Showing 1 words to 3000 words out of 62795 words

Chapter 1 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf

03 Aug 2025

8799

.*AUREN HUCE HAUSHI*

AISHAT ISAH MUSAH

Maman Fateemah.

08055362975

Or

09061432330

Page 80.


.....….….. Subhanallahi mutanen dake parlourn suka dauka, da sauri Ammah da Aunty Hasana
suka matso gurin da Mamar ta Fadi Ammah tana fadin..
"Ikon Allah har yanzu jikin ne kenan da Baki fito ba, Hasana maza Nemo Abdul Hakeem ko
Hamza aje asibiti"O.
"Gaskiya dai Kam tunda abun Yana neman ya Zama wani Abu daban".
Hajiya kaltume ta fada yayinda wata daga cikin bakin tace.
"Anya Bata da hypertension kuwa?".
"Nima abinda nake tunani kenan gaskiya".
Ammah ta fad'a.
Cikin kankanin lokaci Hamza da imam suka shigo yayin da a waje Abdul Hakeem ta fito da
mota, zilai da sahura ne suka dauketa suka nufi waje da ita, Aunty Hasana ta rufa musu baya
suka fice.
Saida komai ya lafa sannan su Hajiya kaltume suka samu Damar fuskantar bakinsu,nan da nan
aka Fara sauke musu ashirin ta arziki Alawiyya da magaji Wanda Bai bi Yan asibitin ba domin
yasan tsabar tashin hankali ne ya haddasawa mama wannan abun ba komai ba, duk Wanda
yace ruwan wani baze tafasa ba nasa ko zafi bazeyi ba. Abinci bakin waje suka ringa fita dashi, sai da bakin sukaci abinci sukayi sallah sannan Aunty
Surayya ta gabatar da Kayan lefen gasu Hajiya kaltume dasu Inna maimuna wadda tun
faduwar Mama taja jikinta gefe tasan mugun nufinta ne ya Fara tambayarta tunda taga duk
yanda ta dunga dakile Lamarin Zahra Ubangiji ya nuna Mata shine Arrazzaqu shike daukaka
bawa duk kuwa yanda makiya suka so su dankwafe mutum sai ya nuna karfin ikonsa a Kan
abun, gashi an waya gari Zahra tayi musu wata irin tazara tamkar tsakanin sama da kasa haka
tazarar take,abinda ko a mafarki ko a hasashe babu Wanda ya taba kawo hakan.

Sun godiya sosai, sannan Aunty Surayyar ta dauko key ta mikawa Hajiya kaltume tana fadin
gashi inji Ammi tace a kawowa Ammah tana gaisheta kafin komai ya lafa tazo su gaisa ace ayi
Mata godiya sosai da sosai.
Duk gurin ba Wanda baiyi mamaki ba na wannan kyautar girman da aka yiwa uwar Amarya.

Matan makotan da suka shigo suka Fara bude kayan ana gani ana Sanya Alkhairi a ciki.
Aunty Mahafuza Matar Ya Ibrahim ce tace .
"Wai ina amaryar tamu ne a rakamu mu gaisa da ita kafin a kaimana ita".
Inna maimuna ce tace "tashi muje ai ba nisa tayi ba tana Cikin dakin nan".
Tashi tayi tana fadin gara muyi sabo tun daga Nan na Zama ta farko da zata sani a cikin matan
yayun mijinta".
Inna maimuna na gaba Mahafuza na binta a baya har kofar bedroom din dasu Zahra suke ita da
mujiba da Yan uwanta da sukazo dasu Inna maimunar Salima da Ibtihal, salima ce ta bude
kofar su Inna maimunar suka shigo idon Mahafuzar Yana Kan Zahra wadda take zaune a Kan
sofa Tasha ubansu lace Wanda ya amsa sunansa tayi wani irin fitinan nan kyau a cikinsa tana
daddanna iPhone sixteen plus dinta tana daga sexy eyes dinta sukayi four eyes da Mahafuzar,
ba shiri ta hadiye wani Abu Daya sille ya wuce Mata Bata shirya ba.
"Tabarakallahu Ahasanul kaliqin, Masha Allah" ta fada a zuciyarta, ai ita a yanda Habibinta ya
fada Mata yarinyar Daya gani a part din Ammi da yake tunanin ko budurwar mahmud din ce sai
taga Bai iya bada bayanin mutum ba Sam.
Da fara'arta ta shigo tana musu sallama da fara'a Suma su salima suka amsa Mata suka
gaisheta, Cikin nutsuwa da Jan ajiya da nuna sanin ciwon Kai Zahra ta gaishe da Mahafuza din.
Gurin Zama su mujiba suka bawa Mahafuzar suna fadin.
"Ki zauna Mana ga guri Aunty".
Gefen gadon ta zauna tana duban zahra a kaikaice, haka Nan yarinyar tayi Mata kwarjini sosai
sai taji duk ta Raina kanta duk da itama 'yar gayu ce kuma ba laifi da nata daidai kyawun Amma
ganin zahra sai taji tayi lakwas tunda da biyu ta nace akan saita biyo masu kawo lefen duk da
mutum hudu kawai ake bukata Mata Saida tayi yanda tayi Dan taga kul uwar daka, tunda daga
waje taji gwiwarta ta sace tasan wannan da alama tafi gaban raini, to Kuma sai gashi taga itama
Zahrar zahra ce ga Jan aji da alama bazata dauki raini ba..
Ganin shirun ya yi yawa yasa Mahafuza tace Amarya zamu tafi "Ni sunana Mahafuza matar
Ibrahim Dange yayan mahmud".
Dan murmushi zahra tayi.
"Na gode Aunty Mahafuza".
Tashi tayi tana fadin.
"Nima na gode Amaryar mu sai kin Karaso naso ace Ina Cikin masu kwana mu tafi tare".
'yar dariya zahra tayi wadda ta Kara fito da sirrin kyawunta.
Bayan ta fita Ibtihal tayi wani tsalle tana fadin.
"Yessss! Adda zahra haka nake son Kama Kai da nemawa Kai mutumci".
Wayar hannunta ta aje tana fadin.
"Ibtihal Baki Jin magana wallahi me Kuma nayi?".
"Meye ma bakiyi ba irin wannan jam class haka kamar wata saraunya fa haka kikeyi acting".
Dan murmushi zahra tayi tana tuna hudubar Hajiyar makwarari lokacin da take Mata karatun
dangin mijinta da yanda zata zauna dasu da yanda zata kama kanta kada ta bada fuskar da
za'a Raina ta, wato ta yarda da maganar da Hausawa ke fada na cewar duk abinda Babba ya
hango yaro baze hango ba ko ya hau itace rimi sai yau ta yarda da hakan, da gani wannan da
salon nata rainin hankalin ta shigo Sai kuma taga an fita iyawa.
Suna Nan suna maida yanda akayi Su Aunty Surayya suka shigo Zahra ta gaishe su, Nan

Aunty Mahafuza ta gabatarwa Zahra Aunty Surayya da kanwar Abbie maman ya Abbas surukar
Aishat sai 'yar kanwar Hajja kakar su Mahmud ta wajen uwa, sun yaba matuka da zabin
mahmud sosai, sunyi musu Addu'ar Albarkar Aure sannan suka fita.
Aunty Surayya ce ta dawo ganin ta dawo yasa su salima suka fice daga dakin.
Kusa da Zahra ta zauna wadda ta sadda Kai saboda wani nauyinta taji ya kamata niyyar
zamewa tayi kasa Aunty Surayyar ta hanata.
"Zauna magana zamuyi dake, kina jina Zaki shiga sabon guri da wasu mutane Wanda zakiyi
rayuwa ta har abada dasu in Sha Allah,to ki nutsu ki fashinci kowa kada kiyi garaje a cikin
tafiyar ki saka hankali sosai gurin wadanda Zaki mu'amalanta babu ruwanki da kowa babu
ruwanki da 'yan matan family din Nan duk yawancinsu burinsu Kan mijinki yake kada wata ta
dauko Abu ta kawo Miki da sunan kyauta naci Kona Sha kiyi amfani dashi idan Kika cire
Amminsa to sai Hajiya Inna, koni idan ban Kwanta Miki ba kada kiyi amfani da abunda Zan Baki
kinji ko".
Kai Zahra ta gyada mata.
"Naji Aunty nagode in Sha Allah Zan kula da abinda Kika fada mini".



"Yauwa Kinga pass na dinner ko? Aishat tace zakuyi waya ki bawa kawayenki na kusa
wadanda Kika San zasuje tunda abune da anan ya Riga ya Dade da wucewa mu a canne yake
sabo, Kuma
gobe insha Allah zaku taho mu yau zamubi jirgi daga Bauchi zuwa sokoto tunda mu duka har
mazan mu bakwai ne, Kuma anan zamu bar Hajiayarsu Abbas da Hajja Asiya tare dasu zaku
wuce goben, ki kula ki daraja Ammi tana sonki matuka kinji".
Kai ta gyada Mata sai taji matar ta burgeta sosai domin a zamanin Nan babu Mai fada maka irin
wannan sai mai kaunarka.
Alawiyya ce tayi knocking ta leko tace "ana jiran Aunty Surayya". Sallama ta yiwa Zahra ta fice
da sauri.

***

Tun kafin aje asibitin Mama ta dawo hayyacinta abun nata kamar iska haka Nan suka karasa a
A/E suka dubata, tambayoyi suka shiga Jero Mata akan wane abune ya daga Mata hankali har
BP dinta ya Mai dari da tamanin kasan ya Kai dari da goma, dagewa tayi ita babu abinda ya
tada Mata hankali, su dai su Aunty Hasana Ido ne nasu, Mama taso su barta su dawo gida
Amma suka riketa saboda sunga karfin Hali ne kawai takeyi Amma Bata da lafiya sosai
zuciyarta ma tana neman kamuwa da ciwo matukar ba'ayi controlling din jinin ba, dole ta hakura
aka saka Mata magani a kasan harshe aka Kuma saka Mata Karin ruwa aka saka Allurar barci
dole tanaji tana gani barci yayi awon gaba da ita, Ammah ta kirawo Aunty Hasana ya Kai sau
uku tana tambayar ya jikin nata.
Daga karshe Aunty Hasanar gida Abdul Hakeem ya dawo da ita ta baro su zilan a can, lokacin
data dawo bakin da zasu tafi sun tafi sai mutum biyun da zasu kwana suma Sana can bangaren
baki.

Kayan ta tarar Makota sun shigo an bude iya Wanda za'a Iya budewa sauran kuma an tattarasu
gefe guda Dan bazasu ganu a Kan kanin lokaci ba.
Yawan akwatunan Aunty Hasana ta tsaya kallo, Saida ta shiga dakin Ammah ta tsinkayo
zancen motar da Ammi ta aikowa da Ammah.
Washe gari tun sassafe motocin Kaya biyu suka dauki hanyar sokoto.
Tun dare Mama ta dawo daga asibitin, matsa musu tayi akan a sallameta dole suka sallameta
duk da Abba yace ta hakura ta barsu suyi aikinsu ta matsa ita dai babu abinda yake damunta.
Zahra har dakin bakinsu salima da Ibtihal suka rakata ta gaishe dasu Cikin ladabi da biyyaya,
shi Albarka dai zahre ta shata.
Lokacin da meyin makeup ne tazo Zahra Ido ya Raina fata da duk gani takeyi kamar wasa ne
babu inda zata tafi shi dai ya dawo ya same ta kamar yanda ya Saba.
Nan da Nan taji wata irin karaya da tashin hankali ya saukar Mata ai ji tayi wancen wasan yara
ne yanzu ne dai za'ayi maganar gaskiya,Cikin abinda be wuce minti talatin ba aka gama komai
tayi kyau kamar me, sai Zuba wani kamshi take na musamman, ita kanta Ammah dauriya kawai
takeyi Dan ganin abun tayi kamar yanzu ne take bikin wancen Wasa tayi duba da yanzu yanda
ake komai da dangin mijinta ba kamar wancen Karon ba da su kadai su kayi budurinsu, ga
tashin Hankali Sam babu nutsuwa haka tana gidan Kullum tana zulumi akan yaron kada ya
gudu da yarinya ko Kuma ya gudu ya barta da ciki ba Kuma asan asalin inda za'a nema shi ba,
Amma yanzu Allah s.w.a ya gama Mata gata ya juya Lamarin 'yar marainiyar Allah ya share
Mata hawayen data Dade tana zubarwa akan tozarcin da ake Mata akan aure, sai gashi Ashe
wani hanin ga Allah baiwa ne, wa ya taba zaton yaron Nan wani ne ko Dan wani? Ba Karamin
toshe kunnuwa Abban Yara yayi ba lokacin da ake Kan ganiyar maganar ana ta ruruta wutar ya
aura Mata Almajiri Wanda ba'a San asalinsa ba Dan ba 'yarsa bace Amma ace duk yanda take
da kyau da cikar halitta ta Kare a kolo fakiri marar madafa, to gashi hakuri Mai tarar da arziki
yau ga Zahra ta Zama farin wata Sha kallo, ga lefen da ba'a taba kwatanta kawo Mata Koda
kwata dinsa ba, yanzu haka wancen lefen suna Nan a daki to ga Kuma wannan Sha kumdum
din.

Wurin Abbanta Aunty Hasana ta rakata yayi Mata Nasiha sosai ya Kara jaddada Mata
mashimmancin biyayyar Aure.
Kafin karfe Sha Daya gidan ya dinke da jama'a abin har yaso ya bawa Ammah mamaki to ita
dai Hajiya kaltume ta dankawa I. V din da Ammi ta aiko dasu na mutanen Ammah ita dai kawai
tasan ta Debi shida ta bawa maman mujiba tace ta aikwa makota Koda Wanda zasuje kada
abun ya Zama na tsegumi. Zahra ma nata mujiba ta debarwa tace ta bawa kawayensu Amma kadan zata bawa ita kunya
ma takeji Ace Wai za'ayi wani Abu kuma na bikinta, daga baya kenan Wai sadaka da bazawara.
Ta bawa magaji ya kaiwa Amatu da Aunty safiya sai wasu Kuma ta bawa sauran malaman duk
da tasan abune Mai wahala suje tunda ko a Nan basuje ba tunda sukaji labarin ance mijin
Almajiri ne.
Zahra na dakin Ammah su Inna suna karayi Mata nasihar zanmantakewar aure tana ta sharbar
kuka, ficewa Ammah tayi Dan itama daf take da sakin nata kukan.
Tun dare Ammi ta Kira Ammah ta fada Mata akwai tickets na mutum goma a Nan hannun wani
a Bauchi Wanda zasu rako Zahra dakinta, Sameer Yana Nan shine ze musu komai ze shigo su

wuce sauran mutanen Kuma motoci sun taho.

Har Cikin jirgi Abbanta ya kaita ya zaunar da ita kusa da Inna mainuna da Hajiya kaltume, Yana
fadin.
"Hajiya gata Nan a mikata hannun Alhaji Muhammadu ace masa ga Amanar 'yata Nan kafin
nazo da kaina,Allah ya saukeku lafiya uwata ayi ta hakuri kinji".
Kai kawai ta iya gyada Masa ya juya ya wuce tabe baki mama tayi wadda ta kafa sai taje
sokoton ita ta warke abinda yaso ya kawo sabani kenan da Abba sai da Ammah ta shiga
tsakani tace ya barta tunda tace zata iya.
Karfe Daya da kwata jirginsu Zahra ya sauka a sokoto,wani irin Abu Zahra taji ya tsirga Mata
gata a sokoto karo na biyu a cikin girma da mutumci kamar ko wace Mace da ake aurowa daga
gaban iyayenta sai yanzu ta Kara fahimtar manufar Ammi na rabata da gidan tun ba'a Farga da
ita ba,wato wannan martabar take nemar Mata kenan. A Hankali take sakkowa daga steps din jirgin sanye da rigar material Mai azabar kyau da sari
fari tasan Mai ratsin flowers coffee kalar material din Aunty Hasana na biye da ita a baya.
Yana tsaye daga gefe shida Tajuddeen ta ringa saukowa wata ni'ima yaji tana saukar Masa, ya
yarda ya amince ta zamar Masa wani bangaren jikinsa ganinta kadai ya saka masa nutsuwa
Yana binta da Ido har suka karasa gurin motocin da aka tanada Dan daukarta.
Tambayar duniya Tajuddeen yayi Masa akan me Suke jira a airport Amma yayi Masa Shiru.
Sai da suka wuce sannan Sameer ya Karaso Yana fadin.
"Ina Ina zamu nufa ne Wai?".
Wani smile yayi Wanda Kama gani kasan Yana Cikin nishadi.
"Gidan uwar gida za'a kaita mana ta kwashi albarka, sannan ku kaita gurin Ammin na fadawa
Shatu komai kuje Dan Allah Naga idanu sunyi yawa a kanta".
"Shegen sama kace wannan model din itace kayo kamu, Wai Dan Allah yaushe ka Sami lokacin
mace yanda nasanka baka da lokacin kowa saina sabgarka, Amma India ce ko?".
"Bafulatanar Adamawa ce?".
Ya fada a takaice yayi gaba inda Naseer yake zaman jiransu, da sauri Tajuddeen yabi bayansa.

Su Zahra na dosar inda masu tarbarsu suke Aishat ta taho da sauri tana rike da Afnan Wanda
suka dauki wanka gayu dai yaci gidansu a gurin, rungumo Zahra tayi tana fadin.
"Amincin Allah da Rahamarsa su sauka a gareki sister Fateemah Zahra. Allah ya albarkaci
Aurenku da zuri'a masu Albarka, barka da shigowa DANGE FAMILY you're welcome".
Afnan ce ta Fara zillo tana rinjayowa gurin Zahra, wato ta ganeta.
Hannu Zahra tasa ta karbi Afnan din daga hannun Aunty Aishat din, Hajiya kaltume da Inna
maimuna suka nufi ubansun motar da za'a dauki Zahrar wadda sabuwa ce Zahrar ce farkon
shigarta bayan direban Daya tukota.
Tun a airport Mama ta Fara Raina kanta yanda taga Mata 'yan gayu na gani kasheni Wai duk
masu tarbar Zahra ne, ga wata yarinya Kuma da suka rungume juna itama wanke hannu ka
taba ga Kuma yanda taga wata farar mace nata kaffa kaffa da Zahrar.
Mama Bata Kara Raina kanta ba sai da suka shigo gidan Hajiya Inna inda taji wasu Mata na
fadin.
"Wallahi soyayyar Hajiya Inna da mahmud tana burgeni sosai kiga fa Saida ya Fara cewa a

kawota gurin kakarsa kafin a kaita gurin mahaifiyarsa".
Wata ashariya Mama ta lafta a Cikin zuciyarta tana karewa gidan kallo me kalaman wadannan
matan ke nufi? Gidan kakarsa wannan din? Ai jikinta har tsuma yake ta nufi kofar shiga da sauri
so take taga zahiri Nan gidan tsohuwa ne, to Ina ga gidan iyayensa da Kuma nasa? Wato
maganar malam na Bande ta tabbata da yace wannan yaron yafi ko wane namiji daya taba
kwatanta Yana sonta karfin arziki saita dauki maganarsa shifcin gizo yaso ya nuna Mata hanyar
da za'a dakile abun duk da yace shi baiga saki a tattare da ita ba.
Wato abinda ya gano Mata kenan tayi kunnen uwar shegu da maganarsa, ga abinda Asabe tayi
Mata ta tabbata da an aiwatar da abin nan da yanzu wata kila Daya daga Cikin yaranta ne Dan
aikin anyi shi da niyyar Zahrar ta bijiere ne taki mahmud fir har Abbansu yaji haushi ya Kara
bashi madadinta da Daya daga Cikin yaran nata, sai kuma Asabe tayi batan dabo Wanda har
yau ko labarin Wanda ya ganta Mama Bataji ba.
Parlour ne na Alfarma tamkar wata fada Dan a tsakanin shekaran jiya da jiya Saida aka canza
komai na parlourn tun Inna na mita harta hakura dan tasan ba fasawa za"ayi ba Cikin barkwanci
Hajiya Inna da jama'arta suka tarbi amarya da danginta, an Sha dariya Dan Hajiya Inna cewa
tayi. "Haba da walakin goro a miya shi yasa ya tubure mini Yana faman rantsuwar baze dawo ba
saiya Nemo ki duk inda kike a duniyar Nan ya kawo mini ke har gida a ranar da ze bar gidan
Nan, Ashe da abinda ya gano, tofa ko yaya ne dai nice ta karfen Kinga ai niya Fara kawowa ke
ko?". Inna maimuna ce tayi 'yar dariyar barkwanci Yana fadin.
"Ai Hajiya duk abinda lauje ya yayo ciyawa ce, Kai da Kaya Kuma duk mallakar wuya ne, ga
Zahra Nan taki ce tunda mahmud nake ne"
Dariya Hajiya innar tayi tana fadin.
"Ato gara na fada Mata kada taga Yana kawo min abu Mai maiko tace ya fifitani akanta."
Akayi dariya dai, duk Mama na zaune kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki ba wani karsashi
ko daya ga rashin dadin jiki karfin Hali kawai takeyi Amma lafiyar dai sai a hankali.
Nan cikin part din Aunty Aishat tayiwa Zahrar da Aunty Hasana masauki kusa da bedroom
dinsa na part din jiya aka hada dakin komai sabo

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login