shi kuma ya miqe cikin gajiya ya d'auki ledan abinci ya nufi
cikin d'akin ,
a gaban ta ya dire mata ledan sannan ya juya yaje ya rufe qofar parlour ya dawo cikin d'akin kai
tsaye ya nufi.......

By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 7⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa* 🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇


Pure moment of life writers


*Na saudau kar da wannan shafi a gareku Salmab Fadeela Fashuna biebie deee Fadeela
Lamid'o Firdaus ina al'fahari daku*


Tsayawa yayi a kanta cikin d'aure fuska ba fara'a ko kad'an ya kuma tab'e baki cikin fad'a da
bada umurni yace.

"Ke kina jina ko."
Shiru tayi bata kula shiba sai kanta da ta sunkuyar tare da fidda numfashin tsoro da far gaba,
shurun nata ya qara tunzura shi cikin tsawa yace.
"Ke kina jina ina magana kin wani share ni ko ke kurma ce?."

A tsora ce ta d'an d'aga mai kai cikin zare ido da tsoro ta gyada mai kai alamar ehh tana jinshi .

Qara murtuke fuska yayi tare da zare mata ido cikin muryar fad'a yace.

"Kina jina ko wlh doka ce zan kafa ya miki ! kuma umarni ne ! Wlh kika kuskura kika sab'a
abinda zance miki Wlh zaki gane kurenki ."

Sai ya kuma d'anyi shiru sannan ya qara tamke fuska yace.
"Kina jina ko?."
Kai ta gyad'a cikin sauri da tsoro .

Cikin bada umurni yace.
"Kinga wannan d'aki toh kada ki yadda kada ki kuskura inga qafarki ko a parlon nanne bare
kuma ta kai ga kin fita cikin gidan nan,
Wlh in kuwa kika yarda kika sab'a umarni nina wlh sai kin gommace kid'a da karatu,
sannan kada ki kuskura kice zakiyi wani abu da zai nuna akwai mutun a d'akin nan in kuwa
kinqi zaki gane kuren ki."

Kai kawai take ta gyad'a mai tana numfashi sama-sama dan tsoro.

Shi kuwa ido kawai ya tsura mata sannan ya juya cikin rashin kula,
jikin Windows yaje ya rinqa zuge glass d'in yana rufewa sannan ya sassauqe labulayen ya juya
ya kunna mata wuta sannan ya fice ba tare da ya kalli inda take ba.


A cikin gidan kuwa su Mama duk sun fito parlorn jin shiru qaran bindigar ya tsaya gaba d'aya
sukayi cirko-cirko suna kallon Captain Sani da ya tsaya kamar dolo.

Mama ce ta kalleshi a yatsine cikin had'e fuska tace.
"Kai Sani wato uban gidan nakane yazo yana mana harbe-harbe a cikin gida kamar wani
mahaukaci,
koda yake ba laifin shi bane mashayi kuma menene bazai aikata ba yaje ya gama d'ura giya
yazo yana qoqarin hallkamu banza asararre ."

Nafeesat ce ta karya fuska cikin sanyi tace.
"Ya Sani ina Hamma Aliyu da gaske tare kuke?."

Abdul ne ya watsa mata harara cikin yatsin fuska yace.
"Can da Allah kauce banza kawai ji yadda kike wani damuwa dashi sai kace qanin ubanki ne
shi."

A fad'ace Mama tace.
"Banza mashayi kawai yazo ya cika mana gida da yan iskan sojojin su mashaya ."

Cikin zage-zagen Abdul ya nufi part en nashi yana.
"Bari inje in sameshi wlh ya shiga hankalin shi."

Yana juyowa Aliyu dake tahowa ya d'aga mai hannu cikin tsawa yace.
"Kai dakata tsaya a wurin kar ka qara ko taku d'aya,
dan wlh duk maison kanshi da lfy kar ya kuskura yace zai zo iya kar part d'ina ko wacce ta
tsaya matsa yinta daga yau kar wanda ya shiga hurumi na inba hakaba wlh zan iya yin komai ."

Baki Mama kam ta saki cikin qanqantar da ido irin na bala'i tace.
"Iyeh lallai ka isa yanzu kai ko ubanka ya isa yamin iyaka da wani wurin a gidan nan?."

Kai ya kad'a tare da cewa.
"Hmmmmm mutun ya goda mana ya gani Wlh"
Sannan ya juya gun cikin tsuke fuska yace,
Sani je ka kwaso kayan dake cikin motar ka kawo ."


Captain Sani kam juyawa yayi cikin bin umurni ya fara kwaso tsarabar da Bappa ya had'o musu
yana shigar dasu har cikin part d'in Aliyun na sawa a fridge duk ya lodasu sannan wasu ko ya
shiryasu a cikin kitchen d'in dake jikin parlour.

Shi kuwa Aliyu a babban parlon nasu ya zauna kan kujera tare da d'ora qafarsa d'aya kan d'aya
yana d'an buga qafan ya kuma manna glass a fuskar sa ya murtuqe fuska tamau.

Mama ko sai kanne ido take tana juya kai da cije lebenta tana ta huci,
shi kuwa Abdul dama duk iskan cinsa yana shayin Aliyu dan baya mai wasa,
Ya Amir kuwa da Nafeesat murmushi sukeyi dan dama susan Aliyu sarai tarawa Mama yakeyi
inya tashi baya sha yinta,
ita kuwa Aysha sai zame jiki tayi ta koma d'akin ta Daddy ko wanda shine mijin Mama kuma
Baban ya Amir da Abdul sai Nafeesat kuma Yaya ne ga mahaifin Aliyu,
shima yana gefe yana hoggo yadda Aliyu ya tsare yau yana juyawa Matar tasa ido har ranshi
yaji dad'i dan dama yana jin zafin abinda matar tasa take yiwa d'an,
d'an uwanshi sai dai ba yadda ya iya da masifar ta.

Shiko General Aliyu Captain Sani na fitowa yace ya gama shigar da kayan ya miqe yaje ya
rufe qofar parlour sannan ya zura key d'in a haljihu suka fice tare.

Ita kam Mama bala'i ta rinqa yi bayan ya fita ya Amir da Nafeesat ko kowa ya kama gaban sa,
itako da Abdul zama sukayi suna ta tubka da warwara ta yadda shima zasu cusguna mishi.

Shiko suna fita kai tsaye Jaji suka nufa suna zuwa ya wuce gidan shi ruwa ya watsa sannan
yasa Esther yarin yar dake mai girki su shara da dai sauran su ta kawo mai abinci yad'an ci
sannan ya shiga ya konta dan yin baccin gajiya.

Esther aiki takewa General Amman ita har ga Allah take sonshi a burin tako koda bai aureta ba

sunyi zaman daduro shiyasa take bin duk hanyar da zata iya kasan tuwa dashi,
Shiko Aliyu ya rigada Allah ya tsare mai imanin shi da sauran jikin shi duk da kasan cewar sa
soja kuma mata shi mai cikar zati.


A Gida kuwa
Tunda Aliyu yayiwa Mama kashedi da karta shigar mai part enshi har yana "a goda agani mana
" gaba d'aya ta rasa yadda zatayi dan tsanar yaron ga Daddy kuma ko da ta kaimai qorafi mijin
Hajia sai cewa yayin "in yazo weekend ki mai fad'a ."

Yau kwana 3 da dawo warsu Gembu Membila Bodd'i kam tunda Aliyu ya qinda ya mata doka ko
bakin qofar parlour bata jeba duk da irin rayuwar kad'aici da takeji ga azabebbiyar yunwar da
takeji gashi bata san yadda zatayi komai ba dan ko bayan gida sai a hankali da tab'e-tab'e ta
gane har ta samu tayi wonka komai dana Aliyu tayi amfanin kama daga soson wanka da brunch
har zuwa towel a haka sai dai tayi wankan ta d'aura towel en ta fito ta d'an goge jikin ta sannan
ta meda kayan jikina tun Wanda tazo dashi,
tunda shi kad'ai ne kayanta gashi irin kayan nanne na Fulani farine wanda yasha aikin Zane da
ulu red da light green sai yellow rigar y'ar qara mace ko cibiyar ta bata gama rufewa ba sai in ta
d'aura zanin sama kad'an kanta ko a tsefe yake sai dai ta d'an tub keshi.

A haka tai ta rayuwa inda taji yau d'in yunwa na shirin hallakata gaba d'aya jikin ta sai bari yake
ko tsayuwa gagararta takeyi kawai sai ta kama kuka.

Shi kuwa Aliyu a office enshi Captain Sani da yake kamar shine do garin sa ya shiga bayan ya
sara mai cikin sanyi yace.
"Oga ya Meenal kwana biyu bamu leqata bafa."

A fili kauda kai yayi kamar bai ji ba a bad'iri kuwa
ido ya rumtse cikin mamaki ya akayi ya manta da ita shi wlh sam ya manta da itama.

Cikin sanyi Sanin ya kuma cewa .
"Oga tun da Yau ba wani aikin yi ya kamata mu leqa cikin Kaduna."

Kai ya jinjina mai sannan ya miqe tare da cewa.
" ba yanzu ba."

Shiru yayi shi kam Captain dan yasan Aliyu kaifi d'aya ne .

Da yamma liris goshin maggariba ya Amir da Sauran mutanen gidan suna tare a babban
parlourn sun zuba ido suna ganin yadda Mama da Abdul suke ta kicini Yar b'allah qofar parlon
Aliyu Mama ta dage sai cewa Abdul take.
"Wlh yau sai mun b'alla qofar mun shiga har cikin muga tsiyar da ya ajiye a cikin d'akin."

Shiko Abdul ya dage sai buga qofar yake ganin bazai bud'u a hakan ba yasa ya fito farfajiyar
gidan ya d'auki qaton dutse yazo yanata bugawa wai shi zai ballah qofar bugu 2 ana 3 ya d'aga
hannu zai buga kenan yaji .......


By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 9⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writers


*Dedication 2 Anty Fauzah & Neena Cool and Maryama Abdool & Momyn sultan*


Toilet ya shiga tare da maida qofar ya datse har ya fara zare rigar jikin sa sai ya lura towel nashi
baya cikin toilet en ganin haka yasa ya mai da rigar sannan ya fito.

Kanshi a sun kuye ya tsaya tsakiyar d'akin shiru ya d'anyi na wani d'an lokaci sannan ya d'ago
kai ya dudduba cikin d'akin bai gani ba .

Ita kuwa tunda ya ajiye mata ledan a gaban ta tana zaune ko motsi ba tayi ba sai wasa da
yatsun ta da take yi tana ta nad'e hannun rigar da yamata yawan .

Murtuqe fuska yayi tare da daqile voice yace.
"Ke ."

Kai ta d'ago cikin tsoro ganin yadda ya had'e fuska, kuma yasa tai saurin yin qasa da kai.

Shiko cika tunxura shi tayi da takaici yana mata magana tana wani mai kallon hadarin kaji.

A kufule yace.
"Ba ke nakewa magana bako?."

Miqewa tayi cikin sanyi da tsoro tace.
"Me zanyi?."
Mitsss yaja tsaki tare da tsuke fuska yace.
"Can tafi ni me zan saki!
ina kika d'ura min towel na ? da kika samu a toilet?."

Sanin akwai abin da ta d'auka a toilet fine ne yasa ta gane me yake nema,
shi yasa cikin sand'a ta wuce gefen shi kan qofar bedroom d'in ta jawo towel d'in da ta shanya
data fito wonka.

A hankali ta taka tazo gaban shi cikin sanyi ta miqa mai kanta a qasa.

Shi kuwa ganin yadda take tafiya da yadda ta wani tsaya kamar marigayin zakara,
shi yasa ya tsura mata ido ba tare daya karba ba,
jin shiru bai amshi towel d'in ba yasa ta d'ago kai ,
cikin sauri tai qasa da idon ta tana kallon enda yake kallon.

Wuyan rigar ta ya d'an kalla ganin wuyan ya mata yawa ga d'aya botur d'in ya bud'u ,
itako ganin inda yake kallo yasa ta matse towel d'in a qirjinta sannan ta cukui kuye wuyan rigar
ta had'a tare da damqe shi da hannun ta d'aya sai ta kuma tsaya tana d'an zare ido irin na
tsoro.

Shi ko General harara ya cilla mata tare da jan tsaki sannan ya komo towel d'in ya fizge ya juya
ya shige toilet d'in yayi wonkan shi tsab.


Itako tunda ya shiga ta koma kan gadon ta zauna tare da yin tagumi fuska na zubda qollah sai
numfashi take fizga cikin son yin kuka mai sauti sai dai kuma tsoron shi take ji.

Shiko yana fita ya bud'e durowar ya zaro blanket mai taushi da laushi sannan ya zare pillow ya
juya ya koma parlour ya konta kan 3str ba tare da jimawa ba bacci yayi awon gaba dashi.

Itako ganin shiru-shuru ba motsin sa ga bacci data fara ji ga yunwa yasa ta zauna kan carpet
d'in tsakiyar d'akin sannan ta jawo ledar ta samu ta d'an ci abin cin tana mai zubda qollah
sannan ta d'an shan juice ta koma tayi konci yarta kan carpet d'in tana cike da kewan yan
uwanta da ta kaicin a haka da ker tayi baccin.

Haka dai sukayi rayuwar kwana 2 tare a d'aki d'aya kuma tun randa ya tabba yeta towel bai
kuma mata magana ba,
Sani ke musu hidi mar girki ko yaje Restaurant ya seyo musu in dere yayi Sani ya tafi d'akin
Abdul mai targad'e ,
shiko General ya koma parlour itako tana daga ciki,
Mama kuwa da Abdul suna nan suna ta shirin shirya mai gadan zare.


Yau Sunday da yamma Sani da General sun gama shirin komawa cikin Jaji Sani kam har ya
d'auki jakar laptop d'in ogan nashi zayi gaba,

ganin General na zaune dole Captain ya dawo ya zauna .

Sukayi gum har zuwa d'an woni lokacin sannan ya miqe cikin d'akin ya nufa a bakin qofa ya
tsaya cikin murtuqe fuska da muryar miskilanci yace.

*"Meenal"*
Shiru bata amsa ba a kufule ya kuma cewa.
*"Meenahl* shiru bata amsa ba.

Cikin quluwa yace.
"Bororiya zaki zo ko na tafi?."

Jin haka yasa ta futo da sauri hannun ta na riqe da wuyan rigar ta jikin ta har rawa yake sai
fidda numfashi tsoro take.

Juyawa yayi ya nufi kitchen,
itako sai ido ta zura mai,
jikin ta na d'an rawa, bayan ya shige cikin kitchen d'inne
Sani ne ya kalle ta cikin rad'a ganin Ogan a kufule yake yace mata.
"

"In kinji ya kiraki da Meenal ki amsa sannan kome kikeyi inya kiraki kizo yanzu maza bishi
kitchen d'in."

Kai ta geda cikin sanyi tabi bayan shi.

A tseki yar kitchen d'in ta ganshi a tsaye sai ta rab'a gefen shi ta tsaya,

Murya a turnuqe yace.
"Kin iya girki ne?."
"ehh." ta bashi amsa a taqai ce

Tsaki ya d'an ja sannan yace.
"Ke ni sauri nake ki matso kiga yadda ake kunna gas d'in sanan ki san abinda zaki dafa kuma
kiyi iya ciki ki."

Ido ya zaro mata tare da cewa.
" kina jina ko?."

Kai ta geda mai.

Harara ya watsa mata sannan yace.
"ai baki da bakin magana aikin banza cikin ki ko cikina."

A d'an firgice tace.
"Ina ji."
Tsaki yaja tare da nuna mata komai sannan ya qara da cewa.
"Wlh in kikayi garaje da barin gas a banzace,
zaki babbaka fuskar ki kuma wlh ni ko a jikina."

Toh kawai take ce mai a haka suka gama ya fito parlour tana biye dashi a baya suna zuwa ya
cewa Captain Sani .
"Mu tafi."
suna fita yaja qofar ya rufe saurin da yake

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login