Showing 3001 words to 6000 words out of 62795 words
Chapter 2 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf
ne, laffayar Zahra ta cire ta kwanta kusa da
diyarta da take ta Wasa da kafafuwa tana dagasu sama da gani tana Cikin farin ciki. Saida
Aishat ta fice sannan Aunty Hasana ta dubi Zahra. "Wacece wannan? Naga Suma matukar Kama da mahmud sai dai ita farace sosai".
"Twins sister dinsa ce kamar keda Ya Hassan".
"Kai! Kice Suma irin mu ne? Ke twins sun sakaki a tsakiya kema Allah ya Baki irin mu".
Ta fada tana murmushi.
Kwal-kwal Zahra tayi tana kallon Auntyn tata.
"Ke! Wai lafiyarki kuwa? kamar wata sabuwar Amarya sai wani rarraba idanu kikeyi tunda muka
shigo garin Nan Naga kin kasa samun nutsuwa".
Hannaun Auntyn ta riko ta janyo ta kusa da ita kamar tana tsoron wani yaji abinda zata fada.
"Wallahi Aunty tsoronsa nakeji nasan no way out a nan".
"Ban fahimta ba tsoron sa kamar Yaya? wani Abu yakeyi da kike gudun ya cutar da ke ko
menene?".
Runtse idanu tayi sai hawaye, sharrrr..
"Aunty wallahi I am afraid about sex.."
Wani shock Auntyn ta shiga tana ayyana.
Babbar magana! Jarimi wato duk tsawon wannan lokacin kallonta yakeyi kenan Saida ya
kawowa iyayensa ita sannan ze nemi hakkinsa duk yanda akayi da dalilinta na wannan shiga
rudun.
Amma a zahiri sai ta dake taja hannunta suka zauna a gefen gadon.
"Haba Zahra me kike son Zama ne?wa kikaga aure ya kashe da zaki tashi hankalinki a banza,
ai wallahi samun yaro irinsa a zamanin Nan sai an tona, ke idan kina da lassafi ko tari kin Bari
ya kubce miki akan duk abinda yake bukata a gurinki ai wallahi yayi rawar gani, kada naji kada
na gani ke ba godewa Allah Zaki ba, ki duba kiga inda ya fito da yanda Allah yayi masa nasibi a
rayuwrsa tunda kananun shekaru da fitinannene da Allah kadai yasan adadin yaran daya Bata
Amma yasan ke tasa ce malak malak ya iya kauda Miki Kai irin haka ai cewa nake zaki ba
marad'a kunya yayi yanda yakeso dake, Naga alamar sai anyi Miki shiri na musamman idan
haka zakiyi wallahi kwana kadan ze lafto miki kishiya kina gani ta shiga gabanki ta kwace miki
fada duk kuwa irin son da yake Miki idan baya samun gamsuwa a gurinki zeji kin fice Masa
daga rai ki nutsu tun dare Bai Miki ba Ashe ganin kitse nake yiwa rogo Ashe ba jaruma bace ke
ai sai ki Bari kiji Yaya Abun yake kafin ki yanke masa hukunci, Ina ganinki kin Kai matsayin da
Zaki yiwa wata wannan karatun Ashe biri boko ce ai Wallahi shima da nasa laifin har yaushe
ze wani saka miki idanu kiyi yanda kike so'.
Knocking din kofar da akeyi ya saka Aunty Hasana dakatawa da fadan da take yiwa Zahra ta
Dan matsa tana fadin.
"Bismillah shigo".
Aunty Aishat ce a gaba wasu 'yan matan buzaye farare tas suna biye da ita dauke da manyan
basket dauke da kayan abinci.
Suka gaishe da Aunty Hasana sannan suka gaishe da Zahra.
Aunty Aishar ce ta gabatar da Zahra a gurin yaran sannan Suma ta gabatar dasu ga Zahra
Radeeya da mardiyya 'ya'yan Mummy badai'a ne wadda sukaje Azare tare matan uncle Ishaq .
Zahra ta nuna farin cikinta Sosai taso su zauna sukace Ammi tace su koma yanzu.
Abinci Aunty Aishat ta zuba musu tare da sauran abubwan da aka kawo sai da Aunty Hasana ta
ce ta Bari ina zasu Kai wannan abincin sannan ta bari.
Sai yamma Zahra ta sake wanka Aishat tazo da Mai yin makeup tayi Mata light ta kawo Mata
wata irin Riga da Alkyabba Fara sol ta saka sai tayi wani irin kyau, Mai makeup din sai zuzuta
Zahra take tana fadin.
"Masha Allah. Wallahi ban taba yiwa amaryar da kwalliyar ta ta tafi da imanina ba sai a kanki".
Murshinta Mai ban sha'awa Zahra tayi sai akayi dace Aishat ta dauketa hoto sai tayi wani irin
kyau Wanda dole ka kalleta ka Kara, sai Kuma ta Fara daukarta video, tana gamawa tayi review
dinsa taga komai yayi ta hada da hotunan ta turawa mahmud.
Mota ta dauki Hajiya Inna da Zahra kadai ta nufi gidan Su mahmud dake Kan titin Garba duba.
Masha Allah gidan ya dauki haramin Dan mutum motocin a tare suka shigo su mummy Badi'a
dasu Aunty Surayya su suka tarbi amarya har cikin master parlourn Ammi wadda Tasha gayu
kamar ba gobe an tarbi Zahra da iyayenta tamkar Dade duniya Ammi Bata taba ganin Zahra ba
sai yau har gurin da Hajja take zaune su mummy Badi'a suka kai Zahra Aunty Surayya na fadin
.
"Hajja ga kishiyarki Nan tazo ta gaisheki"
Hannu tasa ta bude fuskar Zahra.
"Masha Allah sannu yarinya kinji. Allah yayi Albarka ya kade fitina ya hada Arzikinku".
"Allahumma Amin"
Aka amsa, sannan taci gaba da fadin. "saifa kinyi hakuri da halin mijin namu dan miskili ne ga
dukan Mata idan Zaki iya to idan Kuma kin barmana nida Kawata Hajiya Inna to yanda dai Kika
yanke muna saurarenki".
Anyi dariyar kalaman Hajja sosai Aishat ce tace.
"Haba Hajja duk kishin ne haka? kinsan ko ana dara fidda uwa akayi Mai dukan wannan sai
ruwan sama shima sai idan ta tsaya Kice dai kina kishi tafi ku komai".
Gaishe da Hajjar Zahra tayi sannan suka karasa gurin Ammi itama saka Mata albaka tayi,
sanna ta cewa mummy Badi'a su kaita dakinta.
Muzanta iya muzanta Mama tayi Dan sai taji Daman batazo ba Dan ko suturar azo a gani Bata
zo dasu ba tunda Bata taba kawo hakan zata riski dangin mijinna Zahra ba, sai taga zahiri Ashe
ita karyar banza takeyi mijinta Mai kudi Saida tazo taga zahirin inda kude ke magana da kansu
Dan yanda aka tsara gidajen da abinda aka zuba kadai ya Isa ka yankewa kanka hikunci,dan
Nan guri ne tamkar baza'a mutu ba.
Sai kusan magariba 'yan Azare suka samu isowa, part din sameera matar Abbie da suka rabu
aka gyarawa Baki, aka saukesu ba Karamin mamaki Mama tayi ba ganin harfa Hameeda a
cikinsu.
Aunty Hasana ma dakin baki na kusa da Aishat aka bude musu suda su Inna maimuna.
Da wuri suka kwanta duk da ba wata tafiya sukayi Mai tsawo ba tunda a jirji sukazo.
Wurin Sha Daya mahmud ya kirawo Aishat Yana tambayar ta Ina Zahra?
"Tana dakin Ammi fa ni Kuma Ina kasa".
"Dan Allah ki fito min da ita wani Abu Zan fada Mata na Kira wayarta a rufe".
"Kaima kasan wasa ne naje nace ta fito sai dai ka Kira mummy Badi'a ka fada Mata sai naje na
taho maka da ita tunda bazaka iya hakurin goben ba, ni na rasa wane kinibibin ne yasa ka
haramtawa kanka abunda Allah ya halasta maka Saida aski yazo gaban goshi Kuma zaka
tuburewa mutane kawai ai saura kiris dai kowa ya huta, sai kuje can ku karata a hanyar karaye". "Afuwan Aunty na Kece fa kika rudani wallahi, da kinsan bazaki kawo min ita kamar yanda
kikayi min alkawari da Baki turo min hotunan Nan ba gashi kin
Sak."
Kit ta yanke Kiran taga alama nema yake ya saki layi Kuma gara a tattara a Mika masa ita a
wuce gurin, taji suna maganar wani taron yini fa da momin kano tace ta dauki mauyin yinsa.
Tashi Aishat din tayi ta nufi sama tana hawa ta Fara jiyo muryar su batool daga dakin da Zahrar
take, Dan knocking tayi kafin ta turata ta shiga.
"Wai ku menene haka kikeyi? Ku barta ta huta kunsan nisan tafiyar da tayi kuwa da kuka tasa ta
gaba da surutu Kuna ma duba time kuwa?".
Tashi sukayi sun Kai su shida suka fice.
Shigowa tayi ciki tana sakin murmushi tana fadin.
"Nazo a bani sirrin Nima Sweet heart ya ringa rikice min kamar yanda Hussein yake rikicewa ko
a gaban waye idanunsa rufewa sukeyi, sai ki ringa kula dashi yanda baze ringa sakin layi ba
kada ku raba Hali a gaban Ammi yasa kiji kunya".
Hannu Zahra tasa ta rufe idanunta tana fadin.
"Kai Aunty Dan Allah ki daina fadar haka Ni wallahi ba ruwana fa".
"Na sani shine baya iya jure kiyi nesa dashi yanzu ma fa shine yake nemanki a can part dinsa
na Cikin gjdan Nan Wai na Kai Masa ke Yana jiranki".
Wani kwalalo sexy eyes dinta tayi tana rufe bakinta da tafin hannunta.
"Dan Allah Aunty Aishat ki rufa min asiri wallahi bazan iya fita ba, me zanyi masa Kice Masa
nayi barci Dan Allah".
Idonta ya cicciko da hawaye.
"Shikenan kada kiyi kuka Hajiya shagwaba ki Adana abinki tunda Mai lallashin baya Nan".
Dan murmushi a tayi a kunya ce tana kauda kai.
Ficewa Aishat tayi tana saka wayarta a Airplane mode.
*
Da safe sosai gidan ya kacame da Baki kowa sai sabgar gabansa yakeyi, Zahra na daki tun
bayan da tayi sallah ta shiga ta gaishe da Ammy da Hajja wadda a Nan ta kwana tunda Allah
yayi Mata lafiyar kafa daraf take hawa sama.
Daki ta koma duk da Hajja taso ta zauna suyi Hira, tana kwance tana chart da dasu Aneesa
wadda suka nufo sokoton ita dasu Fatima da Khadija.
Sajeeda Kuma sai karfe flight din is karfe biyu zata biyo zuwa sokoto, Jin alamun bude kofa
yasa Zahra dago Kai Aunty Rukayya ce da Fateeha suka shigo, da wani uban tsalle Zahra ta
tashi ta fada jikin Aunty Rukayya tana fadin.
"Daman Kuna Nan Aunty Rukayya? Sannunku da zuwa"..
Ta Mika hannu ta karbi Akram.
"Wallahi muna Nan Amarya ai harda mutuniyar dasu mommy".."
"Kai haba dai harda Hajiyata kuka dauko ga nisa".
"To ya za'ayi tace biki na farar kaza Wai balbela ba gayya ce ba, haka fa ta fada min".
Anan suka baje tare sukayi break fast da ita, kafin Azzahar gida ya gama cika an yiwa Zahra
makeup na garari, ana haramar tafiya gurin walima su Ummee da Aunty Nauwarah da mommy
Haneefa suka sauka Mahmud da Kansa ya dauko baikinsa dan ya cewa Ummee zuwansa ne
bana Zahra ba, Su Ammy na zaune a parlour sukaga ana shigo da manyan jikunkuna daga
karshe su Ummeen suka shigo Mahmud Yana bayansu shida Aunty Nauwarah, 'yan uwa
abokan Wasa sai dan biki suke yiwa mahmud akan yanda yayi kyau Yana baza kamshi, sai
walainiyar yake a Cikin Gezner milk colour ga wani daukar ido take kana ganinsa ango sak.
Har gurin Su Hajja ya raka Ummee Yana fadin.
"Hajiya Inna ga Ummen Zahra wadda kwana biyu kuke waya da ita".
"Muke waya ko kake Mana tafinta Ni ba iya nata yaren nayi ba itama Bata iya nawa ba,kace Ina
musu sannu da zuwa".
Ta fada tana daga musu hannu Hajiya ba Ajami.
Cikin yaren larabci ya fada musu sakon barka da zuwa da Hajiya da saura mutanen gurin
sukeyi musu.
Gurin Ammi suka Karaso da yake Ammi makarantar English tayi sai abun yazo da sauki sun
gaisa sosai dasu kafin a kaisu masaukin su inda sukaci abinci sukayi salllolinsu.
Ammi da su mummy Badi'a da Aunty Surayya suka Kara shigowa suka gaisa dasu Ummeen.
Aunty Surayya ce ta fice ta nufi sama lokacin an gama shirya Amarya tsab,ta shiga dakin komai
yayi Masha Allah Sai dai mak'iyi.
Hannunta Aunty surayya suka fito a hankali suke gangarowa har kasa suna daf da shiga gurin
Ummee ta jiyo scent dinsa Dan juyowa tayi shi ta gani Yana tsaye ya harde hannu a kirjinsa ya
Zuba Mata Idanu.
Ganin kamar Aunty surayyar zata juyo yasa tayi saurin dauke Kai tayi gaba.
Suna shiga dakin Zahra tayi arba dasu Ummee ai Batasan lokacin data daka wani uban tsalleba
ta shige jikin Ummee tana wata irin murmushi Mai dauke da tsantsar farin ciki.
Daya bayan Daya tana shiga jikinsu suna gaisawa.
Anan ta zauna dasu tana ta mamakin Wai meu amor ne ya fadawa Ummee Amma ita Kullum ta
nemesu Bata samu.
Daga Nan Zahra Bata koma sama ba suka wuce gurin walima anci ansha walima ta amsa
sunanta anyi wa'azi Mai ratsa zuciya da zaburar da ma'aurata akan hakkokinsu, jiki yayi sanyi
sosai Dan an kwankwashi ko wane bangare, duk iya zarin mutum sai dai yaci ya Bari anyi
komai na girma da wadatar arziki, ansha hotuna da Amarya da ango Dan burin kowa yayi hoto
da ita 'yan matan dake feleke akan mahmud sun raina kansu Dan sun San mahmud yayi musu
fintinkau da wata irin tazara Mai girma Mai kamar wannan mezeci dasu.
Karfe takwas aka fara Shirin tafiya dinner wadda za'ayi a MABERA EVENT HALL.
Su sajeeda dasu Aneesa su Amatu da Aunty safiya duk sunzo sai suka ringa tuna lokacin da
wancen biki ya lalace komai ya rikice, Amma yanzu gashi ana kara'i.
Sajeeda ce ta kalii Amatullah tana fadin .
"Kunga mahmud sai a kyale shi, wato sai an rama masa bikinsa da ba'ayi ba kenan".
Aneesa ce tace .
"Aini yayi min dai dai wallahi saboda mahassada da 'yan bakin ciki masu yiwa Zahra dariya da
shewa da yi Mata tozarci a ranar da aka kaita gidansa suga yanda Ubangiji ke yin nasa ikon
susan hassada ga Mai rabo taki ce Kuma dare ga Mai rabo hantsine, yau ga Zahra ganinta ma
sai kayi da gaske Dan baka Isa ka haura inda take ba sai anyi maka iso Kinga kuwa ai ko yanzu
Allah ya nunawa masu yi Mata hassada iyakarsu.
Shiru Hameeda tayi tasan wannan maganar da wannan ke saki an Bata labarin abinda ya faru
ne lokacin da Mama da Salma suka sakata tayi rashin kirkin Nan Wanda ya janyo musu sabanin
daya shiga tsakaninsu har inda yau din Nan take.
Aunty Nauwarah ce ta shirya Amarya da shigarsu ta Amaren larabawa, tunda Ammah ta fada
musu halin da ake ciki suka dauro niyyar tahowa duk da daman suna niyyar zuwa ganin
Zahrar,sai kuma ga Kiran mahmud ya fadawa Ummee sannan ya tura Musa iv din dinner, shine
fa Aunty Nauwarah to shiri na musamman akan dinner din gata Daman gwana a gurin makeup
lokacin dasu Aishat suka shigo Basu ganu Zahra ba Dan juyewa tayi tamkar ba ita ba.
Dai dai kunnen Zahrar Aunty Aishat din tazo tana Mata magana.
"Dan Allah a rangwanta Masa kada ya kasa rike Kansa a gurin fa, irin wannan Abu haka'.
Sunne kai Zahra tayi Dan ji tayi kamar kowa yaji abinda ta fad'a.
Sai da kowa ya tafi ya rage daga Zahra sai sajeeda wadda Aunty Hasana tace su zauna tare
kafin a zo daukarta.
Suna zaune suna hira wayar sajeeda ta dauki wani slow music lokacin tana duba wasu kayan
da Mama Haneefa ta kawowa Zahra, Jin special ringtone din nan yasa ta baro gurin da sauri
tana fadin. "Sunzo garin kenan".
"Waye kuma aka samu".
"Kinji ki waye kuwa Banda yayanki daya hanani sakat da soyayyarsa".
Picking tayi tana nufar kofar fita, saura kadan suyi karo da mahmud Wanda shi kuma ze shigo,
da sauri tayi baya tana fadin. "Sorry ban kula yallabai".
"No ba laifinki bane nine banyi knocking ba".
Ya shigo ita Kuma ta fita da sauri.
Tunda Zahra taji muryarsa taji wani abu da batasan ko meye ba ya tsirga mata.
A hankali ya tako har inda take ta sadda Kai kasa,shigar babbar Riga yayi irin dai yanda mafi
akasarin angunan Hausawa keyi, dagota yayi ya Mikar da ita wani lunshe sexy eyes dinta tayi
ba tayi zato ba taji iskar bakinsa mai dauke da kamshin Lister mint ta sauka a Kan fatar
idanunta kafin ya zagayo da hannuwansa ta bayanta ya rungumeta tsan-tsan a jikinsa Yana jera
ajiyar zuciya a dai dai kunnenta ya rada Mata "preciousss kin gujeni why? kinsan yanda na
azabtu da bakya kusa Dani kuwa? Rabon dana jiki a jikina haka fa tun muna India kinsa na
Zama marayan karfi da yaji jiya nayi nayi kizo ko ganinki nayi kika k'i zuwa ko? Can gurin lalube
lalubensa ya jiyo zif daga gefen wedding gown din ya zuge ya shiga Kai kawo da hannunsa
dayan Kuma ya zame Dan veil din da aka makala shi a jikin kamar hula wadda aka saka mata
ya Kuma hade bakinsu Nan da Nan ya rikata Mata lissafi, da kyar ya saurara Mata suna maida
numfashi .
Cikin murya wadda ta dashe ya fara Mata magiyar tazo su wuce basai sunje gurin dinner din
Nan ba, bazei iya Kuma tana nufin a haka zata fita duk Nan a waye ana kallo. Yasa hannu Yana
shafa saman rigar wadda net ne a gurin.
*AUREN HUCE HASHI*
AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah.
09061432330
Or
08055362975
Assalamu Alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu barkamu da sallah muna tayi Al'ummar
musulmi Baki idin qaramar sallah,muna rokon ubangiji ya karbi ibadun mu ya Samu a cikin
bayinsa Wanda yake 'yantawa Dan Alfarmar Annabi Muhammad s a w w.
Page 81
............Suna tsaye yana kallonta daga sama har kasa Yana Kai kawo akan zuwa dinner din nan
yayi dana sanin jan lokacin nan,daya bude aiki da Sai dai ya kawota da ciki ai da ya rufe babin
duk wannan bidi'ar da aka bude, Dan zayyan ya turo Masa yanda gurin ya cika da Dan mutum
tamkar anyi shelar bikin , ga mutanensa da Sameer ya ringa tura musu da iv ta email dinsu
abun har mamaki ya bashi. Dan sunzo ba kadan ba ga alert sai shigowa yake daga different
people shi abun mamaki yake bashi to da bikin da aka shirya Masa ne Yaya kenan?.
Knocking yaji daga waje agogon hannunsa Rolex ya duba sai yaga lokacin yayi sauri hannunta
ya kamo tamkar yanda India suke ya nufo kofar,key din ya murza ya bude. Aunty Aishat ce ita
da Aunty Nauwarah,wata irin kunya ta rufe Zahra.
Dan Bata taba tunanin da sauran wani a part din ba Dan yau har masu aikin Ammi sun dauki
wanka sun fice.
Wani irin kyau sukayi yanda suka fito din Nan sai suka bada wata irin colour mai daukar hankali.
"Dan