Showing 6001 words to 9000 words out of 94348 words
shiga kai masa duka yana harbo shi da ƙafarsa. Jin irin shaƙar da Baba Sale ya yi masa ya sa Baba Inu ya zuciya ya wulwulo shi ya damfara shi da ƙasa, a galabaice Baba Sale ya yarfe hannu yana dafe ƙugu ya ce, "Wayyo Allah Uwale ki zo ya karya ni."
Ihun da Baba Sale ya saki ne ya janyo hankulan mutanen gidan, ba a ɗauki lokaci ba mutane suka cika wurin kowa ya yi carko-carko.
"Subhanallah me yake faruwa Sale?"
Baba Ibrahim ya tambaya a razane, don irin ihun da Baba Sale ya yi za ka ɗauka farke masa ciki ake yi.
Yana daga kwance ya ɗaga hannu yana fitar da numfashi da ƙyar ya ce, "Yaya Inu ne yake ƙoƙarin datse rayuwata da ta Ɗan Bishir, don Allah ku nesanta mu da shi kada ya hallaka mu." Ajiyar zuciya Baba Ibrahim ya sauke, Baba Inu ya yi kicin-kicin ya haɗe rai yana hura hancin yin galaba a kan Baba Sale.
"Don Allah Yaya me kuke yi haka kamar ƙananan yara? Kai ne babba fa, ko me Sale ya yi maka ba sai ka rabu da shi ba ko ka yi masa faɗa. Amma yanzu ina daɗi a ce yara suna ganin irin wannan abin da kuke yi? Ta ina yara za su haɗa kansu?"
Baba Ibrahim ya rufe su da faɗa, saboda lamarin gidan nasu a kullum ƙara taɓarɓarewa yake yi. Baba Inu ya dube shi a sheƙe ya ce, "Kai Iro, dube ni da kyau ka kalli ƙwayar idona."
Baba Inu ya yi maganar yana ware dara-daran idanunsa da girma ya sa suka fara shigewa, sannan ya ɗora da cewa.
"Wane ne wannan?"
Ya tambayi Baba Ibrahim yana nuna Ɗan Bishir.
"Ɗan Bishir ne!"
Baba Ibrahim ya ba shi amsa.
"Yanzu Iro ko Sale ya isa ya zage ni ballanta wannan yaron mai zubin buhun bagco!"
Duka mutanen wurin suka girgiza kai cike da son ƙara ingiza Baba Inusa, saboda kowa ya san rashin kunyar Ɗan Bishir don haka yake da baƙin jini a wurinsu.
Nan take Baba Inu ya ba su labarin abin da ya faru, da abin da Baba Sale ya yi masa. A razane Baba Sale ya miƙe jiki yana karkarwa, ya nufi hanyar sashensa da gudu ganin Ɗan Bishir ya yi hanyar, ya rarumo shi ya riƙo shi sai kawai ya ɓarke da kuka. Kallonsa suka tsaya yi suna mamakin kukan da yake yi, ya tako wurinsu a guje yana saɓule burmemiyar doguwar rigar Ɗan Bishir ya ce.
"Jama'a ku taimaka mini Ɗan Bishir ya sha maganin ƙarin kuzari, wayyo Allah yaya don Allah ka kawo mini ɗauki." Ya ƙarasa maganar yana miƙa wa Baba Ibrahim shi sannan ya ɗora da cewa.
"Don Allah ka yi masa wani abu yaya kai ne likita, Allah Ya sa ba ajali ne yake kiransa ba ban da haka ina Ɗan Bishiri ina shan maganin kuzari?"
Yana gama maganar ya sake ɓarkewa da kuka.
"Ka ga Sale kada ka ɓata wa kanka lokaci, idan har kana son rayuwarsa ka ba ni wani abin ni kuma zan ba ka lambar mai maganin sai ka nemi makarin maganin a wurinsa. Bokan turai ta ina ya san abin da aka haɗa?"
Baba Inu ya yi maganar yana sakin murmushin ƙeta.
Baba Sale ya yi zaman 'yan bori a wurin ya ce, "A kan Ɗan Bishir zan iya sadaukar da komai da na mallaka, Yaya nawa zan ba ka don Allah ka ba ni lambarsa."
Baba Inu ya ɗauke kai gefe cikin basarwa ya ce.
"Dubu ashirin!"
A firgice Baba Sale ya ce, "Ashirin fa Yaya?"
Baba Inu ya yi gaba abinsa cikin halin ko-in-kula ya ce. "Kada ka biya matsalarka ce, ni ko yanzu na mutu akwai masu yi mini addu'a da yawa."
Jin haka ya sake ɗaga hankalin Baba Sale, ya janyo ƙafarsa yana ba shi haƙuri, babu yadda ya iya haka ya shiga cikin gida ya ɗauko dubu ashirin ya damƙa masa. Sannan Baba Inu ya karanto masa lambar mai maganin, jikin Baba Sale har rawa yake ya yi masa bayanin abin da ya faru. Mai maganin ya tabbatar masa da babu abin da zai faru da shi, sai dai ya ja hankalinsu a kan su dinga lura sosai saboda kar gaba a samu matsala.
Ɗaya bayan ɗaya suka fara watsewa, Baba Inu ya koma sashensa zuciyarsa fes don shi wannan abin da ya faru ya zame masa alkairi.
Yana nan zaune ya ji sallamar Malam Jibrin, jin haka ya sa ya dubi su Abu a kausashe ya ce.
"Ke Abu da fatan kun haɗa wa yaran nan kayansu ko? Ga sallamar Malam Jibrin can na ji, bari na je mu gaisa."
Tun da Baba Inu ya fara magana ta haɗe fuska, saboda Allah Ya sani ba za ta iya bayar da yaranta a kai su makarantar allo ba.
Yana zuwa ƙofar gida ya samu Malam Jibrin, daga gefe wata ƙatuwar motar Bus ya gani kusan rabin motar cike take da yara waɗanda za a kai makaratar allo. Bayan sun gaisa Malam Jibrin ya ce. "Malam Inu ina fatan an gama kintsa yaran? Saboda direban motar sauri yake akwai sauƙon da ake jira zai bayar a hanya." Yaya Inu ya faɗaɗa fara'arsa yana jin kamar za a sauke masa wani gingimemen nauyi daga kansa ya ce.
Malam Jibrin ba ka da matsala yanzu za su fito, amma fa an samu ƙarin yara uku." Shiru Malam Jibrin ya yi ya ce, "Yaran kuwa ba su yi yawa Malam Inu? A baya fa yara shida ka ce za a tafi da su. Idan mun yi gaba akwai 'ya'yan Malam Sallau guda biyu da za mu ɗauka."
Duk da yana jin zafin fitar kuɗin amma sanin sauƙi zai ƙara samu ya sa ya zaro dubu uku ya miƙa wa Malam Jibrin ya ce, "A ƙara da wannan Malam Jibrin, ka sha ruwa a hanya, ka san yaran ne duk kansu ɗaya. Da su Barau masu shekara huɗu zuwa biyar ne zan bari amma su ma ai sun tasa, Allah na tuba abu da girman ɗan mutum babu wuya."
Malam Jibrin ya kalmashe dubu ukun saka a aljihu yana murmushi ya ce, "Yo shekara huɗu mene ne ba za su iya yi wa kansu ba? Ai duka sun tasa, kuma Allah ai shi yake raya bawa ba mutum ba."
A daidai wannan lokacin Malam Isiya ya ƙarasa da ɗansa Musbahu mai kimanin shekara goma sha biyu, hannunsa riƙe da ƙaton buhu wanda ya haɗa masa ƙanzo, garin kwaki, sabulu da omon wanki. Bayan sun gaisa da Malam Isiya, ya kawo 'yan kuɗi ya ba shi. Malam Jibrin ya ce, "Malam Isiya ya na ganka da ƙaton buhu bayan jakar hannunsa, akwai yaran da za mu ƙara a motar fa."
Malam Isiya ya yi murmushi ya ce, "Kayan abincinsa ne a ciki, ai ba ka da damuwa Malam Jibrin zan biya kuɗin kujera biyu, don tare za mu tafi. Saboda na je na ga mkarantar da za a kai Musbahu, mu gaisa da malamin kafin daga baya lokaci zuwa lokaci na dinga zuwa ina gano shi ina kai masa kayan abinci."
Malam Jibrin ya kalli Musbahu ya ce, "Lallai Musbahu kai ɗan gata ne, abin da iyaye da dama ba sa yi kenan! Kai ma Malam Isiya Allah Ya sa da gaske kake."
Malam Isiya ya ce, "Me ka ɗauke ni Malam Jibrin? Ai yayansa Ɗahiru da ke garin Kaduna yana karatu, duk bayan wata biyar nake zuwa wurinsa, domin na ga halin da yake ciki kuma na kai masa kayan abinci da 'yan kuɗaɗen sayen abin buƙata. Kawai kuma saboda ka kai yaro makarantar allo sai ka manta da shafinsa? Yara fa amana ce da Ubangiji Ya damƙa mana kuma ranar Lahira sai ya tambaye mu a kan kiwon da ya ba mu."
Malam Jibrin ya jinjina kai, Yaya Inu yana jin haka ya zame ya shige gida yana faɗin zai haɗo kan yaran su tafi. Saboda sho ko ɓarin gyaɗa babu wanda zai ba wa a cikinsu, abin da yake ciyar da su ma Allah amfana.
Yana shiga tsakar gida ya ci karo da su Basiru kowanne ɗauke da ƙaton buhu a kansa, iyayensu ne suka ɗauko ƙanzo da garin kwakin da suka tanadar musu.
"Ku yi sauri ku shirya su Barau, Idi da Iro ƙarami, su ma da su za a tafi."
Sororo suka yi jiki a sanyaye Larai ta ce, "Don Allah malama..."
"Wallahi sai an tafi da su, tun da na rantse babu kaffara. Idan sun zauna yaran uwar me za su yi musu? Kun fi son yara su zauna babu ilimi mutanen gari su dinga zagina."
Sanin halinsa na kafiya ya su Larai suka shiga shirya ƙananan yaran kowacce tana share hawaye, ban da Abu da ta ja ta tsaya ta ki motsawa.
"Ke ba ki ji abin da na faɗa ba ne?"
Yaya Inu ya faɗa yana haɗe rai.
"A gaskiya Malam ba zan iya bayar da Bukar da malami a tafi da su ba, dududu shekarar Bukar nawa? Ko biyar da rabi bai rufa ba. Shi kuma malami shekara huɗu, idan sun je wa zai kula da su ya ba su abinci?"
Abu ta faɗa tana ƙanƙame Malami. Ran Yaya Inu ne ya ɓaci, suka shiga ja'inja yana jan Malami tana ja, daga ƙarshe ya ɗauke fuskarta da mari sannan ya fisgi hannunsu suna ihu da kuka Abu tana yi ya nufi hanyar fita. Da gudu Abu ta bi shi duk da tsohon cikin jikinta, ya waigo a fusace ya ce.
"Wallahi Abu idan har kika tako zuwa soron gidan nan a bakin aurenki tun da ba ki da hankali."
Abu ta yi turus, tana jin wani irin ɗaci a ranta.
"Iyataaaa!"
Malami ya faɗa cikin kururuwa, da gudu Abu ta rufa masa baya har ƙofar gida yana zuwa ya damƙawa Malam Jibrin su, ya fisge su kamar kaji ya watsa a cikin mota.
A zafafa Yaya Inu ya koma cikin gidan Abu ta bi shi tana kuka, ya waigo a zafafe ya ce.
"Daga nan ki wuce gidan ubanki, na warware ragowar igiyar kanki."
Daga haka ya shige cikin gida. Ɗaya bayan ɗaya 'yan masu wayon suka fara fita cike da ɗoki, musamman da suka leƙa suka hango motar da take jiransu a ƙofar gida. Su Barau da yake ƙanana ne suka dinga kuka suna tirjewa iyayensu ma suna kuka. Jin kuka da ihu tare da hargagin Yaya Inu ya sa rogawar mutanen gidan suka fito suka yi carko-carko, Inno ce ta tambayi abin da ya faru a nan Yaya Inu ya sanar da su. Takaici ne ya kama Baba Ibrahim rai a ɓace ya ce.
"Yaya wai saboda Allah wacce irin rayuwa kake yi haka? Yanzu don Allah kamar su Barau za ka kai birni makarantar allo? An ya kana tunanin goben yaran nan?"
Yaya Inu yaji kamar Baba Ibrahim ya zuba masa ruwan zafi, rai a ɓace ya mayar masa da martani.
"Kai Iro kada ka faɗa mini maganar banza da wofi, ba ɗazu ka gama faɗa mini magana a kan rashin iliminsu ba. Kai za ka faɗa mini na hango gobensu, akwai shege ɗaya a cikin gidan nan da yake ciyar mini da su? Tun da ni na samu kaina a gobena ai shi kenan! Daga yau ma kada wani ƙaton banza ya sake shiga hurumin iyalina." Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana fisgar Idi da ko wando babu a jikinsa ya yi waje da shi. Su Larai suka durƙushe a wurin suna sakin kuka.
Suna nan tsaye suka ji tashin motar, hakan ya sake ɗaga hankalansu, a daidai lokacin Yaya Inu ya dawo yana muzurai yana harare-harare.
Bayan Sallar Isha'i
Zaune yake a matsakaicin ɗakin da aka ware masa, daga gabansa wani ƙaton fulas ne cike da farfesun kaji.
Sai da ya zuge tsokar cinyar kazar hannunsa, sannan ya ɗaga ƙaramar wayarsa ya danna wata lamba. Bugu ɗaya ta yi ya ji an ɗauka, ya yi ƙasa da murya ya ce.
"Barka da hutawa 'Yar gwal!"
Malam mai Yasin ya furta yana kurɓar romon naman, amsa masa ta yi sannan ta ce.
"Ni fa na gaji wallahi..."
Da sauri ya katse ta.
"Haba 'Yar gwal, na faɗa miki kwantan ɓauna na yi wa mutanen gidan nan, har na samu na aure tsohuwar nan. Ni na san Inno ba za ta ba ni matsala ba sai dai 'ya'yanta, amma ina aure ta magana ta ƙare. Tatsarta zan ta yi har na tara mana kuɗin da za mu hole, kada ki ji muryata ƙasa-ƙasa har yanzu nuna musu nake ba ni da lafiya."
Daga can ɓangaren 'Yar gwal ta saki dariya ta ce. "Shege Malam Gambo wallahi ko shaiɗan bai kai ka shaiɗanci ba."
Malam mai Yasin ya saki dariyar shakiyanci, suka cigaba da hira sannan suka yi sallama.
Ya kai kusan awa guda a zaune a bakin gadon yana yi mata firfita, saboda ko kaɗan ba ya son abin da zai dagula lissafinta. A hankali Rahina ta buɗe idanunta ta sauke su a kan mai gidanta Labaran, murmushi ya sakar mata ganin za ta tashi ya sa ya ɗago ta zaune sannan ya rungume ta sakar mata kiss a goshi.
"Barka da tashi masoyiya!"
Labaran ya furta cike da so yana jin kamar zai lashe Rahina. Fari ta yi masa da ido ta ce, "Wai tun da na kwanta kana zaune masoyi?"
"Ina zan matsa daga wurinki ƙaunata. Yanzu dai bari na sirka miki ruwa ki yi wanka. Ya ƙarasa maganar ya fita daga ɗakin."
Rahina ta bi bayansa da kallon soyayya tana jin tamkar ita kaɗai ta yi dacen miji a duniya. Tana nan zaune ya dawo ya riƙo ta, ganin za ta tuɓe kaya ya saka hannu ya fara rage mata.
Rahina ta ɗaura zani ta yafa ɗan kwali a kanta, Labaran ya riƙe mata hannu ɗayan hannun nasa yana riƙe da kwandon wanka suka nufi hanyar banɗaki. Sai da ya ga ta shiga banɗakin, sannan ya koma domin ya zuba mata abincin da za ta ci idan ta fito. Rahina irin matannan ne masu tsayi da ƙiba, shi kuma Labaran ɗan tsamurmuri ne ko tsayin kirki ba shi da shi. Yadda yake son Rahina da kishinta ji yake zai iya aikata komai a kanta.
Malam mai Yasin yana daga zaune a ɗakinsa ta labule ya hango wucewar Rahina, ya jima ransa yana biyawa da ita don haka bayan tafiyar Labaran ya yi zaraf, bayan ya ji ta fara sheƙa ruwa ya nufi banɗakin cikin sanɗa. A hankali ya tura ƙofar banɗakin, da yake dare ne sai Rahina ta yi tsammanin ko Labaran ne ya shiga domin ya tayata wankan. Malam mai Yasin yana shiga da sauri ya wara hannuwansa ya dadumo ta, cike da so da ƙauna Rahina ta ce.
"Wallahi ba don kada na saka son zuciya ba, da sai na ce duk duniya babu matar da ta kai ni sa'ar miji masoyi."
Malam mai Yasin don kar ya yi magana ta ji muryarsa sai kawai ya ce, "Ummmmm!" Ya cigaba daduma hannunsa a jikinsa. Rahina tana shafo fuskarsa ta ji gemunsa da gashin bakinsa sun yi mata ƙababa, a razane ta ja da baya da ta ce. "Wayyooo Allah! Masoyi ka zo kwarto a banɗakin nan."
Da gudu Malam mai Yasin ya fice daga banɗakin ya faɗa ɗakinsa, Labaran da ke ɗaki jin ihun Rahina ya sa ya zaro wani kafcecen almakashi irin na aikin gona ya tafi da shi.
Yana zuwa banɗakin ya shiga jera mata tambayoyi, ba ta tanka masa ba sai ji ya yi ta fashe da kuka. Ganin ba shi da wata mafitar ya sa shi ma ya rushe da kuka har da majina, sai da ta yi mai isarta sannan ta ce.
"Kwarto ne ya shigo mini banɗaki, kuma tas ya gama lalube ni."
Wani abu ne ya soki ƙirjin Labaran tsananin soyayya da kishinta ya rufe shi.
"Sai da na laluba gemu da gashin bakinsa, na gane ba kai ba ne tun ba ka da shi." Rahina na ƙara faɗin haka ta sakin kuka. Jikin Labaran ne ya shiga karkarwa zuciyarsa tana zafi, cikin huci ya ce.
"Na tabbata Ado ne! A cikin gidan nan shi ne tuzuru sako zaninki ki tafi ɗaki, wallahi yau sai na guntule shi da almashin hannun nan nawa. Nan gaba sai na ga da me zai nemi yin kwartoncin."
Labaran yana gama magana ya fita a guje yana wani irin ihu kamar wanda zai tunkari maƙiya a filin yaƙi.
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
SHAFI NA HUƊU
Kasancewar yaya Ado dawowarsa daga wurin aiki kenan, ya sa ya shiga rage kayan jikinsa domin ya watsa ruwa ya gabatar da sallar Isha'i. Yana daga cikin ɗakinsa ya fara jiyo ihun Labaran, ya girgiza kansa cike da takaici, yana jin haushin yadda gidansu ya zama tamkar gidan haya saboda yadda zuciyar kowa take a kusa. Ihun