Showing 18001 words to 21000 words out of 62795 words

Chapter 7 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf

03 Aug 2025

8784

abinci masu aiki.
Abinci ne kusan kala biyar funkaso yace ta zuba musu tare da kunun gyada Wanda yaji kwakwa
da Madara, sunci sun koshi sannan suka tashi ya Taya ta suka kwashe kayan da sukayi amfani
dasu. Da suka koma parlourn Basu zauna ba lungu da sako na gidan ya shiga nuna Mata ba
karamin mamaki zahra tayi ba Dan ko a mafarki Bata taba tunanin rayuwa zata kaita irin
wannan gurin ba, kallon mamaki take binsa dashi Amma ya fuske ya nuna kamar baisan abinda
take nufi ba, dakin da suka shiga ne yayi muguwar tafiya da imaninta, dakin Yara ne akayi Masa
wani decorations masu kyau da daukar hankali ga wasu irin Turkish furnitures child size masu
azabar kyau hatta shelves din dake cikin wani kamar Dan dakin glass a bangaren da katayi
Dan karatu child size ne, ga colours din purple da pink ne sai ya bada wani yanayi Mai kyau a
dakin, Kara shigar da ita Yayi jikinsa yana da shafar abinda yake tsone Masa ido a Hankali.
"Yaya me za'a Kara ko a rage banji kinyi comment ba fa tunda muka Fara zagaya gidan naki ko
Bai Miki ba a canza Miki wani? Ga Kuma dakin babies dinmu fa yayi ko a canza musu tsarin?".
Kasa magana tayi Dan hannunsa ba karamin dagula Mata lissafi yakeyi ba ga Wani numfashi
da yake sauke Mata a gefen wuyanta.
"Pls talk to meeeee..zMana kinyi shiru,Bai Miki ba ko?".
A kasalance ta furta "komai yayi fa Allah ya Kara budi ni amma fa gidan Nan tsoro yake bani
yayi min yawa".
Wata shafa ya yiwa saman cinyarta Yana fadin "Ai kuwa Saida kiyi hakuri duk gidajenki haka
suke wasu ma sun fishi girma so nake ku wataya keda yaran mu a Hankali Zaki Saba Kuma me
kike tsoro gani gaki ai ta maganar tsoro ta wuce Kuma".
A Nan ma Saida ya tsotseta tas sannan suka fito yana rike da hannunta, suna dawowa kasa
Baki suka Kara zuwa 'yan uwan momin Kano ne da su Aneesa dole tasa yabar gidan bayan sun
gaisa da bakin.
Direct gidan Ammi ya wuce a gurin Abbie ya yada zango sun Jima suna Hira kafin ya nufi
bangaren Momin Kano suka gaisa sannna ya shiga gurin Hajiya Babba itama ya gaisheta taso
ta tsare shi da surutu sai Allah ya taimake shi aka Kira wayarsa ya fice da sauri.
Bangaren Amminsa ya nufa Yana shiga parlourn farko yaci karo da su Batool sun Shirya Wai
zasu gidansa suka gaishesa Suka wuce, shi Kuma ya shige Yana gaisawa da jama'ar da suke
cikin sauran parlours din.
Bedroom din Ammi na kasa ya shiga Bata nan sai Hajja da jama'arta wasu nata Shirin tafiya
bare yaran cikinsu saboda makaranta da sallama ya shigo,da wani malalacin kallo Hajjar tabi
shi Yana gaisawa da Hajja karima 'yar uwar kakansa uwa Daya uba Daya tana Dan tsokanarsa
irin na jika da kaka. "Kai kuma me Zan gani haka daka fito gari da wadannan kayan Wai bakasan yanzu ka
manyanta bane ba?".
Wata dariya ce ta kwace Masa Yana Zama kusa da Hajjar tare da riko hannunta. "kikace
menene? To meye laifi Dan na fito a haka su wadannan ba kaya bane?".
Harara ta watsa Masa "Dan Allah rufe min Baki Ina wasu Kayan mutunci a Nan gida cike da
jama'a Dan ma surukan naka suna can sabon gininka da kayiwa tawaye kaki zama, Dan Allah
kaje ka sake wasu kayan kada ka shigar musu a haka da wannan Kayan kamar ka roko".

Wata yarinya ce kamar sa'ar su zahrar jikar Hajja karima tace "Haba Hajji ai hakan shine gayu
kinsan kudin kayan da suke jikinsa kuwa wallahi saisu saye duk kayan cikin trolley dinki" .
"Karbi Nan sa'ada ai Naga kema jirgi Daya ya dauko ku dashi, Kullum Kuna cikin wadannan
kayan da aka daukewa Albarka yo ina dalili 'ya'ya kun dauki daba'ar Nasara kun yafa kunce
shine gayu".
"Kinga tashina Daman zuwa nayi Naga yanda kuka waye".
Ya fada yana kokarin tashi daga kusa da ita "Dawo ka zauna ko lafiyar matar taka ai ban
tambaya ba ka sakani surutu, to Yaya ita Fatimar ta tashi".
"Lfy kalau Alhamdulillahi, tace na gaisheki da kyau idan nazo"..
"To Masha Allah haka akeso Allah yayi Albarka a gaisheta ai zamu shiga muga daki kafin mu
tafi da yau naso komawa Baban ku ya Hana yace saina kwana biyu na Dade banzo musu
Nigeria ba".
"Au da tafiya zakiyi ban sallameki ba ai gidana Zan mayar dake sai kin zauna min kamar yanda
na zauna Miki harna fadawa Uncle Ishaq ma tun ranar da kukazo ya Kuma amince Dan cewa
yayi aike tawa ce duk yanda nayi yayi dai dai, Dan haka keda Hajiya Inna Zan hada ku mu
zauna duk kowa ya ramawa kura aniyarta".
"Allah ya tsari gatari da Saran shuka ni naje gidanka na Mike kafa na Kama Zama tare da
matarka ku ringa min dibar Albarkar da zata sakani na rasa Dan sauran Idona ko?".
Baki bude yake kallonta yayin da saura Yan uwa da suka rage a dakin tunda yawanci yaran sun
fice.
"Meye kuke min wani kallo karya nayi? ko bakuga yanda yake cukumarta a gaban dubban
mutane ba to Ina ga daga mu sai shi ai sai yanda ta yuwu Dan daudu a lahira".
Dafe Kai mahmud yayi Yana Kara kallon Hajjar ba tare daya iya furta Mata komai ba,wato Hali
zanen Dutse halinta Yana Nan ita hands free ce babu abunda ya dameta Saida idan ta fad'a
kayi yanda zakayi kawai.
"Allah ya bamu Alkhairi ki gaida gida Amma matata bazatazo Miki Niger ba tunda harda bita da
kullin Wai zamu kashe Miki Ido". Yayi waje yana Jin tana kiransa yayi gaba, Bai haura sama
gurin Ammin ba komawa yayi asalin part dinsa Daya zauna tunda Yana da Kaya a cikin tunda
yawanci kayansa na biki a Nan Sameer ya ajesu. Wani yadin filtex brown Mai kyau da tsada ya saka ya dauko agogonsa Omega ya daura ya
zuba turarensa ya kafa hula shi kansa sai yaji yes hakan yayi masa daidai, Dan murmushinsa
yayi Yana tuno maganar Hajja Wai kayansa kamar na roko. Ficewa yayi daga part din ya koma
na Ammi Amma ta baya ya shiga inda ze sadashi da stairs din basai ya koma ta main entrance
din ba.
Saman ba hayaniya kamar kasan, knocking yayi a kofar bedroom din Ammin Aishat ce ta bude
Masa su uku ne a ciki mummy Badi'a ya Fara gaishewa tana tambayarsa Ina 'yarta, sai
Amminsa ita kuma Aishat wani signing din da suke sukayiwa guna daí ½í± alamar jinjina wannan
dabi'ar normal sun saba tun suna yara. Wani Dadi ne ya rufe Ammi fuskarta sai annuri yake fita saboda yanda taga Hussein dinta ya
Zama babban mutum ko ba'a fada ba kana ganinsa kasan ya samu kwanciyar Hankali.
Kan sofa ya zauna kusa da twins sister dinsa yana kallon yanda suka cika dakin da wasu
jakunkuna masu hotonsu Shida zahra,. Yayin da Ammi ke hada wasu Kaya a cikin jaka daga

gefe da alamar kowa sabgar gabansa yakeyi, rausayar da Kai yayi Yana kallon Ammi wadda
itama rabin hankalinta Yana kansa.
"Ammi..na".
ya Kira sunanta abinda takeyi ta Bari ta bashi full attention dinta tana sauraren meze fada Mata.
Dan sosa Kai yayi kafin yace "munga sako jazakumullahu khairan Ammina, kuma naji kince
Zaki turo Mata housemaid ko?".
"Eh haka nace duk da nasan akwai naka Wanda suke kula da gidan sai Naga ya kamata a Kara
Mata wasu daga nan Kuma wannan kukun naka a canza Masa wani aikin ko Kuma ya koma
kamfani yaci gaba da aikinsa a can Dan baze yuwu su zauna da ita ba, a yanda matarka take
sai kana kula da irin abokanen ma da zaka ringa shigar dasu gidanka gaskiya". "In Sha za'a kiyaye Daman kukun na mayar dashi kamfanin shinkafa dake can kebbi, Kuma
inaga basai an Kai Mata Yara ba ki Bata binta kawai saiki taimaka ki kirawo Amminta ta bar
Mana Aunty zilai wadda suka zauna a kano Naga Bata da matsala".
"Ok babu laifi saina kirata na gane matar itace wadda ta bawa sako ta kawo min Naga alamar
kamar ma'aminciyar su ce".
Ya Jima a gurin Ammin kafin Aishat ta rakashi suka je suka gaisa da dangin zahrar Wanda
suketa Shirin tafiya Dan kayansu ne su Aishat din suke hadawa su za'a bawa Basu Dade ba
suka fito a hanyar da zata kaisu parking lot ne Aishat ke fadar
"Wai ya zahrar ne da fatan babu wata damuwa a tare da ita?".
"Lafiya kalau take kinsan gidan yau zuwa gobe sai a Hankali gidan yanzu na jama'a ne".
"Haka ne Kam ai daga Nan har wani lokaci mutane bazasu yanke a gidan Nan ba sai kayi
hakuri bare Kai Mai jama'a ai sai abinda ka gani, ni addu'ata Daya kada 'yan matan dake
haukar sonka su ringa je Mata gida da sunan kannenka kasan dai baza'a hanasu shiga ba".
Wani malalacin murmushi yayi yana kissima wani Abu a zuciyarsa.
"Naga kana murmushi ko ba gaskiya na fada ba?".
"Gaskiya ce mana amma inaga ba Sai muna garin ba za'a samu matsalar, nifa na takura mutum
da gidansa da matarsa Amma ace ya fito yana teto a titi ai kamata yayi yanzu mutum na gida
Yana hutawa".
"Ai maganinka kenan Dan sweet heart ma ba karamin bekenka ya gani ba, me ka zauna jira
kaida matarka saboda wani dalili naka ka Zuba Mata ido kana kallo har tsawon wannan
lokacin".
Girarsa ta dama ya dan dage Mata kadan "bazaki gane ba komai Yana da dalilin yinsa, we will
talk later in Sha Allah, ai kece best friend dina tunda kin kular min da my previous, yanzu zanje
muyi sallama da bakin da Sameer ya gayyato min Dan tsabar daukowa Kai jidali ya saka
mutane barin harkokinsu suka taho har nan".
"Aini Wallahi yayi min dai dai wani ma Be taba zuwa 9ja din ba sai wannan sanadin".
Har gurin mota sukaje suna tattaunawa da 'yar uwarsa Saida ya shiga harya tashe ta Aishat
tace Masa.
"Wai Ina mutanenka na ganka Kai kadai".
"Na Basu hutu amma fa kinsan duk da haka su zayyan suna waje Dan Ina fitowa suka dafa min
baya nasan bazasu hakura ba".
Motar ya harba yayi gaba saida ya fice daga second gate sannna Aishar ta juya ta koma ciki

zuciyarta fal farin ciki Dan uwanta ya dawo tare da wata irin haiba da kwarjini ga uwa uba cikar
mutuntaka ta aure.

*************

Tun bayan fitar mahmud zahra ke karbar Baki Dan ma Allah ya taimaka su Amatu da kannen
Aunty safiya sun shigo,su suka ringa ba mutane kayan garar da aka kawo da sauran tarka na
plates dasu jugs sai karamar blender ta hannu Mai aiki da batir Wanda ake Masa charge, sai
kusan Sha biyu su sajeeda sukazo Ashe suna asibiti da Mama Hameeda ta kirawota tana
kuka ta fad'a Mata ita tunda kuma ta Kira oga Sameer ta fad'a Masa shine ya Kira hotel din aka
kaita asibiti da yake jiya Mamar saboda tsabar tashin Hankali wadanda aka saukesu a hotel
tabi inda Allah ya taimaketa duk yawancinsu mutanensu ne 'yan Azare cikin dare ciwon kirji ya
addabeta tamkar zata mutum.
Saida safe su Aunty Hasana suka sani abinda ya kawo musu tsaiko kenan a gurin tafiyarsu
saboda jirgin karfe Sha Daya zasubi suda tawagar Ummee duk Sameer ne shida su Bashir
suketa Kai kawo akan komai, dole sai su Ummeen ne dasu Hajiya kaltume suka nufi Bauchin
da Alkawarin su Ummee zasu dawo sokoton kafin su wuce. A gurguje sukayi sallama da zahrar saboda ya Abba da yazo tafiya dasu ita ummansu,zahra ta
bawa su sajeeda Kaya da cosmetics kamar me tunda gasu Nan tamkar kamfanin ne a gidan ga
wasu can a Azare har Kashi biyu duk na lefenta ne, suna kuka share share suka rabu sai
yamma so sai su Aunty Rukayya da Aunty Fateeha suka tafi yayin da Hajiyar makwarari tace
suje jikanta ya maidota Bata Gama abinda zatayi ba.
Zuwa magariba gidan ya Zama ba kowa daga Binta yarinyar da Ammi ta kawowa Zahra sai
wasu yara da Hajiyar kadai.
Zahra Ammi ta Kira tace ta fadawa su Aunty zilai kada suyi komai zata aiko da abinci.
Bayan magariba kadan Aunty Aishat suka shigo da abincin lokacin Zahra na sama tayi wanka
tana shiryawa, wata Riga ash colour ta saka irin ta mutanen Kuwait tayi rolling da veil din sai
tayi wani irin kyau Dan yanzu ne kwarjiinin Amarcin yake bayyana a jikinta.
Saman Aishat ta haura tabar su Radeeya a kasa,sau Daya tayi knocking zahra ta bada
Umarnin shigowa.
Suna arba da Aishat zahra ta rugo kamar yarinya ta shige jikinta tana fadin " Aunty Aishat nayi
fushi idan ke bazaki zo ba ai saiki bada a kawo min Afnan Mana duk kewarta da dameni tana
Ina ne dan Allah?".
Kan sofar dake dakin suka zauna Aishat din na fadin
"Afnan sunje Usman Dan fodio teaching Hospital dubiya, Inna Maimuna ce ta goyata kinsanta
da son yawo".
"Su Inna kuma,to waye bashi da lafiya?"
"Naji dai suna cewa Mama kinsan ba sanin mutanen nayi ba".

" Ayya! haba shi yasa babu Wanda yazo gurina,Saida na gaji na Kira Aunty Hasana Amma kin
fada min tayi sai cewa tayi zasuzo suna da wasu uzururruka ne Ashe Mamace jikin yaki Dadi
Allah ya Bata lafiya".
"Allahumma Amin".

Aishat ta fad'a tana kallon zahra, kokonto ne ya darsu a zuciyar Aishat yanda taga zahra na Yan
guje guje nan tasan ba'a gamu ba Amma saboda ta tabbatar saita cewa Zahrar.
"Dan Allah dauko min turarenki na gani Yana yi min Dadi sosai".
Tsam ta miqe Ras ta tafi ta dauko Mata su ta kawo Mata Aishat din ta dauka tana Kara
shinshinawa tana kwarzanta kanshin su.
Handbag dinta ta dauki ta bude wasu kwalabe ta dauko tana murmushi sai wani kuma Karamin
daurin magani a cikin irin ledar da ake zuba tablet a asibiti ta Mika Mata tana fadin "gasu Nan
inji mummy Badi'a ta dauko wani turare Mai colour purple tace "Kinga wannna ki shiga toilet ki
dan shafa a kirjinki da kasan mararki sai kuma wadannan guda biyun duka jikinki Zaki shafe
dasu, wannann kuma ki zuba Madara ki Sha yau da gobe da jibi ya wadatar, Bari na dauko
cups na hada Miki".
Zahra duk a kunyace take da Aunty Aishat din, ita mamaki take Bata tamkar ba dangin miji ba
ita gani takeyi wallahi Kamar Aunty Hasanarta. Aunty Aishat ce ta tashi ta nufi kofa ta fice.
Bata Jima ba ta kawo cups da ruwa da farm fresh da Hollandis free mik, Aunty Aishat din da
kanta ta hadawa zahra maganinta da Holladia ta Bata ta Shanye, Bata kayan tayi tace ta Adana
kada ta Bari ko mahmud ya gani turaren na Mata ne kawai.
Kai ta gyada Mata tana Mata godiya, kasa suka sauko tare da Auntyn sai wurin 8:30 mahmud
da Sameer suka shigo gidan, Sameer na ganin Hajiyar makwarari yayi turus Yana kallonta cikin
madaukakin mamaki.
"Yanzu saboda Allah Baki bi su Rukayya ba Kika koma gida? to ko zaman daki zakiyi musu ne?
Oh yau Naga ikon Allah gaskiya ko haihuwa tayi Allah bazan kowaki garin nan ba tunda baki iya
cin Dan wake Mai yaji ba sai kin fantsama a ido, gaskiya gara da Allah yasa 'ya'yanki maza
basa kusa dake da rawar gaban hantsi zaki Hana su wallahi, kawai kizo ki nemi guri ki zaunawa
yarinya kina ganin shige da ficenta dan ki hanata watayawa kawai".
Tafi da sallallami Hajiyar ta dauka tana fad'in. "Yau Naga abinda ya isheni kaida ba gidanka naje
ba ballentana kace nayi maka ba dai dai ba, su an fada maka irin kane zalamamme Wanda
baya kauda Ido akan matarsa ai ban mance abinda kukayi min ba Ina zaune kuka kwakume
juna kuna tsotse-tsotse ba kunya ba tsoron Allah saini na bar muku gurin, Amma kaga su da
yake Allah yasa suna da ta Ido ko hannunta kaga ya rike a gaban mu eyeh?" . mahmud ne ya
matso kusa da Hajiyar Yana fadin.
"Hajiya barka da dare, Dan Allah rabu da Sameer baya son zaman lafiya ai Nan dai gidana ne
idan ma kin amince Zaki zauna har iya rayuwa kiyi zamanki daki ma sai Wanda Kika zaba zaki
zauna".
"Allah yayi Albarka ko yanzu ka nuna min Kai cikakken d'ane na halak, Daman Kai nake jira ka
mayar Dani yau can gidan ku Zan kwana ba gurin Hajiya Inna ba".
"Ok Bari na shirya sai muje na kaiki Nima ban shiga ba Nan nayo ya fada Yana nufar stairs da
sauri yayin da Aishat tabi bayansa da sauri, Saida suka bacewa ganinsu Hajiyar ta kalli Zahra
tana tabe Baki "ke Kuma miji ya dawo Kika nemi gurin Zama kamar wata kud'd'a marar wayo,
baki ga ita 'yar uwar tasa ta bishi ba? Maza tashi ki bishi kinji ba'a sake da Lamarin miji". Su Radeeya dai sai dariya suke musu suna daga d'ayan parlourn Dan da alama wannan har
tace Hajja Bata iya ba.
"Yo ta Ina zata iya binsa kin kasa kin tsare kin hanata sakewa da mijinta".
Sameer ya fada a kule.

Shiru tayi masa Bata Kara tanka Masa ba.

Aishat Bata Jima ba ta sauko tana fadin "Sameer Bari mu wuce mukam Saida safe".
Tsam Hajiyar ta Mike muje ki tafi dani kada wannan Mai dacin ran ya kifar Dani a hanya yanda
yake cika Yana batsewa baza'a haifi da Mai Ido ba".
Har gurin mota Zahrar ta rakasu tana rike da babbar jakar data hadawa Hajiya nata kayan
harda na makotanta ta Bata Wanda take ta Kira ana yiwa zahra Allah Sanya Alkhairi, Saida
suka wuce ta dawo.
Tana dosar kofar Sameer da shi suka fito,Sameer din rike da wasu files a hannunsa shi Kuma
Dan gogan yana waya da wani yare Wanda Bata San ko wane yare bane. Rab'awa tayi zata
wuce yayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login