Showing 27001 words to 30000 words out of 62795 words

Chapter 10 - Auren Huce Haushi Book 3 end By Maman Fatimah .pdf

03 Aug 2025

8800

naki yake sai kisan yanda Zaki bida kayanki,
Kinga yaro ne karami yanzu ne yake Kan ganiyarsa sai kin dage da bashi kilawa sosai gaskiya". Ta Jima tana koya Mata dabarun Kama miji a hannu da yanda zata kame iyayensa, idan Auntyn
ta Fadi wani abun kunya take kama zahrar sai taga Kamar ba Aunty Hasanar bace.
Saida sukayi sallah sannan zahra ta raka Aunty Hasanar bangaren Hajiya Inna ta kofar baya
inda suka hade da part dinta.
"A'a wa nake gani kamar zahara'u?".
Hajiya Inna ta fada bakinta yaki rufuwa da gani tana cikin farin cikin ganinta ta taka da kafafunta
ba kamar dazu ba.
Murmushi zahra tayi itama tana kawar da Kai, Dan da gaske kunyarta take ji ba kadan ba,
tunda ya Gama Mata tonon silili Kuma ita meta Samu na k'ararwa.

Zahra taso ta tsuguna ta gaishe da Hajiya Inna Amma ba hali dole tayi Mata me spring kawai.
Sun gaisa da Aunty Hasana sannan ta fada Mata zata tafi driven Daya kawota yana hanya.
"Sannu 'yan biyu kinji, Allah yabar zumunci ai naji shi mijin nata na fadin jirgin safe zakubi ko?"..
"Eh haka ne in Sha Allah Dan ma jikin Mama ai da tun a washe gari zamu juya to sai lalura ta
gitta dole anan zamu barta tunda yayarta tazo dazu ga Kuma Hameeda itama zata zauna tunda
sunyi hutu last week".
"Allah ya bada lafiya ya tsare hanya, akwai sakonki naba magajiya ta Kai can sai ki Kara
tsaraba".
Godiya sosai sukayi Mata suka nufi kofar fita ta gaba. Sun daf da fita hajiya Inna ta Kira sunan
zahar tsayawa tayi tare da juyowa ta Fara kokarin dawowa.
"A'a kuje ki rakata sai ki dawo ta Nan din".
"To".
Ta fada suka ida ficewa Saida suka gangare steps din a hankali sannan Zahra ta dubi Aunty
Hasana.
"Yanzu Ashe gobe zaku tafi Amma Baki fada min ba da saidai na wayi gari naji kun wuce". Ta
fad'a tana Shirin zubar da hawaye.
"A'a ai kinsan bazan bar garin Nan banzo na ganki ba,to saboda waye nazo garin Banda shirirta
irin taki ai kema kinsan hakan baze yuwu ba, shi yasa na wuni a gurinki yau, kuma ai zamu
dawo da Ammah taga irin daular da Allah ya kawo diyarta ciki, wlh Zahra Lamarin mijinki yafi
karfin tunanina na rasa abinda ya kaishi Azare Mai irin wannan mahaukaciyar dukiyar ace ya
jure Zama a shagon kofar gida, dubi wannan part din tunda uwata ta haifeni ban taba ganin
gado irinsa ba wallahi, ga can gidan Aljannar duniya,Zahra ki Kara godewa Allah Dan wannan
Rahamarsa ce ba tsumin mu ba ba Kuma dabararta mu ba, mu dai mun Kaiwa ubangiji kukan

mu akan matsakolinki mun nemi sauki da sauyin Alkhairi a gurinsa, to babu abinda zame sai
muce Alhamdulillahi Allah ya Qarawa Annabi daraja lallai dogaro ga Allah jari ne, duk Wanda ya
dogara ga Allah ya isar Masa".
"Haka ne Aunty Nima fa abinsa Yana bani tsoro kinsan abinda ya bawa sajeeda kuwa ranar da
aka kaini iPhone ce da cheque na two millions, ko wacce kuma aka Bata waya da five hundred
thousand, Dan Allah Aunty waye shi?".
"Ikon Allah Wai mace ke tambayar waye mijinta a gurin wani, mu yanzu ai kece Mai bamu
wannan amsar Kuma".
Kafin Zahra ta Fadi wani Abu sukaga an bude gate wata hamshaqiyar mota ta shigo, suna Nan
tsaye harta karaso kusa dasu Sameer ne ya fito daga seat din driver,sai kuma shi uban tafiyar
ya fito daga Daya side din kananun Kaya ne a jikina sai yayi Mata wani fresh dashi, sai dai
Kamar ya Dan fada kadan. Gaishe da Aunty Hassanar sukayi kafin mahmud yace wa Zahra.
"Ga Sameer Nan shine ze mayar da Aunty gida bana son tukin malam salmanu da dare gaskiya
ya fiye gudu sosai, Sam baya duba a cikin gari yake, Aunty Allah ya tsare sai mun shigo in Sha
Allah".
Oga Sameer din yace "madam an wuni lafiya? Ya bakunta kuma?".
"Alhamdulillahi oga Sameer yasu d'ana sukaje gida?".
"Lafiya kalau d'azu ta kirani take fada min ta Kira wayarki a rufe".
"Eh wlh Zan kirata anjima"
Ta fada a takaice
Hannuwan Aunty Hasana Zahrar ta kama ta rike tana narke fuska.
"Yanzu Aunty tafiya zakiyi ki barni a Nan ni kadai ba kowa kusa dani?".
"Ikon Allah to baga zilai ba Ina cewa Ammi ta Kira Ammah ta nemi abar Miki ita, ko Kuna nawa
auren Zan baro nazo na tare a gidanki? Banda lalurar Mama ma data gitta ai da mun tsufa a
gida, kiyi hakuri na fada Miki kwanan Nan zamu dawo da Ammah fa".
Rungume Auntyn tayi ta saki kuka cikin kukan take fadar "Dan Allah ki Kara min ko sati Daya ne
bani fa da lafiya".

Mahmud ne ya Dan matso ya rabata da jikin Aunty Hasaanar Yana fadin "kuje kawai Aunty
halin zatayi miki'.
Dan zumboro Baki da hawaye sharaf a idanunta tayi tana Masa wani duba Wanda saura kadan
yayi abun kunya a gaban suruka.
Tana ganin Sun yin ribas ta fada jikinsa tana sakin Dan sirirn kukan shagwaba,cak ya dauketa
ganin gurin ba kowa yayi gaba da ita, Bai sauketa a ko Ina ba sai a bedroom dinta Kan sofa
Yayi musu masauki yana fadin " Guduna kikeyi ko precious?".
Girgiza Kai tayi alamar a'a.
"To fada min me nayi Miki kike son ki gudu daga garin Nan kibi Auntyn?".
"Ba kamoi fa, Ina son Naga Ammah ne".
"Kice na tattara na biki, ni Kuma yanzu ai sai yanda kikayi Dani yanda Kika bude min sabon
babin rayuwar nan,Wai Daman Dan Allah haka abun Nan yake Kika kyaleni Ina ta bulayi da
faman Shan magani? k'afata k'afarki duk inda Zan shiga a duniyar Nan Wallahi bazan iya
twenty four hours ban jiki a jikina ba sai a samu matsala, fada min Dan Allah Wai menene sirrin

yau though out ni sai a hankali fa gashi doctor tayi Mana tsakani Wai sai anyi two days bamu
had'u ba".
Ya Kai hannunsa Yana shafa abinda yafi tsone Masa idonu a Hankali. Hannunsa ta rike tana
kara narkewa a jikinsa tare da Dan kukan kissa sabanin na rabuwa da Aunty Hasaanar.
" Plsss.... meu Amor ka.....Bari da ciwo fa har yanzu zafi suke".
"Ya salam! Bari na duba har can din na gani, sorry SHADI I am very sorry nayi laifi ko? Ni kaina
lokacin bana gane komai Allah yayi Miki Albarka ya bamu zuri'a masu Albarka, kin Gama min
komai a rayuwa kin bani abinda ban tab'a samunsa ba, kin bani farin cikin da mafarkina da
hasashena Basu taba hasaso min akwai irinsa a cikin duniyar nan ba, Dan Allah fada min duk
abunda kike bukata a cikin duniyar nan matukar akwai sa zan Nemo Miki In Sha Allah".
Ya Gama fada Yana kokarin zuge zip din gaban rigar data saka Mai Dan balance wadda bazata
ringa takuta Mata ba saboda ba karya taking jiki a kaijin Nan nata.
Tana a'a Saida ya duba ya gani Nan da Nan hankalinsa ya tashi.
"Previoussss! Haka gurin Nan ya kumbura gara muje muga consultant na bangaren".
"Ni fa yanzu babu ciwon sosai Kuma ai kumburin ma babu a Kan dazu, Kuna ai an bani
magunguna ma Kuma Ammah ma ta turowa Aunty Hassana wasu Kuma an sawo su d'azu
suma na Sha kawai ka Bari basai munje ko'ina ba".
Rigar ya gyara Mata duk jikinsa a sanyaye, Yana zargin kansa da nuna Mata karfin da yayi,
Amma Kuma Shima abin ne ya wuce tunaninsa ya kasa controlling din kansa.
Kiran insha'i da Kiran wayar Hajiya Inna lokaci Daya ya shigo kunnensu zip din rigar ya gyara
Mata sannan ya daga Kiran Hajiyar.
"Wai Ina zahara'un ne daga Rakiya Kuma sai naji shiru? To tazo maza yanzu nasa anyi mata
irin abincin daya kamata taci Kuma taje dakina ta kwana kafin ta samu lafiya Dan Naga ba iya
kawar da Kai kukeyi ba 'ya'yan zamani".
Wata munafukar dariya ce ta kubce Masa Yana jinjina karfin halin Hajiyar, tab dole ya tattara su
Kama gabansu so take tasa' yayi kwanan tsaye kenan ai shifa yaga guri Yana jin ko tafiya
zatayi baze iya barinta tayi kwanaki ba Dan saiya zauce gaskiya.
"Wai bakaji abinda na fada bane kayi kunnen uwar shegu dani".
"Naji Mana ai bama gidan ne, mun wuce tun dazu mun koma sai dai idan daukoki zansa ayi ku
kwana tare a Nan din".
Ya fada Yana Dan Jan cheeks dinta yana kashe Mata ido daya tare da dage Mata gira Daya.
"A'a Allah ya tsari gatari da Saran shuka ai shikenan Daman gata ne Zanyi muku tunda kun
gano ba haka ba ki cinye junan ku ai jiki magayi ba'a kwacewa yaro garma ga gurin Nan Bari ba
shegiya bace da ubanta, gashi Nan za'a kawo Mata abinda nasa akayi Mata idan kaga dama ka
Bari tayi amfani dashi taci kuma abincin idan kuma ka Hana duk Daya Wai makafi sunyi
dare,duk Wanda Rai ze yiwa dad'i ai ba Kamar me Shiba".kit ta kashe Kiran.
"Subhanallahi! Allah ya kawo mu kiji min tsohuwa da Hana ruwa gudu, Bari naje masallaci na
dawo mu wuce bazan iya da rigimarta ba gara mu Kara gaba kafin ta Kira Abbie yace nayi wani
abun".


******* Cikin galabaita Salma ta dubi wadda ke tare da ita a asibiti.
"Dan Allah kirowo min nurse din Nan tazo ta dubuta min maganin ciwon baya da mara wallahi

ciwo suoe Kamar zasu fita".
Tsaki tayi matar Mai suna Saude, tana gadin "ba dole kiji jiki ba Ina cewa da hankalinki da
komai Kika biyewa wannan gantaellen yaron Nan kuka dunga badala shi namiji ai ba abin
kunya gare shi ba tunda bashi da tabo mace kuwa? Ina Jin baya garin ma ya wuce warri inda
yake aikin kamfani ya barki da wahal ga kin rasa martabarta ta har abada,'. Tunda matar tafara mata magana Salma ke kuka tayi Dana sani yafi cikin kwando. Ga
mahaifinta da wane Ido zata kalleshi Ranar da yaji wannan.abun data aikata, ga Mama ciwo
Yana can Yana ta nukurkusarta a garin mutane,sai kawai ta fashe da kuka Mai Jinyar tata Dan
haushi kasa bata hakuri tayi ta wuce Abinta ta nufi Kiran nurse din tana fadin "ba dai bin maza
Kika zaba ba bakiga komai ba wallahi yarinya babu abunda Kika nema Kika rasa Amma kin
biyewa wani sakarai Wanda Bai San inda yake Masa ciwo ba.
*_ AUREN HUCE HAUSHI_*

AISHAT ISAH MUSAH
Maman Fateemah.

09061432330
08055362975


DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JINQAI SALATI DA DAUKAKA DA AMINCI SU QARA
TABBATA GA SHUGABAN MU FIYAYYAN HALITTA ANNABIN RAHAMA MUHAMMAD
S.W.W.W DA ALAYANSA DASAHABBANSA WANDA SUKA BISHI DA SALIHAN BAYI HAR
ZUWA RANAR TASHIN ALQIYAMA AMIN.
Muna rokon ubangiji s.w.a ya Dora mu Kan dai dai abinda mukayi na kuskure ubangiji ka yafe
Mana Dan isar Manzon Allah s.a.w.w Domi shine Mai gafara Mai jinqai.

Page. 88

________Cikin shigar Atamfa super Riga half bubu da straight siket sai gyale blue black Dan
madaidaici kalar touching din ganyen jikin Atamfar ta zuba turarenta Mai sanyin kamshi, a
hankali cikin nutsuwa ta ratsa parlours din ta nufi kofar ficewa daga bangaren, haka Nan taji
bazata iya biye Masa ba su yiwa Hajiya Inna irin wannan rashin kirkin ba, gara taje Kamar
yanda ta umarceta idan ta biyewa drama dinsu sai taji kunya a banza ba abin mamaki bane su
tarar ta rigasu zuwa can din to gara ta yiwa tubkar hanci kawai.
Katin data gani a jikin wani da dan abu a jikin bangon kofar ta dauka ta zura a kofar ta bude ta
fice, har lokacin gidan shiru duk da ba wani dare ne yayi ba,yanzu ba dadewa aka idar da sallar
insha'i.
Ta cikin barandar Nan da tayi linking da part din Innar tayi amfani da kofar wadda har lokacin
ba'a rufe da key ba ta shiga, kafin ta karasa taji Hajiyar na fadin "magajiya hada Mata da
wand'ancan kafafun shanun na cikin freezer saita ringa dafa Masa a can nasan tunda yace ya
tafi tafiyar zeyi baya magana biyu, Daman ai kinibibi ne yasa ya kinkimo yarinya ya kawo min ita

tunda shi baya jaffarar rantsuwa, Kuma ki ...
Sallamar Zahra cikin siririyar murya ita ta katse Mata hanzarin abinda zata fad'a.
"Wa'alaiki Salam warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu, yau Naga shegantaka ni Hadiza Ashe
Kuna Nan ya tadani tsaye da tsohon dare yace min kun wuce gida?".
Dan murmusawa Zahra tayi kafin tace "muna Nan fa kawai ya fada ne Dan ya zolayeki, ya fita
sallah ne lokacin da Kika Kira Yana cikin gidan Nan".
"To qaraso ki zauna muyi magana Daman bana son Yana kusa kinsan ba hakuri gare shi ba
akan abinda yasan Yana da gaskiya".
Har kusa da ita ta qarasa ta zauna a Kan carpet tana gaishe da Innar.
"Tashi ki zauna Nan kusa Dani dan mi Zaki zauna a Qasa akul na gara ganin haka, Nan gidan
jama'a ne kada ki Kara yin haka mijinki yaro ne Amma ba karamin mutum bane,Dan Tani babu
komai kishiya ce ki dai ringa yiwa iyayensa haka Amma Banda ni kada kiji nauyina ki sake Dani
Kamar yanda yake sakewa dani baya boye min komai sai rigimar suce kawai nasan yaqi fada
min asalin abin Shima Kuma gajen hakuri nayi na yanke Masa hanzari badan nayi haka ba da
Ina tunani babu Inda ze tafi harna tsawon lokaci Nan to mutum Bai isa ya goge qaddararsa ba,
haka rubutaccen al'amarin yake Sai hakuri gashi kuma ya wuce har abada in Sha Allah, kina
jina ki yiwa mijinki biyayya zakiga Nan gaba yaja Miki layi da wasu mutanen a cikin danginsa to
ki bishi da yanda yake so saboda nasan kome za'ayi baze Kara Hulda da wasu ba sai da
gaisuwar musulunci da zumunci Amma babu mu'amala irin ta da Kuma bazan Hana ba Dan an
Bata Masa kwarai da gaske, kuma Banda yarda da kowa a cikin dangi ki Zama Mai kamewa a
gurin ci da Sha kinji ki nutsu ki gane Ina kowa ya dosa kafin ki yarda da kowa, akwai Yara irin ki
da wadanda suka d'ara ki babu adadi a cikin dangin kowa kuma zeyo chaaa a kanki to kiyi taka
tsan-tsan da kowa, duk Wanda yazo ki karbe shi da girma Amma kada ki yarda da raini a gurin
ko way kuwa,ai kinji abinda na fada Miki ko?".
"Eh naji Hajiya na gode in Sha Allah Zan kula".
"Yauwa haka nake so Bari kici abincin da ze gyaraki da wuri tunda su mazan naku ba masu
kauda Kai bane duk nasara sun Bata su".
Mukus Zahra tayi Dan da alama Inna irin hands free din Nan ne ba ruwanta komai ma saita
fada ita.
Magajiya ta saka ta ciro Kayan abincin daga cikin basket din tasa ta shimfida table mat a Nan
kusa dasu aka kawo abincin.
Sauka ki zuba Mana zahara'u Nima tayaki cin zanyi, ba musu ta tashi ta sauka ba bude babbar
warmer tuwon dawa ne kaura Mai kyau sosai irin 'yar katsina din Nan sai miyar kuka wadda taji
kayan kamshi da Naman rago sai yajin daddawa da pure man shanu, Zahra na ganin abincin ya
tuna Mata da mubi kusan haka abincin Inna mainuna yake. "Matso da wancen kwanon ki Zubar ki Fara cinsa so nake yabi Miki jiki ko kin warware da
wuri,Ni Miko min ruwan can da silver na wanke hannu na".
Saida Hajiya Inna ta matsawa Zahra ta ci dahuwar kusan rabinsa sannan ta kyaleta tace taci
tuwon Shima,Dan kad'an ta zuba Hajiyar Ba tayi Mata korafi ba tasan cikinta ze iya cika Amma
ta matsa ta zuba yajin da man shanun sosai a cikin miyar tana cikin cin tuwon ya shigo da
sallama da alama ita yake nema dan har wani ajiyar zuciya yayi. A hankali yake takowa har inda suke zauna idonsa Yana Kan Zahra, ita Kuma Hajiya Inna nata
idon na kansa tana kallon ikon Allah Dan tamkar ya cinyeta danya yake kallonta.

"Kai Kuma lafiya irin wannan kallon qurillah ai har ka gano muninta haba".
"Me Kika Bata Naga tana jibi a goshinta duk A/Cn dake aiki?"
Wani kallon baka da wayo tayi Masa "abinda nanu iyayen suka bamu a rin wannan lokacin na
Bata ba dai ka kawo min ita ba ai kayi Mai wahalar".
Zama yayi musa da Zahra Yana Kai hannunsa a goshinta ya Dan shafo gumin.
"Kinga fa Hajiya".
Ya nuna Mata tafin hannunsa, na gani hakan ai shi nake son gani Daman,gashi Nan Idan zakaci
ta zuba maka Idan bashi kake so ba kaje ga naka can a Kan tebirin nasara kaci".
"A'a ai kowa yabi tunda taci ai nima dole naci".
Hannunsa ya wanke ya saka cikin abinci Zahrar, Loma Daya yayi da kyar ya hadiyeta saboda
yaji.
"Haba Hajiya kinji kuwa abincin nan? Previous maza cire hannunki ai sai ciwo ya kamata kisani
a uku".
"Ungo nan, ita ai wannan babu abinda ze Mata sai gyara".
"A'a abar shi gaskiya da matsala" ya fada Yana wanke hannunsa.
Kallonsa Zahra take duk ya gigice ita fa bataji wani yaji ba tana tunanin abinda taci ne yasa
gumin ke tsatsatowa Dan ta Fara Jin can kasanta daga cikin Kamar ana hada wani Abu sai
wani Abu takeji.
"Ikon Allah na kwance ya fad'i to Kai Daman Ina ruwan biri da gada kaje kaci nake ita ta fada
maka bazata iya ci ba Ina ganin idan Allah ya kawo haihuwa Dole ka kawo min ita Nan in dai
Allah ya ara Mana numfashin".
Gaba yayi baice komai ba ya nufi dining ya zauna,lokacin Zahrar ta ida cinye Dan sauran Daya
rage tana wanke hannunsa.
"Tashi kije ki bashi abinci, ni Zan shiga daga ciki da safe magajiya zata kawo Miki kayayyakin
dana aka hada Miki ki kula da kanki sosai su maza da Kika gansu ba hakuri ke garesu ba bare
wannan miskilin Daya shafawa idonds kwallin rashin ta Ido baya Jin komai Dan Ina

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login