Showing 6001 words to 9000 words out of 62795 words

Chapter 3 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf

03 Aug 2025

8781

Allah menene haka ka wani kanainaye ta kaki Bari ku fita guri ya hadu ku kawai ake jira
gara dana rako Auntyn Zahra da baka niyyar fitowa kenan?".
Dan matse hannun Zahra yayi yana kallonta kafin ya kalli twins sister dinsa.
"Kina da damuwa zuwa fa nayi mu tafi, nifa da wucewa zamuyi bana son wannan bidi'ar naga
gurin ya cika da maza Kuma dubi rigar dake jikinta duk Nan fa a waje yake".
Ya Kai hannu yana nuna mata, Zahra ji tayi kamar ta nitse a gurin, taga ta kanta shi Wai baya
Jin kunyar Aishat din ne.
"Allah ya shirya gaskiya gara ku tattara ku Kara gaba Naga alamar idan tana kusa da Kai baka
da saiti duk nutsuwarka barin jikinka take, sai kaje ka jiramu abinda Auntyn ta tazoyi kenan tace
wannan fitar batayi Mata ba ta dauka akwai wasu events din bayan wannan nace Mata Babu
sai budar Kai gobe kawai". Jinjina Kai yayi ya wuce Yana fadin.
"Ki fadawa Auntyn Banda Mai net a kirji Dan Allah".
Rike Baki Aishat tayi tana binsa da kallo.

"Kai Kuma naka salon kenan? Auntyn Afnan kuje Auntyn ki na jiran mu gara ayi abunda za'ayi

ku shiga ku kadai ake jira".
Kwalkiyar da akayi yanzu tafi ta farko daukar hankali nesa ba kusa sai Zahrar ta zama tamkar
fure tayi kyau iya kyau Dan ta farko Wasa ce.
Aishat tayi Mata hotuna tamkar ba gobe, wani murmushi ne ya kubce Mata zataga yanda Dan
gidanta zeyi da yake complain din wancen gown din to ga wata wadda tafi waccen sai dai ita
babu ne daga sama ba'a ganin breast din kamar waccen.
Sajeeda ce ta dawo tana fadin.
"Bestie kina Ina ne ki fito ana jiranki fa".
Ganin su Auntyn yasa ta Dan tsaya tana kallon Zahrar ganin Cikin abinda Bai wuce minti Sha
biyar ba an sake Mata wani Shirin na musamman.
" Wow! Masha Allah bestie Allah ya kade bakin mutane kinganki kuwa?".
Dan murmushi tayi kawai.
"Ato gata Nan bansan ya angon naku zeyi ba Naga alamar dan banzan kishi gare shi, wa yace
ya kawo ta gidan a haka? Ai dole ya kauda Kai Dan dinner dai sai anjeta babu fashi in Sha
Allah".
Ita dai Aunty Nauwarah kallonsu take tunda ba Hausar takeji ba.
Wasu tsaraddun turarika ta shiga fesa Mata masu sanyin kanshi.
Tare suka fito suka raka Zahrar a cikin motar da zasu tafi a ciki, shi Dan gogan kasa magana
yayi Dan yana kukan targade saiga karaya ta samu, Yana korafin waccen wedding gown din to
Kuma saiga wannan ita ba transference bace Amma ta fiddo da structure din jikinta sosai.
Bai daiyi complain ba suka wuce Sameer na jansu, Suna fita motocin guards dinsa dake waje
suna dakon fitowarsu suka saka motar a tsakiya suka wuce. Su Aunty Aishat ma suka wuce da
sajeeda.
Suna shiga harabar gurin sajeeda taga yanda motocin Alfarma suka cika wurin tasan ba karya
anzo gurin, Dan tunda suka shigo sukaga yanda Families din mahmud suke suketa mamakin
abun bare ita sajeedar da tasan komai a game da shi, tayi mamakin mema ya fitar dashi daga
irin wannan daular ya gwammace rayuwar da yayi a Azare da wannan. Ango da Kansa ya budewa Amarya ta fito Yana rike da hannunta suna tafiya Yana gaisawa da
jama'arsa suna bin carpet din da a saka musu a hanya photographers sai aikisu suke masu
dauka da wayoyin hannunsu Suma suna ta faman daukarsu Dan wani irin perfect match couple
ne Wanda kafin a samu irin wannan hadin ana dadewa kyau ne ke dukan kyau. Suna shiga da tawagar abokansa na kusa Dana nesa sai kawayen Zahra,r music din Larabawa
na tashi a hankali sai kus-kus mutane kowa na zaune gentle ba wani hayaniya Dan ba karya an
hada manya masu ji da kansu a gurin kowa Yana cewa wane kauce bani guri.
M.C ne ya Fara bazawa Amarya da ango kirari har suka zauna a inda aka tanadar musu, Nan
da Nan guri ya dauki surutun mutane wasu suka taso suna daukar video wasu suna daukar
photo, 'yan Mata da yawa masu son mahmud sunyi giving up, sun San idan ba wani
kwakwkwaran rabon ba babu yanda za'ayi DANGE ya dubesu da sunan soyayya, wakar Auren
su wadda Akayi mc ya saka.
A gurguje Sameer ya bada tarihin mahmud har ranar da suka Fara ganin Zahra ita da Abbanta
a jirgi ya fada, sai lokacin Abban Zahrar ya tantance inda ya Fara ganin fuskokinsu tabbas anyi
haka Dan Mai maganar har Jordan sukaje tare, wato tun lokacin suke bibiyar ta kenan sauran
bayanin ne kuma baisan yanda akayi ba.

A bagaren Zahra sajeeda ce ta fito ta fadi tarhinta a nan da yawa suka San ruwa biyu ce Dan
duk Wanda ya ganta zeyi zaton gaba daya Arab din ce tunda su ta dauko sak, an tanadi abinci
Kala-kala da nama ya Kai Kala goma gashin nan serve your self ne ga drinks Nan tamkar
banza, Zahra tayi mamakin ganin su Abbanta Koda Wasa Bata taba kawo hakan ba tunda bece
Mata zezo ba yace dai sai daga baya ze shigo ya ganta, taga su Ya Abdul Hakeem dasu ya
Hamza bare magaji da taga ya Zama Dan gida ya kasa tsugun.
An saka kidan larabawa wasu Mata Wanda da alama dasu Ummee sukazo suka shigo sukaga
ringa rawar larabawa Mai ban sha'awa.
Daga Nan aka bukaci Ango da Amarya suzo su yanka cake Zahra ji tayi duk ta daburce ganin
Ido yayi Mata caaaa.
Ganin taki motsawa yasa mahmud ya murzawa idanunsa toka Kuma ma dai da biyu yayi hakan
Dan yaga wata fuska sanye da musk Kuma ya hakikance Safna ce Dan ko me zatayi bazata
taba bace Masa ba.
Tsam ya saka hannu ya Mikar da ita abunda yasa matasa dauka tafi Sai Kuma hasken plasher
tako ina.

Shiya Fara Bata cake din sannan ta bashi duk a kunyace, mc Bai Bari suk koma ba
announcement ya Fara Yana neman dangin Amarya da turanci tunda yagansu farare tas, ya
saka wakar Amr Diab 'yar kasar Egypt.
Ummee ce ta taso wasu Mata biyu suna bayanta dauke da wata jaka tana zuwa ta Fara
zazzaga musu ruwan stalling pounds na England sai Kuma su Mama Haneefa dasu Aunty
Nauwarah suka shigo suna ruwan American dollars Nan da Nan guri ya dauki tafi, Ummee Bata
koma ba saida ta yiwa ango kyautar estate a cikin garin madina sannan aka bashi jajayen
rakuma goma da kyauta tickets na kashe biyar na Honey moon.
Aunty Hasana ma dasu Inna mainuna sunzo sunyi rawar gani Dan shanu goma ris ta bawa
ango sannan wasu goman biyar uwa biyar uba da kuma zunzurutun kudi har miliyan ashirin na
dangin uwa da uba sai karsanoni hudu na abokan zaman Ammi sai guda hudu da million daya
nasu Hajiya Inna da Hajja dari biyar biyar. Abinda ya girgiza da yawa daga Cikin masu ganin Zahra ba 'yar kowa bace irin fakarahun
yayan larabawa Nan ne masu azabar kyau din Nan da yawancin mazanmu masu kudi ke
aurowa Dan neman irin Mai kyau Cikin zuri'arsu.
Bayan gama tafi da sowar tuwon girman da Ummee tayi aka nemi dangin miji,sun shigo kamar
Gori maza da Mata sunyi barin kudi kamar ba gobe Ammi ta fito da tawagarta ta yiwa Zahra
liken CFA kudinsu na Niger Hajja ta bawa Zahra kyautar shanu da zunzurutun CFA million
goma. Da sarkar zinari wadda kudinta sun tasarwa million tamanin take aka Miko cheque na eco Bank
tunda shine bankin ecowas.
Amarya da angon sun Sha kyautukan girma suna niyyar komawa wurinsu wata Mata cikin sauri
take ta yiwa mc magana, Nan da Nan ya dakatar da tafiyarsu Yana fadin.
Ga Mai gayya Mai aiki tazo Fulanin Mai Damagaram aminiya ta hannun damar uwar ango
Hajiya zainab.
Wata farar Mace Yar gayu tare da amintattun bayinta sai wata yarinya budurwa dake tare dasu
Saida suka matso sosai Zahra ta gane yarinyar Wadda ta kafa musu Ido ce a train station

lokacin da zasu Jim Corbett national Park a Uttarakhand state. Take Zahra taji wani Abu ya
tsaya Mata a kirji, yanda taga yarinyar na Mata wani kallon kasa kasa irin Mai nuna baka Isa din
Nan ba.
Saboda a wancan lokacin taga irin kallon kurillar data kafesu dashi.
Fulanin na zuwa ta rungume Zahra tana fadin.
"Tabarakallah Masha Allah, Zahra diyata sannu da kwaramniya".
"Yauwa Mama, nagode".
Wani kallon banza yarinyar ta gara jifan Zahra dashi tana wani kawar da Kai gefe tana hade rai.
Liken kudi Fulanin ta Fara Yi musu haka 'yan tawagarta ma haka da alama an shiryawa wannan
ranar, amma ita yarinyar mahmud kadai take yiwa Saida mummy Badi'a tazo ta janye Fulanin
daga gurin ganin lokaci ya Fara ja tasan abokansa da kawayen zahrar suna son Suma su nuna
tasu bajintar, a gurin dollars dai da pounds sunyi kuka. Mama ta Raina kanta iya rainawa taga inda ake maganar arzikin da babu fariyar a cikinsa sai
dai idanunka su fada maka, taga yanda matan uba ke kyautar mamaki Dan kowacce ta bawa
Zahra tata kyautar.
Ba'a tashi ba sai kusan Sha biyu da rabi.
Sai da aka tashi sannan Ammi suka gaisa da Fulani wadda ta sauka a Daren Dan Bata kasar
lokacin da Ammi ta kirata ta fada mata danta ya dawi har da tsarabar Daya dawo musu da ita.
A gajiye aka dawo gida danma an kamawa mutane da yawa dakunan hotels Dan duk matar da
tazo daga Azare a mota ta biyu duka hotel aka kaisu shi yasa sai a gurin dinner Zahra taga
wasu mutanen harda su Aunty zilai dinta Dan har liken Yan dari biyar sabbi tayi Mata. Duk
yanda mahmud yaso ya wuce da Zahra Aishat da Aunty Nauwarah sun kasa sun tsare,dan
Aishat ce tayi Mata tsegumin abinda take zaton ze aikata Dan taga dazu ya birkice da yawa
idan aka barshi ko budar Kan baza'ayi ba ga momin Kano kuma ta shirya masa Dan lokacin da
akaje da maganar ko a hakura dayin wunin tsalle tayi ta dire akan babu fashi sai anyi me zata
yiwa mahmud ta biya shi kaunar da yake yiwa Faruq ya dauke shi tamkar uwa Daya ta haifesu
ya bude Masa yanda ya kamata hatta karatun da yayi mahmud ya zabar Masa saboda ya ringa
yi Masa ayyukansa.

Mahmud yana ji yana gani Sameer ya wuce dasu zahrar ita dasu sajeeda da Amatu.
Zahra a gurin su Ummee ta zauna sun Kai kusan biyu Aunty Nauwarah na saka Zahra a wasu
irin ruwan magunguna masu azabar kamshi ga turaren jiki Wanda sai da kamshimsa ya game
part din gaba daya, abin isar Zahra yayi Dan idan ba so suke yayi Mata lahani ba ya kamata a
kyaleta haka ita kadai ranta sai abubuwa ake Mata Babu sasaauci,ko Dan Basu San abinda
idanunta suka gani bane. Kawai a Riga suke ganin mutum Basu San sirrin dake lullube bane.
Gado Daya suka kwana da Ummee Zahra nata mitar Ummee ta manta da ita, data isheta da
magana Ummeen ta fada Mata Abbu ne bashi da Lafiya ai mijinta ya sani Dan yaje har London
ya duba shi, shine yayi blocking din layinta a wayoyinsu yace idan aka Bari Kika sani Zaki tada
hankalinki gashi kema lokacin yace Baki da lafiya. Gyara kwanciya Zahra tayi tana mitar abun, kamar ta hakura sai kuma tacewa Ummee.
"Wai Dan Allah Ummee a Ina Mika san...."
Sai Kuma tayi shiru.
"A'a Fadi Mana a Ina nasan mijinki".

Dariya tayi tana rufe Ido.
"Makocinmu ne a can Jordan gidansa Yana kallon namu".
Tashi zaune Zahra tayi tana duban Ummee.
"Badai wannan gidan da nake cewa yayi min kyau ba gashi Naga an saka Masa suna a
samansa GIDAN ZAHRA".
Dariya Ummee tayi to ai daman gidan na zahrar ne haka Shima ya fada min tun kafin nasan ke
zahrar tawa yake nufi, ko aikin gyaran gidan Abbie ne ya samo Masa masu yin duk sadda ya
shigo Jordan Yana gidan mu, Bai Kuma taba fada Mana ya sanki ba Koda wata manufar da
take kawosa gidan, sai bayan an bashi ke ya kirani yake fada min an bashi Mata idan ya shigo
ze kawo min hotonta na gani.
Ranar Daya zo da yammaci ya shigo yaci abinci sannan ya bude ya ringa nuna min hotunanki
tun kina 'yar matashiyar ki har na girmanki, ba Karamin mamaki hakan ya bani ba Daman yasan
kina da alaka da Dani ko Kuma arashi ne kawai.
Dana tambayeshi ba wani rufa-rufa ya fada min yasan matsayinmu a gurinki.
Zahra tayi matukar mamaki Amma Dan tahalikin Nan Bai taba nuna Mata yasan su Ummee ba
Koda Wasa, Sai dai Daman tayi matukar mamakin yanda taga suke mu'amala abun kwarai ya
bata mamaki babu wani bakunta a tattare dasu.
Sun Jima Ummee na Bata labarin yanda suka shaku da mahmud din sai taga ita ai ya fita shiga
jikinsu ma sosai.
Washe gari da wuri Aunty Hasana dasu Aunty Nauwarah da sauran mutanen Ammah Hajiya
kaltume ta turasu tare da Aishat wadda zatayi musu jagora suje a duba abinda ya kamata a
gyara a gidan da za'a Kai Amaryar tunda company ne sukayi jeren kayan da akazo dasu na
zahrar duk da mahmud yace ba gurin saka komai, dole ya bada part dinsa na gidan Hajiya Inna
aka zuba kayan tunda baiyi niyyar saka masa komai ba a lokacin domin guda biyu aka Gina
Daya na zahrar to an Riga an saka masa furnitures sai dayan da dole tasa aka yi Masa paint da
abinda ya kamata aka saka kayan a can. Basu wani Dade ba suka baro can din tunda babu
bukatar yi masa komai sai dai turarukan daki da aka saka, Basu dawo gida sai da aka kaisu
gidan da za'a Kai Zahra, permanent gidanta gidan Hajiya Inna temporary ne na week end da
yada zango Idan an dawo daga tafiya Dan Alkawari ne duk inda yaje ya dawo gidanta ne farkon
sauka.
Sunyi santin gidan tamkar ba'a Nigeria mutum yake ba Dan Maman mujiba kasa shiru tayi da
bakinta lokacin da Aishat ke shiga dasu guri guri a kasa taga parlours sun Kai hudu ga sama
sun hau taga common karfen dake Jikin stairs shi Kansa tamkar na zinari sai daukar Ido yakeyi
ga gidan ko Ina daukar Ido yakeyi ga haukatan bedrooms ga toilet ga gani na fada Dan wani
abun ko a hoto Bata taba ganinsu ba. Ja tayi ta tsaya tana kallon Aunty Hasana.
"Dan Allah Hasana Wai Yaya Aljanna take ne?"
Ba Wanda baiyi dariya ba a gurin kuma ita har zuciyar ta tayi tambayar.
Ganin suna dariya yasa ta Kara fadin.
"Wallahi da gaske nake tambayar Nan, ki dubi gidan Nan Wai a sokoto yake? Ni tunda Allah ya
halicceni ban taba shiga makamancinsa ba, Nan gidan zahra ne wadda ake tsegumin an
aurawa Almajiri kolo marar galihu marar komai, ana ta zunden Alhaji idan ya wuce a unguwar, a
cikin gidan Kuma ana sakin habaici an ce kyau ya Kare a Wanda ba'asan asalinsa ba, to yau
kowa yazo yaga inda Allah yasa Alhaji Jafar ya kawo marainiyar Allah gidan da hasashe be

taba hasasowa ba, tunani Bai taba tunanowa ba, Hasana saka wayarki ki daukar min gidan Nan
ciki da waje sai masu tsegumi sun gani da idanunsu, 'yan bakin ciki kuma su mutu tunda
Alkawarin Allah baya tashi idan yace Kaine sai kakai, lallai Dan tsiron da Allah keso ko babu
ruwa saiya rayu, yau Zahra ta Zama farin wata Sha kallo. Masha Allah Arzikin mutum a jikinsa
yake Kuma dare ga Mai rabo hantsine".
Guda ta rangada har sau uku tana Kara fadin . "Idan Rana ta fito tafin hannu baya kareta,
walkiya inta haska wanene ze iya kareta? Hadari In yayya tsawa rufe kunne baya Hana jinsa ga
Zahra ikon Allah sai kallo".
Kudi Aunty Nauwarah ta Ciro dollars ne saura Wanda ta zubawa Zahra ta Zubawa maman
mujiba Dan ko Bata Jin abinda take fada tasan kurare 'yarta takeyi, ko ita da suke a kasashen
da sukaci gaba gidan Zahra ya tafi da ita Dan babu karya anyi gidan tamkar baza'a mutu ba
Dan dukiya dai an kasheta tamkar ba'asan ciwonta ba.

******

Saida zahrar tayi barci Mai isarta sannan ta tashi, lokacin wurin Sha Daya. Wanka ta shiga tayi
data fito tayi break fast sannan ta shirya, Aunty Nauwarah tayi Mata makeup mai daukar
hankali. Doguwar rigar atamfa green Mai milk din fulawoyi ta saka tayi amfani da gyale milk da
takalma plat milk, wayarta ta dauko wadda ta sakata a silent tun daren jiya saboda message din
data gani na mahmud da yake son dole ta fito Yana ta bayan part din Ammin, idan ta fita akayi
Dace wani ya ganta ai noway out, cewa za'ayi har satar jiki take tana zuwa gurinsa, dubawa ta
shiga yi na meu amor ta Fara bi kasancewar Aunty Nauwarah Bata Jin hausa yasa hankalinta
kwance ta kirasa.
Harta yanke be daga ba sai taji wani irin ba Dadi a zuciyarta.
Ya Abdul Hakeem ya Nemo wayar taji a Ina suka kwana.
Dauka yayi suka gaisa kafin ta Dora da fadin.
"Ya Abdul Hakeem a Ina kuka kwana ne? Kuma Ina Abbana wallahi kunyi surprised dina banyi
zaton zakuzo ba wallahi".
"To Ni dai gani Nan a wata unguwa Wai kome? Na manta Abba kuma sunbi jirgin bakwai da rabi
yanzu haka ya sauka a Bauchi sun dauki hanyar Azare".
Wayyo Ya Abdul Hakeem yanzu Abbana yazo garin Nan na kasa gaisawa dashi".
"Kinsan halin Abba ai yace ze dawo special yaga masaukin ki, kinsan ya w
Sun jima suna waya daga baya sukayi sallama.
Aunty Hasana ce tazo ta raka Zahra Dakin Ammi ta gaishesu sannan ta mayar da ita masaukin
da Ammi tayi mata.
Sai wurin karfe biyu mai yin makeup wadda momin Kano ta dauko takanas tazo Shirya Amarya,
tayi Mata makeup light, ta Zuba Mata wani material Mai ubansun kyau ta daura Mata head sai
zahrar ta fito a tauraruwarta dan komai hassadar

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login