Showing 54001 words to 57000 words out of 62795 words
Chapter 19 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf
da ita.
"Zahra munga sako fa. Allah ya saka da Alkhairi mun gode kwarai da gaske".
"Meta kawo ne haka Ammi?".
"Ina ruwanka ku tashi ku tafi kada kuyi missing flight".
Narai narai Zahra tayi da fuska kamar zatayi kuka.
"Tashi kuje kinji Tunda haka yakeso Allah ya tsare gobe ma Rana ce sai kizo ki wunar min din
kinji".
A kunya ce ta tashi tana fadin " To Ammy nagode mun tafi sai mun dawo".
Har gurin mota Aishat ta takasu tana mitar Bai Bari zahrar ta shiga sauran parts din gidan ba.
"Bari kawai da anan zata wuni sai Kuma ta nemi ta hanani sakat idan na tafi ma babu nutsuwa
Dan yanzu ta birkice min a hanya ai gara muje tayi min bayanin abunda nayi Mata, idan tana
Nan ai wallahi aiki baze yuwu ba zuwan banza zanyi, nifa Naga alama sai yanda Hali yayi Dan
yarinyar Nan..., Ki bari kawai sai mun zauna". Hannu Zahra tasa ta dafe kirjinta, tana mamakin furucinsa.
"Wallahi Aunty fada kawai yake ni babu Abinda nayi masa kawai dai bana son Yana min
maganar wannan doctor din shi Kuma Koda yaushe sai ya yi ta yi min maganarta ni Kuma
banaso".
"A'a gaskiya tayi ma hakuri idan nice saina maka yaji wallahi kawai ka tasani gaba kana min
zancen wata ai baka taki gaskiya ba" ."Hummm kinsan abinda yarinyar nan tace Mata Ranar
dana nuna Mata sabon gidansu?"..
Girgiza Kai tayi alamar a'a.
"Cewa fa tayi Wai mace ba gaba ba baya"
Aishat Bata San lokacin data fashe da dariya ba.
"Well done, wallahi ba karya tayi ba to Kai karya ta fada?".Kiran wayar da akayi masa ya katse
maganar da sukeyi.
Abinda aka fada masa yasa yayi saurin duba agogon dake daure a hannunsa.
"Bari mu wuce lokaci yaja kada muyi late".
Karfe Sha daya har sun karasa gidansa na Lagos Tunda tsakanin gidan da airport din babu nisa
sosai nan ma Aljannar duniya ce dan Sai taga kamar yafi kowane gida kyau ma, dan daya wuce
wurin meeting kasa Zama tayi a kowane parlour, bedroom ta koma ta rufe kanta dan abin yafi
karfin tunaninta, to Dan Allah shi wace irin dukiya ya mallaka haka da kananun shekaru irin
nasa? ita fa tana Jin tsoron irin wannan dukiyar a gurin matashi kamarsa gaskiya.
AUREN HUCE HAUSHI.
Maman Fateemah
09062432330
08055362975
Page 96
________Karfe shida da kwata su Mahmud suka shigo gidan shida Sameer da zayyan dake
driving dinsu, Basu tab'a tunanin zasu Kai wannan lokacin ba a gurin meeting din, suna cikin
meeting ne kiran gaggawa ya shigowa sameer injinan sabon kamfanin hada Madarar gari da
'yar Amana condensed milk suka karaso Wanda za'a bude a Azare,tunda tuni an Gama ginin
gurin, to dole suka nufi deport can tincan island, Saida sukayi clearing din komai suka baro
gurin, sai Kuma goslow ya rikesu.
Mahmud na sauka Shima Sameer ya sauko zayyan ya wuce da motar ma'adanar aje motoci,
ciki suka shiga shi Kuma zayyan ya wuce nasa masaukin dake wani bangare na gidan.
Shiru parlours din duka babu alamar dake nuna da mace a gidan Dan da alama ko abincin dake
saman table ba'a tab'a ba, jakar laptop dinsa Sameer ya aje Yana fadin."Bari naje ba watsa
ruwa naji Kiran da madam ke jera min lokacin muna meeting kasanta Bata da hakuri yanzu
haka danta ne yake Zazzabi Dan dazu da safe take fada min wai taji jikinsa da dumi ga Kuma
mura".
Kallo daya Mahmud yayi Masa Mai nuna alamar baka da hankali.
"Meya faru kuma?".
Coat dinsa ya cire ya nufi ciki ba tare Daya tanka Masa ba, Dan murmushi Sameer yayi yasan
halinsa na son Yara da tattalin mace wato yayi laifa kenan.
Shima juyawa yayi ya fice Yana ayyana idan oga yayi nasa yaran ko Yaya, yasan dole ya Basu
kulawa fiye da tunaninsu dan Sam baya Wasa da Lamarin Yara Allah ya jarabce shi da son
Yara matuk'a.
A kalla Saida ya shige parlours biyar sannan ya haura steps ya shiga corridor Wanda aka
kawata shi da wani irin mirror Mai shegen kyau irin Wanda ake ajewa din Nan a
corridor,bedrooms hudu ne biyu na facing din biyu, Wanda ya barta a ciki ya nufa, ya gaji iya
gajiya, Kati ya saka ya bude kofar, can karshen gado ya ganta a takure kamar Mai barci, da
sauri ya karasa Yana fadin.
"Menene precious?".
Shiru tayi Masa Dan yau dai tayi dana sanin biyo shi Lagos yafi sau shurin masaki, Dan wuni
tayi da yunwa ga fridge din dakin ruwa roba biyu ne kawai a ciki sai tarin lemukan gwangwani
irinsu Pepsi da Coke ita Kuma ba kukanta Nan ba.
Zama yayi kusa da ita Yana dago da fuskarta, ba zato yaga ruwan hawaye suna bin Kumatunta.
"Subhanallahi! Previous meya faru?pls fada mini, baki da lafiya? Me yasa Ina ta kiranki Baki
daga ba?".
Babu amsa Daya data iya bashi sai kwantar da kanta tayi a jikin gwiwuyinta.
"Ya subhanallah! Wai fushin ne har yanzu ba'a huce ba? Kiyi min magana Dan Allah kada ki
sakani a damuwa mana, to Bari na Kira Miki Ammi ko Ammah wata qila su ki fada musu Abinda
yake damunki".
Ya fada Yana kokarin Kiran wayar.
Da sauri ta karbe wayar tana fad'in.
"Ni wallahi tsoron gidan nakeyi tunda ka tafi ko kofar dakin Nan kasa fita nayi Ni dai ka mayar
Dani sokoton gara can da nan, kace wuni Daya zamuyi gashi har dare ya kawo jiki muna garin
babu alamar tafiya, Kuma nifa gaskiya hankalina ya kasa kwanciya da abubuwan da nake gani
a tare da Kai,Wai kana nufin wannan mahaukacin gidan ma naka ne, idan haka ne to sai dai
idan kana da wata sana'ar a boye wadda ba kowa ne ya sani ba" .
Mahmud tsayawa kawai yayi Yana kallonta, bil haqqi da iya gaskiyarta take maganar, tsura
Mata idunusa yayi Yana Kara nazarinta, yama rasa Abinda ze ce mata.
Saida ya hadiye wani busashshen yawu Daya kalato daga bakinsa ya hadiye sannan ya Sami
zarafin yi Mata magana.
"Kice ko abinci Baki fita kinci ba kenan? To me kike tsoro a gidan Nan Dan Allah? Gida da
jama'a a kalla sun Mutum talatin Amma Kika takure kanki? Na fada Miki yanzu ma Zan Kara
fada wallahi babu Abinda ze sameki sai ikon Allah Amma Dan mutumci dai Kam kafin ya
cimmiki ya Kai kasa da karfin Allah,wayarawa an zo a duba min ke ance bakya Nan a duk
parlours din gidan, sera tace Sam throughout Bataga ko gilmawarki ba,na shigo Mai makon
special we'll come sai bacin Rai harda hawaye ga zirgina da kika Bari shedan ya sauwala Miki a
zuciya, kina zargin ko Ina kauce hanyar Allah a gurin nema na ko? To Bari nayi sallah na dawo
nayi Miki Abinda Ina ganin kamar ze gamsar dake".
Ya tashi tsam ya wuce toilet ya barta tana shefe hawaye.
A gurguje yayi wanka ya fito baibi ta kanta ba ya Dan shafa lotion ya zura jallabiya ya baza
turarensa ya wuce masallaci.
Itama shiga tayi tayo Alwalarta Bata bukatar wanka Dan wurin biyar da rabi tayi nata da taji
wani Abu Yana fita daga jikinta, ita abun harya Fara damunta ita kadai sai tayi ta mutsu mutsu.
Bai shigo ba sai kusan takwas da kwata Dan harta kwanta suna chart da sajida da Amatu a
group da suka hada mujiba ce Bata online sai Dan biki suke mata data fada musu suna Lagos,
Dan caaa sukayi Mata suna fad'in lallai a samu musu Dan Legos ladar meeting.
Kusa da ita ya zauna Yana Dan leken wayar boyewa tayi.
"Inyeh kice na zage dantse kenan, da Ina Shirin mubi flight din seven thirty,kice na fasa booking
din mu kwankwaje a nan tunda bestie ta zabar Mana nan'.
Shiru tayi masa kamar kurma.
"Ke! Wai Dan Allah me nayi da zafi haka ne? Ki rufa min asiri kada na kasa gane komai, wallahi
kinji na rantse Miki duk abinda Kika gani da Wanda Baki gani ba duk halaliyata ne idan Ina wata
sana'ar da take haramtacciya ko Ina wani Abu daya sabawa shari'a Ubangiji ya....... Da wani irin
hanzari ta toshe bakinsa da tattaussan tafin hannunta tana girgiza Masa Kai, idanunta sun
cicciko da hawaye.
"Wallahi ba Ina zargin kana sabawa Ubangiji bane kawai abun ne Yana bani tsoro, naganka
yaro da Kai Amma ka mallaki Abinda yafi karfin tunanin mai karamar brain irin tawa, amma kayi
hakuri bazan sake maka tambaya irin wannan ba Naga kana niyyar debo rantsuwa kawai Dan
kaga Ina fushi,na fa maganar Dr din Nan ce banaso, Allah da gaske bana sonta har zuciyatw
wallahi".
"Sorry my previous na daina har abada kada ayi min tawaye a gudu Jordan kamar yanda akayi
niyya a can baya saboda ita, da yake Allah ya tarfawa garina nono yasa a ranar naji kamar ana
ingizoni na taho da yake Allah Alhakimu ne Saida aka nemo min ke da tsohon dare danma a
lokacin ba wani caring kawai dai gani Nan ana kallona Ina ragaita ba'a nunawa kurciya baka ba,
tashi muje ki Samar min Abinda Zan saka a bakin salatina kafin nayi aikin bada hakuri kada ayi
min nak'i".
Ya fada yana dariyar Nan tasa Mai sakata shagala da kallonsa.
Itama dariyar tayi tana kokarin tashi tana fad'in "yau dai anyi abun kirki babu 'yan.."
Bata karasa tunanin ba taji saukar hannunsa a jikinta, Batasan lokacin Daya furta "Ashe ba'a
yabon dan kuturu Saiya shekara da yatsu".
"Gaskiya Kam ai kena gani kamar kina bukata ta a kusa dake ko ba haka bane?".
Shiru tayi Masa idan ta biye Masa zeta Bata kunys ne kawai, ta rasa ta Ina ma ya ganota.
Basar da maganarsa tayi.
"Tashi muje kaci abincin kaji meu Amor,.nasan kana Jin yunwa ko?.
"A'a muci dai kema ai bakici ba, tun break din safe". Tare suka fito Yana manne da ita.
"Wai me kike tsoro a gidan nifa tsoron Nan naki Yana damuna kinga duk gidajen ki haka suke
sai dai idan abokiyar Zama kikeso to wannan fa sai ta ringa debe Miki kewa yanda zakuna Jin
motsin juna ai hakan yayi Miki ko?".
Da sauri ya raba jikinta da bass kamar wadda huta ta yiwa shocking.
"Kishiya Kuma? Har ka gaji Dani Nan da Nan haka? Daman abunda kake fada min ba gaske
bane harka Gama Dani Kuma sai wata? Na shiga Tara, Dan Allah Dame na kasa maka ko ba
irin type din da kakeso nake ba"..
Sai hawaye sharrrr.....
"Ya salam.! Previous meya hau kanki ne Wai tsakanin jiya da yau? Wace iriyar magana ce
wannan marar dadin saurare, kece na gaji dake? koko ba irin type din da nakeso ba? Wallahil
Azim ban tab'a son wata mace ba kamarki tunda Allah ya halicceni idan Kika cire uwata to
ba'ayi ba Kuma Ina ganin har abada babu wata mace da zata samu matsayi irin naki a wannan
zuciyar, kin Dade da mamayeta tun ban gama Zama mutum cikakke ba, maganar type Kuma ai
ni har kin wuce sanina wato so kike na nuna Miki true colour dina a wannan fannin ko? Naga
alama kema jirgi Daya ya dauko mu, Bari ki bani abinci mu gani daga Nan zuwa asuba ko mun
Kai ga inda muka dosa inaga da tsarabar Lagos zamu koma SKT, da alamar ma Nan gaba
kadan saina Fara service gaskiya".
Sunne Kai tayi a kirjinsa tana fad'in a'a wallahi bada fa wani Abu na fada ba cewa fa kayi Wai
zaka kawo abokiyar Zama ai kowa yaji yasan banyi maka dai dai bane shi yasa zaka karo
Aure".
"Ya salam! Previous yaushe Mika zama haka Dan Allah? To Bari na fada Miki kinyi min fiye da
tunaninki wato Naga kin Zama sai a hankali ko? Kada fa na Fara guduwa da kafata kisa ace
min ragon miji".
******Tunda su Ammah suka tafi Salma ke aikin kuka, bakin ciki goma da ashirin gana wannan
wulakantaccen Auren gana Makarram ga Kuma uwarta Mai daure mata kugun itama tana wata
uwa duniya da tata lalurar,ga mijin da aka Bata Wanda ta rainawa ajawalin shima ko kyeyarsa
ma bataci arzikin gani ba har karfe Daya na dare ga unguwar irin sabuwar Nan ce wadda Bata
da cikowar mutane, barci dai sai barawo Dan sai ana Kiran sallar asuba ta farka, haka ta wayi
gari kamar mayya ita kadai a gida, sai wurin takwas taji ana buga gate din gidan da farko banza
tayi Saida taji bugun Yana damunta sannan ta fito sai lokacin taga yanda gidan yake Dan Sam
Bata fito ba, Data bude daga cikin kannensa ce mata, ba laifi ita da sauki Bata da halin sauran,
murmushi ta yiwa Salma itama murmushin ta mayar Mata duk da zuciyar ta babu Dadi.
"Sannu da zuwa".
Salma ta fada tana Bata hanyar shiga.
"Yauwa sannu Aunty salma".
Kofar Salma ta rufe suka juyo cikin gidan ba laifi ya tsaru dai dai misali self content ne sai wani
Dan karamin part Kamar boys quater.
Basket din hannunta ta aje ta zauna tana fad'in ga abincin break Nan inji Umma tace a gaisheki
Kuma kada kiga Ya Anas baizo ba Aunty Bara'atu ce bata da lafiya tunda aka fada Mata Ya
Anas din yayi Aure ta Kama Aljanu a kanta aka kwana yanzu ma zasu tafi gumau can Toro
local government gurin mai Magani ance dai ko kwana akeyi a can din yace dai sai sun dawo ze
shigo Nan gurinki yace na zauna na tayaki Zama zuwa dare".
Tunda Hafsa ta Fara rattabo Mata bayani taking wani tashin hankali ya rufeta sai gumin goshi
takeyi, wulakanci dai ta tabbata a Nan ya Gama nunawa duniya ita ba komai bace ita da banza
duk daya, Bata tab'a Jin tayi nadama ba sai yau, duniya tayi Mata juyin waina, ba haka ta
shiryawa rayuwa ba taci buri kala-kala amma karshe ga yanda ta kare, Nan da Nan taji idanunta
sun cicciko da hawaye Bata damu ba da Hafsa da take Zaune kuka ta fashe dashi tamkar
wadda aka aikowa da sakon mutuwa, bare data tuna hotunan da magaji da mujiba suka Dora
na bikin Zahra da irin gidajen da taga ana sabgar a ciki da Kuma gidan da majiba ta Dora
hutunansu tana gani tasan shine gidan Zahra Dan taga magaji ma yayi hotuna a cikinsa.
Hakuri Hafsa da dinga bawa salma Dan ko ita abun yayi touching din ta Dan ance ciwon 'ya
mace na 'ya mace ne.
Abincin dai kasa cinsa tayi Dan dankalin Hausa ne sai kunun tsamiya da jallof din taliya, abunci
dai gashi nan tasan da gangan akayi Mata shi Dan kada ace ba'a kawo Mata ba.
Har dare ya kawo jiki ba Ango ba labarinsa ko Kiran wayarsa babu, Amma dai zuwan Hafsa sai
yasa Salma ta Dan ware suna Hira da Hafsa din tare suka dafa abincin Rana tunda babu
Abinda Abba baisa anyi Mata ba haka Ammah ma tayi nmijin kokarin hada Mata duk Abinda
uwa takeyi, ganin dare ta Fara yasa Hafsa tafiya a tabar salma ita kadai.
Zahra a ranar ta karbi kidan general Dan ta gane shayi ruwa ne Lipton kadai ke canza Masa
kala, Dan babu daga kafa Saida yaga da gaske ta gaji sannan ya kyaleta, Amma dai ya yaba
mata Dan ta shayar dashi ruwan mamaki ta haddace karatun tas har Kari aka samu, Saida
sukayi sallar asuba suka kwanta, Dan migonowa yayi jikinta ya rungumota jikinsa ya furta. "Previous.. wallahi kin gama min komai, Allah ya sakawa Ammah da Alkhairi data Baki tarbiyyar
da tasa aka dunga Adana mun kayana, kin fa bani mamaki, ilove the way you..,kiss, licked my
ears,look at me as you blew me.... Pls tell me who can teached you how to do this special
making love?". Wata kunya taji ta rufeta sunne kanta tayi wallahi ya Sanya jin kunyarsa ba kad'an ba.
Ganin ta qudundu ne kanta a kirjinsa ganin hakan yasa ya Kai bakinsa kusa da kunnenta Yana
hura Mata iska a hankali.
"Please precious tell me what should i do to prepare you for second round?".
"Ya ilahiy! Shike nan ta tarowa kanta match wallahi".
"Ok let's talk about what we can do differently next timeeee..." Ya karasa fada Yana Kara hadeta
da jikinsa.
"Dan Allah ka Bari wallahi nifa kunyarka nakeji".
Wata dariya yayi a hankali.
"Amma yarinyar nan, kin sakani a daki kinata sarrafani kamar zan zauce na haukace shine Zaki
wani rufe Ido kice kina Jin kunya ta tab da kunya ta Kare a duniya".
Saida ya huta yanda ransa keso sannan sukayi wanka, sukayi breakfast sannan ya jata suka
fita Sai lokacin ta karewa gidan kallo ba karya ya hadu iya haduwa Kai da gani kasan gidan ya
lashe mak'udan kudi Dan karshen gayu dai an tanada a cikinsa sun zagaya ya nuna Mata
yanda komai yake sai lokacin taga she ba wani irin Babban Nan bane Dan gidan sokoto ma ya
fishi girma sai dai wannan din ma yaji ababen more rayuwa, da yamma suka fita beach anan
taga yanda Mata ke yawo cikin tubarriji ba kunya ko tsoron mahalicci dole ta matsa Masa suka
nufi irin gurin da ake hutawa, suna Zaune suna Hira duk Wanda ya kallesu Saiya qara kallo,
daga gefensu Zahra kaji ance "Jadida".
Da sauri ta juya tasan ko wacece tare sukayi F.G.G.C KAZAURE da ita Dan yawanci 'yan class
dinsu ke fada Mata sunan wani teacher dinsu Muhammad Naseer mutumin Sudan ya saka
Mata suna a washe garin da aka kaita makarantar yake tambayar ta Ana jadida? Saboda ya
ganta Balarabiya, ai kuwa sai 'yan class suka dauka wasu ma cewa suke Zahra jadida kawai. Ai kuwa tana juyawa sukayi arba da zainab murtala Aliyu 'yar Jos ce amma mazauna Lagos
babanta Dan canji ne.
Da sauri ta karaso ganin da gasken itace ta fada ne Dan tabbatarwa ne kawai rungume juna
sukayi cikin farin cikin ganin juna babu zato,Saida suka Gama murnar su sannan Zahra ta