Showing 12001 words to 15000 words out of 94348 words

Chapter 5 - GIDAN LIKITOCI BOOK COMPLETE BY AMEERA ADAM.txt

29 Sep 2025

833

Isha'i Yaya Inu ya shigo gida, sai ga shi a ranar ya yi jinkirin shigowa don har kusan goma saura. Haka ta zauna a gefen gado har ta fara gyangyaɗi, sannan ta ji shigowarsa. Da sauri ta ɗauko Hannafi ta kai shi gefen Uzairu ta kwantar da shi, saboda ta ji Hajiya Zanni ta ce ba a zuwa turaka da yara suna takurawa uwargida da mai gida. Turarenta na Binta sudan haɗe da jan miski ta ɗauko ta sake bulbulawa, ta janyo wani fakeken gajeren wandonta a drower shi ma ta shafe shi da jan miski. Ta nufi ɗakin Yaya Inu hannunta ɗauke da tiren abinci, dama daga ita sai ɗaurin ƙirji wanda hakan duk yana cikin lecture Hajiya Zanni. Tana shiga ta ajiye masa abincin a gefe sai kuma ta ja ta tsaya a wurin, Yaya Inu ya ɗago fitilarsa ya haske ta yana shirin yi mata magana sai ya ga Indo ta saki zanin jikinta ya faɗi ƙasa. Saboda duk huɗubar da Hajiya Zanni ta yi musu ta haddace ta kanta. Da mamaki Yaya Inu yake bin Indo da ke tsaye tumɓur sai ɗan kanfai, da wata sakakkiyar rigar mama a jikinta wacce suk ta zuge ta saki kamar gugar jan ruwa saboda yawan sakawa.

"Ke Indo lafiyarki kuwa?"
Yaya Inu tambaya a tsorace.
Indo ta ji daɗi har ranta, don ta ji Hajiya Zanni ta ce akwai wani shauƙi da miji yake shiga idan an yi masa haka. Indo ta fara harba ƙafa tana wani juyi ita a dole rawar India za ta yi a gabansa, Yaya Inu zai sake magana Indo ta wurga masa wannan burgujejen gajeren wandon da ta ɗauko, wanda ta jiƙe shi sharkaf da turaren miski da Binta sudan. Gajeren wandon ya sauka a saman fuskar Yaya Inu, ya yi sakatoto yana bin ta da kallon mamaki. Indo ta yi wani tsalle tana harba ƙafa haɗe da fisge rigar maman jikinta, kusan lokaci ɗaya ta kifar da kwanon miyar abincin Yaya Inu. Kuma a daidai lokacin rigar maman ta faɗa saman wuyan Yaya Inu da ya gama kai wa wuya.

07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA

SHAFI NA BIYAR

Ko kaɗan Indo ba ta damu da ganin ɓarnar da ta yi masa ba, saboda ta ji Hajiya Zanni ta ce duk cikin sirrikan da ta ba su babu na yarwa indai a ɓangaren mallaka da saye zuciyar miji ne. Don haka ta yi wata girgiza ta cake a wuri ɗaya, ta fara miƙa masa hannu ɗaya irin yadda jaruman india suke yi, idan za su miƙa wa masoyinsu hannu domin su yi rawa. Ta miƙe ƙafa gaba da zummar ta yi tsalle ta dira a gaban Yaya Inu, ta yadda za ta ɗago shi ta manna a jikinta kamar yadda Hajiya Zinni ta kwatanta musu, bisa tsautsayi ƙafarta ta harɗo labulen ɗakin ya faɗo a kanta. Kukan Hannafi ta fara ji sama-sama da alama ya tashi daga bacci, amma sai ta basar ta tunkari Yaya Inu da zuciya ta gama cika shi. Don yadda yake ji ransa ya ɓaci kamar ya tashi ya shaƙe Indo, saboda wannan sabon iskancin da take ƙoƙarin kawo masa. A gabansa ta tsaya tana wani rangaji, iska ta fara kaɗo cikin ɗakin saboda sanyin da ake busawa. Burgujejen gajeren wandonta ya fara kaɗo fuskar Yaya Inu, Indo ta yi masa wani far da idanu ta ƙanƙance murya ta ce.

"Taso mu yi rawa lantarkin zuciyata..."

Kalaman Indo suka katse sakamakon fisgowar da Yaya Inu ya yi mata, ta faɗi ƙasa daɓas! Gwiwoyinta suka bugu da ƙasa.
A tsammanin Indo shauƙin da Hajiya Zanni ta ce maza suna shiga ne ya fara kama Yaya Inu, don haka ta shanye zafin da ta ji ta sake wurƙila idanu da sunan fari tana wani banƙarewa kamar kazar mayu ta ce.

"Na jima ina alla-alla kwanakin girkina su dawo, saboda na shayar da kai romon soyayya..."

Takaici ya sake lulluɓe Yaya Inu, ya ɗaga hannu ya yi wa Indo mahangurɓa a fuska. Wani irin mummunan yanayi ya ratsa ta, don haka a gigice ta miƙe da niyyar ceton kanta. Yaya Inu ya shatalo ta da ƙafarsa ta faɗa kan miyar kukar da ta zubar.
A fusace ya ɗaga hannu ya zabga mata mari cikin fusata ya ce. "Wannan iskancin a gidan uban wa kika koyo shi? Wallahi ko kukar bulukiya ce a kanki sai na sauke miki ita."

Indo ta fashe da kuka tana jan jiki gefe ta ce, "Yanzu mai gida duk abin da na yi maka ban birge ka ba, saboda Allah duk wannan kissa da kisisinar..."

"Au to, sai yanzu na gano! Wato saken da kika samu na zuwa cikin gari, shi ne kika haɗu da siraran karuwai suka koya miki wannan karuwancin ko? To ba a gidana ba, tun wuri ki watsar da abin da yake kanki idan ba haka ba ki ƙara gaba." Shiru Indo ta yi tana share hawaye. Daga can bakin ƙofa Hansatu da Larai suka ƙaraso suna tambayar abin da ya faru saboda sun ji ihun Indo, Yaya Inu bai tanka musu ba saboda har lokacin haushin Indo yake ji. Ita ma Indo ban da hawaye babu abin da take yi, don haka kowacce ta ƙunshe dariyarta cike da ƙeta suka koma ɗaki. Saboda dama haushin Indo suke ji, a kan shan ƙamshi da kallon wulaƙancin da ta dinga yi musu.

A kunyace Indo ta tashi za ta fita Yaya Inu ya ce, "Kuma tun wuri ki gyara mini ɗaki tas, kika ɗebo siraran cinyoyi kamar tsinke ashana. Yo ni akwai wani iya shege da wata figaggiya za ta yi mini?" Takaici ya sake cika Indo, jiki a sanyaye ta ƙarasa ta zare rigar mamanta da ke saƙale a wuyansa. Ta ɗauki zaninta ta ɗaura sannan ta shiga kiciniyar gyaran ɗakin, a cikin ranta ta shiga tsine wa Hajiya Zanni da miyagun shawarwarin da ta ba ta.

Washegari

Tun kusan kimanin ƙarfe huɗun asuba ya farka yake sharɓa kuka, tun yana yin na zuciya har ya dawo yin na sarari. Sautin sasshekar kukan da Baba Sale yake yi ne ya farkar da Uwale daga baccin da take. Gabanta ne ya yi mummunan faɗuwa, da sauri ta zaro ƙaramar wayarta a ƙarƙashin filo ta haske ɓangaren da Ɗan Bishir yake bacc. Ganin yana bacci cikin kwanciyar hankali ya sa, ta dubi Baba Sale ta ce.
"Me yake faruwa mai gida?"
A maimakon Baba Sale ya ba ta amsa sai ya sake kallon wurin Ɗan Bishir ya fashe da kuka. Jikinta ne ya yi sanyi don rabonta da ganin kukansa, tun wata rashin lafiya da Ɗan Bishir ya yi kusan shekara ɗaya da rabi kenan.

"Mai gida don Allah ka cire ni a cikin duhu, wallahi hankalina duk a tashe yake."
Uwale ta furta jikinta yana rawa, don ta ayyana abubuwa da dama a cikin ranta.
Baba Sale ne ya faɗa jikinta kamar wani sabon maraya, ya ja majina cikin kuka ya ce.
"Kamar kin manta yau ne za a yi wa Ɗan Bishir shayi! Yau ne fa wa'adin kwanakin da za a yi masa kaciya ya cika."
Baba Sale ya yi maganar yana share ƙwalla, haɗe da shigewa jikin Uwale kamar wani ƙaramin yaro. Ya ɗago murya a dashe saboda kukan da ya ci ya ce.

"Uwale hankalina a tashe yake, wallahi duk wani abu da zai taɓa lafiyar Ɗan Bishir ba na son shi..."

Kuka ya sake cin ƙarfinsa, takaici ya mamaye Uwale amma gudun kada su fara raba hali tun da asuba ya sa ta ce.

"To ya za a yi, ai dama kowa da haka ya fara. Yanzu dai ka tashi ka je ka yi sallah na ji har an shiga masallaci."
A hankali Baba Sale ya fita yana jan majina, ya ɗauro alwala ya wuce masallaci. A lokacin da ya ƙarasa masallaci a raka'ar ƙarshe ake, bayan an idar ya tashi ya ciko raka'a ɗaya sannan ya yi sallama. Baba Sale hannu ya ɗaga ya fara zazzago addu'a, mutane ba su yi tsammani ba sai ji suka yi ya fashe. Sororo mutanen wurin suka yi, Yaya Ado har zai fita ya koma ya zauna. Duka mutane suka yi carko-carko suna kallonsa, Malam Rabe ne ya yi ƙarfin halin zuwa kusa da shi ya ce.

"Sale me yake faruwa ne?"

Baba Sale ya sharce majina ya fara wata shassheka kamar wanda uwarsa ta mutu ya ce, "Ina buƙatar addu'arku. Domin kowa ya san ɗana ɗaya ne a duniya wato Ɗan Bishir! Kuma ina fatan ya haifa mini jikoki ashirin da huɗu sai dai kash..."

Kuka ya sake cin ƙarfinsa. Gaban su Baba Labaran ya faɗi, don duk wanda ya ci karo da irin kukan da Baba Sale yake yi za ka ɗauka mutuwa aka yi masa. Cikin haɗin baki hankali a tashe duka mutanen cikin masallacin suka ce.
"Sai dai me?"

Baba Sale ya rungumo hannun Yaya Inu ya shiga goge fuskarsa da shi ya ce.
"Ku yi mini fatan a yi a gama wa Ɗan Bishir shayi, an jima Bala wanzan zai zo ya yi masa don ni ba zan iya ba. Ba ni da ƙarfin zuciyar ta guntule Ɗan Bishir."

Jin haka ya sa takaici ya mamaye su, a zafafe Yaya Inu ya fisge hannunsa ya ce.
"Kai dai ka zama gantalalle ɗan wahala. Yanzu shayin da za a yi wa Ɗan Bishir ne kake wannan iskancin, kai Allah Ya tsine iskanci da magoya bayansa. Shi ya sa ka sakar mana murya kamar an kunna generator kana ihu, Allah wadaran naka ya lalace."
Daga haka Yaya Inu ya fice daga masallacin rai a ɓace. Ɗaya bayan ɗaya haka mutane suka watse kowa yana mita, Baba Sale ya koma gida ya sake saka Ɗan Bishir a gaba yana lailaya shi kamar zai mayar da shi ciki.
Tun da Ɗan Bishir ya tashi daga bacci Baba Sale ya ɗauke shi ya rungume, hatta abinci a baki ya dinga ba shi. Kimanin ƙarfe tara na safe Bala wanzan da yaransa suka ƙarasa ƙofar gidan, Uwale ce ta iya ɗaukar Ɗan Bishir ta miƙa masa. Domin Baba Sale uwar ɗaki ya shige ya haɗa kai da ƙarfen gado yana kuka. Saboda shekara ta uku kenan ana cewa za a yi masa shayi yana ɗagawa saboda soyayyar da yake yi masa. Yana nan zaune Inno ta aika kiransa, da ƙyar ya iya fita ya nufi sashenta fuskarsa ta kumbura saboda kukan da ya sharɓa. 'Yan'uwansa ya gani gabaɗaya a zaune, ya yi mamki matuƙa don haka ya zauna a gefe yana kallonsu. Inno ta dube su ɗaya bayan ɗaya, sai kuma ta saki wani murmushi zuciyarta fes ta ce.

"Dalilin da ya sa na tara ku a wurin nan ba komai ba ne, illa na sanar da ku wani abin alheri kuma abin farinciki da ya tunkaro mu. Kuma na tabbata za ku ji daɗinsa, domin cigaba ne da zai iya kai ni aljanna da ku bakiɗaya."
Fuskarsu ɗauke da fara'a gabaɗaya suka furta.

"Ma Shaa Allah, gaskiya wannan abin farinciki ne Inno. Allah Ya sa mu dace."
Inno ta sake washe baki fuskarta wasai kamar gonar auduga ta ce.
"Amin Ya Rabbi."

"Amma Inno wanne abin farinciki ne haka?"
Baba Labaran ya tambaya.

Inno ta rangwaɗa kai gefe ta ce, "Dama zan sanar da ku mun gama daidaitawa da Malam, don haka ma na ce zan sanar da ku a ɗaura mana aure ranar Juma'a mai zuwa."

Sororo gabaɗaya suka suna kallonta cikin mamaki Baba Ibrahim ya ce.
"Inno aure fa kika ce?"
Inno ta haɗe rai ta ce, "Eh sunnar Annabi!"

Ajiyar zuciya Yaya Inu ya yi ya ce, "Yanzu Inno tuntuni ba ki yi aure ba sai yanzu? Saboda Allah tun da ƙarancin shekarunki bayan da Baffa babba ya rasu ba ki yi ba sai yanzu da girma ya cim miki? Gaskiya Inno ki yi tunani."
Inno ta yi wa Yaya Inu kallon sheƙeƙe ta ce, "Ka karanta mini aya ko hadisin da Allah Ya haramta wa tsohuwa aure! Yanzu Inusa sunnar Annabi kake ƙoƙarin daƙilewa?"
Yaya Inu ya yi shiru don zuciya ta gama zuwar masa wuya. Saboda dama tun farko jininsa bai haɗu da Malam mai Yasin ba.

"Yanzu Inno da za ki ce za ki auri mutumin nan mu da ba mu san asali da tushensa ba, babu wanda muka sani na shi fa. Abu ɗaya ne fa ya haɗa mu da shi taimakon da muka yi masa a airport, sanadin kamen da aka yi masa wanda har yau babu wanda muka sani a cikin danginsa. Gaskiya ko za ki aure shi sai mun san wani daga cikin danginsa."
Baba Ibrahim ya yi maganar fuska a haɗe.

"Wallahi kai ka ma yarda ta aure shi, na rantse da Allah yadda na tsani ƙyamusasshen tsohon can idan ban sheme shi ba Allah Ya tsine mini!"
Yaya Inu ya faɗa jikinsa yana karkarwa.
Inno ta yi karaf ta ce.
"To wallahi ku shaida duk wanda na ji ko kallon banza ya yi wa Malam sai na ɗaga masa mamunana. Kuma dama na faɗa muku ne saboda na fita haƙƙinku na 'ya'ya atoh, don kada ku ji muna kashewa da binnewa ni da shi a ɗaki ku fara yi mana ɗan zargi. Duk da dai dama na faɗa masa auren ɗauko buta za mu yi."
Inno ta sake kallonsu ɗaya bayan ɗaya ta cigaba.
"To ku ban da abinku ace yau uwarku ta mutu da aure a kanta ba ya fi daraja a wurinku ba? Allah na tuba duk haƙurin da na yi da ubanku tsawon shekaru bai wadatar ba? Wallahi da shi ne ma ba zai ɗauki shekarun da na ɗauka bai yi aure ba, a toh a yanzu na samu wanda zai ba ni walwala da kulawa gwargwadon farincikina. Da ku ɗaura mini aure da kar ku ɗaura duk ɗaya, saboda yanzu zan tafi wurin Malam Liman ya zama waliyina shi kuma Malam Ladan ya yi wa Malam walicci ashafa mana fatiha."
Shiru ta ji sun yi ba tare da sun tanka mata ba, ta kalle su rai a ɓace ta ce duka su fice mata daga ɗaki. Nan take duk suka fice, Baba Ibrahim zai fita ya waigo ya ce.

"Idan Allah Ya kai mu zan ɗauki jininki da na Malam ɗin sai na yo muku gwajin da ake yi kafin aure."
Haɓa Inno ta riƙe ta ce.
"Kai Iro ka fita a idona na rufe, uban me zan yi da wani gwaji ni da zan yi auren ɗauko buta." Baba Ibrahim ya fita don ya lura Inno a fusace take, sai dai ya ci alwashin zai shawo kanta ya yi musu gwajin koda ba za ta haƙura da auren ba.
Malam mai Yasin da yake raɓe abayan katanga yana jin duk abin da suke faɗa ya saki murmushi a fili ya ce.
"Ashe na kusa ɓarje amarci tun da na tsinci dami a kala. Na ci mai kyau na sha mai kyau, nan gaba kuma na kwashi ganima son raina." Ya ɗaga kansa yana kallon tanƙamemen gidan gandun ya ce.
"In Shaa Allahu har wannan gidan sai na mallaka, da ni kuke zancan dan ubanku."
Yana jin motsin tafiya ya yi sauri ya faɗa ɗakinsa ya saki labule.

Tun da Laraba ta dawo gida ta ci alwashin idan sama da ƙasa ce za ta haɗe ba za ta sake zuwa makaranta ba. Kuma ko da gari ya waye, sai ta yi shirin makaranta kamar wacce za ta je da gaske, amma sai ta nufi cikin gari ta shiga yawace-yawacenta. Ta jima tana tunanin hanyar da za ta ɓullo wa Mai garu da su Malam Sule, a kan cin zarafin da suka yi mata amma har lokacin ba ta samu mafita ba. Sai da ta daidaici lokacin tashi ya yi sannan ta kamo hanya ta fallo da gudu, a bisa tsautsayi za ta tsallaka wata hanya shi kuma wani matashi ya shawo kwana da motarsa ya ɗan make ta. Laraba tana ganin haka ta sake bajewa a ƙasa tana numfarfashi, a gigice matashin ya fito daga motar jikinsa sanye da uniform ɗin NYSC. Laraba ta ƙyallere ido a kaikaice bayan ta hango fitowarsa ta sake runtse ido tana ihu.

"Wayyo Allah! Ƙafata da kaina za su ɓalle. Wayyo Allah."

Ganin yadda matashin ya gigice ya sa Laraba ta sake narkewa.
"I'am very sorry dear!"
Ya furta a gigice yana ɗago ƙafar Laraba da ya ga ta dafa ta. Laraba ta yi shiru tana bin zara-zaran dogayen yatsun hannunsa, don dama ba ta fahimci abin da ya ce ba.

"Lets go to hospital..."

"Wayyooooo jama'a ya karya ni."
Furucin Laraba ya sake katse shi.

"Ki yi haƙuri please mu je hospital, a ga me ya faru da ke."
Kallon da Laraba take wurga masa da dara-daran idanunta ya sa tsoro ya kama shi, a ransa yake raya ko dai aljana ya bige? Yana nan tsugunne ya ji ta bushe da dariya. Ta sake zaro masa ido ta ce.

"Kai an gaya maka gadon gidanmu suna zuwa asibiti? Mu za ka nuna wa boko?"
Cikin Mahmud ya kaɗa, gabansa yana faɗuwa ya ce.
"Ku yi haƙuri me kuke so."

Laraba ba ta tanka masa ba, ta nuna masa wata katuwar bishiyar kuka da ke gefe. Ganin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login