Showing 9001 words to 12000 words out of 81932 words

Chapter 4 - BANDIRAWO BOOKS True (1 to End) Na Aisha Aliyu Garkuwa .pdf


"Nayi alqawari zan taima ka maka kuma zan riqe amana bazan kuma k'asa taima ka maba."

Cikin jin dad'i yayi ajiyar zuciya sannan ya kalli mutanen wurin tare da riqe hannun Sani.
" yace Sani Kaine shaidan Aliyu a garinku in kun koma."
Ya kuma juya ya kalli taron mutanen wurin cikin d'aga murya yace.
"Ku kuwa kune shaida na da alqawarin Aliyu."

Kusan a tare su kace
"Ehh".

Murmushi qarfin hali yayi sannan yace.
" Aliyu na baka auren Amina Bodd'i bisa alqawarin da kayi min!
Kuma yanzu za'a d'aura auren!
yanzu kuma zaku tafi da ita!"

Shi kam Aliyu ido ya zaro woje tare da bud'e baki zayyi magana .

Da Sauri
Sani yace.
"Alqawari kayi oga kuma tsaka ninka da ubangiji kai wannan alqawarin."

Yana rufe baki ya juya ya zaro kud'i masu yawa a cikin moto sannan ya d'auki kondon dibino
d'aya cikin sauri ya dawo gaban Aliyu daya murtuqe fuska kamar zayyi ruwan jini.

Kud'in ya miqawa Bappa tare da cewa.
"Ga sadakin ta dubu 50 sannan ga dibino kawai yanzu a d'aura Aure,
shi oga namiji ne ya halatta ya karbawa kanshi Aure." .....

Gaddara ta rigayi fata General Aliyu yanaji yana ganin wata gaddarar rayuwa ta auka mai
Wanda dole girman alqawari da bakinshi ya karbawa kanshi Auren Amina.

Ana gama daurin Aureb tare da shaidun mutanen rigar Bappa ya shiga cikin gida,
cikin sanyi da tausayawa kanshi da matarshi da Bodd'i ya kalli Inna ba tare da wani baya niba
ya kamo hannun Bodd'i tare cewa Inna.
"Kiyi haquri wannan shine mafita kuma wannan itace sabuwar gaddararmu."

Itako Bodd'i sai binshi tai yana riqe da hannuta.

Gaban Aliyu ya tsaya da ita tare da miqa mishi hannuta cikin sanyi yace.
"Aliyu ga matar ka!
Bodd'i kekuma kibi mijin ki!"

Ita kam bata fahimci komai ba a zancen nasu sai dai ta fahimci tafiya zaiyi da ita shiyasa sai
hawaye ke bin fuskar ta.

Shi kuwa kamar makaho Bappa ya jashi har cikin mata Sannan Sani ya shiga suka tafi .

Suna fita cikin rugar ta gefen dutsen Membila sai ga motocinsu da suka bari cikin Membila cikin
mamaki Aliyu ya kalli captain Sani da neman qarin bayani duk da dai ya gane Sanin ne ya kira
su dan suzo su bawa mutanen rugar kariya.
hakan ko yace mai .
"Oga nina kirasu."

Kai ya gyad'a sannan yace .
"Toh motoci 4 su isa wanda sojoji kusan 28 a cikin sannan yace .
mota d'ayar kuma ta juyo su koma tare.

Haka kuwa Akyi matoci 4 suka nufi cikin rugar,
suko su Aliyu sunka nufi Hanyar Gembu
domain zuwa Yola..

A cikin motar kuwa Bodd'i ta.....

By
Garkuwar Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 6⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writers


*Wannan shafi nakune ku kad'ai Sisters In Islam Mmn jhadijah tare da Y'ar mutan wudil sa'a tafi
manyan kaya nis@ online writers & Hurairayabo and Feedoh*



Dungu lewa tai wuri d'aya tana mai wani irin kuka mai sanyi da tausayi dan,

gani take shike nan an rabata da tushenta gatan ta ji take kamar an rabata da farin cikin ta,
a ranta take tuna meyasa Bappa baiyi tunanin komai ba ya had'ata da wannan mutumin mai
fuskar mugaye,
cikin jin zafin zazzabin da yake shirin rufeta ta d'an bud'e idonta tana mai kallon tsaunu kan da
tsirren da suke ketawa yayin da suke bawa rugar tasu baya a take ta saki wani kuka mai cin rai
tare da qamqame jikin ta,
ta takure can gefe jikin motar.

Shi kuwa Aliyu ido kawai ya rumtse cikin wani irin zafi da ranshi ke mishi ,
tunani yake shi da yazo neman mafita da samun sauqi sai gashi wani baqin shafi ya shiga cikin
littafin qaddarar rayuwar sa,
shin ina zai Ajiye wannan yarinyar da wani matsayi zai nunata ga Mahaifin shi? da yayan
mahaifin nashi ?
shin da wace fuska zai nunata ga sauran abokan aikin shi ?,
kai ya kuma juyawa da qara rumtse idon shi tuno Mama da yayi ko me zatace kan wannan
batun ! wanne sherri kuma zata bishi dashi !,
shi a wanne yanayin yazo duniya da ya kasance ba mai ji bantan lamuran shi .

Haka yai ta tubka da warwara,
yayin da shiko Sani driving kawai yake,
zuciya yarsa cike da farin ciki ko ba komai yasan insha Allah nan bada jimawa ba Ogan shi zai
samu sauyi a rayuwar sa a haka suke tafe kowa da abinda ke ransa, Bodd'i ko tayi kuka har
muryarta ta dashe fuska ta kumbura.

A haka har suka bar jihar Taraba suka fara nausawa cikin jihar Adamawa Yola tafiya suke cikin
sanyin safiya yayinda Sani ya samu hanya ba cunko son ababen hawa ya rinqa tsula gudu
kamar masu firewa yayin da. motar su Garbe ke biye dasu a baya.

10:25 Am Suka isa dai-dai Gurore inda hanyar ta kasu 3 d'aya hanyar da zata sadaka da cikin
birnin Adamawa d'ayar kuma wacce zata fiddaka Adamawa zuwa su Gombe Bauchi Jigawa
Kano Kaduna Abuja Katsina Sokkoto da dai sauran sashoshin dake gefen,
d'aya hanyar kuma wacce ta kanta suka bullo itace hanyar tafiya Taraba kuma itace ke sada
mutun da qasashen kudancin Nigeria kama su Calaba Onitsha Binuye da dai sauran su.

Suna zuwa dai-dai wurin Sani ya juyo cikin neman izini yace.
"Oga cikin Yola zamuyi ne ?"

Ba tare daya bud'e ido ba ya bud'e baki cikin bada umurni yace.
"Miqewa zakayi kawai muyi tafiyar mota dan bazan tsaya jiran ✈ bare ma wannan bororiyar
bata da komai bare muyi tafiyar da jirgin."

Toh yace tare da juya hancin motar suka kama hanyar Gombe,
Allah sarki,

Badd'i bata taba zaton rayuwar ta zata juya mata haka ba yau gashi tabar rugarta tabar jihar ta
gashi har tana qetare sauran jihohin da suke maqobtaka da jihar su, zuwa yanzu tabar jin ko
yanayin sanyin jihar ta bare qamshin furannin rugarsu,
kuka ne tayi shi har qarfin ta ya qare gashi dama ba abinda taci.


Tafiya ma bud'in ilimi Mahmud Yau yai nisa,
yauko Amina ce tai nisa inda tabar sunan Bodd'i a rugarsu ta d'auko sunanta. Amina daga
Gombe ko taji wani sabon suna a bakin Sani .

1:00 pm suna cikin birnin Gombawa diban fari ba'a kwana damuba a tashi.

Kai tsaye Shagalin ku Restaurant suka wuce,.Suna isa bayan Sani yayi parking kafin ya fitoh
mah su Garba sun fito daga tasu motar a guje suka bud'ewa General Aliyu mota tare da sara
mai kab suka qame har saida ya fito,
Sannan suka bishi a baya har ciki yayin da ma aikatan wurin suka fara yi musu hidima cikin
karra mawa suka isar da Aliyu can cikin wurin na musamman su kuwa suka koma baya gun
sauran mutane gaba d'aya aka shirya musu abinci da nasha suka fara ci domain sauri suke Yau
suke son zarcewa Kaduna.
Shi kuwa General zama yayi cikin nitsuwa sannan ya lumshe idonsa tare da shaqan qamshin
wurin wanda ya had'e da sanyin A,C a hankali ya rinqa sauqe ajiyar zuciya har zuwa wani d'an
lokaci sannan ya bud'e idon shi cikin furza numfashi ya d'an juya kenan ya haggo Captain Sani
ta cikin glass din wurin wanda yake kib da area park daga duk kan alamu magana yakeyi
amman bai jin abinda yake fad'in ganin haka yasa ya zaro phone enshi ya kirashi ,
bugu d'aya ya d'aga cikin tsuke fuska yace .
"Kai Sani me ka tsaya yi ka dai san akwai sauran tafiya a gaban mu kai sauri ka shigo kuci
abinci muyi sallah sai mu tafi."

Cikin kula yace.
" Oga Meenal taqi ta fito tazo taci abinci kuma sai kuka takeyi."


Baki ya tab'e cikin tsawa yace.
"Toh sai me cikin ka ko cikin ta ? ai in taji yunwa zama taci wani bai saniba kar taci mana kai me
naka a ciki,
kawai dai inma baza taci abinci ba toh ta fito tayi sallah tun kafin su Garba su fito su ganta aikin
banza kawai."

Ido ta tsurawa Sani cikin zubda qollah dan kab taji abinda yake fad'in ga uban tsawan d'aya
buga wanda ya firgitata,
cikin zubda qollah ta zuro qafafun ta cikin dishewar murya tace.

"Bandirawo a ina zan samu wurin sallan?."

Gefen wurin ya nufa da ita sannan ya kaita gun masalacin dake wurin Wanda ga fomfunan da
keta zubda ruwa a nan tai al'walah sannan tai sallah duk Captain Sani na tsaye yana mata gadi
tana idar da sallah ta komai cikin mota,
shiko ya shiga ciki ya d'an ci abinci a gaggauce sannan ya musu Othern abinci yaje ya aje cikin
mota sannan suna fitowa sukayi sallah 1:35 pm dai-dai suka bar garin Gombe.

Kafin 2 ma sun isa Darazau Dara birnin bauchi daga nan suka harba jigawa dutsen kafin 6 sai
gasu a Kano ta sabo tumbin giwa .

A nan suka tsaya suka ci abinci sukayi Sallan maggari ba sannan suka jira har zuwa isha bayan
sunyi ishan ne suka fara shirin tafiya bayan sun dudduba lafiyar motocin nasu sannan suka
kama hanyar Kaduna.

Allah Sarki ita kam Meenal gani take tunda take a rayuwar ta bata taba irin wannan tafiya mai
nisan ba tun a Yola ta fara tsinkewa da cewa shike nan an rabata da iyaye ta bare yanzu da
taga bayan kanon ma gaba zasu qara kawai sai ta ringa tsiyayar da qollah tare da jan wani irin
numfashi ta duqqule wurin d'aya.

A ganin su Captain Sani wanda ya taso Taraba 2 Kaduna in yazo Kano ai ya iso gida.

Dan haka yanzu tafiyar suke a tsanake ,
9:00 pm Suna cikin birnin Kaduna kai tsaye agguwar Sarki suka nufa cikin tafiyar shaidawa
mutanen gari General Aliyu na gari.

Jiniyar su ce ta shaidawa mutanen gidan nasu Aliyu ya dawo,
Sani na gama parking ya fito su Garba ma duk suka firfito sauran sojojin dake biye dasu ma duk
suka fito kab suka zo gaban General din nasu suna Sara mai tare da yimai sannu da zuwa.

Cikin murtuqe fuska ya d'aga musu hannu tare da murza yatsun sa yana kad'asu alamar su tafi
kawai ganin haka yasa cikin bin umurni suka juya suka tafi kab d'insu sai Captain Sani daya ke
binshi a baya.

Cikin gida kuwa
Kab suna tare a harabar babban parlon Aysha matar Ya Amir ce zaune a gefen Mama da keta
surfa mata masifa sai Abdul d'an goyon bayanta da yake gefen ta yana cillawah Aysha harara
cikin izzah yake cewa.
"Mama ai ita bata san zafin haihuwa bane shiyasa take mana iskancin da taga dama tunda
tasan ni bancin tuwo ai sai ta dafa min abin da zanci."

Nafeesat ce ta kalleshi cikin tsoro tace .

"Ayyah Yaya Abdul Anty Aysha bata da lafiya fa."

Cikin yatsuna fuska yace.
"Ke kuma muna fuka waya kasa dake?."

Maman ne ta kai mata mari cikin fad'a tace.
"Ba nace ki dena as mana baki ba in muna maganar mu."

Shiru tayi tana kallon yadda Aysha ke zubda qollah shima ya Amir sai sunkuyar da kai yayi
cikin tausayawa matar tasa.

Ga masu aiki ya kawo amman dole an maida matar sa y'ar aiki sam baza'a barsu su sake ba.

Suna cikin haka
General Aliyu Haiydar ya shigo cikin murtuqe fuska da manna baqin glass a fuskar sa dan ya
tabbata Mama zata tare shi da baqar magana sanin haka yasa cikin cije lips enshi ya zaro bindi
garshi ya d'aga sama ya danna kuna mar ya rinqa sakin harbi ba qaqqautawa gaba d'aya ya
cika gidan da qara Captain Sani ma dake bayan shi sai hannu yasa ya kama kanshi tare da to
she kunneshi.

Su kuwa su Mama gaba d'aya suka waste a guje parlon ya zama ba kowa ganin haka yasa
cikin sauri da takun cikar zati ya komai farfajiyar gidan kai tsaye motar ya bud'e sannan ya
rarumo hannun Bodd'i ya fizgota woje sannan ya jata sukayi cikin gidan,
shi kam captain sai sake baki yayi tare da binshi da ido.

Kai tsaye part enshi ya wuce da ita yana janta da qarfi suna shiga ya jata har cikin bedroom kan
gado ya cillah ta sannan ya juyo da qarfin ya rufe qofar sai ya kuma dawo kan.........



By
*Garkuwar Fulani*
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*BANDIRAWO* page 8⃣
Na
*Aysha Ali Garkuwa*
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇

Pure moment of life writers

*Dedicated 2 Aishat A Muhammad & Ummyn Yusrah and Ummu yahya musa sisin mama &
Sadnaf and Husna Abubakar Bauchi*

An kama hannu shi cikin tsoro ya zaro ido woje ganin Aliyu ne tsaye cikin murtuqe fuska ga
woni irin cabke mai hannu da yayi ya riqe cikin matsar qashin hannun nashi lokaci d'aya yaji
wani irin azaba na ratsa shi cikin in ina baki na rawa yace.
"Hamma Aliyu zaka karya min hannu fa ni ka sake ni ."

Bai kulashi ba sai qara damqe hannun yayi tare da soka yatsar sa tsakanin jijiyoyin hannun shi
d'in.

Cikin jin zafi Abdul ya saki qara mai qarfi tare da sunku yawa yana cije hagoran sa a wahal ce
yace.
"Wayyo Mama Hamma Ali zai karya min hannu Mama zai tsinka min jijiyar hannun."

Matsoshi tayi cikin isa ta d'ago hannu ta yarfa mai mari tare da cewa.
"D'an iska kawai a gabana zaka karya min hannun d'an nawa dan kai baka san dad'in d'aba
sannan baka san yadda uwa ke son d'anta ba,
ai ko mutuwa tana jin kunyar uwa bare kai Aliyu."

Ihu Abdul ya kuma saki da qarfi har kamar zaiyi fitsari a jikin shi.

Jin qaran da ya kuma yine Maman ta leqa fuskar Aliyu da yayi jawur dan takaici bawai dan zafin
marin da tayi maiba gaba d'aya idonshi sukayi jazir leben bakinshi sai rawa yake dan fushi
hakan yasa ya had'e hannun shi da qarfi wanda har saida hannun Abdul yayi qaran targad'e .

Yana tabbatar da ya targa d'ashi ya yarfar da hannun shi cikin fuzgar magana yace.
"Next time in kayi gigin bud'e qofar nan karya ka zanyi."

Yana kaiwa nan ya bud'e qofar sannan ya shiga tare da cewa Captain Sani ya shigo.

Itako Mama kamar ta bishi ta cinye shi d'anye takeji bala'i take kamar ba gobe fad'a take ko
numfashi bata ja .

Shi kuwa Abdul kan kujera ya koma ya zauna tare da tallabe hannun da hannun shi mai lafiyan
yana maida numfashin wahala.

Su kuwa su Aliyu suna shiga a parlour ya zauna kan 3 str ya koma ya jingina kanshi tare da
lumshe ido yana mai jin zafin kalaman Mama a kanshi ko yaushe bata binshi da kalma mai kyau
sai baqin alkaba'i,
gefen shi Sani ya zauna riqe da goran Faro mai sanyi cikin fargaba ya miqa mai murya can
qasa yace.
"Ser ga ruwan sanyi ko zaka Sha?."

Baiyi magana ba kuma bai bud'e idon shiba sai kad'a qafa da yakeyi .

Ganin haka yasa Sani yayi shiru sai shiga kitchen da yayi ya kunna gas ya d'an d'aura musu
ruwan tea.

Har yanzu idon shi a lumshe yake a hankali ya farajin zuciyar sa tana d'an sanyi dan addu'a da
yake tayi,
lokaci d'aya kuma ya fara jin sautin a hankali yaji sautin kukan ta na tashi daga cikin bedroom
en sai shesheqa takeyi cikin rawan murya take ta kukan ido ya d'an bud'e sannan ya zurawa
qofar d'akin ido zuciyar sa na tafasa.

A ranshi yake tuna cewa ,
Itace qarin matsalar sa ko ya zaiyi ne ma shi bai saniba .

A fili yace.
"Ni bansan ya ake kula da wani ba dan ban taba samun kulan ba nike kula da kaina sai gashi
an had'ani da wata jarabar tsiya."

Shiru yayi yana sauraron ta,
har Sani ya fito da y'an cup guda biyu da ruwan tea mai kauri a ciki sai qamshin citta da
kanamfari yake,
yana zuwa ya jawo Stol ya ajiye mai a gaban shi tare da cewa.
"Ga tea ."

Shiru baiyi magana ba har zuwa woni lokacin,
shi kam Sani bai kuma magana ba dan ya ga ogan nashi a sama yake .

Can dai ya miqe tare da cup d'in tea d'in a hankali yake takawa har zuwa cikin bedroom en ,
kan gado ya ganta konce rufda ciki tasa hannu biyu ta riqe cikin ta tana kuka murya can ciki tare
da yin magana cikin kukan.

"Wayyo cikina wayyo Allah na wayyo Bappa na zan mutu yunwa zata kashe ni qirjina ciwo kaina
ciwo."

Duk tana maganar ne cikin fillanci shi kuwa tsayuwa yayi dab da ita sannan ya d'aga kanshi
sama tare da kawar da idon shi daga kanta murya a daqile yace.

"Ke ya isheni haka banson sakarcin banza ya zaki zauna kina mana ihun yunwa."

A take ta had'iye kukan nata sannan ta yunqura cikin rawan jiki ta zauna tana bari kar-kar.

Ba tare daya kalleta ba ya miqa mata cup din cikin bada umurni yace.
"Shanye ki ban cup d'in."

A yadda take jin yunwa kamar zata kasheta wai a bata abu a d'an cup d'in nan .

Tana cikin tunanin da qoqarin matsowa ya juyo kanta cikin wani irin cilla mata mugun kallo da
yana yin zaki karba ko yaya.

Jiki na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login