Showing 30001 words to 33000 words out of 62795 words

Chapter 11 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf

03 Aug 2025

8794

guri cewa
fa yayi ko daukoni za'ayi naje gidan ku mu kwana, to kuwa ba karamin aikinsa bane yayi abinda
zesa na fita da gudu, nasan tunda ya ambata tafiyar zakuyi".
"Kai Hajiya Dan Allah na kwana a Nan din Mana".
"Keni rabi da kinibibi ku Kama gabanku, nagode hakan ma duk da raddi ne ya mayar min".
"Dan tagwaye mu kwana lfy na shiga ciki a rufe min kofata ta baya tunda Kaine me abin
budewanda rufewar".
Tayi gaba abinda.
"Allah ya tashemu lafiya".
Ya fada tana daddanna wayar hannunsa da alama Abu Mai mashimmanci yake turawa.
Kujerar daura dashi ta janyo zata zauna ya janyota ya zaunar a cinyarsa Yana fadin.
"Me yasa kikayi min haka keda a gabanki nace Mata bama gidan shine Kika since min zani a
kasuwa ko?".
Yana kwanto da kansa saitin wuyanta wannan kamshi Mai sakashi a cikin wani yanayi yaji Yana
shigar masa hanci.
"Ina tambayarki kinyi shiru".
Wayar ya aje Kan table din da Alama ya Gama tura sakon, duka hannunsa ya saka ya zayayo
ta saman cikinta ya Kara kwantar da kansa sosai a gefen wayan nata Yana Dan hura Mata iska

kadan a gefen fuskarta.
"Ba komai kawai dai gani nayi nace Mata Zan dawo ne kaga bazataji dad'i ba idan ban dawo
ba".
Dan lakuce cheeks dinta yayi "Mai wayo kawai,bani abinci naci mu tafi barci nakeji'.
Shima tuwon semovita ne da miyar agushi.
"Barshi bazanci ba".
Dago da kanta tayi ta kalleshi, Kai ya gyada Mata yana mik'ewa da ita tsaye.
"Muje ki bani coffee kawai, ji nayi Shima Kamar yajin zanji".
Ya riko hannunta suka gangaro parlour. Ta bayan suka fice ya rufe kofar suka wuce. Mai makon
taga sun nufi part din da sukayi masauki Wanda ya zamar Mata wani gurin tarihi a cikin babin
rayuwarta, sai taga ya nufi wata motar da akayi parking dai dai karshen barandar.
"Ina kuma zamu?".
"Inda mukafi wayo ai Nan Kuma aikinsa ya Kare sai dai Idan munyi tafiya mun dawo to Nan ne
farkon sauka haka tsarin yake Nan ne kashen sallama Kuma farkon sauka".
"To muje na dauko kayana Naga Kai baka barin a dauki komai Idan ka tashi kawai gaba kakeyi
baka daukar komai Ni kuma da magunguna a ciki".
"Cool down shadi, harda turarikan dake hanani sakat na dauko ai ba'a Wasa da garin gona,
Fad'a min wai waye ya baki wadannan turarikan ne?".
"Ance kada na fad'a maka fa".
"Kai! harda sirrin da Zaki boye min yanzu precious? Ni fa na Gama ganin karshen sirrin?.
Ya Dan shafi wani guri.
"Wash!!! ka Bari Dan Allah, wallahi da ciwooo har yanzu. Kuma turarikan Aunty Aishat ce ta
kawo min su fa tace mummy Badi'a ce ta taho min dasu".
Baki ya bude ya kasa magana, babbar magana wato su Mata basa girma wallahi, Bai Kara ce
Mata komai ba suka nufi motar.
Shiya bude Mata ta zauna sannan ya zagayo gurin driver ya zauna.
Suna fita taga ya dauki wata hanyar Dan kallonsa yayi.
"Ina zamu kuma Naga ka biyo ta wata hanyar?".
"Very good, gaskiya kina da sharp brain in some days kin Fara gane Kan garin nan, to Nan
bypass ce zamu bi".
Sunyi nisa Zahrar ke nuna Masa wata mota a bayansu wadda take binsu sauda kafa Kuma taki
wucewa.
Hannunta dake cikin nasa ya Dan qara matsewa.
"Kina tsoron kada ayi kidnapping dinki sunga kalar da za'a karbi dollars ko?"
a tsora ce da dube shi "Da gaske kenan ana yin abin Nan ga garin nan?".
"Of course ana yinsa sai dai in Sha Allah kina da kariyar da babu Wanda ze iya cimmiki ta zahiri
data badini, wannan motar su zayyan ne a cikinta da Shirin Kota kwana shine Babban guard
dina Yana tare da yaransa ne na zahiri kenan, kinsan wasu sun wuce mu suna gabanmu kosu
zayyan din Basu San da zamansu ba, wasu Kuma suna bayan su zayyan din ai kin gane, ko ke
kadai ce Kika fito to ki qaddara team kusan uku suna biye dake duk inda Zaki shiga kuwa ba
mazan ba ba matan ba".
"Mata Kuma?'.
Kai ya gyada Mata alamar haka ne "kina mamakin hakan ne?".

"Eh gani nayi aikin maza ne wannan'.
Saida ya shiga wata kwana sannan yace Mata.
"Ai kuwa Mata suna bada gudunmawa sossi a cikin aikin DSS sunyi abinda mazan basuyi ba
gurin Kama criminals sai da aikin akwai risky a cikinsa sosai gaskiya" .har suka shiga unguwar
tasu ta mawadata Yana yi Mata bayanin irin gudunmawar da Mata ke badawa.
Lokacin da suka shiga ciki shiru gidan ba motsin kowa Amma ko Ina neat sai kamshi ke tashi da
sanyi mai nutsuwa.
Hade jikinsu yayi Yana Kara shinshinarta.
"Previous da sauki ko? Tunda Naga tafiyar ta Dan gyaru muje kiji dani wallahi a matse nake
dake?".
Bai jira amsar ta ba yayi sama da ita ya nufi stairs.
Kuka take Masa ba k'ak'k'autawa shi kansa ya rasa dalilinsa na koma Mata duk da itama ta
bada goyon baya kafin yayo famin Daya ruda Mata lissafi, Tasha sambatu kamar ze zauce yau
dai da Bata Suma ma taji abinda ya girmi kunnuwanta Albarka kuwa har Amminta yau Tasha ta
saboda jiya baze iya karar da komai ba Amma na yau yayi abin cikin hankali da nutsuwa yaji
wani bakon lamari tunda itama ta taka rawar gani kafin labarin yasha banban Amma dai taji jiki
saida yayi ta faman ban Baki da lallashi saboda Kuka wiwi ta rirrik'e shi tana yinsa ga Daman ya
lafiyar kura.




******** Karfe goma Mai kyau Abba ya sauka a sokota shida Hamza da Abdul Hakeem,. Sameer
ne yaje airport ya dauko su direct asibitin suka nufa, lokacin da sukaje dakin likitan bayan Nan
yaje round duba patient dinsa basufi minti biyar ba doctorn ya dawo office hannu sukayi dasu
Alhaji Jafar tunda ya gansu da Sameer yasan mijin matar can ne patient din DANGE. Tare suka shiga ciki Saida suka zauna sannan doctor din ya cire glass din dake idonsa ya dubi
Sameer Yana fadin .
"Alhaji ne mijin patient din tamu?'.
"Eh shine doctor kuma sirikinku shine mahaifin ita wife dinsa".
"Ah haba dai?".
"In Sha Allah haka yake".
Wata gaisuwar ya Kara yiwa Alhajin Yana fadin .
"Ai Dange abokina ne tare mukayi karatu a UK dashi sannu da hanya, to Alhaji Yaya akayi
ciwon zuciya yaso yayi karfi a jikina Hajiya Dan yanzu haka zuciyar a kubure take Dan ma anyi
Mata allurai Kuma Sameer yaje Abuja jiya ya kawo magunguna tunda mu a nan sun yanke
mana, Kuma muna bukatarsu emergency, gaskiya ka zauna da ita a tambayeta me yake
damunta da yayi cussing din irin wannan ciwon lokaci Daya Dan da alama da abinda ya tada
Mata da hankali ba zato din, yanzu Shawara Daya ce akwai wani asibiti a Egypt suna da
consultant cardiologist a can ya kamata a tarbi abun gaskiya".
Wani gumi ne ya tsaststafowa Hamza yasan duk abinda ya samu Mama Yana damfare da
matsalar Salma sai Kuma abinda yake Mata fada a kansa ta daurawa Kai wahala akan Zahra
bare Kuma da tazo taga irin daular da Allah yabawa yarinyar yasan harda wannan damuwar.

' Mun gode kwarai da gaske doctor,yanzu ka bamu address din asibitin kawai idan Allah ya
yarda a cikin week din Nan sai muyi komai mu tafi"
Alhaji Jafar din ya fada cikin damuwa ya rasa me Rabi'a keso a wannan' rayuwar dai dai
kwarkwado tana cikin rufin asirin Allah yasan ko banza bazata rasa kadara da zuzzurutun kudi
sama da millions of naira ba tunda duk alherin daya samu matansa suna da kaso Mai tsoka a
ciki. "A'a Abba ai an Gama komai tun jiya yanzu visa muke jira naso na shiga Azaren yau sai Kuma
Abdul Hakeem yace min Kuna Nan zuwa yau koma Mahmud ban fadawa ba zuwan nake
saboda jiyan dare yayi".
"A'a doctor bani address maza yaushe za'ayi haka na Zama uban banza kenan,ni fatana a rike
min uwata da mutumci bawai na Zama Mai idon cin naira bane, nagarta na duba naba shi
bansan shi ba a lokacin duk da da wuya a fadi sunansa a fadin k'asar Nan ace ba'a San shi ba,
hotunansa dake yawo da Kuma a social media da banbanci kwarar da gaske da yanayin da
muka same a ciki shi babu Hadi ko Daya shi yasa bamu fashimta ba, kuyi hakuri mun gode da
wannan hidimar da akayi ma ta wadatar Allah ya saka da Alkhairi".
Duk yanda Sameer yaso Abban ya fahimce shi ya nuna Sam baza"ayi hakan ba, doctor din ya
Basu full address na asibitin da tsare-tsarensu duka sukayi godiya sosai suka fito Sameer yayi
musu jagora zuwa dakin da aka kwantar da Mamar lokacin da suka shiga tana barki sai su
Aunty Hassana da suka shigo su ganta ita da Inna mainuna su duba jikin nata kafin su tafi,
sunyi mamakin ganin Abba dasu Hamza tunda ba Wanda suka fadawa sai Sameer duba da
duka yaushe suka bar garin.
Gaban gadon Abban ya tsaya Yana warewa mamar kallo fuskarta da kafafunta sun kumbura
harda hannuwanta, gurin sun Aunty Hassana
Abban ya juyo Yana gaishe da Inna mainuna ita Kuma ta jajanta Masa lalurar Mamar.
"Ina Hameeda da Salman suke ya jefawa Aunty Hassana tambayar dai dai lokacin da Aunty ladi
ke shigowa yayar Mama.
Duk Saida daburce batayi zaton ganinsa a garin ba a irin wannan lokacin.
Cikin alamun rashin gaskiya ta Fara fadin "Alhaji kune a hanyar haka sannu da zuwa, Ina
kwana?".
"Lafiy kalau ya Mai jikin?".
Jikinta da sauki gashi har tana iya barci".
Hameeda ce ta shigo da sallama da tea flasks da basket na abincin da aka kawo da dare jiya
tasan ana daf da kawo na safe shi yasa ta tafi ta wanko kayan.
"Lah Abba sannu da zuwa Ina kwana?
"Lafiya kalau Hameeda ya Mai jikin kuma? Ina Salma take ku hada kayanku gida zamu tafi flight
din karfe biyu zamu bi".

,Ya Abudul, ya Hamza Ina kwanan ku?".
"Lfy kalau ya Mai jikin".
"Da sauki, Abba naji kana maganar Ina Aunty Salma ai batazo Nan ba".

Hamza Abban nasu ya kalla kallon tuhuma. Cikin kaushin murye yace.
"Shin abinda magaji ya fada min da gaske ne Rabi'a tasa ka fita da Salma da Asuba ta kofar

baya tana kuka?"
*_ AUREN HUCE HAUSHI _*

AISHAT ISAH MUSAH.

Maman Fateemah.


09051432330
Or
08055362975


*Page 89.


_________Cikin kid'ima Hamza ya fara rantse-rantsen babu ruwansa ganin da sameer a dakin
yasa inna maimuna yin magana.
"Dan Allah Alhaji a bar maganar nan sai an koma gida nan garin mutane ne ga mai lalura tayar
da maganar a gabanta baze haifar da d'a mai ido ba, ayi hakuri abi komai a sannu sai Allah
yayi magani ko menene".
Cikin wani irin bacin rai Alhajin yace " shi kenan inna Allah ya kaimu gidan lafiya".
"Yauwa Amin ai hakan yafi".
Zuru-zuru Aunty laran tayi tasan idan ta tashi ba karamin ruwa aka ballo mata ba.
Da sasarfa Abban ya wuce yabar dakin su sameer suka rufa masa baya, gefe sameer ya koma
ya kira Mahmud Wanda lokacin suka tashi daga barci tun bayan idar da sallarsu ta asuba suka
koma yana kara lallashinta da kasheta da kalaman soyayyarsa.
Zahra na jikinsa kiran sameer din ya shigo ita ta miko masa wayar.
Kiran ya daga yana fadin " ya akayi?".
"Abban madam ne ya shigo tun wurin ten shida su Abdul Hakeem da Hamza, Amma fa yace
maganar fita da Hajiyar mubar zancen biya shi ze dauki nauyin komai abunda akayi a nan ma
Ala amfana".
Tashi zahra tayi tunda taji duk taji abunda suke fada .
" meu amor wai Abban ne yazo garin nan bai nemeni ba? wallahi yanzu Abba ya yayeni baya yi
dani".
Sai hawaye wasu na bin wasu, wayarta ta dauko ta shiga Neman Ya Abdul Hakeem cikin ikon
Allah ta same shi yana dagawa ta fara masa kuka tana fadin "yanzu ya Abdul Hakeem har
Abbna yazo garin nan Amma akaqi a fada min nazo na Ganshi tunda shi bazezo yaga inda
nake ba kodan ni basu Hameeda bane..."? saita karasa sakin kukan sosai ta jefar da wayar a
kan gado.
Janyota Mahmud yayi jikinsa yana fadin " Haba precious meye haka Mike fada akan Abbanki
kada na qara jin magana mai kama da ita daga bakinki ai Abba bai cancanci haka ba gurin
marar lafiya yazo keda ba cewa akayi yabar garin ba, idan ma baizo nan ba ina cewa shiya

kaiki dakinki na Azare wancen ai shine farilla na nan kuwa ai tsabar bidi'a ce kawai tashi muje
na gasaki da kyau kada muje gurin Abban kina ware kafa ya gane yarinyar tasa ta girma gara
idan tukuicin ya fita kowa ya gani ko ba haka bane?"
Ya fada yana dauke tears din dake gangarowa da harshensa, jin ze saki layi yasa tayi saurin
barin jikinsa tana cije lips dinta saboda zogin da takeji.
"Haba Ya Mahmud kaifa malami ne ina ruwanka da irin wannan sabgar karfa dan malam yaqi
halin malam naga abun nake fa Yaya ba sauki wai ka manta nifa yarinya ce"
Dariya ta bashi wallahi yarinyar nan 'yar duniya ce tun Daren jiya ta Dame shi da wani Yayan
shegantaka.
Tashi yayi shima suka shiga wanka saida ya qara hada mata ruwan zafi ta shiga sannan sukayi
wankan suka fito yana maqale da ita, shiya shafeta da lotion yanayi yana mata dan abinda
baza'a rasa ba, ya saka hand dryer ya busar mata da gashin kanta ya gyara shi tsab, ita
mamaki yake bata idan taga ya zage yana irin wannan abun kamar ba shi ba. Clotset suka shiga ta saka Riga abaya 'yar dubai shi yayi mata rolling shi kuma ya saka wani
wagambari fari tas, lokacin da suka fito har breakfast yazo daga gidan Ammi tunda ta Hana ayi
musu a nan duk da jiya binta ta Dawo da gamma tunda bayan sun wuce da dare yayi waya da
laminu daya daga cikin masu gadin gidan ya fadawa Tanimu ya kai yarinyar gida tunda 'yar gari
ce washe gari da gamma sai ya koma ya daukota.
Suna saukowa Abincin ya zama ready yarinyar da alama ta horu da iya aiki, abinci ne kusan
kala hudu sai ruwan tea mai hadin su na'a na'a dasu lemon grass da kayan kamshi. A plate
daya ta zuba musu cheeps din sai kuma pepper soup din zabbi da fattira ta zuba musu black
tea din.


******
Tunda Abdul Hakeem ya fara waya hankalin Abban ke Kansa saida ya sauke wayar Abban
yaga yana bata rai ne ya tambaye shi.
"Me Uwar ta fada maka daya bata maka rai nan da nan haka?"
"Rabu da ita kawai Abba, shirme zata yiwa mutane wai fa kuka ta kama dan an fada mata ka
shigo garin, duka da yaushe mukazo da zata fara yiwa mutane halin nata ita batasan ta gima
ba, abu kad'an kuka kamar wata baby, ai yanzu kuma sai dai yaranta suyi wannan abun".
Dan murmushi Abban yayi. " yi hakuri Abdul maza kirawo min ita ".
Tana ganin kiran Ya Abdul Hakeem din tayi saurin dauka tana fadin.
" Ya Abdul Hakeem zakuzo dan Allah ".
" Ba Abdul bane uwata nine ki kwantar da hankalinki gamu nan, bawa mijinki wayar na fada
masa".
"To Abbana na gode".
Ta mikawa Mahmud wayar,da kallo ya bita sam bata jira taji me zasu fada ba ta nufi kitchen
taga me zata yiwa Abban nata mai sauki kuma favourite dinsa.
Suna gama waya da Abban Mahmud ya kira zayyan yace yaje ya dauko masa Hajiya Inna
Kitchen din yabi zahra ya samu tana ta kokarin hada abinci dan ma da alama wasu abubuwan
an dafa su irin su nama haka nan da nan gidan ya dauki kamshi, taya ta wasu kanaun

abubuwan yayi nan da nan suka gama suka hada table sannan suka koma sama sake watsa
ruwa sukayi zahra na fesa turare taji wayar Mahmud ta dauki slow music Sameer ne.
Dauka yayi taji yana fadar " OK ganu nan".
"Sun karaso?".
Kai ya gyada mata ya nufo In da take tsaye.
" oya! Muje mana sun shigo ciki fa".
Hannuwansa ta rike duka biyun "nifa kunyar Abban kuma nakeji wallahi sai naga idan ya kalleni
kawai ze gane".
Ai Mahmud bai San lokacin daya fashe da dariya ba saboda da iya gaskiyar ta tayi maganar.
"Wai daga jiya zuwa Yau meya hau kanji wannan yarinyar? Yanzu fa kika gama matse yan
hawaye akan baizo ba kuma yazo zaki dauki kinibibin kina jin kunyarsa, yaushe ze wani gane ai
ba Wanda ze dauka ba karbi sadakina ba har mukazo nan ki share kawai".
Ba zato ya janyo ta gaba daya saida tayi dan kara " oh sorry ke dince sai a hankali".
Gaba tayi ta fice daga dakin a hankali take tafiyar cikin nutsuwa dan bata fatan kowa daga
cikinsu ya gane ta.
Suna parlourn farko, tunda suka dosa gidan Abba ke Hamdala ga Allah s.w.a ko yanzu ubangiji
ya fitar dashi daga zargin mutane akan auren da yayiwa yarinyar nan.
Kafin ta karasa shigowa Mahmud ya sameta a hanya.
Tare suka shiga, tana ganin Abban wani farin ciki ya rufeta da dan sauri ta karasa inda yake
zauna shima fara'a fal a fuskarsa fadi yake "Masha Allah uwata"
A gabansa ta tsuguna tana gaishe shi, shima Mahmud din kusa da ita ya zauna yana gaishe da
Abba hannu ya miki masa sukayi musabaha dashi sannan su Abdul Hakeem ma suka taso
suka gaisa, duk yanda Abban yaso Mahmud din ya tashi bai tashin ba itama zahrar da gaske
nauyin Abban nata tajeji Yau Kamar wani sirikinta. Tashi tayi ta nufi kitchen lokacin suna hira da Mahmud dasu ya Abdul Hakeem.
Binta ta tarar tana wanke kayan da sukayi aiki dasu gaishe da zahra tayi tana fadin "wlh Aunty
barci ne ya daukeni bayan ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login