Showing 60001 words to 62795 words out of 62795 words

Chapter 21 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf

03 Aug 2025

8801

tasa bazeqi fada Mata ba, to bayan ta Kira ta fada Mata yanda sukayi da Kuma
Abinda result din scanning ya bayar shine mummy din tace ko gida ze dawo da ita tunda ga
yanda abin yake kada su birke cikin, da kyar ya shawo Kan Ammin ta hakura suje umarar daga
can suje Jordan din.
Sunyi umara sun karasa azuminsu a saudia ranar idi suka koma Madina duk da can suka sauka
sukayi ziyarar qabarin Manzon Allah s a.w.w

A bin mamaki a can suka samu Ummee da Abie Suma sun zo sunyi umarar sunso Zahra ta
kwana a gurinsu Amma kememe ta k'iya tace unguwa zasuje jidda gobe sun dawo,haka tabi
Mahmud suka wuce ai Bata son Abinda ze raba su dashi Nan kusa saboda yanzu ne komai ze
tafiyar Mata daidai an Gama Azumi Sun Riga su Ummee zuwa Jordan a gidan daya saya kusa opposite dasu Ummee suka zauna
gidan da yake tafiya da imaninta ga shi ansa masa gidan Zahra Ashe nata ne.
Ranar dasu Ummee suka dawo a can take wuni har dare da yake ba 'yan fitinar bane a
kanta,tun a saudia Ummee ke ganin zahra da wata Kama Amma fata furta Mata ba ta dai San

da magana.
Watansu Daya a Jordan suka wuce Oman 'yar karamar k'asar larabawa ce Mai dadin Zama ga
wadatar arzikin man fetur.
Nan ma sunyi kwanan wata Daya a cikinta lokacin cikin watansa hudu dai dai lokacin ne Ammi
ta hurawa Abbie wutar nacin ya yiwa Hussein magana ya dawo da yarinyar nan gida tunda cikin
ya Fara mik'awa dole tasa yayi maganar, badan Mahmud yaso ba suka tarkato suka nufo
Nigeria, suna dawowa da sati daya suka nufi Azaren katagum, murna gurin Zahra kamar ta
zuba ruwa kasa Tasha zayyan ne ya daukosu daga Bauchi inda suka sauka, Saida suka Fara
shiga Azaren sai Kuma wata irin kunya ta rufe zahra a hankali ta Kara shigewa jikinsa saboda
da Abinda yayi musu shamaki da zayyan din da Daya daga cikin yaransa dake gaba.
"Nifa kunyar Ammah nakeji wallahi tunda magaji ya kirani yace min wai yagi su Ammah suna
magana da Ammy Wai Ina da ciki bakaga ko Ammyn na kasa hada Ido da ita ba? Kowa fa
yasan Abinda akayi kenan fa".
Baisan lokacin daya Fara dariya ba, dan bilhaqqi da gaske kunyar takeji, ya gani a kwayar
idonta.
"Gyara Mata Zama yayi sannan ya lakuce Mata cheeks dinta.
"Ki share kawai kowa yayi aure Abinda ake fatan ganin an samu kenan shine Albarkar Auren ai
bakiga idan babu haihuwa ana shiga damuwa ba har ya Zama matsala wani karshen Auren
Kennan?".
Kai ta gyada Masa badan zata iya murje idanun ba.
Sai kusan shida na yamma suka shiga unguwar Famfon shanu direct gidan Malam suka nufa
Wanda aka rushe akayi ginin zamani,Sam zahra batayi mamaki ba indai shine to zeyi Abinda
yafi haka. Suna tsayawa mutane sukayo chaccc saboda zuwa lokacin an San waye Mahmud
din malam, suna Dubai ya turowa da Habib kudi aka sayi shinkafa dasu filawa da suga,mai,
gero da masara aka raba a unguwar a wadace harda kakocin unguwar unguwar.
Ciki Zahra ta wuce bayan sun gaisa da Baba malam ta samu iya Abu da wasu Mata biyu da
alamar bak'i tayi, da farko bata gane zahra ba Saida ta karaso sannan ta waye da ita.
Sun gaisa tana ta kakabin yanda zahrar ta koma.
Bata Jima ba ta fito har lokaci Mahmud Yana tare da jama'a Amma tun fitiwarta hankalinsa ke
kanta harta shige gida, da Auta ta Fara cin karo da gudu ya juya yana fadin "Ammah! Ammah!!
Ki fito ga Adda zahra".
Magaji ne ya dakatar dashi.
"Dallah ka cikawa mutane kunne a gidanwa kaga zahrar bayan dazu mukayi waya nasan kuwa
da zasuzo zata fada min".
Sallamar Zahra ta kashe Masa fadan da yake yiwa Auta, Ammah ce ta fito tana bin ba'asin
fadan da ake yiwa danta sai ganin Zahra tayi tana shigowa cikin parlourn.
Ai tuni Zahra ta manta da wata kunya ta fada jikin Ammah.
"Kibi a hankali Mana keda bake kadai bace".
Sinne kanta tayi jikin kafadar Ammahn.
"Kai gaskiya gara dai ki haihu mu huta da halin yaran Nan da kike Mana a gidan Nan".
Magaji ya fada Yana nufo inda suke.
Bayan magariba Ammah da zahra suna Zaune suna hirar yaushe gamo irin ta da da mahaifi
Ammahr ke fada Mata bikinsu Abdul Hakeem fa an saka shekaran jiya duk gaba Daya za'ayi

harda kanwar mijinki da aka bawa Habibun malam.
Sai lokacin ta tuna sakon sajeeda ta gani tana fada Mata an saka Rana ta basar ta dauka tana
zolayarta ne.
Baywn insha'i Mahmud ya shigo suka gaisa da Ammah tayi Masa godiya abin Alkhairin da yayi
Mata duk da tayi Masa ta waya, gurin Mama yace Zahra ta raka shi ya Kara dubata, sai lokacin
zahra ta tuna da ita a gidan Dan tunda ta shigo ko duriyarta bataji ba.
Tare suka fita suka nufi dakin a hanya zahra ke tambayarsa.
"Amma dai ba rashin kirkin zaka Kara Yi Mata ba dai ko?".
"Kai! Nine marar kirkin?".
"To ai Lamarin naka ne ba'a ganewa a fuska sai ka aiwatar ake gani".
'yar dariya yayi.
"Kinci bashi".
Sau biyu zahra tayi knocking sannan aka bude, Saratu ce Autar su Mama ta bude ita gaskiya
tana da kirki ba kamar su Mamar ba, da fara'a ta Fara fadin "Masha Allah Ashe Amarya ce,
sannunku da zuwa". Ya fada tana Basu hanya, Saida suka shigo ta rufe kofar ta biyo bayansu
tana Kare musu kallo ta tashihi ga ubangjiin dake tsara halittar bayinsa. Mamar tana Zaune da casbaha a hannunta tana lazimi, saura kadan dariya ta kubcewa Zahra
ita dai iya saninta da Mama Bata tab'a ganinta a Zaune Wai tana zikitillahi ba, tayi collapse tayi
wata irin Rama ga bakinta ya karu sai idanu a waje, tana ganin Mahmud ta sadda kanta kasa
tana jiran taji yau Kuma Dame yazo. Har kusa da it's suka karasa zuka zauna a kujerar kusa da ita, saratu ta gaishe da Mahmud duk
da ta girmesa nesa ba kusa ba,ya jajanta Mata Mai jiki, sannan Zahra ta gaisheta suka gaishe
da Mamar da jiki, Zahra dai tayi shiru taji yau Kuma meze baro Amma sai taji yayi shiru daga
karshe ya Bata cheque na kudi Wanda suka girgiza zahrar yace a Bata gudunmawar bikin Yara
da akayi ta tashi tsam ya nufi kofa Saida ya kusa Kaiwa kofa ya jiyo muryar Mamar tana fadin
Dan Allah ka karbi kudinka wallahi Abinda kayi min ma nagode.
Baibi ta kanta ba ya fice Zahra ma ta tashi tana fadin "Allah ya Kara sauki".
"Amin ya Hayyu ya Qyyum".
Saratu ta fada tana faman godiya, Mama na shafe hawaye ta Fara fadin "Zahra Dan Allah ki
yafe min Kona samu salama wallahi sharrin.shedan ne da Shawarar Aunty ladi Amma in Sha
Allah bazan Kara yiwa kowa mugun Abu ba, Dan Allah ki bawa Abbqn ku hakuri yasa Baki 'yar
uwarki ta koma ta karasa karatunta tinda ita shafi ce ta shafeta, to mijin yace sai yaji daga bakin
Abban naku ze barta ta koma shi Kuma nayi Masa magana har Ammah ma tayi yace duk
Wanda ya Kara masa magana zega bacin ransa".
Sai hawaye, itama zahra zuciyar imani sai taji nata idon ya ciko da hawayen da sauri ta nufi
kofa ta fice itama, Dan da gaske tausayin Mamar ya kamata babu nuna isa ba izza ba nuna kin
jini saima nadama karara a idanunta.
Data fito bayanan ya fice sai wurin goma ya kirata yace ta fito su wuce.
Satinsu Daya a Azare suka koma sokoto, cikinta nada wata biyar da 'yan satittika aka Fara
bikinsu Habib da suhailat, Ya Abdul Hakeem da sajida, sai Aunty Rukayya da zakariyya Ya
Abban sajida, ita Zahra abun ya hade Mata amma Kano ta nufa tunda an sassab'a kwanakin
programs din da za'ayi.sun hade daurin Auren a Kano tunda na Ya Abdul Hakeem a kanon na
suhailat a kanon Dan Alhaji sa'ad mahaifin su Sameer ne ze daura gana Rukayya Shima dai a

kanon A masallacin Jama'a na round din Dangi aka daura Auren.
Sai dinner ce suka hade ta a Nan Azaren tunda Nan za'a kawo Amaren sajida da suhailat,
Aunty Rukayya Kuma sukayi tasu a ShopRite, ranar Azare taga bak'in 'yan gayu na gani kashe
ni, anci an Sha a walimar Dan ko yaran makarantar malam Saida aka sabunta musu abinci Dan
sun Sha gara a ranar lemon roba da ruwa kuwa tamkar a kamfaninsu, lokacin da ake bikin
Ubaidat tazo wani bikin itama a garin Nan take Jin labarin Habib yayi Aure a sokoto a family
dinner su wani Mahmud Daya zauna a gidan malam Ashe shine young Rich guy din Nan MM
DANGE Wanda yayi fice a kasar Nan harma da kasashen duniya, to shine fa ya bashi kanwarsa
Kuma ya bashi aiki a Dubai.
Hankalin Ubaidat ba Karamin tashi yayi ba Dan kuwa hangen hadarin nesa tayi Ashe mugun
matsolone ta aura bajintar a waje take sai dai da gida Mai kyau Amma wani lokacin taliya da
manja ake dafawa tayi data sani tafi sau dari.

Zahra Bata raka kowace amarya ba Mahmud ya dauketa suka wuce gidan Dan ta gaji iya
gajiya.
Da asuba ma da kyar ta tshi tayi sallah, har Mahmud ya fice Zahra na barci Karan wayarta be
ya tasheta wurin Sha daya, sunan sajida ta gani yana yawo akan screen din.
Dauka tayi tare da sallama, Mai makon taji yanda ta Saba jinta sai ta jiya lukui kamar garin
masarar daya sha nikan laushi.
",Ke Wai meye haka Zaki kirani kiyi shiru, ai ba zato taji shashshekar kukanta.
Wani murmushi Zahra tayi ta ayyana "anzo gurin".

"Bestie menene Wai kike kuka keda ba halinki ba".
Daga can taji dif an kashe wayar ta yukura ta tashi tana fadin "ku karata a ke soyayya ba ai gata
Nan sai anji jiki kafin a Fara fuskarta komai 'yan Mata anzo hannu".
Kwanansu hudu suka juya fir ya hanata zuwa gidan Amaren yace sai sun zama 'yan gari taje
shifa yayi hating din wannan d'abi'ar ta malam bahaushe.
Sajida tayi mita harta bawa uku Lada ita dai Zahra bada hakurine nata tunda tasan ba'a kyauta
Mata ba to yaya zatayi da shi tunda yace a'a.


*****Bayan wata uku.****

Zahra na kwance a jikin Mahmud Yana Mata tausa tun bayan da sukayi break taji mararta tana
Dan karta Mata kadan bada damuba tasan tana Jin hakan a wasu lokutan to Amma na yau
taking gaba yakeyi, tun tana daurewa har abin tafi karfinta Dan babu zato Mahmud yaji ta rirrike
hannuwansa jikinta ya dauki wata karkarwa. Cikin zafin ciwo tace.
"Wayyo.... Meu Amor.... Mutuwa zanyiiii...bayana marata ciwoooo...".
Gaba Daya ya rud'e ya gigice gashi tayi ram dashi, gasu a parlourn sama suna Zaune a kasa
Kan carpet tayi pillow da cinyarsa duk yanda yaso ya tashi ta Hana, ga wata irin karkarewa da
jikin ya dauka Nan da Nan sai jibi ya rufeta duk da sanyin A/Can daya cika parlourn, wayar ta
dake gefe ya dauko duk ya rud'e da kyar ra gano number Ammi ya Kira Batool ce ta dauka tana

kokarin gashe shi Yana fadin "maza ki fadawa Ammi ga precious Nan Bata da Lafiya".
Ai da gudu gudu ta ringa hada steps tana sauka a kitchen ta samu Ammin ta rattaba Mata
yanda sukayi da yayan nata, da sauri ta karbi wayar ta Nemo number zilai tace Mata maza take
gurin Zahra Bata da lafiya ta gani ko haihuwar ce su wuce Asibiti.
A haka Aunty zilan ta samesu sai muk'ususu take sai jibi ne yake binta, da sauri ta karaso tana
fadin.."sannu ikon Allah yanzu fa kuka dauro sumul da ita, tana matsowa tace "ai haihuwa ce ga
Zaki Nan Yana fits yallabai kama min ita muje ciki gata Nan inaga faya ce ta fashe'.
Dago tan da zeyi tace Aunty zilai cire min wani Abu ze fito.
Cikin ikon Allah a Nan ta haifi danta Masha Allah, kalarta sak kana ganinsa kaga Dan larabawa.
Nan da Nan Mahmud ya rude gani yake abin kamar a shirin film, da sauri ya nufi kasa Yana
Kiran Amminsa.
Zahra na rungume da babyn da Aunty zilai ta dora mata a Kan cinyarta tana mayar da
numfashin wahala su momin Kano suka hauro saman Dan Ammi na Gama wata da zilai ta Kira
momin ta fada Mata.
"Ikon Allah! Masha Allah sannu Zahra Allah ya bada lafiya, shi Kuma Bakon sai yanyara kuka
yake Yana neman tsotsar hannu.
Nan da Nan aka gyara zahra da babyn, aka gyara gurin momi ta Kira doctor zainab tazo ta
duba zahra duk da tasan da wahala ta karu tunda tasan yana yin ta.
Kafin la'asar labarin haihuwar ya karade Dangi, Ammah sai Kira take tana tambayar babu dai
wata matsala ko? Duk Wanda ya kamata ya sani ya sani zahra sai amsa waya take ta masu yi
Mata barka, Dan Hajiya Inna daki ta Kama a kasa tace ita zata dunga kula da Mai jegon.
Sai kusan karfe Sha Daya Mahmud ya shigo gidan shiru an gyara ko Ina tas gar ze wuce sama
yaga Daya daga cikin bedroom din kasa da wuta a kunne Yana karasawa yaga Hajiya Inna a
ciki, tura kofar yayi sosai ya shiga Yana fadin.
"Nice gaske kikeyi da kikace Nan Zaki dawo?".
"Eh ka dauka karya nekeyi ai Ina Nan Ina kula da shige da ficenka kada ku jawa yaro qazamin
goyo".
Tabe baki yayi meye Kuma qazamin goyo?".
"Ban sani ba tafi ka tqmbayi iyayenka inaga su sun sani".
Ta fada tana gyara kwanciya .
"Ka kashe wutar idan ka tashi fita.

Zahra na rike da babyn Wanda yake kuka da alamar makoki ne, Mahmud din ya shigo da
sallama,sai sukayi masa wani irin kyau kamar ya lashe su. A hankali ya nufosu ya saka hamnu
ya daukeshi very fine baby tamkar Zahra tayi kaki ita ya biyo sak, Zama yayi kusa da ita Yana
fadin. " Sannu precious Daman haka mata ke Shan wahala idan zasu haihu gaskiya sannu da
kokari,Dan ma dai kin min wayo yaron Nan babu inda ya baroki har idanun anya kunyi min
adalci? Nine fa asassin Amma sai na Zama Dan kallo".
Dan kwantar da kanta tayi a jikinsa tana fadin .
"Raba dai dai mukayi Ni ya dauko kalata da kamanni Kai Kuma ya dauko jinsinka da jarumta irin
taka in Sha Allah".. Nan suka saka yaron ga bada har wurin Daya suna kallonsa.
A tsakanin kwanakin zahra taga Baki fiye da tunaninta ga kayan baby da zannuwa na kece raini

kamar hauka,
Su Aunty Hassana dasu momi kaltume duk sunzo, ganin baby ana gobe suna ma suka dawo
sunan yayi armshi fiye da tunanin Mai tunani yaro yaci sunan mahaifin Zahra Abbie ne yace ayi
Mata Kara. Taro ya tashi lafiya inda Zahra ta samu Kaya da zunzurutun kudi. Yaron suna
kiransa da suna Ayyan. Bayan suna babu yanda Hajiya Inna batayi ba akan ta tafi da Zahra
gidanta Amma ya k'ek'ashe kasa yace babu wannan maganar dole ta hakura ta zauna a gidan
Dan tace bazata zuba Ido ba a cuci yaro.

BAYAN SHEKARA BIYU.

Yaro ne fine boy Yana sanye da jc na club din real Madrid a jikinsa, suka fito daga cikin stadium
ta old Trafford dake ingila ina akayi Wasa tsakanin Manchester United da Madrid din in da
Madrid ta lallasa Manchester United da ci uku da nema. Motarsu Mai shigen sport car suka
shiga Mahmud ya harba Kan titi, Saida suka dauki hanya sosai sannan ya shafa sumar yaro
mai laushi da santsi.
"My Ayyan..".
Fararen idanunsa ya dago masu Kama Dana uwarsa ya kalli uban.
"Yessss my papa"
Ya fada da salon iriin Hausar Yara.
"Me mameen ka tace ka sawo mata?".
Shiru yayi Yana tunani sannan yayi tsalle akan seat din da yake tsaye a gaba kusa Mahmud ya
Fara fadin.
"A. P.P.L.E".
"That is right my Ayyan".
Sun biya sun sawo Mata Apple din da sauran fruits suka nufa gida tana kitchen tana girki suka
shigo da sauri ta fito tana ga fadin.
"Babana Ina sakon Dana baka".
Ledar Apple din Mahmud ya mika Mata Yana fadin. Da alama an Dace Dan wannan karon
masoyin Apple ne ko masoyiyar Apple ko masoyan Apple".
Ayyan ne ya wuce dakinsa da gudu da ledar chocolates dinsa Dan kada Zahra ta rage tace zata
hada nasa makaranta.
Saida ya shige sannan Mahmud ya bude Mata hannuwa ta shige tana dariya, cikinta ya Dan
shafo Yana fadin maman twins muje aji dani Naga alama wannan karon ta juya tunda mune a
ciki.
Tammat bi hamdillah.
Subahanakallahumma wabi hamdik Ashshahadu an la'ilaha illa anta Astagafiruka wa'atubu ilaik.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login