Showing 36001 words to 39000 words out of 62795 words
Chapter 13 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf
ba, Idan ka tabo shi saiya rama tun Yana
yaro haka yake.
Ba'afi minti uku da gama wayar ba zayyan ya shigo da ledoji guda biyu a hannunsa ya dan
risina Yana fadin "gasu sir".
"Ba kowace ta ta".
Nan da Nan ya cika Umarnin uban gidan nasa, ya aje Kayan da asabe ta kawo na turarikan
wuta a gaban Mama sai Wanda aka karba a gurin asaben dai Wanda ya Zama sanadin da tabar
garin da Kuma tatsar bayanai daga gurinta.
Gasu Nan idan Kuna da bukarsu a gaba saiyi muku amfani, ke Kuma Idan mun fita saiki nuna
Mata wadanda bata kaiga ganinsu ba, Kuma yanzu haka Salma ta sauka a Azare zata amsa
tambayoyin Abba tunda kinqi fad'a masa irin tarbiyyar da kike bawa yaransa".
Bai Kara tofa komai ba ya janyo Zahra suka nufi kofa su zayyan suna take musu baya, suna
Daf da barin dakin suka jiyo kukan Aunty larai tana Fadi "na shiga uku Rabi'a ki tashi"
Shi dai Bai juya ba ya dai nunawa su Sameer akan su koma.
A hanyar su ta komawa ne suka hadu da doctor zainab ta fito daga Gyne emergency.
"A'a wa nake gani kamar 'yata? Yallabai lafiya na ganku da daren nan haka a asibiti daba sai a
kirani ba".
Gaishe da ita sukayi Zahra sadda Kai qasa Dan ji tayi duk kunya ta rufeta, Mahmud ne yace.
"Ba komai doctor munzo gaishe da marar lafiya ne".
"A to Allah ya qara sauki, 'yata ya jikin naki?"
A kunyace tace "jiki da sauki mummy".
",To Masha Allah, Dan Allah ki kiyaye shanye shqnyen magungunan Nan badan jikinki Mai kyau
bane da an samu matsala sosai" .godiya sukayi Mata sannan Sukayi sallama,ta wuce Suma
suka wuce, har sukaje gurin mota babu Wanda ya tofa ko kalma Daya a tsakaninsu Dan ita
Zahra ji tayi tana wata shakkarsa Bata taba zaton ze iya shafawa idanunsa toka yayi irin
wannan rashin kirkin haka ba.
*_ AUREN HUCE HAUSHI_*
AISHAT ISAH MUSAH
(Maman Fateemah)
09061432330
08055362975
Page 91
_________ Tunda suka dauki hanya yake sharara gudu sabanin dazu da suke tafiya a slow,
taso tayi Masa magana to ganin Yana yinsa yasa tayi shiru ta zubawa hanya idanu, zuciyar ta
fal da mamakin rashin kirkinsa Daman haka yake?.
Har suka shigo rukunin gine-ginen unguwarsu Bai tanka Mata ba Saida sukazo dai dai wani
gida Mai farin fenti da ash colour sannan ya Dan juyo ya dubeta, "Kinga gidansu dodanniyarki
Nan".
"Wacece Kuma dodanniyar tawa a garinku nida ko one week ban cika ba a garin da har zanji
tsoron wata".
"Dr Haseenah ba dodanniyar ki bace?".
"Allah ya sauwak'e wallahi meye abin tsoro a tare da wannan Mai siffara mazan, mace ba gaba
ba baya, Kace 'yar garinku?".
Ba zato taji ya fashe da wata dariya Yana duka sitiyarin motar da hannunsa.
"Amma wallahi kin cuceta, tana ganinta Mai zafi Amma ke kina siffantata da maza".
Hannu ya Kai ya Dan shafi gefen cinyarta "ba wannan ko?".
Dan zumburo Baki tayi tana matsawa "to karya naji Kai idonka baya gani, wallahi har naji bana
son unguwar".
"Kai! Kuji mu da yarinya haka kike da kishi? Kince kin tsani Kano Kuma my home city din ma sai
Kice Bai Miki ba saboda kishi,to Yaya zamuyi dake idan Zan kawo miki 'yar buzuwata diyar
Mama filani, Dan ta kirani mun zauna tace idan kin kwana biyu kin Zama 'yar gari ta bani Insiyya
in Kara da ita Wai Daya tayi min kadan". Wani irin kallo ya zuba Masa da sexy eyes dinta.
"Ki rufa Mana asiri mu karasa gida lafiya,kada kisa a tashi damu a social media ace Amare
sabbin Aure sun rigamu gidan gaskiya a sanadin hadarin mota suna tsaka da cin amarci".
"To Ni menayi,?".
Ta qara kada Masa idanun tayi, wani smile yayi.
"Naga alama wannan kin wuce tunanina Bari muje gida kiyi min bayani da yaren da zanfi
ganewa tunda kin Fara Zama 'yar hannu".
"Meye kuma 'yar hannu?".
Dariya ya qara yi "kije ki tambayi hausawa".
Ya fad'a Yana saka signal na shiga wata kwanar.
"Ina Kuma zamu? Naga ka shigo wani gurin nifa barci nakeji".
",Fadi gaskiya dai yarinya, ko dai...?.
Rufe fuska tayi da tafukan fararen Sol din hannuwanta Wanda suka Sha lalle.
Wani irin kyau tayi Masa ba kadan ba.
"Kunyar wa kikeji a Nan?".
Dai dai lokacin da taji ya Danna horn Sau biyu abinda ya tilasta ta bude idon ta kenan.
Budewar idanunta da bude gate din sai suka Zama kusan lokaci daya.
Hannu kawai ya dagawa securities din yayi gaba, wasu gine-gine ta gani masu azabar kyau ga
titi Nan dodar sai haske kamar Rana ga flowers Nan masu kyau an qawata gidan dasu, Bata
ankare da Ina bane Saida taga sun karaso main ginin da aka kawota ciki, Bata tab'a zaton
girman gidan da Hajiya Inna take fad'a ya Kai irin haka ba,to ai wannan sai a dafa mutum a
cinye na wancan gate din ma basujin ko labarin ba, parking lot na motocin gidan Wanda suke
tamkar kamfanin siyar da motoci ya nufa da alama ba 'yan milkin bane a kansa Dan tana ganin
yawanci sai dai a shigar da Masa da ita ciki.
Kallonsa take galala Kamar wata 'yar kauye.
"Lafiya irin wannan kallon haka? Duk gidanki ne gate uku gareki dayan sai kin kwana biyu kin
warke tas mu zagaya kiga inda yake, gasu Nan compartment compartment sai inda kikeso Zaki
zauna".
"Ko dai zamu zauna ai Ni Kuma na Gama shiga taitayina nasan wannan gidan mace hudu ne
wata kila harda kwarkwara ma tunda da abun".
Bai tanka Mata ba ya bude ya fito, itama ta fito tana Kara waiwayen hanyar da suka biyo sai
yanzu ta Kara karewa gidan kallo, ita abin yafi karfin sannin ta gaskiya da data ambaci tsoro
Ashe ba tsoron takeji ba sai yanzu.
"Oya let's go".
Ya fad'a Yana janyota jikinsa "Wai tunanin me kike ne haka Kona Dr.din ne?.
"Dan Allah ka daina fada min sunanta".
"Tona daina muje kiyi min wanka kiyi min tausa yanda zanji Dadi Baki labarin nawa wata Kila
mu gama zuwa asuba".
*********Tunda su Abba suka sauka a Bauchi yake Kiran wayar magaji Amma amsar Daya ce
not available, malam Bala ne yaje dauko su tare suka taho dasu Aunty Hassana da Inna
mainuna da Hameeda. Dan daga gidan zahrar airport suka wuce inda suka samu su Aunty
Hassanar, tunda su Abba suka baro gidan Zahra Bai Kara kallon Hamza ba Dan idan ya dube
shi ji yake zuciyarsa tana wata irin tafasa, Bai tab'a zaton haka daga gare shi ba, yayi zaton
hankalinsa da tunani sun wuce haka kenan da hadin bakinsa aka munafurce shi anyi masa
lullubin biri.
Karfe biyar saura suka shiga cikin garin Azaren katagum.
Gidan shuru kamar babu mutane a cikinsa su Aunty Hassanar suka shigo, parlourn Ammah ba
kowa sai kamshin turaren daki Dana girki Daya cika shi.
Saida Aunty Hassanar tayi sallama sau biyu sannan Alawiyya ta fito daga kitchen tana amsa
sallamar tare da fadin
"Lah Aunty, Inna sannaunku da zuwa mutanen sokoto ya hanya?".
"Hanya Alhamdulillahi mun dawo lafiya, ya muka sameku?".
Inna maimuna ta fad'a tana zama a Kan two seater.
"Lfy kalau Inna ya aka baro Amarya? mu ai mun tsufa a gida, Ashe Mama bataji Dadi ba a
can?".
"Wallahi kuwa jiki kam babu Dadi tunda har za'a fita da ita can misira".
"Allah ya Bata lafiya, sannu Hameeda ya Mai jikin?".
"Jiki da sauki Alawiyya nagode".
Ammah ce ta fito daga cikin corridor din bedroom dinta.
"A'a Masha Allah! Inna sannunku da hanya, ai tun dazu nake zaman jiranku da naji shiru Baku
karaso ba na shiga daki gurin wayata da ake Kira".
Abinci Alawiyya ta kawo musu da drinks.
"Waini Hajiya Ina su Hanifa ne naji gidan shiru alhalin an bar Miki 'ya 'yan Amana".
'yar dariya tayi "suna gurin Babansu tun safe dayazo gurin Abba suka tattara suka bishi".
Aunty Hassana Yi mamaki ba Daman tasan za'a rina Banda ta taushesa da kalamai masu dadi
cewa yayi sokoton ze biyota ya gaji ta barshi ba matallafiya. Gaishe da Ammar tayi ta tashi ta
shige ciki ta barsu da Inna suna Zaune suna Kara jajanta jikin Mama yayin da Hameeda ta nufi
nasu part din ta aje luggage dinta da sauran tarkacenta na biki da aka basu. Kiran sallar magariba ya tashe su daga hirar da Inna ke yiwa Ammah na irin daular arzikin da
Allah ya Kai yarinyar su wadda ko a mafarki Basu tab'a zaton hakan ba.
Suna sallah sukaji kamar hayaniya daga parlour da sauri Aunty Hassana ta fito tana fadin.
"Menene haka nakejin hayaniya?".
Ai batasan lokacin daka kwalla Kiran" Daddyyyy....ka Bari wayyoooo Allah Ammah ku fito za'ayi
kisan Kai a gidan Nan".
Da gudu ta karasa gurin dasu Ya imam da ya Abdul Hakeem keta kokarin banbare hannun
Abban daga wuyan Salma wadda take wani irin kakari kamar na fitar Rai.
Magaji ne ya shigo da gudu baiyi wata wata ba ya girgije Abban ya raba hannunsa da jikin
wuyanta ya dauketa cak kamar yarinya yayi Kan three seater da ita Yana fadin "ku bani
ruwaaa..". Da gudu Aunty Hassana ta shige kitchen dauko ruwan sukayi kicibus da Alawiyya ta
nufo parlourn da gudu da ruwan hawaye na bin Kumatunta. Da kyar su Abdul Hakeem suka zaunar da Abban sai huci yake Yana fadin.
"Wallahi banga amfanin haihuwar ki ba Salma kinci mutuncina kin tozartani kunci amanata keda
uwarki da Dan uwanki, damena rage ki? A gidan Nan abinda kukayi min na barku da Allah sai
munyi shari'a da Rabi'a a gaban zatin Allah, Kuma a gobe ba jibi ba a gidan miji Zaki kwana ko
wanene, Kuma karatu kin Gama a gidana har abada, itama Hameeda su kawo sadaki ko Bai
Gama gidan ba ya zaba cikin nawa su tare".
"Haba Alhaji idan Rai ya baci ai hankali baya gushewa kada a hau dokin zuciya sai ayi aikin
Dana sani, ka Bari abi komai a sannu Allah zeyi maganin komai,kowa da irin jarabawar da
ubangiji keyi Masa, wasu ta 'ya'ya wasu ta dukiya wasu ta lafiayrta jiki ayi hakuri dan Allah ka
taushi zuciyarka kada kayi aikin Dana sani". Ba zato sukaga hawaye ya zubo Masa abinda Ammah Bata tab'a gani ba kenan duk iya
zamansu, sai itama nata Hankalin ya ninka na dazu tashi ta matso kusa dashi tana fadin.
"Dan Allah Dan darajar Manzon Allah kada ka Zubar Mata da hawaye kayi hakuri kamar yanda
Inna ta fada abi komai a sannu sai kaga an samu masalaha a Kai".
"Haba Asma'u wane irin tashin hankali ne wannan ace Dan daka Haifa kake lokarin Kare duk
wani haqqi nasa da ubangiji ya Dora maka, amma a ce an wayi gari ya kangare ya Zama fasiqi
duba medical report din Nan ki gani"..
Ya Mika Mata takardar dake cukuikuye a hannunsa.
Jikinta na Bari ta shiga warware takardar,bayani ne tiryan tiryan na adadin cikin da aka Zubar a
baya da nasu bincikrn da sukayi da tambayoyin da likitan yayi mata da Kuma irin matsalar da
aka Samu garin Zubar da wannan cikin.
Zuface keta ketowa Ammah ba qaqqautawa, wannan wace iriyar masifa ce a gidan Nan?.
A hankali ta furta "innailaihi wa inna ilaihi raji'un".
Ta manta dasu Inna da Yara ma a gurin ta zauna kusa dashi daf tana shafe hawaye..
"Kayi hakuri Abban Yara kowa da tasa' jarabawar Kai taka a haka tazo ka karba kayi hamdala a
kowane yanayi sai ubangiji ya saukar maka da Rahamarsa"
Su Abdul Hakeem ne suka Fara fita kafin inna ma ta koma daki,Alawiyya ma ficewa tayi daga
part din gaba daya, ya rage daga Salma dake mayar da nunfarfashi ruwan hawaye na Mata
anbaliya ba sassauci,sai Kuma su Aunty Hassana da magaji sai Kuma su Ammar.
Ban Baki Ammah ketayi akan ya janye furucinsa Amma ya kafe ba canji.
"Haba Asma'u karuwa a gidana,a cikin 'ya'yana, wace irin masifa ce wannan, Kuma Dan
yayarta uwa daya uba Daya ace yayi min irin wannan abun su kansu Dame na ragesu Banda
tambadaddune sunki karatu sai sakarci, da sun msayar da hankali da yanzu Basu Samu tudun
dafawa ba? Ina cewa tare suka Fara karatu da imam ba ya kasa akayi withdraw dinsa daga
makarantar, to Aure babu fashi Kuma kowaye na samu saina aura Mata shi in Sha Allah.
Su Aunty Hassana suka shiga da Salma dayan bedroom din Ammah tana ta rusa kukan da
baya fitowa.sabida wahala ga zafin ciwon da Bata Gama warwarewa ba.
Abban ma bangarensa a part din Ammah suka nufa da kyar Ammah ta lallashe shi yayi wanka
ya Sha tea kawai ta bashi pcm ya sha, saida ta saukar da fushinsa Mai zafin sannan ta fito ta
nufi parlour lokacin wurin Tara da Arba'in da biyar na dare
A Nan ta iske magaji da Aunty Hassana wadda har lokacin Bata tafi ba, dan Ammar cewa tayi
magaji kada ya tafi ya jirata a nan.
Fuska babu annuri Ammah ta karaso inda suke Zaune.
"Me kayi kenan sulaimanu? Ka kyauta kenan ka hada tashin hankalin mutane banda Allah ya
tsare me kake tunanin ze faru? kasa ayi Mana kisan Kai a gida, to kaji Dadi hankalinka ya
kwanta wato Kai koje sarkin labari ko Kuma suda Mai bakin magana, to kaji dadi ka hada
husuma saika zuba ruwa a qasa kashe burinka ya cika Abbanku ya sani sai me kuma?". "Kiyi hakuri Ammah wallahi gani nayi idan nayi shiru naci Amanarsa yanda yake tsaye a kanmu,
Kuma ni bada gulma na fada Masa ba kawai dai nace Naga sun fita ta baya da asuba tare da
Ya Hamza Mama ta rako Salman tana kuka, daga Nan ban qara ce masa komai ba, bansan
Wanda ya fada Masa sauran zancen ba, sai dazu da safe yace min sunyi waya da Ya Mahmud
yace Zan raka Bilyaminun gidan Baba Malam Jos, shine fa muka tafi a hanya Ya Mahmud din
yayi min text message na inda Zan raka Bilyinun da address din asibitin da zamuje da number
likitan da zamu nema, wallahi Ammah ki yarda Dani bansan gurin waye zamuje a Jos din ba
Saida likitan da muka samu yayi Mana jagora zuwa dakin da take sannan Naga itace, Ni kaina
mamakin abin yaki bani to meya hada Salma da Ya Mahmud Taya akayi yasan halin da ake ciki,
nayi tunanin ko Zahra ce ta fada masa sai Kuma nayi tunanin ai Nima fada tayi lokacin Dana
fada Mata".
Nisawa Ammah tayi tana jinjina maganganun magajin, haka Aunty Hassana ma.
"Allah ya kyauta ya rufa asiri, Amma abin da mamaki dai gaskiya".
Dan murmushi Aunty Hassana tayi. "Babu mamaki wallahi Ammah, wannan mijin na 'yarki ba
karamin mutum bane ni lamarinsa ya daina bani tsoro idan akace miki yasan abinda mu Bamu
sani ba a cikin gidan Nan kada kiyi mamaki Dan Naga Bai dauki Lamarin 'yar Nan taki da sauki
ba ze iya yin komai saboda ita kina jifa tun zuwan su Zahra Jordan ita da Abba suke bibiyar
yarinyar nan".
Tashi magaji yayi Yana fadin "Allah ya huci zuciyar sirikar masu abun, nifa yace can Zan koma
kusa da Zahra tunda Aminiya ta ce, Ina ga fa hijira lahu ta tabbata a gareni, Idan kin shirya
Aunty ki fito na kaiki gida".
",Kai dai Allah ya shiryeka wallahi gidan kanwarka zaka tafi ka tare saboda abun kunya gaba ka
bashi ba baya ba".
Aunty Hassana ta fada.
Dariya yayi kawai ya fice.
*******
Zahra na kwance tayi pillow da cinyar Mahmud bayan sunyi wanka Yana tunke Mata gashin
kanta Daya zare Banda din yana fadin "precious kinsan Allah na yarda da abinda Hausawa ke
fadin ta ciki na ciki ta baka na baka, Naga fuska biyu muraran, Bari na dauko Miki abun daga
tushe yanda Zaki fi gane abinda za fada Miki".. Gyara kwanciya tayi tana facing dinsa shi Kuma Yana Wasa da wani zare da ake daure gaban
rigar barcin dake jikinta Wanda shi kadai ne ya rufe gaban rigar.
"Sunana Mahmud Muhammad Dange mahaifina general Muhammad Dange Dan asalin garin
Dangen shuni ne, local government ce Mai zaman kanta a Nan sokoto, mahifinsu Abbie
sunansa Alhaji sa'idu jibrin Dange Mai kudine na gasken gaske su goma Sha hudu ne a gurin
mahaifinsu goma uwarsu Daya ubansu Daya sai Sa'id shi kadai uwarsa ta Haifa ta rasu sai
Kuma Halisa itama uwarka ita kadai ta Haifa Amma ita uwarta tana gidan, sai Allah ya sakawa
Alhaji jibrin tsananin soyayyar sa'id tunda yaro ne mai hakuri da wuya ya Fadi anyi masa Abu
Saidai idan Alhajin ya gani ya tsawatar, ko a harkar kasuwa Alhajin yafi son ya tafi da Sa'id ko
gidajen man petrol dinsa ze je to da said yake tafiya abinda ya kawo rashin jituwa kenan a
tsakanin Sa'id da 'yan uwansa, sannu a hankali Sa'id na bin Alhajin guraren cinikinsu har Allah
ya hada sa'id da wani Alhaji sani gada,Wanda shine sila ta samun asalin dukiyar data yad'u har
jikoki, Dan tankar Mai ya Ringa sauke masa yana bashi a kan farashin kamfani, kafin wata
shida jari ya kankama, kafin shekara sa'id ya hada jari na ban mamaki.
Ganin haka sai 'yan uwansa suka huro wuta akan kasuwarsa.
Sa'id Bashi da tsoro ko alama haka akayi ta juyawa da :yan uwansa.
Zuwa lokacin da zasuyi Aure shi sa'id Allah ya hada shi da Hadiza 'yar Asalin kwantagora ta
jihar Niger.
Cikin ikon Allah 'yan watanni kalilan ciki ya bullo jikin Hadiza sunyi rainon cikin tare, Dan Allah
yayi shi mutum ne Mai son 'y'y ga tausayin mace gashi daidai k
Lokacin arzikinsa sai Kara habaka yake, abinda ya tsone idanun 'yan uba kenan duk da kowa
da nasa rufin asirin sosai tunda Allah ya saka Albarka a cikin neman nasu Amma saboda sa'id
ya Zama zakaran gwajin dafi sai yafi tsaya musu a wuya sosai gashi matarsa Hadiza Bata
daukar raini