Showing 42001 words to 45000 words out of 62795 words
Chapter 15 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf
ce.
Lokacin Dana tashi zuwa Niger taso ta bini na hanata har gurin Abbie ta Kai karata nace masa
bazanje fa da ita ba dole ta hakura.
A haka Muka share kusan wata hudu a gida ana ta processing na admission din mu inda Abbie
ya hada harda Sameer ya Samar Mana a Oxford university ta London inda Aishat suka Bata
physiology Ni Kuma business administration inda Sameer yayi Accounting, anan muka hadu da
Mutuniyarki Dr Haseenah inda ita Kuma take medicine 'yar abokin Abbie ce tun haduwarmu ta
farko ta ringa nuna min sign na soyayya Ni Kuma saina basar saboda Sam Bata cikin tsarin irin
macen da nakeso, faruq sun bashi pharmacy haka mukayi ta karatu babu Kama hannun yaro
ga Kuma Mr Johnson a gefe Yana kula damu, ba kowace semester ba Mike zuwa gida Muna
level two hundred ne Akayi bikin Aishat Dan Kanwar Abbie na biyu Kinsan shi ya Abbas lokacin
shima Yana PhD a Nan Auren Aishat ya taimaka Mana kwarai da gaske Dan abubuwa da yawa
sunyi min sauki tunda Ina da gurin da inda zan aje abubuwana safe.
Idan anyi hutu ban fiye zuwa Nigeria ba sai idan Hajiya Inna ta matsa,a kwai zuwan da mukayi
nida Sameer nayi mamakin girman Safna ta Zama budurwa sosai, lokacin hatta abincina ita
take dafa min Bata gajiya da Yi min hidima Saidai idan ban bukata ba haka mukayi ta rayuwa
idan na dawo mu dinke idan Ina can muna waya Idan na samu sarari, muna shekarar karshe ne
munzo hutu lokacin na Dan Fara gwada business zamuje Istanbul ganin wasu Kaya da nayi
magana da kamfanin ta website dinsu a ranar na Fara ganinki keda Abba kina Masa tabara da
girmanki Wai Baki son seat din da kike kinfi son saitin window, kin tuna wani yazo yace Miki kije
gurinsa ki zauna shiya zauna a naki gurin Yana sanye da facemask?".
Gyada Kai tayi alamar ta tuna "to nine".
Gyara Zama tayi tana kallonsa "shifa wancen yaro ne ba kamarka yake ba".
"Kin jini da yarinya to ke lokacin Yaya kike?"
Zan nuna Miki hoton ki gani, Kinsan a ranar Saida Sameer ya biku tunda yaji Abban na fadin
Jordan zai kaiki hutu shi Kuma ya wuce saudia.
Sameer na biye daku har Saida ya tabbatar da inda kujene sannan ya dawo mukayi abinda
zamuyi muka wuce London, haka muka ringa juyawa karatun da Dan kasuwanci.
Wani hutun da mukazo harda Aishat mukazo lokacin tana da cikin farko na yarinyar data Haifa
ba rai.
A hutun ne Ubangiji ya bude min kofar nawa arzikin Dan Ina sokoto uncle Ishaq ya kirani a
waya yace min ga condensed milk Nan wani abokinsa yayi order dinta Kuma kafin ya Kai
kasuwa wasu Kayan nasa da sukafita mahimmanci suka shigo shine yake son ya sayar dasu a
tsaye shine ya bani rancen kudin idan an sayar na maida masa da kudin. Kamar wasa aka kawo Madarar da Sameer muka shiga kasuwa muna yiwa mutane talla kafin
sati Daya gaba Daya ta kare sai Kuma costumes ta ko Ina ana booking dink Kayan nan da nan
uncle Ishaq din yayi magana da kamfanin suka saya lokacin harda powder milk yayi order shi
yazo har Nan sokoton ya Kama min store sai daga baya Alhaji kakana yayi ta fadan Dan me
za'a Kama hayar store Alhalin gasu Nan kamar banza hakuri uncle Ishaq din ya bashi yace
saboda kada abun ya Zama fitina shi yasa Amma idan kudin sun kare ba za'a sake ba.
Kafin wani lokacin abubuwa sun bungasa Kota Ina kudi shigowa suke Nan da Nan jari yayi karfi
na ban mamaki, da kyar muka koma london saboda kasuwa ta kankama.
Cikin ikon Allah muka Gama jarabawar lafiya muka tattaro muka dawo aka Dora daga inda aka
tsaya, lokacin su Aishat suka koma India da zama.zuwa lokacin munyi wata irin shakuwa da
Safna komai ta nema take zanyi Mata tunda kudi dai Allah ya hore,da taimakon uncle Ishaq
muka dunga fita kasashen duniya sawo Kaya da bada aiki a kamfanoni. Kafin shekara biyu Ni kaina bazace ga abinda na mallaka ba lokaci Daya saida muka bude
kamfanoni a cikin gida da manya manyan stores na Kayan abinci yawanci a states din mu na
arewa muka Fara muke diban yaran mu na gida muke Kaiwa suna aiki sayar da Kayan mukayi
musu tsarin kamar makaranta Dan harda Mai gadi idan suka dawo daga sallar insha'i Kuma ba
Mai fita Saida lalura saboda yanda zamani ya Zama abinda ya Zama.
A cikin shekara ta hudu ne komai ya fito Dan lokacin ne aka bude kamfanin riguna abaya a
Dubai da materials da laces na garari aka bude na jewelry a India sai wasu Kuma a China
wallahi precious Ni kaina bansan ta ina na samu wannan dukiyar ba nasan dai condensed ce
sanadin. Kinsan har lokacin Sameer Yana bibiyar min ke duk inda kikayi makaranta Ina da masaniya ke
har korar masu son Aurenki gaskiya mune Abu daya ne bamu da Hannu na yaron Nan Dan
uwan momin Kano shi ne dai bansan inda aka haihu a tagayar ba.
Wata zabura Zahra tayi, janyo yayi jikinsa.
Wata ranar lahadi Ina Zaune a gurin da aka tanada Dan hutawa Ina ta faman aiki saiga Safna ta
nufo inda nake da system a hannunta, tayi kwalliya sosai tunda Ni kaina nasan Ina Mata hidima
Dan duk abinda na bawa kannena to tare nake Basu da ita Dan irinsu kudi ma saina Bata sau
biyar ban Basu sau Daya ba. Sannu Tayi min tana zama daf Dani har breast dinta Yana Dan tabani, ta tashi daga gurin nace
Mata saita shagwab'e fuska tana fadin Dan Allah na barta ta zauna kusa Dani wani Abu Zan
nuna Mata, kamar rufin Baki saina kasa musa Mata cikin Jin Dadi ta furta Thank you dear.
Wani website ta shiga ta Fara nuna min wasu tsala-tsalan sarkoki na gold masu Azabar kyau
tana fadin na tayata zabe Wai Aunty Sameera ce zata saya Mata Wanda zata saka tanar bikin
kawarta 'yar ministern Albarkatun kasa, ba zato mukaji salati daga bayanmu da sauri na juya sai
Naga kawu saminu Yana tafa hannu Yana fadin wane irin rashin mutumci ne haka da yammacin
Allah wata'ala na shigewa yarinyar daba muharramata ba irin haka Ashe Nima lalataccen ne.
Saboda bakin ciki ko kallonsa banyi ba na dauki wayoyina nayi gaba, ko akan wani bana son a
jefe shi da kalmar Nan bare Ni a kaina.
Ina gurin Ammi sai gashi ya biyoni Nan muna Zaune ya shigo Yana huci Yana fadin har yaushe
nayi arzikin da Zan wulakantashi Yana min magana kada na lalata yarinya tunda giyar nera na
dibata shine nayi tahowata na barshi ga banza.
Hakuri Ammi ta bashi ya juya ya fice Yana kananun maganganu.
Fada sosai Ammi tayi min lokacin tace kada ta Kara Jin makamanciyar irin wannan magqnar a
gidan Nan idan son yarinyar nake ayi magana ita Bata son kananun maganganu, na fada Mata
babu wata soyayya a tsakaninmu da safna.
Abu kamar ya wuce da dare saiga Kira daga Abbie a waya naje Yana nemana.
AUREN HUCE HAUSHI
AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateenah
BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM
Page 92.
_______Ba bata lokaci na shigo mota ni da Abubakar muka nufo gidan ban shiga dakin kai
tsaye ba tunda naga kusan takalman mutum biyar, ina nan tsaye saiga uncle mustapha ya fito
yana waya saida ya gama ya karaso inda nake tsaye yake tambayata meya farau tsakanina da
safna ban rufe masa komai ba na fada masa duk abinda ya faru, girgiza kai yayi kawai cikin
bacin rai yace na koma kawai ba saina shiga ba, haka na juya ba musu na nufi mota muka fice
daga gidan, ni dai bansan yanda suka kaya ba tun daga lokacin wata magana bata kara tashi
ba amma na janyewa safna sosai sai abinda baza'a rasa ba, amma dai ban fasa yi mata hidima
ba duk abinda zanyiwa su yaran gidan babu bambanci da ita wani abun ma sai nayi mata ban
yiwa su Batool ba tunda Aunty sameera samunta bai kaina su Ammi ba tunda suna business
sosai ita da momin kano.
Wani sabon salon da safna ta dauko kuma na zuwa part dinmu wai zatayi min gyara ko kuma
ta dafa abinda tasan shine favourite dina ta dauko ta kawo min, nayi nayi ta bari amma saita
ringa min magiya akan ita bada wata manufa ba takeyi, wannan yawan shige min din da tajeyi
saiya kara mana shakuwa da kusanci sosai har ya kasance wata rana Dana dawo da dare na
sameta tana barci a dakina sai abin ya daure min kai na juya na futa daga dakin na shiga part
din Abbie na sameshi shida uncle mustapha saboda tare muka shigo gidan, kiransa nayi muka
fito tare kafin na kaiga yi masa bayanin komai uncle saminu ya nufomu afujajan yana fadain su
dai an haifo musu masifa a cikin zuri'a daman duk namiji mai aure aure hakance ke faruwa to
azo aga ga yarinya can a dakina na gama lalata da ita.
Wani wawan Mari uncle mustapha ya sauke masa yana fadin ban taba sanin kai mahassadi
bane kuma masharranci sai Yau wallahi ka guji Fushun ubangiji a kanka yaushe ka zama haka
haba ka rasa Wanda zaka ringa jifa da qazafin Zina sai dan zumunka kabar jaki kana dukan
taiki, me yaron nan ne ya tsare maka? kullum idanunka da bakinka basa nufin alkhairi a kansa,
to ka sake wata dabarar wannan batayi ba tun nagariba muke tare dashi a mabera sai yanzu
muka rabu ya nufi nasu gurin Nina na shigo kiran da Alhajin yake mini,ko maganar bamu fara
ba ya shigo ya kirani kafin ya kaiga fada min dalilin kiran kazo kana yiwa mutane shirme da
girmanka da komai to kaddara ma abinda kake fadar gaskiya ne bazaka iya daukar matakin da
saidai a wayi gari a ga ka dauka ba,amma ka zama jakadan yada munafurci da son hada
husuma ka yiwa kanka fada wannan ba rayuwa bace,ka bawa shedan dama yana walagigi da
kai haba meka nema ka rasa da har samun dan cikinka ze tsone maka idanu ne ayeh?.
Tunda uncle ya shara masa Mari ya dafe kunci bai kara dago da Kansa ba, bai kuma kara tofa
wata ba yayi min wani kallon qasqanci yayi gaba, tsaki uncle mustaphan yayi yana fadin
wahalallan banza Wanda hassada ke dawainiya dashi, gurina ya juyo yana fadin kayi hakuri
Mahmud kaji babu wani Abu na batanci daze sameka in sha Allah, lokacin na fada masa safna
Dana gani tana barci a bedroom dina, yayi mamaki kawai da gaske tare mukaje amma abun
mamaki bata dakin ko alamar mutum ya kwanta a gadon babu, dan murmushi yayi kawai ya
juya yana fadin take care.
Wallahi a Daren banyi barcin kirki ba saboda damuwa na rasa mena tsarewa uncle saminu ne
yake bibiyata da irin wannan Abu na bacin suna? Sai kuma zargin da hadin bakin wani ake min
wannan bita kullin.
Naso na fadawa Ammi amma saina share, amma naje har part din Aunty sameer, tana ganina
ta tarbeni da murnarta asual muka gaisa kafin nayi korafin abinda ya kawoni Auntyn ta rigani da
fadin kasan kuwa jiya mutuniyar a dakinka barci ya dauketa tana jiranka wai tayi maka coconut
drink ta zauna zaman jiranka saida naga shirun tayi yawa na tura safara'u yarinyar da take min
aiki ita ta taso ta, ai kuwa nayi mata fada sosai irin haka ai sai zargin wani Abu ya shiga dan
haka nace ta saina shiga part din tunda duk maza ne, wallahi precious duk saita daureni da
jijiyoyin jikina na rasa abin fada haka nan na fito daga part din nata.
A cikin satin tafiya ta samemu nida sameer muka tafi, a lokacin shares na saya a manyan
kamfanin motocin duniya na zuba large share sosai a lokacin ne na canzawa kannena mata
sabbin mitoci abinda ya ruda da yawa daga yara mata na family din mu 'ya'yan da iyayen
sukayo min caaaa da kowa burinta ace muna tare da ita sai kuma safna ta fara fuskantar yan
hamayya daga cikin dangin saboda ta saje da yaran gidan babu bambanci.
Lokacin da muka dawo ne aka fara magabar bikin Gambon mu Khadija wadda ke Germany.
Aishat ce ta bani bill na duk abinda suke bukata ni kuma na bawa sameer nace yaji dasu, sun
kace raini a bikin nan dan komai unique Aishat ta sawo musu a Dubai da sukaje tunda dai kin
ganta 'yar gayu ce ta bugawa a jarida kuma duk abinda ta sawo babu bambanci tare da safna
tayo shi hatta da gold na mahakatan kudi saida aka sawo da ita. A wannan bikin ne idanun safna suka bude fiye da dah, ta zama babbar yarinya tayi sabbin
kawaye tunda ta shigo gari ga motor ta alfarma tana shiga ga suturu na kece raina ga 'ya'yan
banki basa mata wahala.
A cikin wata hudu tayi wani irin fice a sokoto sai kuma lamarin ya zama marar tsabta ta shiga
sabgar samari 'ya'yan Hutu, koda yaushe bata zaman gida ga yawan kawo samari gida
barkatai, sabanin yaran gidan,dana samu Ammi da maganar ta takamin burki tace babu ruwana
ai mai gidan da sauran yayuna suna gani, haka na zuba ido ina kallo amma bana jin dadin abun
ko banza ina kaunar safn tunda zuciya tana son mai kyautata mata,amma dole na dauke
idanuna nayi kamar bana gani mataki daya na dauka kawai na saina daina shiga sabgarta na
daina tura mata kudin da nake tura mata special na daina mata komai hatta da tsaraba idan
nayi tafiya na Dawo wadda sameer ke assasa ayowa yaran na fada masa a daina yi da ita,
abun saiya dameta ya tada mata hankali duk yanda tasan zatayi mu hadu ma nayi blocking
dinta.
Previous Ashe wannan matakin shine ze zaman mafarin faruwar Marsalar shine zaren da aka
kulla kaddarar tawa dashi. Ashe shine sanadin da za'a samu sabani mai girma Wanda yasa
mahaifiyata barin gidan aurenta na tsawon watanni ya dagula rayuka da yawa ya kawo sanadin
da aure ya mutu murus.
*_ AUREN HUCE HAUSHI_*
_AISHAT ISAH MUSAH_
Maman Fateemah
Da sunan Allah mai Rahama Mai jinqai salati da Daukaka da Aminci su tabbata ga shugaban
mu Annabin Rahama Muhammad s.a.w.w.
Page 93.
_____ Precious wato Ranar wata talata 1/6 ranar da ta Zama baqar Rana a gareni da duk wani
Mai kaunata, ranar da aka sak'a zaren mummunar kaddarata ranar data rikita Mana zaman
lafiya ta Zama ranar da wani ko wasu suka dagula lissafin mahaifina ya Zama sai yanda akayi
da shi dama duk wani Mai fada aji ya Zama soko marar katabus. Tunda na tashi da misalin hudu da rabi na asuba yanda na Saba Sam najini a wani yanayi Sam
banajin Dadin jikina ga faduwar gaba wadda da ita na tashi har nayi nafilolina na wuce
masallaci gani Nan dai, sai da nayi karatun Qur'an sannan na samu relief na faduwar gaban, a
ranar ko breakfast kasa fita nayi sai Sajjad autan momin Kano ya kawo min tunda Ammi Bata
barin yaranta Mata shigowa part din mu ko Mai aiki Bata Bari su shigo gyaran part din ma maza
ne keyi Kuma ko su zayyan basa shigowa gidan suna waje Bata hana suyi min aiki ba Amma
Banda shigowa gida.
Haka na zauna Ina ta juye-juye a gado na rasa me yake min Dadi ga Sameer lokacin ana ta
shirye-shiyen bikinsa a yanda mukayi ma a ranar Zan shiga Kano Dan na tura su naseer a
sakawa gidan Dana Gina Masa furnitures tunda komai yazo, ban fito ba sai lokacin sallar
Azzahar daga masallacin bangaren Ammi na wuce Ina Nan har la'asar tayi tambayar duniya
akan meya sameni amsar Daya ce nake Bata ba komai, haka ta hakura ta kyaleni Amma itama
sai Naga ta rage walwala.
Daga sallar la'asar ban dawo gidan ba Saina wuce mabera gidan Hajiya Inna a can na zauna
nayi ta aikina har kusan Tara da rabi, nida zayyan ne kawai muka taho shiya tuk'o motar Sai
goma muka shigo gidan saboda mun tsaya an sawo fruits saboda Dana shiga kitchen Naga
sauran kadan Dan Apple da pear ma babu, ban shiga part din Ammi ba Amma na Kira su
Batool nace suzo su shiga da kaya ciki.
Zayyan ya wuce Nima na shige ciki Dan har lokacin ji nake kamar Wanda aka yiwa duka, na
gaji matuk'a.
Ina shigowa naji atmosphere din dakin ya canza daga daddad'an kamshin turarikan daki sai
wani irin kauri marar dadin shaqa a dakin, ban zauna ba gudun A/C din parlour din na Kara na
kunnu electric din da ake zuba masa turaren daki, tun a parlour na cire Kayan jikina wannan
kuma normal d'abi'a tace ban fiye shiga bedroom da Kayan jikina ba idan na fita dasu Saida na
cire na saka a washing machine ya Zama daga ni sai boxer short na wuce bedroom dina da
niyyar nayi wanka na hada coffee na Sha tunda Ina da coffee maker a daki.
Ina shiga ba zato ba tsammani naji an rukungumeni gaba daya, sautin muryar Safna naji na
fadin Dan Allah kayi hakuri,wallahi ka sakani a cikin mawuyacin Hali ka tausaya min idan ka fita
a rayuwata mutuwa zanyi wallahi, Kai kadai nakeso nake muradi a rayuwata, kaji tausayi na,
wallahi duk abinda kakeso Zan baka ko kaina Zan baka kaji dadi Dan nasan kana dasu da yawa
Nima kazo wallahi kayi abinda kakeso Dani.
Rudewa nayi gaba Daya na rasa in da Zan saka kaina, wani abune da bantab'a zaton faruwarsa
ba ya sameni bagatatan, kokarin raba jikina da nata nake kokarin Yi Amma kamar Wanda
akayiwa dabaibayi a hannunsa sai Kara shigewa jikina take ga ta hade kirjinmu sai goga min
jikinta take cikin kukan dana kasa tantance wane iri ne, da kyar na iya kokartawa ba juyar da ita
ta tafi zata fada Kan gadona banyi aune ba naji