Showing 42001 words to 45000 words out of 81932 words
Chapter 15 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf
kad'uwa yace.
"Ammi....
By
*Garkuwar Fulani*
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*BANDIRAWO* page 3β£1β£ to3β£2β£
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*Wannan shafi sadaukar wane gareki k'anwata ta gari har kullum kina raina Ummee Garkuwa
ν ½νΈν ½νΈ*
Pml
yace.
"Ammi kin san abin da muka gani kuwa jiya da hantsi?."
Murmushi tayi cikin kula tare da maida hankalin ta kan d'an nata gudan jinin ta mai sata farin
cikin mai share mata k'ollah a duk sanda suka koranyo a fuskar ta mai cike da tunani da bagen
wani abun da ta rasa.
Kai ta jinjina tare da cewa.
"Me kuka gani Ramadan har ya rud'aku haka?."
Ido ya tsura mata tare da yana yin mamaki yace.
"Ammi jiya ba munje gidan uncle Ibrahim duba jikin shiba?."
kai ta gyad'a mishi tare da cewa.
"Ehh."
Matsota ya kuma yi tare da rik'o hannun ta cikin shak'uwa da mahaifiyar tasu yace.
"Ammi jiya a gidan uncle ni da Rayhana mun had'u da wani Soja a dai-dai k'ofar shiga part d'in
uncle Ammi kin ga yadda Sojan nan yake kuwa?."
Ido ta tsura mashi tare da girgiza kai cikin son jin k'arshen maganar.
Cikin muryar mamaki yace.
"Ammi dana ganshi zuciya ta tayi ta bugawa tsikar jikina gaba d'aya ya rink'a tashi idona sai
rawa suke a kan kaman nin fuskar sa hankali na kuwa ya tashi Ammi."
Rik'o hannunshi tayi cikin tsoro kar d'an nata yayi gamo ne tace.
"Ramadan me ka gani a fuskar sa? shi mutun ne ko aljan?."
Kai ya jinjina tare da sauk'e ajiyar zuciya a hankali yace.
"Ammi ina da tabbacin mutun ne shi,
Ammi kamannin fuskar Sojan nan ya bani mamaki da tsoro,
Ammi komai fa na fuskarsa da halittarsa irin nawa ne,
Ammi hatta farin mu irin d'aya ni dashi Ammi hatta k'wayar ida nunshi irin nawa ne,
Ammi hatta sajen dake fuskar sa irin nawa ne ,
Ammi wallahi ko yatsun hannushi irin nawa ne,
Ammi kamata da wancan Sojan yayi yawa har takai kamar da nakeyi dashi wallahi ko Rayhana
da muke tagwaye bamuyi irin wannan kamar ba,
Ammi tsawo kawai da d'an k'iba ya fini alamun ya d'an girma ni a haife,
Ammi wallahi kwana nayi ina mafarkin shi yana kuka yana k'iran sunan ki yadda muke kiran ki
Ammi shima haka yayi ta k'iran cikin mafar kina,
Ammi shi kad'ai na gani a mafarkin yana rayuwar kad'aici ba wanda ke kusa dashi dake nuna
mai k'auna ko kulawa sai wata budurwa ita kuma tayi nesa dashi sai wani haske da yake tsaka
ninsu sai kuma na haggo wani duhu a hannun wata mata tana turawa cikin hasken daga gefen
shi kuma Hamma Jabeer ne yana jan hannun wannan budurwa."
Sai hawaye cur-cur a fuskar sa murya na rawa ya kifa kanshi jikin gadon ,
wanda Rayhana ke konce tana jin duk abinda suke fad'a tuni itama sai kuka take yi sun had'a
kai wuri d'aya suna kuka a hankalin.
Ita kuwa Ammi bugawar zuciyar tane ta tsananta,
lokaci d'aya hankalin ta da tunanin ta suka koma kan d'anta Aliyu Haiydar wanda ta rebu dashi
tun yana d'an shekara bud'u,
a badiri kullum Ammi Aliyu na cikin ranta dashi take kwana dashi take tashi tana son d'anta
tana son ta kasance dashi ta bashi kulawa da tarbiya wacce ko wanne d'an yake samu gun
mahaifiyarsa,
amman ina haka bata samuba dan fushin da iyayen ta sukayi.
a lokacin da Abban Aliyu ya saketa,
ya kuma karb'e d'anshi haka yasa Babban yayan ta mahaifin Captain Sani da Dr Jabeer ya
d'auke ta daga garin Kaduna ya koma da ita Adamawa Yola inda yake aikin sa cikin gidan shi ya
ware mata part nata ita da mahaifiyarsu,
ya rink'a kula dasu da duk wani dawaini yarsu,
Karin konciyar hankali linsu matar sa Hajia Asma'u mahaifiyar su Dr Jabeer da Captain wacce
suke kiranta Nenne ,
macece mai mutunci da sanin ya kamata ta d'auki dangin mijinta kamar denggin ta ,
ta taimakawa mijinta wurin kula da y'ar uwarshi da mahaifiyarsu du-du yaran Nenne 2 ne Dr
Jabeer sai Captain Sani ,
amman ganin d'an uwanshi bai tab'a haihuba wato (Alhaji Ibrahim mai dala),
sai ya d'auki d'anshi na biyu Captain Sani kenan ya bawa k'anin shi,
daga nanne Captain Sani ya koma Kaduna da zama.
Ita kuwa Ammi bayan fitan ta gidan Abba da wata d'aya ciki ya bayyana inda take laulayi kamar
zata rasa ranta,
cikin kulawa d'an uwanta Barrister Lawan mai dala ya kaita Asibiti gojin forko aka gano tana
d'auke da cikin wata 3 a jikin ta,
Ammi tayi farin ciki dan ita a zaton ta ko dan albarka cikin yayunta da mijinta zasu gyara auren
ta koma kan d'an ta gudan jininta,
haka kuwa sukayi Alhaji Ibrahim yaje ya samu Abba da batun cikin,
amman da yake a wancan lokacin asirin da Mama tayi ya kama shi yana aiki a kanshi shiyasa,
fir Abba yak'i yace shi wannan cikin ba nashi bane can suje su nemi uban cikin dake jikin ta,
shi ba ruwan shi ,
wannan kalma ta cewa ciki ba nashiba yasa Barrister Lawa fushi mai tsanani Wanda daga nan
ya yanke duk wata alak'a da zata had'a Ammi da gidan Abba hatta kadunan Barrister ya hana
Ammi zuwa kota-kota,
Ammi kam da tajin maganar tayi kuka kamar ranta zai fita sana din wannan abin ta samu hawan
jin,
inda mahaifi yarta da Jabeer suka zama abokan zaman ta Jabeer yana son Ammi a ranshi fiye
da zaton d'an adam Jabeer jin Ammi yake tamkar ita ta haifeshi domin komai a part nasu yake
yi Ammi kemai duk abinda Uwa keyiwa d'anta Ammi ce abokiyar shawaran sa itama shine
abokin shawaranta tasha zama ta bashi labarin Haiydar shima Jabeer sai yayi ta kuka yana son
d'an uwan shi kuma shine kad'ai yasan yadda Ammi ke shiga damuwar rashin d'an nata, yayin
da Kaka ke basu kulawa gaba d'ayan su,
bayan watanni 6 Ammi ta haifi yan tagwayen ta inda Ramadan ya fito mai kama da Aliyu sak da
sak ,
ita kuwa y'a macen sun rasa dawa take kama ba abin da ta dauko na kowa a zuriyarsu sai
muryar tace kad'ai irin ta Ammi da zaran ta bud'u baki tayi magana toh sautin muryar Ammi
sak.
Haka yara suka tashi cikin gata da kulawa da tattalinsu da ake a cewar Alhaji Ibrahim su yaran
basuma ishesu ba bare a wulak'an ta musu y'ar uwa a banza su zasu rik'esu har iya rai da
mutuwa,
ita kuwa Ammi tun daga nan bata kuma yin aure ba aceqarta zata kula da yaranta,
Dr Jabeer da Ramadan da Rayhana sun tashi gida d'aya d'aki d'aya gaban Ammi ta musu
tarbiya mai kyau sun tashi cikin k'aunar juna da shak'uwa.
Alhaji Ibrahim kuwa duk sanda zaije Taraba Gembu Duba yarshi Amina yakan biya cikin Yola ya
d'auki d'an yayan nashi wato Jabeer suke tare,
toh shi Jabeer daga nan yasan Meenal haka kuwa yasa kullum k'arshen sati sai ya shirya yaje
Yola to Membila yaje ya duba k'anwar shi Ammi ma da su Ramadan da Barrister da Nenne tare
da Kaka duk suna zuwa su kaiwa Meenal ziyara,
a haka shak'uwa mai tarin yawa ta shiga tsaka ninsu ,
shiko Captain Sani kasan cewarsa a makaran tar sojoji yake da yanayin karatu shi da aikin shi
yasa bai tab'a zuwa canba ko sau d'aya,
Sannan Abba kuwa yana sakin Ammi Mama ta kuma mishi asirin da dole zaman Kaduna yafi
k'arfin shi saida ya k'aura ya koma Katsina yana Katsina ya karisa ginin gidan da suke ciki a
yanzu suka k'aura suka koma can yayin da Aliyu ya tare a part d'in Abba shi yana rayuwa shi
d'aya a haka ya girma komai na karatu Abban na mishi, toh sana din k'auran nasu yasa Alhaji Ibrahim bai kuma ganin Aliyu ba bare da ya girma Alhaji
Ibrahim bazai gane shi ba kuma shi Alhaji bai tab'a zuwa gidan su Aliyun ba dan in yaje kam zai
had'u da Daddy toh dole zai gane Aliyu .....
Toh yanzu sanadin B'atan Meenal yasa Alhaji Ibrahim ciwon zuciya da hawan jini,
shine fa Barrister Lawan ya shirya da iyalanshi kab da Kaka mahaifiyar su da Ammi dasu
Rayhana da Nenne duk suka zo Kadunan duba Alhaji Ibrahim d'in da jikin yayin da suka sauk'a
a gidan Barrister Lawan d'in dake nan cikin kaduna,
toh su Ramadan sun zo sun gaida Uncle Ibrahim d'inne sun fito zasu koma suka had'u da
General...
*Mu koma kan labarin*
ajiyar zuciya Ammi ta sauk'e tare da zubar k'ollah tana mai kama hannun Ramadan da Rayhana
da
Ramadan kuka kawai suke yi cikin kukan Ramadan yace.
"Ammi nasan fa akwai abinda kuke b'oye mana nida Rayhana Ammi na fara zargin mahaifimu
na raye,
Ammi wannan sojan d'an uwanmu ne duk yadda akayi mun had'a jini dashi."
Cikin kuka sosai Ammi ta basu labarin abin da ya faru shekaru 26 da suka wuce ta kuma d'ora
da cewa.
"Ramadan ina ji a jikina Sojan nan d'an uwanku ne yayan ku Haiydar ne shine yayanku Uwa
d'aya uba d'aya,
Amman ko kunce zakuje yan uwana zasu ha naku dan sun rik'e mahaifin ku a ransu."
Hannu Ramadan yasa ya rik'o nata cikin share k'ollan fuskarsa yace.
"Ammi mu dai Abba mahaifin mune bamu da wani uba daya fishi kuma mu ya watsar da mugun
furucin ,
mu kuwa nida Rayhana mun yafewa mahaifin mu muna kuma son uban mu zamu kuma
nemoshi muna son d'an uwanmu zamu je gareshi zamu raba shi da zaman kad'aici zamu sashi
happy a rayuwar sa dan haka karki gayawa su Uncle komai akan zamu nemi Abban mu,
bamuga laifin su Uncle ba dan dole suji zafin abin da akayi miki a matsayi su na yayunki."
Kai Ammi ta jinjina cikin zubda k'ollah tace .
"Rayhana kinji abinda Ramadan yace kuma kema kina bayan shi?."
Kai Rayhana ta jinjina cikin kuka sosai tace.
"Ammi inason Abba na in ason in ganshi ina son Hamma Haiydar naji tausayin Hamma Haiydar
ya rayuwa tamkar maraya alhalin iyayenshi na raye,
haba ashe shiyasa fuskar Hamma Haiydar ba fara'a baida sakewa ashe cikin kuncin rashin Uwa
da uba yake rayuwa ba d'an Uwa ba y'ar Uwa a kusa dashi ina son d'an uwana Ammi."
Cikin kuka Ammi ta dafa Kansu tare da cewa.
" Allah ya muku albarka rabbi ya kaddara saduwar ku da mahaifin Ku na amince kuje gareshi."
Murmushi Ramadan yayi tare da mik'awa Rayhana hannu,
ta d'ora nata hannun kan nashi,
cikin yana yin jinjina ni yarsu,
itama Ammi murmushi tayi a ranta koba komai farin cikin ta zai dawowa gareta d'anta abin
al'fahari ta Aliyu Haiydar..
Shi kuwa Aliyu yana shiga bedroom d'in lokacin daya bi bayan Meenal jikin durowa ya tsare ta
cikin had'e fuska yace.
"Ke me kike ta min kallon munafurci kina wani zaro ido kamar mayya."
Shiru tayi cikin kallon shi a tsorace tana mai girgiza mishi kai tare da cewa.
"Mayyahh."
Fuska ya kuma tsukewa tare dasa hannu kan....
By
*Garkuwar Fulani*
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
BANDIRAWO pg3β£4β£to3β£5β£
Na
Aisha Ali Garkuwa
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
MI YETTI ALLAH MI YETTI LILADO ALLAH, BANDIRABE AM ONON MA MIYETTI ON I IRI
YIDDE DE KOLLOTO DO YAM MIMMA I MIDI ON FU DONTO GONDON ν ½νΈν ½νΈν ½νΈ
General Aliyu ba qaramin wahala ya ke sha ba in har dare yayi, sannu a hankali ciwon ke qara
ba Meenaal tsoro, yau kam ciwon ya fi na kullum, gashi ya hana ta sanar ma Abba, dabara ce
ta fado mata a sukwane ta nufi falon shi ta dauko dodilo zamzam a Kofi ta dawo kusa da shi
addu'a ta rinqa tofa mishi irin su Ayatulkursiyu, Qulhuwa, Falaqi da Nasi, da Amanarrasulu, ta
tofa mishi, don Baffan ta hk ya ke mt in in ba ta da lfy kuma cikin hukuncin Ubangiji sai ta samu
sauqi shi ne ya fado mata ta ce bari ta gwada mai kilan shi ma ya samu sukuni, haka ta tallabo
kan shi ya ta ce hamman Haydar tashi ga zamzam ka sha zk ji sauqi in sha Allah, bai musa ba
yai Bismillah ya sha ta shafe mai sauran a duk jikin shi, tun yn rawar sanyi a hankali ya dena
zafin jikin ma yn sauka sosai ya ji dadin wannan taimakon da Meenaal ta ba shi tare da
mamakin yadda shi sam tunanin shi bai bashi ya rinqa addu'a yn sha ba, ko da ya ke in
zazzabin ya tashi ko bakin sa ba ya iya motsawa, cikin jin dadin jikin sa ya jawo ta jikin shi ya
rungume ta a hk bacci ya kwashe su,
Ramada sun karbi no captain Sani a gun Dr Jabeer,.ya tabbatar musu za su gan shi da zaran
ya samu lokaci, Captain Sani bai samu zuwa ba sai bayan kwana biyu, fara tambayan shi
sunan ogan shi da sk gan su tare a gidan uncle Ibrahim suka fara haba yan qanne na ba ko
gaisuwa sorry bross ina wuni hankalin mu ne yai gaba, lfy lau ina Ammin sun fita da mummy ok,
don Allah ka gaya mana sunan shi mn cewar Rayhana to sis sunan General Aliyu Wani ihu ta
buga tare da rungume Ramadan tana fadin Wallahi shi ne Ramadan shi ne, Ramadan ko
Alhamdulillah kawai yke jerowa captain Sani kuwa baki a hankade yake bin su da ido ban gane
ba me kuke nufi, Ramadan ne ya fara mgn ka bari Ammi ta dawo ita za tai mk bayani da kan ta,
wannan kenan
Can gurin General Aliyu kuwa Alhamdulillah jiki ya yi sauqi sosai zazzabin ma yayi sauqi sosai
don suna ganin alamun shi za su debo zamzam su tofe shi da addu'o'i ya sha sai ya mai da shi
wajibin sa zai sha da sassafe da yamma ma hk in ya manta ma ko yana sauri Meenaal zt sa
mishi a gora ya tafi da shi yn qoqarin ganin da shi yake karyawa, Meenaal ce ta roqi anuty
Aysha ta na son gayen magarya murmushi aunty Aysha ta yi ta ce ai ni bana rasa shi saboda
amfanin shi gurin mu mata, ita dai Meenaal ba abun da ta gane da ta dauko mt karba tayi tai
godiya, kan ya dawo duk tayi addu'o'in da ake yi saboda Baffan ta ya dade da koya mt da ganye
magarya 7 ta tofa ta ajiye ms, yau bai shigo da wuri ba sai bayan isha yn wanka ya fito ta dauko
mai mgn a cikin jug ta ba shi, yn ganin magarya a ciki ya gane nufin ta amma sai ya bita da ido
yn da kallon tambaya, tce mgn ne in kai amfani da shi zk ji dadin jikin ka Baffa na ne ya gaya
min bai musu ba don shima da yn yi duk bayan wata 3 ynz ne da aiki yai mai yawa ya dena
tana ganin yana shirin shafawa ta ware falo, gaskiya ba qaramin dadi da mamaki yarinya ta ba
shi ba tare da birge shi ya fahimci ta samu tarbiya mai kyau, da dare yayi ne fa kida ya so ya
canza don suna kwance sai ya ji lakwanin shi na mikewa in yai kokarin mai da ta sai byn yan
mintoci sai ta qara mikewa abin da bai taba yi ba Meenaal na kwance sai ta ji kmar an zungure
ta tofa sunan wani turare wai shi Zandariya ν ½νΈ
SORRY FANS DIN AISHA GARKUWA KU YI HAQURI TA DAWO JIBI TAYI MN NA GASKIYA,
DON NG WASU HAR SUN SAKI IDO DA BAKI ν ½νΈν ½νΈν ½νΈν ½νΈν ½νΈν ½νΈν ½νΈ KU YI HAQURI TA DAWO
WANNAN JUST FOR FUNNY,
Ruqayya Aliyu
Maman Khalil
ν ½ν³ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*BANDIRAWO* page 3β£4β£ to3β£5β£
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½ν Όν½
*Dedicated 2 Amina Aminu ( Meenah parrot)*
Yaji wani irin azababben ciwon ciki,
gaba d'aya jikin shi ya rink'a b'ari kar-kar dole ya zame tare da damk'e mararshi,
ita ma Meenarl komawa tayi ta zauna tare da jingina da jikin gado cikin rawar murya da
tausayawa ido na zubda k'ollah ta rink'a cemai.
"Sannu Hamma Haiydar Allah ya baka lafiya ehsa Hamma am."
Shi kam Aliyu zamewa yayi ya konta kan cinyoyin ta tare da tura kanshi cikin fatar cikin ta
sannan yasa hannu duka biyu ya zagoyo k'ugunta tare da rumtse ido sai karkarwar da yakeyi
gaba d'aya ya dunk'ule a jikin ta,
ita ma cikin tausayawan ta ruggumo shi da kyau tare dasa hannun ta tana shafa wuyan shi
zuwa kafad'an shi tana kuka tana mishi sannu,
hannun ta na rawa ta tura hannun kan marar tasa cikin mamaki da tsoron ta zaro ido tare da
cewa.
"Hamma Haiydar ji mararka kamar wuta ga tauri kamar dutsen."
Shi kam kanshi kawai yake turawa cikin jikin ta kamar yaro k'arami a cinyar mahaifi yarshi,
hannu tasa kan marar tashi ta d'aura a hankali sannan tasa yatsunta ta rink'a murza marar tashi
a hankali tare da sunku yowa tana karan ta addu'oin tana mishi tofi a kai tare da murza marar
tana danna wurin tare da murza wurin da taji yayi tauri da zafin.
Shi kuwa General
K'ara K'ak'k'ame ta yayi tare da murza kanshi cikin jikin ta yana wani irin numshi da k'arfi sai
mutstsu kata yake yi tare da yin magana cikin wahalcecciyar murya.
"Lahaulawala k'utah illabillahi aliyul azim wayyo Allah na wayyo jikina cikina