Showing 60001 words to 63000 words out of 94348 words

Chapter 21 - GIDAN LIKITOCI BOOK COMPLETE BY AMEERA ADAM.txt

29 Sep 2025

841

Shukra suka kwasa gabaɗaya. Jafar da Ibrahim ne ba su da irin halinta sai Auta don haka har sun fi su Shukra sabo da mutanen cikin gida.

Gidan marigayi malam Haruna mai shanu gidan gandu ne da ya haɗa kakanni, iyaye, jikoki da kuma 'ya'yan jikoki. Baba Mamman da Baba Yunusa ne kaɗai ba sa zaune a cikin gidan, kasancewar yanayin aikinsu da sauye-sauyen garuruwan da ake yi musu a wurin aiki. Amma kowannensu yana da ɓangarensa a cikin gidan, idan suka zo hutu suna sauka da iyalansu a ciki.

Marigayi Umaru Haruna Mai shanu shi ne mahaifin Uwani, ya rasu tun mahaifiyar Uwani na da cikinta wata bakwai sakamakon hatsarin mota. Maryama Shu'aibu shi ne ainihin sunan mahaifiyar Uwani, dalilin mutuwar mahaifin Uwani ya sa Dada da su Baba Mamman suka ci gaba da kula da ita. Bayan wata tara Allah Ya sauke ta lafiya ta haifi jaririyarta, ta ci burin idan namiji ne ta mayar da sunan mijinta Umaru. Amma da ta haifi mace su Dada suka tambaye ta sunan da take son a raɗa wa jaririyar, da kanta ta ce a saka sunan Dada saboda irin karamcin da suka nuna mata, sai ake kiranta da suna Uwani. Bayan da aka yaye Uwani ne mahaifin Maryama ya nemi da ta dawo gabansa da zama, domin zawarawa suna ta zuwa kai masa gaisuwa da nuna ƙoƙon bararsu a kan aurenta. Ranar da za ta tafi ne Dada ta nemi da ta bar mata Uwani saboda soyayyar da take yi wa mahaifinta, idan tana ganinta za ta dinga jin daɗi. Bayan komawar mahaifiyar Uwani gidansu ko shekara ba ta rufa ba aka ɗaura mata aure da wani mutum, a lokacin yana da aure da mata ɗaya da yara huɗu. Maryama ta aure shi ne ba don tana son shi ba, sai don kawai ta yi wa mahaifinta biyayya amma har lokacin zuciyarta na ga mahaifin Uwani. Garin da take aure yana nesa da garin su Uwani sosai, kuma ta haifi yara biyu da malam Salihu mace da namiji, sai dai ko kaɗan ita da kishiyarta ba sa jin daɗin zama da shi sakamakon mugun halinsa.

Uwani ta taso a hannun Dada cikin kulawa da nuna tsantsar soyayya, tun bayan tafiyar mahaifiyarta baba Mamman ya so a ba shi riƙon Uwani amma fir Dada ta hana shi, lokacin da Hajiya Saratu ta ji ba ƙaramin daɗi ta ji ba. Shekarun Uwani goma sha huɗu a duniya kuma irin fitinannun yaran nan da suke fita zakka ko a cikin unguwa. Rashin ji, rashin tsoro, kafiya, naci, tsokana rashin yafiya sune halayen da suka mamaye Uwani har mutanen garin suka saka mata suna 'Uwani 'Yar Ƙashin Gwiwa' saboda hatsabibanci da rashin jin ta. Duk cikin gidan mai shanu Dada ce kaɗai ba ta ganin laifin Uwani, don haka ma duk wurin da ta shiga sai dai su bi ta da harara.

Jafar ma'aikacin ɗan sanda ne mai ɗauke da muƙamin ASP, shekarunsa talatin da biyu cif a duniya. Ya yi karatunsa tun daga primary har zuwa matakin degree a jami'ar Bayero University. Miskili ne bai cika surutu ba, sai dai wani lokacin bauɗaɗɗan hali gare shi. Yana da kirki ga wanda suka fahimci juna sai dai wani lokacin yana da saurin fushi. Ba ya son raini ko kaɗan kuma yana da kykkyawar mu'amala da abokan aikinsa. Lokacin da ya fara aiki jihar Kaduna aka tura shi bayan wani lokaci ne ya samu sauyin aiki zuwa garin Katsina daga baya aka mayar da shi garin Lagos, ya kwana biyu a Lagos don bai cika zuwa hutu sosai ba. Ko da ya zo ma a gurguje yake kawo wa Dada ziyara shi ya sa Uwani ba ta wani san shi farin sani ba. Tana yawan jin labarin irin kulawar da Jafar ɗin ya dinga ba ta a lokacin da take yarinya, sai dai a wannan karon sam ba ta ga kalar mutumci a tattare da shi ba. Wannan hutun da Jafar ya samu kusan wata guda zai yi kafin ya koma, kuma ya ji labarin zuwan mahaifansa hutu da tariyarsu don haka shi ma ya yada zango a nan sashen Dada.

Mu Koma Labari

Tamkar sabuwar munafuka ko ɓarawon da yake sanɗa a daidai gaɓar da yake ɗaukar abin da ba na shi ba, haka Uwani ta shiga cikin ɗakin saɗaf-saɗaf tana tafe tana waige. Sai da ta kai ga ƙuryar ɗakin sannan ta sauke gwauruwar ajiyar zuciya.

"Uban 'yan iyayi ashe ba ya cikin ɗakin, da tuni yana nan a naɗe a kan katifa kamar mai karyayyan ƙugu." Ta furta cikun salon kwaikwayon muryarsa. Motsin da ta ji a bayanta ne ya sa ta yi mutuwar tsaye, zuciyarta ta fara harbawa tamkar za ta bijirewa zama a ƙirjinta, cikinta ya shiga juyawa yayin da zazzafan gumi ya shiga keto mata. Caran zakaran da ta ji a bayanta ne ya sa ta sake sauke ajiyar zuciya, ta saki murmushi a fili sannan ta furta.

"Lawan wallahi ka cika binbinin tsiya, yanzu ɗakin Ofisa ma sai ka biyo ni. Idan kuwa ya kama mu wallahi sai ya kusa murɗe maka wuya." Tamkar zakaran ya san da shi take ya ci gaba da takawa yana tafe yana sakin kashi a tsaftataccan ɗakin da ya sha gyara ta ko ina sai zuba ƙamshi yake.

  Kafin Uwani ta ƙarasa kan katifar ɗakin tuni zakaranta da take kira da Lawan ya yi mata jagora zuwa kan luntsumemiyar katifar da ta sha gyara, a ɗame take da zanin gado kamar gadon sabuwar amaryar da za a kai ɗakin miji.

"Lawan ina ka baro Fanteka, uwar 'ya'ya na san tana cen tana yawo ita da 'ya'yan iya." Uwani ta yi maganar kamar da mutum ɗan'uwanta take yi. A saƙale ta hango uniform ɗinsa na kayan 'yan sanda masu bulun riga da baƙin wando. Da sauri ta janyo ta hau kwaɓe kayanta kafin wani lokaci tuni ta saka a jikinta, sai da ta gama soshe kanta da ya cukurkuɗe sannan ta kafa baƙar hularsa a kanta. Cikin ƙwambo ta fara taku ɗaiɗai sannan ta cake a wuri ɗaya.

"Ba na son hayani matsa daga kaina, ƙazama mai kwarkwata." Ta yi maganar cikin kwaikwayar maganar Jafar, tana faɗin irin maganganun da yake faɗa mata.  Ta jima a tsaye tana surutanta sannan ta ƙarasa gaban mudubin da ke can gefenta, kamar a mafarki haka ta hange shi tsaye ƙyam kamar wanda ya haɗiyi falwaya. Fuska a haɗe kwatankwacin ta fusataccan bujumin sa. Nan take yawun bakinta ya ƙafe, ƙafafuwanta suka ɗauki rawa ƙirjinta ya shiga harbawa. Sai dai dakiya da ƙarfin zuciyar Uwani ya sa ta basar kamar ba ta gan shi ba.

"Iya iya iya." Ta ji 'ya'yan kazarta na faɗa yayin da zakaran da ya gama kasaye ɗakin ya fara cara, da sauri kazar ta tunkaro ɗakin da niyyar shiga a fusace Jafar ya sa ƙafa ya yi ball da ita. Wata azababbiyar ƙara Uwani ta ƙwalla kamar da ita Jafar ya yi ball, ta fara tafiya wandon uniform ɗin yana zamo mata.

"Innalillahi kashe mini fantake za ka yi..." Uwani ta yi maganar tana shirin fita daga ɗakin, yayin da Lawan (Zakaranta) ya firgice yana tsalle-tsalle a ɗakin, yana jefo masa kwalaben turare.

"Gidan uban wa za ki?"Jafar ya wurga mata tambaya rai a ɓace.
"Ina da gidan da ya wuce ɗakin Dada..." Jafar ya katse maganarta ta hanyar bige bakinta da ƙarfi.

"Wallahi na ba ki nan da minti goma ki gyara mini ɗakin nan, sannan ki yi gaggawar cire mini uniform tun ranki bai ɓaci ba. Kuma idan kin gama zan gauraya da ke."

"Sai ka fita na canza kaya."
Sororo ya yi yana kallon Uwani don bai san lokacin da ta raina shi ba. Yana shirin sauke yatsunsa biyar a fuskarta wandon uniform ɗin ya zamo mata, gajeren wandon da ke jikinta ya bayyana. Fari ne amma dauɗa da jirwaye sun sa ya dafe saboda ƙazanta. A ƙazance ya kawar da kai gefe haɗe da tofar da yawu.

"Ka san dai kallon tsiraici haramun ne, ka fita na sauya kaya. Kuma ni dai ba 'yar iska ba ce..."
"Idan ba ki rufe mini baki ba wallahi sai na haɗa miki jini da majina a wurin nan. Sakarya fuska kamar ta aljanu, daga yau ko wani ne ya aiko ki ɗakin nan ba za ki ƙara marmarin shigowa ba." Tun da Jafar ya fara magana Uwani take kallonsa sheƙeƙe tun daga sama har zuwa yatsu biyar na ƙafarsa. Ba ta yi aune ba ta ji ya zuba mata rankwashin da ya sa ta gagara gane muhallin da take tsaye. Cikin sauri ta fisge hular kanta, ta zame dogon wandon uniform ɗinsa da ke jikinta.

Jafar na nan tsaye ya ji tuuush! Lawan ya jefo sabuwar kwalbar turarensa, a firgice yake miƙa wuya yana cara haɗe da ci gaba da taka kayan da ke saman mudubin. A zuciye Jafara ya jefa masa takalmin kanbas ɗinsa. Firgitar da Lawan ya yi har cikin ran Uwani don haka cikin ɓacin rai ta ce, "Allah dai ba ya zalinci yana kallon baƙaƙen azzuluman duniya masu baƙaƙen kaya." A fusace Jafar ya yo kanta rai a ɓace, ganin haka ya sa Uwani ta zuba a guje kai tsaye ta wuce sashen Dada Jafar ya rufa mata baya. A daidai lokacin da Jafar ya nufi sashen Dada shi kuma malam na Madina ya kawo kai, cikin rashin sani Jafar ya bangaje shi kaɗan ya rage gemunsa ya taɓa ƙasa.

"Jafaru! Kai Jafaru kana ji ka angije ni kamar ka angije dabba? Wallahi duk laifin Kulu ne ni take nunawa 'ya'ya da jikoki sun fi ɗan uwa." Ya ci gaba da tafiya har bakin ƙofar Dada yana kiran sunanta.
"Kulu! Kulu kina ina ne..." Cikin sauri Malam na Madina ya datse ragowar kalaman bakinsa jin furucin da Jafar ke faɗa.

  "Wallahi tun wuri ki wuce mu je ɗakina don har kan katifa..." Uwani ta yi farat ta katse shi.
"Amma dai ai ka bari na saka kayana yaya Jafaru, wallahi na fita a haka ka san dai mutanen gidan nan kowa sai ya san abin da yake faruwa." Jafar ya yi ƙwafa yana shirin ba ta amsa daga can waje ya ji muryar Malam na Madina yana sallallami.

"Yanzu Jafaru dama munafurcin da kuke aikatawa kenan? Shi ya sa saboda sauri har ka angije ni ko waige na ba ka yi ba. Ba da ni ba, wallahi ba zan zauna ana aikata alfasha ina kallo ba, lokaci ɗaya Ubangiji ya halakar da mu." Sai da Jafar ya fito daga ɗakin Dada ya samu Malam na Madina da ke bin shi da ƙazantaccan kallo.

Ficewa ya yi daga sashen Dada ya faɗa ɗakinsa, akwatin kayansa ya janyo ƙiiiiii yana kokawar fito da ita Dada ta sako kai ciki. Jin motsin ya yi yawa ya sa ta fara mita.

"Waɗannan dabbobi na Uwani yadda kasan tare aka shayar da su saboda duk hatsabibancinsu iri ɗaya ne..." Ganin Malam na Madina ya janyo akwatinsa ƙiiii ya sa Dada sakin baki, "Wai Muda ne a wurin nan ko Usumanu?" Ta wurga masa tambaya tana ɗan ƙanƙance ido. Sai da Malam na Madina ya fito sannan ya ce.

"Ki yafe ni Kulu don kar na tafi da haƙƙin wani a kaina."

Baki sake Dada ta ce, "Yaya wani abin aka yi maka ne?" Malam na Madina ya share ƙwallar idonsa, ta waiga wurin da Jafar yake tsaye a bakin ƙofa ya jefa masa mugun kallo sannan ya furta.

"Ubangiji aka yi wa laifi, ni dai tsakanina da mutanen gidan idan na ce an yi mini wani abu na ɗauki haƙƙinsu. Amma ni kam ba zan zauna ina ji ina gani a dinga saɓon Allah ba, gara na mutu salin-alin da a tashi idanuwa su bada shaidar baɗala ranar Lahira." Malam na Madina na gama magana ya fara jan akwatinsa ƙiiiii, da sauri Dada ta sha gabansa don tuni hankalinta ya tashi idonta ya fara ciko da ƙwalla. A duniya idan akwai abin ta tsana shi ne a ɓata ran Malam na Madina.

Jafar ya kafe Malam da kallo yana jin kamar ya ƙarasa ya shaƙe shi ko ya rufe shi da duka.
"A duniyar nan dai Yaya ka san mu biyu kaɗai muka rage, kuma kai ne uwata kai ne ubana kai nake gani na huce rashin su marigayi, (Iyayensu) don Allah ka faɗa mini abin da yake faruwa."Dada ta yi maganar tana share ƙwalla.

"Waye wancan a tsaye?" Na Madina ya nuna Jafar a daidai lokacin Uwani ta leƙo don jin abin da yake faruwa daga ita sai gajeren wandon jikinta, ta tuɓe riga ta rufa hijabinta a saman ƙirjinta. Dada ta kai kallonta wurin ta ce, "Jafaru ne sai Uwani da ta fito."

"Amma a rigar kwasam na san ba za ki manta Iron Alto ba?" A firgice Dada ta kalle shi, ba ita ba hatta Jafar ya san labarin Iron Alto a bakin Dada. Dada na shirin magana Malam na Madina ya katse ta.

"To Ta'adar Iron Alto na ji waɗannan yaran suna aikatawa..." Tun bai rufe baki ba Dada ta saki butar hannunta wacce ta ɗauro alwala da ita jiki na rawa.

Yau dai bari mu tsagaita dariyar na ga jiya har da masu shiɗewa 😂


07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
[10/06/2024, 10:59] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.


SHAFI NA SHIDA


Dada ta zuba musu ido ganin yanayin da Uwani take ciki ya sa ta aminta da kalaman ɗan'uwanta, ta san dai ba zai taɓa yi musu ƙarya ba. Runtse idonsa Jafar ya yi yana fesar da iska mai zafi, ya buɗe idanunsa da suka rine jawur kamar gauta ya sauke su a kan malam Na Madina. A fusace ya ƙarasa gabansa ya cukwikwiyo babbar rigarsa ya riƙe shi wuri ɗaya rai a ɓace ya furta.

"Wallahi ba don ina duba tsufanka ba, da yau sai na bambamce maka tsakanin zuma da maɗaci." Jafar ya sake shi sannan ya wuce ɗakinsa, saboda tsoro tuni malam Na Madina ya yi mutuwar tsaye. Dada ta bi bayan Jafar da kallon tsoro baki a sake.

"Yaya an ya Jafaruna ne ba aljanu ne a kansa ba..." Kuka ya katse maganar da Dada take yi.

"Sharrin ƙwaya ce Kulu, na sha faɗa miki wannan aikin ɗamarar ba zai haifar da samun ɗa mai ido a cikin zuri'armu ba. Yanzu wa gari ya waya? A ce Jafaru bai san Kano garin Musulunci ba ne? Ya ɗauka rayuwar da yake yi a Legas ita zai yi a gidan nan. Kin ga dai abin da ya faru a gabanki. Da fa dukana zai yi, kaico rashin haihuwa ne ya ja mini haka." Na Madina ya fashe da kuka, Uwani da ke gefe ko a jikinta ta shige ɗaki ta ci gaba da sauya kaya. Don ita hakan da ya faru ma daɗi ta ji, ko ba komai ta san Jafar da zuciya ba lallai ya sake shiga sashen Dada ba sai bayan kwana biyu, ballantana ya hora ta a kan laifin da ta yi masa.

Tana gama sauya kaya ta fice a nan harabar gidan ta ga Lawan da matarsa Fanteka, 'ya'yan ta ɗibo ta yi hanyar keji da su uwar ta rufa musu baya. Sai da ta dawo ta ga Lawan yana tsince-tsince a wurin akuyoyinta.

"Kai dai Lawan ka cika ɗan kishiya riƙon mai haƙuri, wallahi da kiwon ka aka ba ni da ka ja mini zagi a ce na bar ka da yunwa." Uwani ta yi maganar tana ƙoƙarin kama shi, Lawan ya yi tsalle zai dira a kan katangar gidan Baba Isuhu da ƙyar ta kama shi tana sakin murmushi.

Kai tsaye sashen Dada ta wuce tana shiga ta ci karo da Jafar ya fito ɗauke da jaka a kafaɗa.

  "Marar gaskiya ko a ruwa gumi yake. Yaya ka ga yaron nan saboda ya san tsiyar da ya shuka fita zai yi ya bar mu, ni dai wallahi Sa'idu ya cuce ni duk wannan abin da yake faruwa Sa'idu ne sila." Jafar bai bi ta kan su Dada ba ya fice daga gidan har yana hankaɗe Uwani.
"Kulu Allah Ya ba mu alheri, wallahi Jafaru ba zai yi mana turun jeka ka mutu ba. Ya shuka bishiyar tsiya mu da ba mu ji ba, ba mu gani ba mu girbe masa." Malam na Madina ya sake jan jaka ganin haka ya sa Dada ta ce.

"Ka jira ni yanzu zan kira Inusa dole ya tara mini 'yan'uwansa a gidan." Dada ta yi maganar tana faɗawa ɗaki domin ɗauko wayarta.

"Inusa a yanzu ba sai gobe ba ka tara mini 'yan'uwanka, wallahi idan ba haka ba zan bar muku gidanku na shiga duniya. Kuma ku yi gaggawar kiran Jafaru ku ce ya dawo don zaman nasu ne, shi da Uwani ne suka ƙulla tsiyar da bakina ba zai iya furtawa ba." Daga haka Dada ba ta sake cewa uffan ba ta kashe wayarta, da kashe wayar babu jimawa Baba Yunusa ya sake kiranta, Dada na ɗauka ta ce.

"Yunusa wai wa muke yi wa Sallah da azumi?" Daga can ɓangaren Baba Yunusa ya ce.

"Allah."

Dada ta sake haɗe fuska kamar yana ganinta ta ce. "Da ma saboda na fita haƙƙinka a matsayinka na babba shi ya sa na kira na sanar da kai, wallahi idan ba ka haɗo mini kan 'yan uwanka ba sai dai ku nemi wata uwar ba ni ba." Dada za ta katse da sauri Baba Yunusa ya ce. "Shi kenan Dada ga mu nan zuwa yanzu In shaa Allah." Ta amsa masa sannan ta katse wayar, sai da ta lallami Na Madina sannan ya mayar sa akwatinsa.

Falon tsit ya yi da ka kalli fuskokinsu ka san kowanne yana cikin damuwa, Baba Yunusa ne ya yi  ƙarfin halin cewa.
"Dada gaba ɗaya ga mu mun hallara." Jafar tun da ya sunkuyar da kai ƙasa zuciyarsa ke tururi, Uwani na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login