Showing 12001 words to 15000 words out of 62795 words

Chapter 5 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf

03 Aug 2025

8783

miki".
Suka fito parlourn farko na sama ba kowa a ciki sai wani irin kanshi da sanyi Mai kwantar da
hankalinki a tsakiya Amatu ta tsaya ta rike Qugu tana karewa gurin zuwa dayan parlourn kallo
ta Dan busar da iska daga bakinta tana kallon Aunty safiya dake tsaye tana kallon Amatu data
ja ta tsaya. "Wai lafiyarki Kika ja tunga Kika tsaya?".
"Bari kawai Aunty aini lokacin da kike bani labarin Families din su mahmud jinki kawai nake gani
nake kamar kina kurarasa ne kawai. Amma yanda Naga gidan kakarsa kadai sai Naga ai
Bakima iya bada labarin ba ban Kara sarewa ba Saida na shiga gidan mahaifiyarsa to ga Kuma
Mai kankat, Dan Allah Aunty safiya waye mahmud din Nan nifa na sare da Lamarinsu gaba
Daya dole kiyi kokontonsa a wancen gidan Daya sakani Santi Ashe akurkin kaji na gani".
Tafin hannuwanta ta bude ta Fara kwararo Addu'a.
"Ubangijin sammai da kassai ka zauna da Zahra lafiya a gidan Nan Dan isar Annabin Rahama
ka tsareta daga dukkan qalubale na rayuwar Aure ka dubi gwagwarmayar data Sha a baya ka
Zama gatanta, ubangiji ka jibinci lamuranta Dan soyayyar ka da Manzon Allah ka dorata a Kan
duk wani mahassadi da 'yan bani na iya ka dauwamar da soyayyarta a zuciyar mijinta, ubangiji
ka dubi maraicin baiwarka ba Dan ta rasa gata ba".

"Allahumma Amin".

Sukaji an fada daga bayansu.
Da sauri Aunty safiyar da Amatu suka juya, Mahmud suka gani ya shigo ciki ta wani corridor
Basu San ta Ina ya biyo ba.
Kunya Aunty safiya taji abinda take ta gudu kenan kada ya shigo da abokansa su sameta a
gidan duk da ba wani girmansa tayi da yawa ba Amma ita ai Yaya ce".
Cikin daburcewa Aunty safiya ta gaishesa tayi Masa Allah ya Sanya Alkhairi, Amatu ma
gashesa tayi.
Zasuyi gaba mahmud din yacewa Aunty safiyar.
"Auntyn mu ko ta Nan Zakibi sai zayyan ya mikaki gida mun gode kwarai".
Tana Jin haka tasan abokansa suna kasa da sauri ta juyo tana fadin.
"Nagode jazakumullahu khairan".
Saida ta gangara kasa sannan ya Ciro waya ya Kira zayyan.
"Ga Auntyn mu nan ka mikata gida a fadawa Sameer ya Bata itama".
Kit ya kashe wayar Yana kallon Amatu yana murmushi.
"Ashe dai sai wani yayi min iso gurin previous din kenan,ai nayi zaton dukkan ku kuka yoye kun

bar min ita kadai".
"A'a wane mu da barin sarauniyar Mata a daki ita kadai yanzu haka suna tare da sajeeda".
Gaba Amatu tayi ta nufi kofar ba wani knocking ta tura ta rike kofar tana kallonsu, sajeeda ce
tace.
"To uwar iya wace gulmar Kuma ta dawo dake dakin Nan yanzu dai ba kyaleki zamuyi ba tunda
babu idanun kunya".
Shigowa tayi tana fadin. "Alheri ya dawo Dani Mai gayya Mai aikin ne na rako dungurungun
Dan haka kema tattarko ya naki ya naki Mai gurin yazo".
Wani irin Ras zahra taji, Ita fa abun Nan ya Fara Bata tsoro Wai me yasa a baya Bata jin haka
ne Sai yanzu? turo kofar da yayi ita ta datse Mata tunanin data fada.
Shine Cikin shigar shadda sky blue sai walkiya take tamkar a matse Mai a jikinta ga wani
ubansu kamshinsa na dindindin Daya kashe na kowa a dakin.idanunsa yana kanta wani irin
azababben kyau tayi Masa Ganin ya shagala da kallonta kada a saki layi a gabansu sajeeda
yasa tayi magana. " Yallabai barka da dare, ya hidima? Allah ya Sanya Alkhairi ya bada zaman lafiya da zuri'a
d'ayyuba. To zamu tafi gata Nan Zan baka Amabarta a karo na biyu, kamar wancen karon, kaji
tsoron Allah a Cikin zamantakewar ku ka tsare Mata mutuncinta a da Basu San waye Kai ba,
Amma a yau ko baka fada Mana ba mun gani da idanunmu, nasan bestie zata iya fuskantar hari
daga masu burin samun matsayi irin nata a gurinka, ko ba'a fada ba tunda a Dan kwaramniyar
bikin Nan naji views din Mata da yawa a kanka. Gata Nan Bata da kowa a garin Nan daga Allah
Daya halicceta sai Kai daka kawota,ka zamar Mata bangon da zata jingina dashi ka zamar Mata
suturar da zata Kare Mata martabarta, kada ka cutar da ita Dan girman Allah Zahra marainiyar
Allah ce duk da Bata rasa komai na gatan gidan duniyar Nan ba Amma tana bukatar samun
nutsuwa tunda a can akwai 'yar kasan da ake soya Mata Aya a tafin hannuwanta ba tare da an
ankare ba Saida tafiya tayi tafiya, Allah ya amintar dake bestie a Cikin gidan Aurenki ya Baki
kariya irin wadda yake Kare bayinsa salihai da ita, ya amintar dake kamar yanda ya amintar da
Annabinsa Ibrahim A.S daga wutar Namaruzu. Dan Allah kiyi Masa biyayya ki rufe masa sirrinsa
kinji, Allah ya Baku zaman lafiya Mai dorewa ya kauda muku fitina"..
Sai Kuma muryarta ta Fara rawa, sai hawaye, da sauri ta nufi kofa ta fice. Zahrar ma share
hawaye take haka Amatu itama idanunta sun cicciko da hawayen,Shima Dan gogan tunda
yarinyar ta Fara magana yaji kamar ta Dora Masa bulo inci Tara a kansa, ya yarda kaunar
precious da yarinyar Nan ta gaske ce babu algus a cikinta saboda yayi wani Abu Wanda ya
gaskata hakan, Dan ranar Daya bijiro Mata da maganar soyyyarsa dan Karamin hauka sajeedar
tayi Masa da kyar ya fahimtar da ita cewar gwaji ne yayi Mata ba Wai da gaske yake ba, duk da
haka Saida ta nuna Masa kada ya karayi Mata irin haka za'a iya samun matsala.
A can main parlour kuwa abokan angone tare da kawayen Zahra sai wasu 'yan Mata na family
din, tun a can ya fada musu Bai Hana zuwa sayen Baki ba Amma babu Mai shigar Masa dakin
barci babu Kuma Mai Kara gane Masa Mata Ganin gurin dinner ma Ala amfana.
Yasha caccaka gurin friends dinsa yayi kunnen uwar shegu dasu shine dalilin Daya saka yayi
amfani da kofar baya ya hauro stairs din shi kadai.
A Nan su sajeeda suka Sami su Khadija dasu Aneesah da sauran mutanen, Tajuddeen ne ya
taso ya nufi Amatullah yana fadin. "Daman kina sama duk Kiran da nake Miki bakya amsawa?".
Dan bude hannunta tayi alamar babu waya a gurinta.

Jinjina Kai yayi suka nufi waje.
Addu'a sukayi aka shafa sannan kowa ya fito da wata Leda Mai shegen kyau a hannunta da
alama kyautar girma ce daga bangaren anguna.
Saida suka fito sannan salis ya Kira mahmud Yana fadin .
"To yallabai ango mu zamu wuce asuba ta gari".
Wani Abu mahmud din ya fada Masa ya fashe da dariya wadda ta janyo Hankalin da yawa daga
mutanen gurin Yana fadin. "A'a kayi zamanka wasu har sun Fara ficewa daga cikin gidan ka
duba time lokacin yaja da yawa".

Tun bayan fitar su Amatu zahra tayi tsilli-tsilli, sai taga yau ya Kara Mata wani kwarjin da girma
gani tayi kamar ya cika dakin, numfashi ma neman tsaya Mata yayi wallahi wani irin Abu take
gani a cikin idanunsa.
Yana sauke wayar daga kunnensa ya nufo zahrar Yana sakin tsadadden murmushi, ya Dan
tsuguna a gabanta ya saka hannu ya dago fuskarta wadda hawaye ya bata.
"Ya salam!"
Ya fada Yana Zama kusa da ita, tafin hannunta Daya Sha lalle ya rike Yana Dan matsawa kada
dayan hannunsa ya saka ya zare Alkyabbar daga kanta Yana karewa fuskarta kallo, be tab'a Jin
ya gaji da kallonta ba shi dai ya yarda Allah ya jarabcesahi da wata irin soyyaya a kanta shifa ji
yakeyi ko baze kusanceta ba ze iya rayuwa da ita har iya rayuwarsa. Wani irin kanshi ne ke fita daga jikinta na musamman ba Wanda ya Zama constant ba a'a an
samu Karin wani na musamman a Jikin.
"Welcome to Dange's house Mrs Mahmud Muhammad Dange, Alhamdulillahi bini'imatihi
titummus salihat, Fateemah Allah yayi Miki Albarka yau gaki a gidan Mahmud Kuma gidanki da
Zaki rayu a cikinsa ki dasa Mana bishiyar Zuri'armu a cikinsa ta girma ta yadu har asha
inuwarta, Fateemah duk burina na duniyar Nan game da mace a kanki na ta'allaqa shi ki zamar
min bargon daze lillib'eni ki hanani Jin sanyi sai dumin jikinki, ki daukemin duk wata kishirwar
data addabeni akan diya mace kinji my princess, duk duniyar Nan da ke kadai na aminnta na
bayyana Mata sirrina ciki da waje ke kadaice macen data tab'a gani ainishin waye ni tunda nayi
Hankalin kaina, ki tallafeni kada ki Bari na shiga rubibi a hannun Mata kinji my previous, na baki
amanar kaina da kaina tunda ni babu Wanda ya Baki Amana ta amma ke kowa fada min yake
gaki Nan Amana na kula dake to nima ki kula Dani Dan tamkar marayan da bashi da uwa bashi
da uba haka nake a gurinki ki bani dukkan kulawa kinji, kuma Dan Allah ki daina tsorona nifa
babu abinda Zan Miki na cutarwa idan na cutar dake Nina cutar da kaina, duk wani burina
nandora shi a kanki".
Ya fada Yana shigar da ita jikinsa Yana sauke ajiyar zuciya a jajjjere, lif tayi a jikinsa Amma fa
yaji yanda heart dinta ke beating very fast. Lumshe ido yayi ya rasa meya canza Masa ita take
irin wannan Jin tsoron nasa yasan ba dabi'arta bace hakan ko ranar Daya Fara fito Mata a
mutum sak ba tayi irin wannan tsumar ba kawai dai ta Dan rikice Masa na dan lokaci Amma
Daya saka Mata pressure dole ta nutsu tayi Masa abinda yake so a lokacin harya saida ya
samu relief, Amma yanzu duk ta rikice Masa a Hankali yayi Mata magana a kunnenta.
"My previous me kike tsoro a tare dani, fada min kinji?".
Ya fada Yana Kara shigar da ita jikinsa yana kuma Dan shafa gashin kanta Daya Sha gyara na
musamman, sanyi da salama da wata irin nutsuwa suna sauka a cikin zuciya da gangar jikin a

lokaci daya.
Lif ta qarayi a jikinsa dan da gaske tana Jin wani irin Abu da ada Bata jinsa a tattare dashi, sai
yanzu take jin da gaske fa auren ne a kanta sabanin da da take jinta dai gata nan.
*AUREN HUCE HAUSHI*

_AISHAT ISAH MUSAH

_*Maman Fateemah_*

08055362975
My
WhatsApps number.




*Page 83.

______Kara shigar da zahrar yayi jikinsa, nan da nan yaji labarin Yana neman canza salo shi
Kuma harga Allah Yana bukatar privacy saboda matukar ya tab'a wannan shugwababbar 'yar
raki sai abinda Hali yayi. Don yasan za'a Sha danger da ita ga mutanen biki suna Nan yasan da
safe baza'a rasa masu zuwa suyi Mata sallama ba, yafi son sirri gaskiya. Amma dai zasuyi
nafilar da Manzon Rahama yayi umarni da ma'aurata su yita.
"Cikin nasa salon da yasan Yana yin rinjaye a kanta ya Dan fara shafa cikinta a Hankali.
"Da yunwa a cikin Nan gaskiya, Bari na kawo Miki abinda zakiçi kada Nan gaba ayi min gorin
ranar da akazo gidana ko abincin tarba babu Ina ta kurin sokoto aga nayi failing ko ba haka
ba?".
Ita dai zahra shiru tayi masa shi ya kasa ganewa yau jinta take tamkar Bata taba wata kebewa
tare dashi ba,taga sai wani rawar jiki yakeyi abinda ba halinsa ba, duk wannan kanewar ta nemi
nata gurin wani sabon mahmud take gani ba Wanda ta sani ba.

Ya tambaya Yana kokarin zare Mata Alkyabbar gaba Daya daga jikinta wani fitinan kamshin ya
mamaye shi, ga wani mahaukacin feeling da yaji Yana fusgarsa zuwa gareta, kankameta ya
karayi a jikinsa da gaske ya shiga wani yanayi,ba Karamin yak'i yayi da zuciyarsa kafin ya
sassauta Mata rikon da yayi mata Yana maida numfashi.
Alkyabbar ya aje gefen gadon ya Zama daga ita sai wata rigar atamfa wadda akayiwa wani
fitinannan dinki Wanda ya fito Mata da ikahirin halittarta ta kirji zahiri, yabi shafaffen cikinta
abinda ya Kara fallasa asirin kirjin nata kenan da suke a cike tsan-tsan, ai baisan lokacin Daya
Kara mannata a jikinsa ba Yana fadin "Ashe wannan abar ba Karamin sitirtamin kayana tayi
ba" Yana Kai hannunsa gurin.
Dan zabura tayi ta rike hannunsa ta shagwab'e Masa fuska tare da juya Masa sexy eyes dinta
"Please meu amorrr.....ba kyaufa ka Bari Dan Allah".

Saitin kunnenta yayi magana a hankali..

"Meye ba kyau din fada min abinda nayi Daya sabawa shari'a? Ina son Jin tempareture din
jikinki ne naji kamar tayi high".
"A'a...ni lafiya ta qalau".
"Ok, to bari nazo".
Ya fada Yana gyara Mata zip din rigar, fuskarta ya dan shafa kadan tare da Bata wani light kiss
a gefen wuyanta Wanda yasa tadan fitar da wani Karamin sound da yaso ya Hana shi fitar.
Babbar rigar ya cire ya aje a kusa da ita Yana nufar kofa ya fice, Dan kwanciya tayi a gefen
gadon tana Jin wani Abu Yana circulating a cikin jinin jikinta.
Bai Jima ba ya dawo dauka da Leda Mai tambarin na Maru suya spots, da plates da sauran
tarkacen su knife da cups da su forks, a kan Karamin Conner table ya Dara idanunsa na Kan
Zahra wadda ta lumshe Ido tana sauke numfashi a hankali,wani special smile ya saki yana
godewa sarki buwayi gagara misali da yayi Masa irin wannan kyautar, Saida ya aje komai
sannan ya nufeta ya tsuguna dai dai saitin fuskarta Yana dan shafawa a hankali narkakkun
idanunta ta bude tana kallonsa.
"Oya tashi kici abinci".
Ta lumshe idanun tayi. "I am ok fa, bana Jin yunwa barci nakeji".
Bai saurareta ba ya saka hannu ya dagota daga kwancen Yana fadin "Ni nagano yunwar a tare
dake".
Nama ne Wanda ita dai bazata ce ga yanda aka sarrafa shi ba, ya gyara hannun rigarsa ya
Fara Bata tana mitar ita ta koshi Amma Bai barta ba Saida ya tabbatar da ta koshi sannan ya
dauko Mata mutuniyar farm fresh ta strawberry ya cika cup ya kafa Mata a Baki ta Sha rabi ta
kawar da Kai kamar yanda yaran goye sukeyi idan suka koshi da Abu. "Pls precious ki shanye mana farm fresh ce fa, ko kin daina yayinta ne? Naga tunda mukazo
kabi nema ba alhalin an cika Miki store da ita".
A shagwab'e ta dago sexy eyes din ta tana Masa wani kallon Daya nemi jefa shi a wata nahiyar.
"Nifa na koshi kamar na cikin mafa ze dawo nakeji".
"Ok. Shike Nan Bari na dauke kayan sai ki shiga kiyo Alwala kafin na dawo".
Har ya kai kofa ya tsinkayo maganarta tana fadar "pls naga zaka mayar Kai bakaci komai ba".
Kafeta yayi da Ido Yana nazarinta "Da kina son naci ai da kin bani, amma Baki bani ba tunda
na dauke kuma sai wani jikon Wanda kikaci shikenan is enough for us, koba haka ba?".
Ya dage Mata gira ya fice.
Tsam tayi da ranta tana hasaso mezeje yazo, ita fa duk lamuransa sun tsaya Mata a Rai yanda
ya downgrade din kansa a Azare da yanda ya ringa mu'amalantar Almajiran malam, a yayin
zamansa a can, ita fa gani take wallahi yanzu yafi karfin ajinta nesa ba kusa ba duk da tasan
itama yes ba karya Ubangiji ya Gama Mata gata ya dauke Mata iyaye Amma cikin
Rahamaniyya tasa saiya saukake Mata duk wani tsananin rayiwa, duk da Tasha badaqala a
baya sai gashi ya zama tariihi.
Allah be Bata ikon tashi ba har ya dawo, ruwan dake hannunsa na laimar alwala ya Dan yarfa
Mata sai tayi figigit tana sauke ajiyar zuciya.
Gaba yayi ya nufi kofar da take tunanin toilet ne, ta Mike a hankali tabi bayansa hanya ya matsa

ya Bata tare da fadin "shiga kiyo Alwala Ina jiranki".
Ya juya ya fice daga dakin, brush ta bude sabo ya wanke bakinta sannan tayi alwalar gurin
mirror ta nufa ta karewa kanta kallo, wallahi tausayin kanta da kanta takeyi tasan sai yanda hali
yayi Dan ita kadai tasan me take hangowa a cikin idanunsa.
Tana tsaya taji alamun za'a bude kofar tayi saurin barin gurin, Yana budewa tana zuwa bakin
kofar jallabiya ce sabuwa fara Kar a jikinsa sai Zuba kamshinsa nan nasa na musamman
yakeyi, hannu ya Miko Mata yana sakin murmushi Yana fadin "inye 'yan matan gidan mahmud
Dange, yarinyar Nan kina yanda kike so da Dan malam din Nan wallahi sai cika kike kina
batsewa irin kada a kawo Miki wargi din nan ko?".
Kauda Kai tayi tana sakin murmushin ta Mai shagaltar dashi "Ni wallahi ka Bari idan wani yaji
saiya dauka haka ne fa".
Hannu ya rike ta fito daga toilet din.
"To da karya na fada ba cikar kike kina batsewa ba kawai Dan ki Sara min allo ki hanani rawar
gaban hantsi ni da halaliyata za'a hanani dama daddawata da moda".
Ya fada Yana kafeta da tsumammun idanunsa, sadda kanta tayi kasa Dan abinda take gani a
can baya ta gani yau muraran a idanun nasa ta rasa wane irin abu ne da yake sakata a rudu
haka.
"Muje muyi sallar".
Hijab taga ya dauko Mata fari sol dashi Mai laushi irin na mutanen Indonesia din nan ya zura
Mata,Yana janye da hannunta suka nufi wani guri kamar space din da ake saka dining table
suna zuwa taga an yi gurin ne domin ibada kawai ba Bata lokaci ya shige gaba yaja musu
sallah, raka'a biyu yayi musu yayi sallama ya Jima Yana musu Addu'oi da harshen larabci
Wanda har Saida zahra ta dago da kanta ta Zuba Masa idanu tamkar shine Dan mun gada din,
a hankali ya matso inda take saune ya dafa kanta ya ringa kwararo Addu'a, Nan da Nan jikinta
ya hau tsuma sai kuka Dan Allah ji tayi tamkar tafi kowace mace sa'ar samun miji Mai addini
Dan Bata taba tunanin iliminsa ya Kai haka ba tun a wancen lokacin bare kuma yanzu da taga
ra'ayal ainiy.
Sai da ya Gama Mata Addu'oin sannan ya daukota cak ya rungume abarsa Yana fadin " pls
precious kinsan bana son kukan naki ko? Ki daina kuka babu abinda Zan Miki ki saki jikinki Dani
kinji, Nima na gaji sosai babu abinda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login