Showing 9001 words to 12000 words out of 62795 words

Chapter 4 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf

03 Aug 2025

8785

mutum ya kalleta ya Kara kallo Dan da gaske
zaharar ce. A Hidima event center Wanda ke bodinga road, behind Nipost sokoto south za'ayi yinin, lokacin
da aka shiryata photographer yazo anyi hotuna kamar me sunje part din momin Kano ma anyi
hotuna a Nan Zahra taga kanwar maman Musbahu Aunty batayi mamaki ba tunda taga

musbahun da Faruq tare a Kano da alamar sun jada relation dasu.
Daga bangaren Momin akazo tafiya da Zahra gurin da za'ayi event din Mai gayya Mai aikin ya
Kira momin da Kansa yace suje za'a kawo ta.
Abinda yaso ya Zama na magana a Cikin family kenan sai da momin ta tsawatar saboda momi
ba Wasa tasan kanta yanda ya kamata Bata daukar wargi domin itama daga babban gidan
sarautar Kano aka daukota, shi yasa tasu tazo Daya da Ammi ma Dan itama Ammi tasan ciwon
kanta Kuma da fadarta gurin miji, Sam Bata shiga shirgin tsugune tashi na family din. Sameer yazo ya tafi da Zahra su Amatu sunso subi Zahrar Amma Sameer yace ba can suka
nufa ba yanzu da inda ze kaita, dolensu suka hakura da bin motar Amaryar.
Direct kalambaina road suka nufa ita dai Zahra ikon Allah take kallo.
Gaban wani plat house mai wani irin gini na daukar hankali taga sameer ya tsaya Yana yin Horn
har suka Karads shiga ciki wayar Sameer ta dauki kida da sauri ya dauka Yana fadin.
"Har munfa karaso".
Da yake a handsfree take sai Zahra taji yace .
Ku wuce kawai akwai mutane a gidan".
Wani sanyin dadi ne ya rufe Zahra Daman tunda suka taho addu'a take haka Nan Bata San
kebewarsu a tsakanin Nan dan salon da yake fito Mata dasu yafi karfin dan Karamin
tunaninta.gaskiya, hamdala dai tayi tafi ciki carbi.

Guri yinin ya hadu ya kuma Tara matan da suka amsa sunan su mata, Dan momin kano ba
Karamar gayya tayi ba tunda ita Ammi ta bawa wannan bangaren, mutanen Ammi na Niger
sunzo kamar Gori, gurin ya dinke da matan gayu sai sabgogin arziki akeyi an sakata Zahra a
wata kujera a tsakiya hall din ga kidan wakokin bikin na tashi Dan a kalla su Kai kala biyar Dan
ma abun ne yazo a Qure.
Kafin yamma an sakewa Zahra dress ya Kai sau biyar da mahaukatan laces na makudan kudi
duk karkashin momin kano tunda itama 'yar kasuwa ce ta gaske Dan wasu abubuwan ma tare
da Ammi suke juyawa irin kayan da ake shigo musu dasu daga kasashen dasu mahmud suke
da kamfanoni a can. Da yamma Zahra na Dakin da ake Mata canjin dress Hajiyar makwarari ta shigo iita da Aunty
Rukayya, Hajiyar Tasha wani ubansun lace tayi gwagqgwaron tsofaffi ga jaka da takalmi da
gyale duk iri Daya.
"Ina zahara'un take? Zuwa nayi na tofeki da lahaula saboda naji bakin mutane yayi yawa a
kanki to kada aje ba'a sani ba Koda Mai kambun baka, gara ki shiga gidanki salin alin salamun
qaulin, yo Ina dalili! A sakawa yarinya Idanu kowa wuwww,haba surutu ake cacacccc fadi akeyi
ai Daman mahmud sai irin wannan, to idan kasan bakin wani ai baka San na wani ba". "Kai! Hajiya wallahi kin Zama trouble haba Dan Allah tun dazu kike fada da wannan matar ta
Baki hakuri Ashe Baki hakura ba sai kin tofeta da Addu'ar'.
Ita dai Zahra kallon su take ita da abinda ya Sha Mata kai, mahmud ya sakota gaba da fitinar ta
biyewa su Ammi sai wanesa sukeyi su bashi matarsa sun Kiya sai tsaraba suke fito Masa da ita
Kala-kala shifa ya gaji hakurinsa ya Kare.
Dan murmushi Zahra tayi tana kallon Hajiyar makwararin.
"Babu abinda ze sameni Hajiya in Sha Allah, ki rabu dasu kada ace ana fada da kakata ai babu
Dadi,kiyi min addu'ar'".

"Yauwa yanzu naji magana Amma ke Rakiya ba lafazi Mai Dadi yarinya ta fiki iya kwantarwa".
Waje Rukayya tayi tana fadin "Ayi mutum sai rikici gara mu tattara mubar garin inga da Wanda
zakiyi Kuma".
"Jeki dai bazan Zuba idanu ayi ta yiwa yarinya baki ba a banza, mu tafi din ai dai nazo nayi
abinda zanyi dazu har gidanki naje aka yi addu'a kinsan malam na sanka ya taso yaro ya biyoni
Nan akayiwa gidan addu'ar tsari, yaushe Zan fadawa wannan fesado din daga sameeru sai
mijinki suka sani". Har yamma likis anata sabgar arziki an raba jaka Mai hutunan amarya da ango mabanbanta da
turamen atqmfofi wasu shadda wasu lace fa tarkacen kayan biki a ciki duk Wanda Allah yasa
rabon mutum ne shi za'a bashi, da gani kudi sun Sha kashi a gurin.
Lokacin da suka dawo gida anata Kiran sallar magariba.
Ammah ta turo kudi bana Wasa ba tace su Hasana da Hajiya kaltume su bincika yanda Al'adar
sokoto take ayi komai a nan, to Masha Allah su maman mujiba da Wanda sukazo tare da Inna
mainuna sun shiga kasuwa tare da taimakon masu aikin Ammi sun sawo har da abinda ba'a
fada bama, anyi bada komai Cikin girma da wadata. Directly sama su Aunty Hasana suka wuce da Zahra ta gaji iya gajiya, suna kokarin shiga dakin
da Ammi ta sauki Zahra aka bude kofar dakin Ammin doctor Haseena ce tare da wasu matan
suka fito wata daga cikinsu na fadin "Haba Haseenah kamar ba mace ba ki kasa shanyo Kan
mahmud har Karamar yarinya ta shige Miki gaba ta kwace Miki shi kina kallo kin Sha dakon
soyayyarsa shekara da shekaru a banza kuma ai..."
Sai tayi saurin Kama bakinta ganin su Zahrar a kofar bedroom din dake kallon na Ammin.
Wata daga Cikin matan ta nufi su Aunty Hasana tana fadin.
"Sannunku Ashe Amaryar tamu harta karaso?".
Cikin nuna wayewa da iya zama da mutane Aunty Hasanar tace musu.
"Wallahi kuwa gata Nan ta dawo kafin mu wuce mubar muku abinku ai Kuma ta Zama taku
mutu ka raba".
"Gaskiya Kam Allah ya tabbatar da Alkhairi ya bada zaman lafiya"

Matar ta fada lokacin har saura sun wuce saida da suka shiga Zahra ke fadawa su Aunty
Hasana harda likitar da mahmud ya turata ta dubata a Kano wadda tace zatayi Mata aiki, ai
itace ake cewa tayi dakon soyyaya a banza yarinya ta kwace Mata shi.
Nisawa Aunty Hasanar tayi tana tuna maganar da taji wannan yarinyar 'yar da sukazo da
Fulanin Mai Damagaram Bata San dangantakar dake tsakanin Zahra da Aunty Hasanar ba
ranar dinner ta ringa waya da kawarta a waje lokacin Aunty Hasanar ma taje amsa wayar
Daddyn su Faruq taji tana fadin. Wallahi bazata hakura da mahmud ba tunda ta ganshi Kuma yayi Mata yanda take fatan mijinta
ya kasance,aurensa Bai dameta ba ko matansa uku zata iya Zama dashi a haka tunda taga
type dinta ne, to kuma ga wata, ga kuma labarin da suka Dan samu na dalilin Barinsa gida ga
Kuma 'yan matan Cikin family dake Kara kaina a kansa, sai taji tausayin kanwar tata ta shigo
Cikin wani rikicin Kuma bayan Wanda Tasha a baya.
A hankali ta nisa tana duban Zahrar.
"Kina jina ki dage da addu'a bake Kika kawo Muhmud ba Allah ne ya kawo shi Cikin rayuwarki
kuma shine ze iya miki da kowa a kansa kada wadda ta Baki tsoro kina da duk abinda ake

nema a gurin mace Abu Daya Zaki cire a Zuciyar ki matukar kina son ki Zama 'yar lelensa ciki
da waje, to ki jurewa bukarsa a gado kada ki kuskura ya gane ke raguwa ce a wannan fannin, ki
zamar Masa briefcase duk inda ya saka kafarsa a duniyar Nan ki mayar da taki, ki rirrata shi
kamar jariri ki Hana shi kallon kowace Mace ki, zamar masa 'yar duniya ta gaske a daki ki birkita
Masa lissafi, mijimki yaro ne Mai Jini a jika ga dukiya Allah ya bashi idan ba tsarewa ta Allah ba
da yanzu dai sai abinda aka gani kawai. Amma Allah ya duba maraicinki yayi Miki kyautar da
babu Wanda ya zata, to ki kula matuka ki Kama iyayensa da danginsa Banda rowa duk da
nasan ba halinki bane, ki bar ganin masu wadata ne ko kogi Yana son Kari ki yi abinda ze Kara
Miki daraja da kima a idunusu kinji. Ina Kuma Kara fada Miki ki cire tsoron Nan nasa ki masa
biyayyar aure kinji shi ze Kara Miki matsayi a zuciyarsa ki bashi hadin kai, Kinga baya iya boye
soyayyarki a gaban kowa to ki kosar dashi ya kashe duk wata kishirwarki dake tattare dashi".
Kai kawai Zahra ta iya gyadawa Auntyn tata saboda wasu hawaye da taji sun cika Mata Idanu,
tasan shikenan Nan da 'yan awoyi labarin ze canza, tunda wannan hannu ka Mai sanda ne
Aunty Hasanar keyi Mata.
Bayan insha'i ne Aunty Nauwarah ta shigo da wasu irin turarika da burnner Dana ruwa na
wanka, toilet ta shige ta hada mata komai, ita kanta zahra tasan kamshi dai ya gama Kama
Mata jiki dan ko jibi tayi kamshi ke fita daga cikinsa, ita kanshin harya isheta Saida ta Gama
tsugune-tsugunen magunguna sannna tayi wanka ta fito Mai makeup na Zaune tana jiranta
kwalliya kadan tayi Mata Amma Mai daukar hankali, Atamfa ta saka tayi kyau sosai sai aka
Dora Mata Alkyabba Fara tas, su Inna maimuna dasu Ummee su Hajiya kaltume harda Mama
Hajiya kaltumen ta hado Dan cewa tayi ta taso itace madadin Ammah ita zata Kai Zahra
dakinta.
Sun kaita dakin Ammi daga Nan Ammin ta saka Aunty Surayya da Mummy badai'a suka rakasu
part din Hajiya Babba dana momin Kano.
Gurin Abbie ne karshe Hajiyarsu ya Abbas ce da Aunty Surayya suka raka Zahra yayi Mata
nasiha sosai akan biyyyar Aure, mahmud yasa waya ya Kira yace yazo Yana son ganinsa, da
take yana Nan kusa a Anka road ba Bata lokaci ya shigo duk da sam baya son hayaniyar
jama'a dole ya taho. A master parlournsa ya samesu yayi mamakin ganin Zahra a gaban Abbie dinsa, da sallama ya
shigo ya gaishe da Abbie din sannna ya gaishe dasu mummy, ya nemi guri ya zauna kusa da
Zahra Yana shakar wani fitinann k'amshin da jikinta ke fitarwa.
Dan gyaran murya Abbie yayi Yana duban su mahmud da Zahra wadda kanta ke duk'e.
"Mahmud".
Abbie ya karawo sunansa.
"Na'am".
ya amsa a ladabce.
"Ga yarinyar mutane Nan kaji tsoron Allah Cikin zamantakewar da zakuyi da ita iyayenta masu
karamci ne, sunyi abinda ba kowa ne zeyi a wannan zamanin ba, ka Kare Mata mutuncinta da
kimarta kada a bada fuskar da wani zeci mutuncinta ko waye kuwa, idan hakan ta faru za'a ga
bacin Raina matuka. lallai naso na riga shi Abban nata zuwa Amma yanayi yasa yazo, mun
Dade muna magana dashi ya warware min har abinda baka fad'a Mana ba, yace a Kara Yi
maka godiya, yaso mikata dakinta a Karo na biyu, to saboda Yana yin aiki dole ya bar min
amanar 'yarsa.

Kaje gidan ka jirani Zan kawota da kaina ida yaso masu zuwa ba'a hanasu ba suna iya binta
daga baya suga guri.Allah yayi muku Albarka ya Baku zaman lafiya da zuri'a Mai Albarka".
" Allahumma Amin".
Su mummy suka amsa suna mikewa zasu fice tunda Daman an Shirya ta kawai tafiya za'ayi.
"Tashi ka rakata mota na Nan Haruna Yana jiran fitowar mu.
*AUREN HUCE HAUSHI*

AISHAT ISAH MUSAH.
Maman Fateemah
09061432330
08055362975


Wannan littafin ba MALLAKIN kowa bane gurin juya shi ko sarrafi shi Audio ko wata sigar Saida
izinin marubuciyar.


Page 82.
....... Mahmud na tsaye a compound din gidan motar Alhaji Muhammad ta shigo a hankali har ta
tsaya a dai dai steps da ze sadaka da babbar kofar shiga ciki, da sauri mahmud yaje ya budewa
Abbie kofar dake tsakiya ya fito yayin da Malam Haruna ya budewa Zahrar kofar karshe ta fito,
mahmud ne yaje ya bude kofar Abbie na gaba Zahra na biye dashi. Suna shiga Cikin Zahra taji wata irin karaya tasan karshen tika tik, duk wani zagaye zagaye yau
dai ne final, gata a sokoto a gidan mahmud inda ya ta'allaka duk wani burinsa da yake kanta.
"Ya Ilahiy!"
Ta furta da siririn sauti.
Har bedroom dinta Abbie ya kaita yayi Mata umarni data zauna a Kan gadon ta, ba musu ta
dosana tare da Bismillah ta zauna a darare, Abbie din da Kansa ya dunga kwararo musu
Addu'oi Cikin harshen larabci mahmud na fadin Amin.
Abinda ya karyawa Zahra zuciya kenan shaukin mahaifanta ya taso Mata yanzu da itama nata
suna Nan da watakila shine a tsaye yake kwararo masu wadannan Addu'oin, duk da su Ammah
da Abbanta Basu taba Bari tayi kukan maraici ba,amma masu iya magana na fadin gurbin idon
ba Ido bane, ita kaunar d'a da mahaifi daban take Allah s.w.a. ke sanyata a tsakaninsu, ba zato
sukaji saukar siririn sautin kukanta.
"Haba Fateemah ya zakiyi kuka Kuma? keda nake ganinki jaruma, ai masu babban suna basa
kuka, ko su Abban naki da Malam dole sukayi Miki suka hadaki da Hussein? fada min yanzu na
koma dake kije ki zabi Wanda kikeso na aura Miki kinji 'yata".
Zuru mahmud yayi yana kallon Abbie din yasan da a wancen lokacin ne irin wannan ranar da
Abbanta da Abdul Hakeem suka Kai Masa ita ta samu irin wannan damar babu abinda ze
hanata fadar Bata sonsa, sai dai yanzu yasan ko tana Shan giyar wake bazata Fara ba Dan shi
Kansa yasan ya Bata darussan da barinsa ze Mata wahala duk talauci kuwa Dan yasan duk
shegantaka ce ke sakata wannan koke koken Bata ji dai dai ba da tuni labarin ze canza.Amma
a juri zuwa Rafi da sannu za'a fasa tulu.

Shiru Zahrar tayi tana ajiyar zuciya, dan murmushinsu na manya yayi ya nufi kofa Yana fadin.
"Kiyi hakuri haka shine girma kinji Diya ta,idan yayi Miki ba dai dai ba ki fada min nine Zan
hukuntashi Allah yayi muku albarka ya Albarkaci aurenku da 'ya'ya masu Albarka ya kade muku
fitina ya Baku Zama lafiya ayi ta hakuri kinji 'ya ta Zan tafi, ki yiwa mijinki biyayya ki bashi
girmansa da Allah s.w.a ya bashi kinji'. Kai kawai ta iya gyada Masa saboda kukan da takeyi. ficewa yayi daga dakin Yana Jin wata
nutsuwa ko ba komai Dan nasa yayi dacen da kowane uba ke fatan dansa yayi, yasan in Sha
Allah za'a samu nagartacciyar uwa a gurin Nan.
Da sauri mahmud ya biyo shi a baya sai ganinsa yayi.
"Yaya ka fito ka barta kaje ka lallasheta Mana kasan mata 'yan lallashi ne".
Sunkuyar da Kansa yayi sai yaji Yana Jin nauyin hada Ido da Abbie din nasa, Dan shafa gefen
fuskarsa yayi, Shima Abbie din murmusawa yayi ya nufi mota Yana kissima yanda Dan nasa
yake Cikin farin ciki Dan masu iya magana suna cewa labarin zuciya a tambayi fuska, Sai dai
yana nuna kawaici ne a gabansa. Abbie na barin gidan Shima ya shiga motar da yazo da ita ya fice Yana fita motocin Ammi suka
doso gidan Daya Aishat ke ja sauran Kuma be tantance ko su waye ba, fitila Aishat tayi masa
tayi gaba itama ta gane shi.
A Cikin motar Aishat su Ummee ne sai Mama sauran Kuma su Hajiya kaltume ne 'yan tawagar
Ammah sai tawagar Ammi dai saura motocin gidan Kuma jama'ar su Mahmud ne da matan
gidan.
Tun a kofar gate din gidan Mama ta Raina kanta balle da aka shigo ciki, take taji kirjinta ya Fara
ciwo har wani jiri yake daukarta a daddafe ta shiga ciki a Nan Kuma taga abin al'ajabin Daya so
ya zautata Dan abinda Bata taba tunanin ze faru bane take gani. Wai wannan gidan na zahra
ne itace mamallakiyarsa ita zata rayu a cikinsa. Lungu da sako ba inda Aishat Bata shiga dasu
ba,master bedroom dinsu ne kadai Bata bude ba,da yawa sun Zama 'yan kauye a gidan, dan
sunga abinda Basu taba gani ba, dakin Zahra da kawayenta Wanda suka shigo Babu dadewa
suka shiga suna ta rarinarsu da dauke dauken hotuna. su Hajiyar suka shigo ai ganin da gaske
Zahrar ce a zaune a Cikin dakin Kuma da sunan mamallakiyarsa.
Wani Abu Mama taji ya soketa a kahon zuci da kyar ta iya sulalewa ta zauna a bayan wata
Mata tana dafe kirjinta.
Babu Wanda ya lura da halin da Mamar ta shiga tafi minti uku a haka kafin ta samu rangwamen
ciwon ta Mike ta fice tana Jan kafa Dan ji tayi sunyi Mata wani irin nauyi.
Har goma da rabi gidan da jama'a Amma da yawa bakin sun wuce sai danginsu na Cikin garin
sune suka nemi gurin suna baza hajarsu ta yin hotuna, sai Aunty safiya wadda gidansu babu
nisa da unguwar da aka Kai zahrar. Yawancin kawayen duk kasa suka sauko ya rage daga
Zahra sai sajeeda da Amatullah. Aunty safiya Batasan lokacin yaja haka ba Saida ta duba
wayar hannunta taga quarter to eleven sannan ta ankare ta cewa Amatu ta taso su wuce.
Sallama suka yiwa Zahra Amatu na fadar.
"Kiyi Masa biyayya dai yauwa kada naji kada na gani, ko Aunty safiya?"..
Ta fada tana kallon zahrar wadda ta sadda Kai kasa tana Wasa da siririn zoben gold da yake
hannunta.
"Dan Allah Amatu ki rabu da ita tun safe kika damunta, ba gara ita ba Dan an kusa shatanta ta
warke ba, ke kuwa kece a kwana Dan Naga wannan Tajuddeen din da yake dama-dama dake

guda ne da alama kema garin namu Zaki shigo".
"Ki rabu da ita Aunty safiya Zan rama ne, wallahi yanzun ma Ina Jin kunyar Aunty na ne baiwa
bani da bakin magana ba ki Bari dagani sai ke kiji magana, Naga alamar ko irin Jan aji Nan
bazakiyi ba Daya kiraki kike Fara tsuma kamar wata tsohuwar kilaki".
Ta saka gefen Alkyabbar ta rufe fuskarta dashi tana Mata dariya.
"Wallahi kinci bashi saina biya Shi kuwa Dan tsabar iya sharri Zaki wani ce Daya Kira nike kama
tsuma".
Hannun Amatu Aunty safiya ta janyo tana fadin.
"Zomu tafi ramawa tayi tun farar safiya kike Mata Dan biki ai kadan ma tayi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login