Showing 78001 words to 81000 words out of 81932 words

Chapter 27 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf

Allah ya yafe mana,
kai kuma Abdul aini a sanadi abinda kaso yiwa Meenarl ya zama sana din haduwata da iyayen
na,
dan haka kai kam yafiyar Meenarl zaka nema."

Haka kuwa Abdul ya rarrafa gaban Meenarl da kakarsu yace.

"Meenarl ki gafar ceni."

Da sauri ta katseshi tare da cewa.
"Haba dai Hamma Abdul wallahi tuni na yafe maka kaifa d'an uwana ne na jini na yafe maka
Allah ya yafe mana baki d'aya."

Gaba d'aya suka amsa da .
"Amin! Amin! Amin ya rabbil izzati."

Haka aka waste taron da Addu'a.

Inna kuwa suna tashi taja hannun Meenarl suka nufi part ensu na musam man,
shiko General dasu Ramadan d'akin Ammin su suka zauna suna d'an hira Ammi tasa Rayhana
ta kawo musu Abinci sannan ta had'a nasu Inna kuwa takaici musu.

A parlour ta same su Meenarl na konce Inna ta tasata a gaba tana cewa.
"Na tabba yeki meke damun ki kink'i fad'amin sannan kinzo kin konta kina ta rawan sanyi ga
fuskar ki duk a kumbure ki tashi muje d'aki kince ke a a ."

Ammi na shiga ta zauna gefen ta cikin kula tace.
" Bodd'i tashi ki zauna."

Kai ta juya cikin rumtse ido dan gaba d'aya raunu kan sunyi tsami tunda ko parasitomol bata
shaba,
bata son yiwa Ammi musu yasa ta mik'e da k'er ta zaune a kaikaice sai kuma hawaye shar-shar.

Ajiyan zuciya Ammi ta sauk'e cikin fahimta y'ar d'an uwanta ta tace.

"Bodd'i meke damun ki gaya min ?."

Sai kawai ta fara kuka cikin sanyi tace.
"Ammi babu komai fa."

Shiru Ammin tayi tare da kamo hannunta ta mik'e cikin kula tace.
"Muje cikin d'aki ."

"Toh" tace tare da tafiya a hankali tana d'ink'ishi Ammi kam da Inna shiru kawai sukayi dan sun
gano da wata y'ar matsala.

Suna shiga Bedroom d'in ,
shiko General ya shigo parlour Innan dan yaga shiru Ammi bata komaba tsoro yake jikar su
ritsa Meenarl ta gaya musu wani abu,
Inna ya kallah cikin tsuke fuska yace.

"Ina Meenarl?."
Ido ta tsura mishi cikin tuhuma tace.
" Bata da lafiya kuma tace bacci take ji yanzu ta shiga ita da Ammin ka."

Yana jin haka ya koma gefen ya zauna yana latsa phone enshi.

Ita kuwa Ammin suna shiga bedroom d'in,
toilet ta wuce ruwan d'umin ta had'a sannan ta fito tace.
"Bodd'i shiga kiyi wonka zakiji dama-dama."

"Toh" tace sannan ta shige,
tana shiga ta samu ruwan d'umin ta gasa kanta da kyau dan koda Asuba da Hamman ta ya
gasata ta d'an ji sauk'i sai kuma da ta dad'e a zaunen ne taji zafin ya dawo .

Wonka tayi sannan ta kara amfani da ruwan zafin,
tana fitowa ta samu Ammi ta kawo mata abinci tamkar mai jego,
ta sata taci abinci da gasheshen naman da tayi mata mai romo-romo sannan ta had'a mata tea
maikauri tasha ta kuma bata magungunan da tasa Ramadan ya seyo,
sannan ta kalleta cikin kula tace.
"Toh konta kiyi baccin ki."

Toh tace tare da konci yar.

Ammin na fita.

General ya mik'e ya nufi cikin d'akin Inna na biye dashi a baya.

Suna shiga Aliyun ya zauna gefen ta cikin tausayawa yace.
"I love you so very very much sweet heart'
sannu ko Minali na Allah ya miki albarka Allah ya faran ta miki kamar yadda kika faran tamin."

"Amin ya Allah ,
Hamma na."

Cikin rad'a yace.
"Allah yasa baki gaya musu abinda nayi miki ba?."

Cikin kunya tace.
"Ban gaya musu ba Hamma na kuma har abada ba wanda zan gayawa dan wannan sirrin mune
ni dakai kawai ba maiji."

Murmushi yayi cikin Satan kallon Inna ganin hankalin ta baya garesu yasa,
yayi sauri ya subbaci goshin ta tare da cewa.

"A hubbuki ya Habeebatee."

Murmushi sukayi su duka ,
sai Inna kuma ta matso gaban Meenarl d'in rik'e da y'ar k'aramar k'oriya tare da had'i na
musamman had'in fulanin Gembu Membila cikin kula tace.
" karb'i ki shanye."

Ba musu ta karb'a ta zuk'eshi sannan ta fara lumshe ido alamun baccin haka yasa General
shafa kanta tare da jamata blanket suka fita shida Innar..


Koda dare yayi fir Meenarl tak'i fitowa su koma dole ya hakura ya tafi.

Washe gari kuwa a ranar aka d'aura auren Captain Sani da Nafeesat Doctor Jabeer da
Rayhana,
Inna kuwa da Meenarl sun samu mafakar kin Meenarl ta koma Jaji,
Inna kuma sai faman tsuma jikarta take gashi duk had'in da za'a bawa amare sai an bata.

Gaba d'aya sun hana General ganin matarsa gashi yanzu koda yaushe cikin begen ta yake.

Anyi biki an gama duk bak'in sun watsa.

Yau kwana 6 kenan Aliyu bai samu yaji d'umin matar saba,
yanzu misalin karfe na 8 dare ya fito babban parlour nasu,
gaba d'aya suna parlour sai Meenarl da bai gani ba bayan ya gaida iyayenshi cikin sunkuyar da
kai yace.
"Inna ina Meenarl?.

Murmushi tayi ganin yadda ya tsuke fuska tace.
" tana wonka."

Shiru yayi kamar bai Jita ba a ranshi kuwa. hamdala yayi.

Can dai yaga hankalin su baya kanshi sai yayi nor-nor ya zulle.

Kai tsaye cikin d'akin ya shige yana kiran.
"Meenarl! Habeebatee! sweet heart! sheriyel am."

Shiru tayi tana toshe bak'in ta dan dariya ke son kubce mata,
shi kuwa k'ofar ya turo hankali ,
itako idon ta a lumshe jin k'arar k'ofar ne ta bud'e ido,
ganin shi ne yasa tayi sauri tayi baya jikin gini ta jingina.

shiko cikin wani irin shauki ya matsota tare da turata jikin ganin cikin rawan jiki ya...



By
*Garkuwar Fulani*




*BANDIRAWO* page 6⃣0⃣

*Na*
*Aysha Aliyu Garkuwa*







*A madadin sauran 'yan uwa Fulani nake mik'a sak'on ta'aziyar mu da jaje ga yan uwanmu
Fulani mazauna Gembu Membila tare da Jos akan rashin da akayi musu sakamakon mugayan
yan ta'adda da sukayi ta k'ona musu rigogin su da sace musu dukiyoyin su tare da b'atawa
yaransu mata yarintar su uwa uba kashesu da akayi , Allah ya karb'i shahadar wad'an
aka kashe sun rabbi ya karemu mu saura da muke raye Allah ya bimana hak'k'in mu, Allah ya
bawa gomnati kuma damar kula da Fulanin dake cikin tsaunuka da rigogi a matsayin su na 'yan
k'asa suma a basu kulawa, Allah ya isar mana kan abinda bazamu iyawa kanmu ba*






Kirjin shi ya manna da nata cikin lumshe ido tare da sauk'e ajiyar zuciya rugume ta yayi a jikin
shi yana shafa gadon bayan ta tare dayi mata tafiyar tsutsa yana mai sinshuna wuyanta,
Ido ta lumshe a hankali dan wani irin kunya da taji ya rufeta gaba d'aya ji take kamar ta nitse
cikin k'asa zamewa ta rink'a yi a hankali har ta tsuguna a k'asa kife kirjin ta tayi a cinyoyin ta
tafin hannun ta kuma ta rufe fuskarta,
shima biyota k'asan yayi ya tsuguna yana fuskantar ta har cikin ranshi yake jin kaunarta na
ratsashi haka nan kuma yake jin kunyarta na burgeshi dan tabbas ita kunya adoce ga d'iya
mace matsota yayi murya can k'asa yace.
"Meenarl ki tausawa Hamman ki mana wallahi na gaza samun sukuni a rayuwata a cikin kwana

kin nan da kikayi nesa dani bana iya bacci cikin nitsuwa a cikin bacci na ko a ido biyu ke nake
gani da marari,
Meenarl nifa mijin kine meyasa kike son yin nesa dani?."

Shiru tayi sai k'ara sunkuyar da kai tayi tana k'ara matse jikin ta,
ido ya tsura mata tare da yin murmushi a hankali yasa hannushi tsakanin cinyarta da kirjin ta ,
ido ya lumshe da sauri tare da sauk'e ajiyar zuciya,
itama ido ta lumshi da karfi tare da d'an zaro ido woje kan jin yadda gaba d'aya ya cusa
hannayen shi kan kirjin ta yana mata wani irin salon mai tafiya da hankali gaba d'aya ya kashe
mata jiki ya sakar mata wata iriyar muguwar kasala sai numfashi take fiddewa da sauri-sauri
murya na rawa tace. "Hamma Aliyuuuuuuuu."

Matsoto ya kumayi tare da mik'ewa da ita ya jingina ta jikin gini towel ya jawo a hankali ya
d'aura mata shi a k'ugunta sannan ya juyota kirjin shi ya manna a bayan ta kanshi ya d'an
sunkuyar ya cusa cikin kafadarta hannayen shi kuwa kirjin ta ya zagayo dasu cikin kasala yace.
"Na,am Minalin Hamma Aliyuuuuuuuu meke faruwa ne?."

Shiru tayi tana sauk'e numfashi,
shi kuwa gaba d'aya ya susuce yana neman susutata kab shi ya manta a gidan su Abba suke
ya mance cewa a toilet suke bare ya tuna a part d'in Inna suke bare daya samu itanma ta narke
mishi a jikin shi sai faman mak'aleshi takeyi tana shafa sajenshi tare da rugume shi.

Su Inna kuwa ana watsewa hiran ta shigo Part inta kai tsaye bedroom ta shige cikin yin mik'a
alamun bacci ta had'awa Meenarl had'in data saba had'a mata tana gama had'awa ta juyo kan
gadon ido ta mutsike ganin Meenarl d'in bata kan gadon cikin mamaki tace.
"Toh ina take."
Sai kuma ta fara kiranta cikin d'aga murya tana.
"Bodd'i ! Bodd'i! Kai Bodd'i! Ina kike ne?."

Ita kuwa Meenarl a cikin toilet d'in cikin sanyi tasa hannun tana mannawa General bel d'in shi
d'aya fara kuncewa cikin sanyi tace.
"kayi hak'uri Hamma kaji Inna na kirana gashi dare yayi kuma kace zaka koma cikin Jaji."

Kamota ya kumayi cikin lok'osa kai kamar yaro yace.
"Ni dai a,a wallahi na gaji mutafi tare kawai In ba so kike na shiga wani halin ba."

Zatayi magana kenan ta kuma jin kiran Inna ido ta zaro cikin shafa kanshi daya manna da kirjin
ta yana murzata ido ta lumshe tana.
"Wayyo Hamma na zaka zautar dani,
kaji fa Inna na kirana."

Zare bakin shi yayi a hankali ya kuma manna hannushi kan kirjin nata ido yatsura mata cikin

rad'a yace.
"Kai wannan tsohuwar fitinar ta nada yawa,
ki amsa mata mu huta daga nan bazan fitaba sai tayi bacci."

Ganin bayi da niyar saketa yasa cikin d'an daga murya tace.
"Na'am Inna yanzu dai nashiga ban fara wonkan bama ke kam kiyi konci yarki."

"Toh in kin fito ga maganin ki kisha."

"Toh" kawai tace,
sannan ta kalli General da ya susuce a kirjin ta murya can k'asa tace.
"Allah k Hamma zanyi kuka fa."

Hannun ta yajawo ya cusa a jikin shi murya a raunane yace.
"Ni fa zan iya rasa lafiya ta plxx Minali na mukoma gidan mu ba kowa a can dagani sai ke."

A zahiri taji tausayin shi so Amman kuma tana tsoron shi.

Rugume juna suka kumayi tare da newa Kansu sassaucin abinda ke damunsu su suduka biyun.


Ita kuwa Inna kan gado ta zauna tana yin addu'ar konciya kenan Ramadan ya shigo daga
parlour yake ta kiran.
"Hamma Aliyu! Hamma Aliyu! 11:55 pm baka tafiba ,
Abba na kira kazo ka tafi tunda kace ba kwana zakayi ba."

Tunda yaji Abba ne ke kiran shi ya d'an saketa cikin kasala ya manner bel d'in shi tare da
manne boturan rigarshi hannun shi yasa ya tallabo habarta cikin so ya had'a lips ensure a
dai-dai lokacin kuma Ramadan ya sakezuga mishi kira.
"Hamma Aliyu."

ba tare datuna komai ba yace.
"Na'am gani nan zuwa."

Inna kam ido ta d'an fitar cikin mamaki ta sake cewa.
" Bodd'i. "

Cikin mantuwa Meenarl d'in ma tace.
"Na'am."

Tana amsawa kuma sai suka ankara da cewa Inna da Ramadan sun gane su suduka biyu suna
cikin toilet d'in,
Ido Meenarl ta zaro tare da cewa .

"Hamma ka amsa."

Shi kam General kunyace da takaici suka rufeshi wai mutun da matarsa a maidashi kamar
b'arawo.

Bai kulata ba sai lips enta ya murza iya son ranshi sannan yasaketa yana haki kamar wanda
yayi gudun pampalak'i idonshi yayi jazir fuska a murtuk'e yace.
"Meenarl bakya tausaya min keda gidan ki kin wani dawo gida kin zauna kin barni kamar mara
mata."
Sai ya juya ya fice fuska a murtuk'e .

Shiko Ramadan dama tunda yaji suna tare da Meenarl ya fice abinsa.

Itama Inna sai ta konta ta lumshe ido kawai .

Shiku General a General d'in shi ya fito dan tabbas yaji kunyan abin.
A bakin gate ya samu Abba,
cikin girmamawa ya mishi saida safe sannan ya tafi.
ranshi cike da k'una.

Ita kuwa Meenarl gaba d'aya sai taji tausayin shi ganin yadda ya koma gashi ranshi ya bacci da
ita.
Shiyasa itama sai kawai ta tsinci kanta cikin bak'in hali,

Tana fitowa Maganin tasha sannan ta fito parlour a hankali take kiran.
"Ya Ramadan."
Ramadan kuwu da yanzu ya fito part d'in Ammi shi parlour Innan ya nufa,
yana zuwa yace .
"Bodd'i mene na kira a daran nan?."

Fuska a tsuke tace.
"Ni ka kira min Hamma Aliyu a woyar ka."

Ka ya sunkuyar dan dariya ke son kubce mishi ,
ki ranshi yayi sannan ya mik'a mata woyar sannan ya fice.

Kan 3 str ta konta tana ji woyar na ringgin bai d'aga ba har saida ya kusa tsinkewa sannan taji
yana cewa.
"Menene kuma Ramadan?."

Ajiyan zuciya ta sauk'e a hankali tace.
"Hamma nice fa."

A kufule yace.
"Menene zaki kirani me zai cemin?."

Cikin sanyi tace.
"kayi hakuri Hamma na ka gafar ceni naga kamar ranka ya b'aci dani."

"Baki da matsala dani ai shiyasa ki ke min abinda kike so kina sane inada muradinki a kusa
dani bakya sonane ai shi yasa."

A marairai ce tace.
"kayi hak'uri Hamma na wallahi ina sonka."

Murmushi yayi tare da jin dad'in furucin ta a zahiri kuma cewa yayi.
"A a kam."
sai kawai ya kashe woyarsa .

Ita kuwa Meenarl haka ta kwana cikin damuwa,
da asuba kuwa kusan da addu,a ta tashi a firgice dan mafarkin da tayi Hamman ta ya rasu
tana zubda k'ollah ta gayawa Inna.

Daga nan kuma ta wuni cikin bak'in hali.

haka ta wuni har dare koda Inna ta matsa mata da naci da tabbayar dalilin ta na had'a fuska
kawai sai ta kama zubda k'ollah wasa-wasa Inna taga Abu fa zai zama gaske har ta fara
sheshshek'a haka yasa taje ta kira Ammi.

Ammin na zuwa ta sata a gaba cikin lumana tace.
"Me yake miki ciwo Bodd'i?."

Kai ta girgiza cikin zubda k'ollah tace.
"Babu komai Ammi zuciya tane ke tsinkewa."

Ido Ammi ta tsura mata sannan tace.
"Toh meyasa zuciyar taki tsinke wa?."

Kai ta sunkuyar cikin Murza yatsun k'afarta tace.
"Ammi nayi mafarkin Hamma ya rasu ne,
kuma tunda garin ya waye ya Ramadan keta ki ranshi baya d'agawa."

Sai kuma hawaye cur- cur .

Ita ko Ammi murmushi kawai tayi tare da cewa.
"Toh bari inzo."

Itako Inna harararta tayi tare da cewa.
"Toh kice komawa gun mijin ki kike so mana haka kawai ki tsiran mani bak'in hali wato shegiyar
tsohowa ta shiga tsaka ninki da mijin ki ko?."

Ita dai cib d'in ta sai hawaye.

Ita kuwa Ammi d'akin Abba ta nufa cikin murmushi tayi mishi bayani.
Shima dariya yayi tare da cewa.
"Kune baku san shak'uwar dake tsakanin Haiydar da Meenarl ba da kun sani da bazaku rik'eta
ba,
yanzu-yanzu kusa Ramadan ya mai data d'akin ta gidan mijin ta."

"Toh" Ammi tace ta fice tana murmushi.

A parlour ta samu Ramadan da Abdul suna zaune sunata. hirarsu aiken Abba ta gaya musu
sannan ta tasasu a gaba har parlour Inna.

Suna zuwa tace.
"Inna Abban su yace Ramadan ya mai data gidan ta yanzu."

Inna kam rai a had'e tace.
"Toh gata nan aini Bodd'i ta bani mamaki wato Aliyu yafi mata ni yaushe ma kika sanshi? ."

Ita kam Ammi dariya kawai take musu sannan tace.
" Bodd'i tashi ku tafi maza maza kar Abba ya fito ya samu baku tafi ba."


Cikin sanyi ta mik'e abinta tabi bayan su Ramadan har sun fita Inna ta kuma biyota da yar robar
had'in tace.
"Gashi ki sha kije ki sameshi daram tunda ya fimiki ni."

Karb'a tayi murya na rawa tace.
"Nagode Inna kuma ni ina sonki Hamma Aliyu baifi mini kuba dan bashi da lafiya ne shiyasa."

Murmushi Inna tayi sannan sukayi sallama .

A motar tayi ta shan had'in nata Ramadan da Abdul ko hirarsu kawai suke.

Suna sauk'e ta suka rakata har bak'in parlour suna tura k'ofar ta bud'u ganin haka yasa
Ramadan ya kalle ta cikin. Murmushi yace.
"Toh madam saida safe mu zamu koma."

A kunyace tace.
"Toh Allah kiyaye hanya."


Suna tafiya Ita kuma ta shige cikin parlourn.

A hankali take takawa tare da yin salama.

Shi kuwa General tunda ya fito wonka ya konta a k'asa kan carpet yayi rufda ciki yana jin zafin
yadda aka rik'e mishi mata a haka bacci ya saceshi.

A hankali ta shigo cikin d'akin ganin shi a konce yasa ta karisa gunshi da sauri tana zuwa ta
zauna a hankali ta fara ki ranshi tana d'an tab'a kirjin shi.

Kiran forko da tayi ya farka amman sai yayi shiru yana jin yadda take shafa kirjin shi sai kuma
yaji ta fara kuka a hankali tare da manna kanta a kirjin shi tana.
"Hamma! Hamma na ka bud'e idonka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login