Showing 24001 words to 27000 words out of 62795 words

Chapter 9 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf

03 Aug 2025

8786

sofa ya kwantar da ita daga ita sai towel a jikinta hawaye kuwa ba'a
magana sai sauke ajiyar zuciya take. Bedsheet din gadon ya yaye yaje ya jefa a washing machine ya dawo, duk ya rude ya rasa
Yaya zeyi da ita ba zato ya tsinkayo Kiran sallar farko.
Shima ga Zazzabi ya rufe shi sosai.

*_ AUREN HUCE HAUSHI_*

AISHAT ISAH MUSAH

(Maman Fateemah)

09061432330

08055362975



Page 86.

........... Da kyar ya lallabata sukayi sallah sai kananun koke-koke take masa, cak ya daukota
ya Dora a gadon Yana cire mata hijab din daya saka mata, cikin jikinsa ya sakata yana Dan
shafa bayanta a hankali tana ta sauke ajiyar zuciya, duk ta dagula masa lissafi Dan shi kansa
dauriya ce kawai kada ayi haihuwar guzuma 'ya kwance uwa kwance, dan zazzabin jikinsa
Shima k'aruwa yakeyi, sunanta ya Kira very softly,Bata amsa ba sai Kara shiga jikinsa da tayi
tana Dan rawar sanyi tare da rik'e hannunsa tana cije lips dinta na kasa
"Pls... precious forgive me,you make me lose my control, iam so lucky to have you... Precious
you're special, i love every part of you, every time with you is specia I love you.. Ilove you with
all my heart..
Kiran Daya shigo wayarsa shiya dakatar dashi daga abinda yayi niyyar fada.
"Kizo Dan Allah Ina mabera sabon parta din Nan, da fatan Kinga text message dina?".
"Eh na gani gamu munzo da doctor zainab din Saida na biya na daukota motarta ce taqi tashi".

"Ok, ku shigo kawai kofar a bude take".
Rigar jikinta ya gyara Mata, sannan ya tattare gashin ya saka masa band ya hade shi a tsakiya
ya sakeshi baya. Kalamansa sun tsaya Mata a zuciyarta, mamakinsa ya girmama a gurinta idan
ta kalleshi sai taga Kamar bashi bane totally ya canza mata, wani sabon Mahmud take gani ba
ainishin wanda ta sani ba.

Suna daf da karasawa kofar da zata sada ka da babban parlourn suka tsinkayo muryar Hajiya
Inna tana fadin. "Kai su wanene haka da asubar fari suka shigo min gida babu sanarwa? me
zakuyi a Nan? to babu kowa a cikinsa da kuka nufa kuna ta sauri Kamar masu amsa Kiran fada,
ai Ina Jin karan shigowar mota na leko Naga kun nufo Nan yasa na fito bansan mahalukin Daya
bude min kofar bama" .ta karasa fada tana kusanto su Aishat din.
Dr zainab ce ta gaisheta, sai lokacin ta gane doctor din tunda itace family doctor dinsu.
"A'a likita lafiya Kika zo Mana da sanyin asuba nan Ina ga kinyi makuwa kuwa ai Nan babu
kowa kinibibin ne yasa aka gina shi kawai Dan fariya, yo inba fariya ba yaushe za'a kashe irin
wanan dukiya a banza".
Aishat ce ta matso tana fadin.
"Dan Allah Inna ki koma ki kwanta mune ba wasu baqin Ido ba, zamu shigo gurinki yanzu wani
uziri ne ya kawo mu, doctor Bismillah".
Tsaye Hajiya innar tayi tana kallon Aishar tana ayyana wani Abu a cikin ranta.
"Shatu, waye babu lafiya a gidan nawa Wanda ni ban sani ba saike da kike wata unguwar Kika
sani?".
"Dan Allah ki barta muje daga baya nayi Miki bayani".
Ta nufi kofar doctor zainab na biye da ita da sauri, ai itama hajiya Bata tsaya neman wata
maganar ba ta rufa musu baya tana fadin. "Muje Naga ikon Allah, tunda abun ya Zama na
Qumbiya-Qumbiya Kuma".
Suna shiga dukkansu Saida suka girgiza da ganin yanda aka qawata part din ba qananun kudi
aka narkar ba a cikinsa, cikin corridor din ta nufa Kamar yanda ya fada Mata a hankali tayi
knocking daga ciki ya Basu Umarnin shigowa.
"Masha Allah!!"
Abinda bakinsu furta kenan lokacin da suka shiga da sallama, saboda babu Qarya ko Mai
hassadar mutum saiya yaba bedroom din Nan, suna Kan gadon tana jikinsa, da sauri Hajiya
Inna ta natso tana fadin "me Zan gani Mahmudu? Daman Baku tafi ba a nan kuka kwana? Ikon
Allah meya sameta Naga lfy-lfy mukayi sallama daku". Dan dafe kansa yayi Wanda ke Sara Masa, ya dago idanunsa Yana kallon Aishat da alamar
tuhuma a cikinsu.
Basarwa tayi tasan dai maganar Daya ce meyasa ta tado Hajiya Inna, ita Kuma tasan
karambaninta ne yasa ta fito Kuma tasan ba komawa zatayi ba shi yasa ta rabu da ita kawai.
Doctor ce ta matsa suna gaisawa da Mahmud Wanda har lokacin kanzil Bai cewa Hajiya Inna
ba.
"Lfy kalau doctor".
Ya amsa gaisuwar,Zahra kuwa lif tayi ta rufe idanunta Kamar me barci Dan ji tayi bazata iya
hada Ido da Hajiyar ba.
'Yallabai ku dan bamu guri na dubata ko".
Kanta ya zame daga kan cinyarsa ya mike Yana fadin "ok doctor Dan Allah a dubata sosai
jikinta yayi zafi da yawa, muje ki fada min meya fito dake yanzu da sanyin asubar nan?".
Ya riko hannaun Hajiya ji tayi Shima nasa jikin yayi mugun zafi.
"Yo ai kaima ba lafiyar gareka ba, yau Naga abinda ya isheni,Ina cikin gida Amma ka kasa fada
mini meye amfanina kenan? Maza lalubo min Babanka ya turo likita ya duba min Kai yaushe
za'a zauna da ciwo a jiki".

Suna ficewa Aishat ta karaso kusa da Zahra ta zauna wadda har lokacin idanunta a rufe suke.
"Sannu zahra, ki tashi nasan idonki biyu ga doctor tazo ta dubaki kinji".
Rinannun idanunta ta bude ta kalli Auntyn Nan da Nan taji idanunta sun kicciko.
"Aunty Aishat Dan Allah kirawo min Aunty Hasana".
Sai hawaye sharrrr... Suka biyo kumatunta.
Hannunta farare sol Aunty Aishat ta rike tana girgiza Mata Kai.
"Pls ki daina kuka gashi Nan za'a dubaki".
Kanta kawai ta iya gyada Mata.
Tashi Aishat din tayi tana fadin "doctor Bari Naga bros".
Tayi waje tare da ja musu kofar tana Jin tausayin zahra da gani Bai saurara Mata ta ko kadan.
"Sannu Daughter kinji Bari na duba na gani sai asan abinda za'ayi Miki, hands glove ta saka ta
umarci zahrar ta gyara ta dubata.
Jikinta tsima ya Kama da kyar ta Bari doctor zainab din ta dubata cikin ikon Allah Bata karu ba
sai dai gurin Kam sai a hankali, dan Allah ya taimaketa jikinta irin roba din Nan ne Wanda ko
haihuwa masu irin jikin sukayi Basu fiye budewa ba, jikin ba gautsi, a cikin Mata dari da wuya ka
fitar da goma masu irin wannan halittar. Ruwan zafi ta shiga ta hada Mata da kanta ta sakata tana hawaye tana komai, Saida ya canza
Mata sau uku cikin ikon Allah sai taji jikin Yayi Mata Dadi fitowa doctor din tayi zahrar tayi wanka
ta fito simple Riga ta Bata ta saka sannan ta leka ya fad'awa Aishat ta hado Mata tea Kofi daya
ta koma a kitchen din bangaren ta hado saboda babu abinda babu a ciki. Tea me kauri sosai ta hado Mata a gefen gado ta Samu zahrar tana Zaune yayin da doctor ke
hada wasu allurai.
Hajiya Inna ce keta fada akan Mahmud yaki Kira Mata Abbie dinsa ya Kuma Hana Aishat ta
kirawo Mata shi.
"Dan Allah ki tashi ki koma Zan Sha magani kawai, nifa lafiya ta kalau kawai dai bana Jin Dadi
ne".
Cikin hukuncin Allah saiga kira ya shigo wayarta alamar mota data gani tasan Mustapha ne da
sauri ta dauka Kota Kan sallamar da yake Mata Bata bi ba ballentana ta Sami zarafin amsawa.
"Kanaji na Mustapha maza ka taho da likita gidana tunda Aliyu baya gari ya duba min Dan biyu
gashi Nan Zazzabi Yayi Masa rigijib ko daga Kai baya iyawa" .
Ta kashe wayar, Baki bude Mahmud yabi Hajiya Inna da kallon mamaki Wai ko Kai baya iya
dagawa "ikon Allah".
Can Kuma uncle Mustapha suna tare da Abbie tun bayan da aka fito masallaci suke Zaune a
harabar masallacin suna hirar zumunci shine uncle Mustapha ya Kira Hajiya ta tambayeta ko
akwai abinda ze taho Mata dashi Dan daga Nan can gidanta ya nufa.
Yayansa ya kalla Wanda shima shi yake kallon domin wayar a speaker take.
"Ikon Allah meya Kai Mahmud kuma gidanta shida ga gidansa can, ko Kuma da yaji ciwon ne
ya tafi can kasan shida ita tasu Bata baci".
Uncle Mustapha ya fada.
"To waya sani ka Kira doctor Anka sai ku hadu a can ya duba shi".
Sallama sukayi Abbie ya nufi cikin gidan Yana kokarin Kiran Ammi, yayin da uncle shima ya nufi
motarsa ya shiga Yana kokarin lalubo number doctor Anka din.

Allurai kusan Kashi uku ta yiwa zahra wadda Saida Aunty Aishat ta riketa akayi Mata sannan ta
Bata Analgesic table ta Sha ta bawa Zahra wani tube na cream tace ta shafa a can da Kuma
Kan breast dinta inda shima ya dade, ta Kuma jaddada Mata shiga ruwan zafi Kamar sau biyu
kafin dare Dan yanda gurin yayi sai a hankali kawai Dan ma dai Tana cikin Wanda ubangiji Yayi
musu special gift da labarin ba wannan akeyi ba.
Tare da Aishat suka fito suna Nan second parlour shida Hajiya innar sallama tayi musu tana
fadin "yallabai in ganka mana".
"A'a babu inda zaya shima ba lafiyar ce dashi ba,ko meye Fadi Masa a gabana ai ba kunyata
yakeji ba tunda ya tsallake gidansa yazo gidana ya taki matarsa ai shikenan Daman ya fada
min".
'kai! Hajiya you have a lot problem wallahi, doctor muje gaskiya kina da damuwa wallahi".

Yayi gaba ya nufi parlourn farko.
"Yo saika Hana na fada ba haka ka fada min ba?".
Ita dai Aishat Bata tanka musu ba, tasan sunfi kusa koka shiga kaji kunya bare ita da ba inuwa
daya suke Sha ba.
Godiya sosai Mahmud ya yiwa doctor zainab din a Nan take fada Masa ya Dan d'agawa zahrar
kafa zuwa two to three days haka Dan ma Allah yasa babu ciwo masu yawa.
Key din mota ya mikawa Aishat ta Bata tana parking lot sannan yace ta bawa Aishat account
number.
Godiya take Masa Kamar zata zube masa a Qasa yi take tana karawa Kamar zata Ari baki,
itama Aishat din ta tayata yi Masa godiyar, komawa Yayi ciki kawai shi baiga wani abun yiwa irin
wannan godiyar ba.
A sabuwar motarta doctor zainab ta koma murna kamar me Dan tasan wata Rahama ce
ubangiji Yayi Mata, motarta tafi kwanan wata biyu tana fama da ita yanzu haka tana Kan cinikin
wata motar jira kawai take a Bata adashenta ta Saida tata ta hada kudin ta tura musu a kawo
Mata motar Sai gashi cikin hukuncin Allah da sanyin safiya tayi Gam da katar da motar da Nan
kusa Bata tab'a tunanin mallakar mota irinta ba ta millions of naira.
Direct bedroom din ya wuce ji yake kamar ya cire mata ciwon daga jikinta, lokaci bayan lokaci
Yana sakin smile shi kadai, mamaki yake yi Wai Daman haka lamarin yake ya tsaya Yana cutar
da kansa a banza ai da yasan haka ne da gara yayi tun tuni yayi kaffarar rantsuwar a wuce
gurin, Bai samu Hajiya a parlourn ba. A ciki ya sameta tana waya a yanda ya fuskanta da Ammi take wayar Dan lafazinta na karshe
Daya tsinkaya ji Yayi tana fadin "yauwa turo min da ita Badi'a din tazo da Kayan biqin amaren".
"Ilahiy wa Rabbi" ya furta hankali yau ya jawowa kansa barbade Ina maganar privacy a wannan
lamari kuma.
Gurin zahrar ya karasa Yana Mata wani duban kasa-kasa dan ji Yayi wani Abu na sama yawo
duk da Zazzabin dake nukurkusarsa, zama Yayi Yana Kai hannunsa wuyanta.
"Are you okay?".
Kai ta gyada Mata sexy eyes din ta Nan da Nan sukayi narai-narai da hawaye.baiya wata wata
ba ya rungumo kayansa Yana fadin "pls kiyi hakuri Zaki warke na daina kinji my previous".
Baiyi aune ba ya jiyo salatin Hajiya Inna a kansa fadi take tana karawa.
"Muhammadu Rasulullahi me Zan gani ni Hadiza, Shatu duba min Nan Dan Allah Anya abokin

tagwitakar taki ne kuwa?".
Ta jefawa Aishat tambaya wadda ta shigo daga raka doctor zainab.
"Wannan Kuma ai tsakanin ku ni me zance kiyi hakuri Bata da lafiya ne shi yasa Amma ai
badan rashin kunya yayi ba".
Kokarin kwace kanta zahrar take itama wallahi Batasan ya akayi ba ta yarda suka manne juna,
Amma Yayi musursisi yaki sakinta.
"To Inna ya kike son nayi kukan fa zatayi".
"To wayace ka jankwalo tsiyar aida saika cigaba da saka Mata Ido tunda abinda ka zaba
kenan".
Runtse idanunsa Yayi dole ma Yayi hijira daga gidan Nan Ashe martch ya tarowa kansa Bai
sani ba.
Kiran uncle Mustapha ne ya shigo wayarta Hajiya Innar.
"Yauwa ku shigo sabon gurin Nan da aka Gina Dan fariya".
Ta yanke Kiran ya juyo tana fadin saika taso idan ka Gama shafe ta kana neman ka lalata
yarinya ai Daman tun jiya kake Mata kyarkyara".
A parlourn farko suka zauna, Mahmud na gaba Hajiyar na baya tana kananun maganganu.
Hannu ya bawa su uncle suka gaisa sannan ya zauna, gaishe da Hajiyar sukayi lokacin tana
Zama kusa da Mahmud din.
"Likita Dan Allah duba min shi Zazzabi yakeyi duk karfin hali ne kawai yakeyi Amma jikin kamar
wuta yake".
"To Hajiya za'ayi abinda ya kamata in sha Allah".
Zafin jikinsa ya auna tare da 'yan tambayoyi doctor Ankan yayi Masa, Allura ya bashi tare da
'yan magunguna, doctorn ya jima Yana mamkin Mahmud a yanda Allah ya hore Masa dukiya da
kananun shekaru ba qaramin mamakinsa Yayi ba, ace yau shine Karon farkon saninsa da
mace to Ina isalin labarin Daya dunga yaduwa game dashi?. Lokacin da uncle Mustaphan yazo rako doctor ne uncle saminu shima ya shigo gidan da tasa
motar kusan wannan dabi'ar su ce duk safiya suna zuwa suga yanda tsihuwarsu ta kwana.
Kusa dasu yayin parking ya fito Yana fadin .
"Lafiya doctor na ganka a gidan Nan da sanyin safiya?".
Dariya doctor Anka yayi Yana Mika Masa hannu sukayi musabiha sannan sukayi da Uncle
Mustapha.
"Jarimin kamilin danku nazo na duba"
"Wa kenan?".
"Mahmud Mana kasan yawanci ko namiji matukar ba mazinaci bane to duk ranar Daya Fara
sanin mace sai kaga ya Samu irin su Zazzabi haka da
abinda baza'a rasa ba na bakon yanayin da aka samu Kai kai a cikinsa to shima hakance ta
kasance wannan shine first time Daya Fara sanin mace a rayuwarsa, gaskiya na sarawa
kamewarsa Allah ya taimaki 'yan baya muma ya tsare Mana namu iyalin".
"Allahumma Amin ya Rabbi".
Tunda doctor ya Fara Kora bayani uncle Mustapha ke yiwa Dan uwansa wani kallo na yau dai
an Kama kyafa a tarko Dan shine agent na yad'a Mahmud mazinacine shiya Kama shi da kansa
harda shedar hotuna a waya.
Uncle Mustapha baiyi kasa a gwiwa ba ya jefawa doctor Anka tqmbaya.

"Shin doctor Dan Allah irin wannan Condition din da akan shiga ga sabon shigar Tarawa da iyali
shin sau nawa ake iya samun Kai a wannan yanayin?".
"Sau daya ne saboda abinda jiki Bai taba jinsa bane daga haka gaskiya ba'a qara shiga irinsa".
"Ok thank you very much doctor sai munyi waya".
Ya karasa gurin motarsa ya wuce da dunbun mamakin young rich Guy din Nan abinda Bai taba
kawowa ko a mafarki bane ace Yana da irin wannan kamewar.
Wani duban kaji kunya uncle Mustapha ya yiwa uncle saminu ya wuce ya koma bangaren
Muhmud tunda acan ya baro Hajiyar.

Tunda Ammi suka Gama waya da Hajiya inna taji wani irin farin ciki ya rufeta fadi take.
"Alhamdulillahi! Alhamdulillahi!! Alhamdulillahi!! Allah na gode maka ko yanzu ka wanke min
yarona daga zargin Zina ga matarsa ta sunna ma ya dauke Mata Kai tsawon lokaci bare har a
jefe shi da kazafin Zina harda cikin shege.
Wato wannan 'ya'yan sai a kyalesu wato 'yar uwarsa ya Kira tazo ta kula Masa da matarsa.
Wani murmushi tayi tana fitowa zuwa dakin dasu mummy Badi'ar suke, ta labarta mata yanda
sukayi da Hajiya Inna, babu b'ata lokaci Mummy bada'ar ta shirya ta dauki duk abunda zatayi
Mata amfani dashi suka nufi gidan Hajiya innar tare da Aunty Hasana duk da yau suketa shirin
barin garin tunda likitoci sun tabbatar da Bazasu sallami Mama ba sai sun Gama duk abinda ya
kamata Dan da gaske ciwon zuciya Yana barazanar kamata shine Mahmud ya Hana a
sallameta har Abba ya Kira ya nemi izinin barinta ta warware a nan.
Duk hankalin Aunty Hasanar a tashe Dan lokacin da Aishat din ta kirata kafin doctor tace Mata
zahrar nata sharbar kuka.
Ranar Nan dai kusan yini sukayi da ita Tasha gashin ruwan magunguna gurin mummy Badi'a
Dan tsaye tayi a Kan zahra Saida taga yes ta aminta da gurin sannan ta koma,dahuwar Naman
rabo Mai kayan maganin bikin amare Ammi tayo Mata da kanta.
Zahra ta kirawo Ammah tana Mata kuka shagwaba Wai tace Mahmud ya dawo da ita Azare ita
bazata iya Zama a Nan tare dashi ba.
Dan murmushi kawai Ammar tayi tasan wasa kenan dama da baisanta ba ya dauko abinsa ya
taho da ita to bare yanzu da Mai rabota da wannan garin sai Allah,itama da Dade tana mamakin
halin dattako da kawaici irin na yaron.
Amma saita lallabata da dadin bakin tayi hakuri zuwa gaba sai Abbanta yayi magana.
*AUREN HUCE HAUSHI*

AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateemah.


09062432330


_Page 87.

_________ Sai kusan magariba sannan Aunty Hasana tayi haramar tafiya lokacin suna parlour
a zauna su biyu kadai,dan zahrar taji sauki sosai sai dai tafiyar ce sai a hankali take yinta, Kara
matsowa Aunty Hasanar tayi kusa da zahra ta gyara Zama tana Mata kallon Kai tsaye.
"Kina jina abinda nakeso dake ki kwantar da hankalinki ki nutsu ki aje duk wata shiririta ki
fuskanci rayuwa,yanzu kin hau wani stage na girma ki kula da mijinki ba
Kada ki bada fuskar da wata zata shiga gabanki a gurinsa ki Zama Mai yuriya a gurin biyan
bukatarsa kada ki yarda ya gane Baki da juriya tanan zaku iya samun baraka Mai girma, ki
tsaya ki nutsu ki fashimci a wane rukuni mijin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login