Showing 78001 words to 81000 words out of 94348 words

Chapter 27 - GIDAN LIKITOCI BOOK COMPLETE BY AMEERA ADAM.txt

29 Sep 2025

852

sashensu ta ɓarke wa Mami da wani irin kuka.

"Yaya Shukra lafiya? Me ya same ki a goshi? Mene ne wannan yake wari a jikinki kamar kwata? Ina shi Yaya Salim ɗin?" Auta ta jero mata tambayoyi, sai dai babu ɗaya da ta iya amsawa ban da hawaye da ke shatata a fuskarta. Mami da Auta suka taimaka mata ta gyara jikinta sannan ta faɗa musu abin da ya faru, suka shiga zagin Ba ka da nauyi suna mamakin in da Salim ya je bayan motarsa na ƙofar gida.

Jin ihun Dada ya sa su Atika shiga sashenta da sauri, ganinta a daskare daga ita sai ɗan tofi ya ba su mamaki domin Dada ba ta taɓa sauya kaya a gaban mutane.
"Dada lafiya?"
Hannu na rawa ta nuna uwar ɗakin.

"Wani tabbataccan kwarto ne ya fisge mini zani ya yi uwar ɗaki. Ni Kulu ban san uwar me zai laluma a jikin tsohuwa ba." Da sauri su Atika suka leƙa ɗakin, ba su iya hango komai ba sai 'yan idanun Salim da ke duƙe a ƙarƙashin gado. Fa'iza ce ta kira Baba Isuhu, da sauri ya ƙarasa hannunsa ɗauke da ƙatuwar gora ya fisgo Salim.
Sai dai sororo ya yi yana bin yadda halitar fuskar Salim ta sauya.

"Wa nake gani kamar Salim? Kai uban me ya kai zanin Dada hannunka?"

Salim da gefen baki zuwa fuskarsa ya kumbure sundundun ya ce, "Baba wani mahaukaci ne zai sauke mini fuska don Allah ku ɓoye ni. Ya ɗauke Shukra a ka ma ya tafi da ita." Sai a lokacin suka fahimci wurin da maganar Salim ta dosa, Baba Isuhu ya miƙa wa Dada zaninta. Ya kama hannun Salim suka fice Salim sai tirjewa yake, a zuciye baba Isuhu ya waigo ya furta.

"Me kake yi haka ne wai? Ka san Allah ka ci sa'a na gane kayan jikinka don mun gaisa ɗazu kana ƙofar gida, wallahi da don ta wannan sukunbiyar fuskar taka ne ba zan gane ka ba. Dubu fa yadda ka koma fuska kamar ta sumammiyar akuya. Mu je na raka ka ƙofar gida ka tafi don indai Ba ka da nauyi ne fiye da haka ma zai yi maka." Sai a lokacin Salim ya saki jiki suka ƙarasa, da sauri ya shige mota ya fusge ta da gudun gaske ko waige ba ya yi.

Su Dada suna tsaye suna mayar da yanda aka yi wayar Dada ta fara ringing, da sallama ta ɗauka jin muryar Maryama mahaifiyar Uwani ya sa ta furta.
"Ke kuwa Maryama da ƙuruciyarki amma waya ta nemi ba ki wuya, tun daren jiya nake kiranki na sanar da ke abin alheri amma waya a kashe." Maryama cikin shasshekar kuka ta ce. "Dada hankalina ne ba a kwance ba."

"To Allah ya rufa asiri ai ni dama tun da na ga yanayinki na san Aramma na zalintarki, ki ci gaba da haƙuri Maryama komai ya yi don kansa." Maryama ta saki kukan da ke cinta, Dada na son Maryama shi ya sa duk lokacin da suka yi waya take tausarta.
"Kin ga ki yi shiru 'yar nan su maza fa haka suke, ni tsorona ma kada Aramma ya zo ya ji kina mini kuka ya ce ko Umaru kika tuno. Yanzu dai ba wannan ba jiya da dare dai an cika alƙawarin da aka ɗauka, Uwani dai an ɗaura aure ita da Jafar. Abin ne ya zo a gaggauce, amma dai tariya sai nan da watan maulidi." Maryama ta ji daɗi don ta san waye Baba Mamman, amma har a ranta ta so a ce Uwani ta yi hankali kafin ɗaurin auren. Sai da ta kwararo addu'a sannan ta sanar da Dada dalilin kiranta.

"Dada dama kiranki na yi na faɗa miki Me sunan Iya ce ta rasu (Babbar 'yarta ta gidan Aramma.)" Salati Dada ta rafka sannan ta yi mata gaisuwa ta kuma yi mata alƙawarin washegari za su shiryo su zo mata gaisuwa. Bayan sun gama waya Dada ta miƙa wa Uwani waya, suka gaisa sannan ta yi masa sallama.

Kimanin ƙarfe goma na safe su Dada suka isa ƙauyen da mahaifiyar Uwani take aure, sun yi kara sosai don har su Baba Yunusa gabaɗaya suka je mata da matansu. Tun da suka faka motoci yara ke zuwa kallonsu, mazan suka zauna a tabarmar da ke ƙofar gida suka tambayi mijin Maryama aka ce musu ya shiga cikin gida. Su Dada kuma suka shiga ciki.

"Gata nan da ran Allah ita ta san inda ta kai mini yarinya aka cinye ta, amma idan ta zauna ta ishi mutane da kukan munafurci. Daga zuwanta garinsu ta dawo da yarinya ba lafiya, wai muna zuwa aibitin gangare da suka tura mu babban asibiti a binni aka ce sikila ce, yo ban da ƙaryar likitoci lokacin iyaye da kakanni aka san wata sikili? Ta kai mini yarinyar dai mayu sun cinye kawai." Shigar su Dada gidan suka samu Aramma na zazzaga wa Maryama masifa yana kumfar baki, tana durƙushe a gefen yayan Aramma da ya zo yi mata gaisuwa. A lokacin Aramma ya zo wucewa ya shi ne yake yi mata sababi. Ganin su Dada da yanayin shigarsu ya sa ya hau yashe baki. "Barkanku da zuwa Hajiya."

"Barka dai." Dada ta amsa a daƙile. Jin muryar Dada ya sa Maryama ta miƙe tana goge hawaye ta shiga yi musu sannu da zuwa.

"Ai kuwa wannan mutumin sai na gyara maka zama." Uwani ta faɗa a ranta.

Maryama jiki a sanyaye ta miƙe za ta wuce da su ɗaki.
"Ke Maryama wanne irin rashin hankali ne haka kina ganin baƙi ba za ki kai su ɗaki ba." Aramma ya faɗa cikin faɗa shi a dole sai ya birge su Dada. Ɗaki ta kai su bayan sun gaisa suka yi mata gaisuwa cikin jimami, Dada har cikin ranta ba ta ji daɗin irin zaman da Maryama take yi da Aramma ba, domin mace ce mai sanyin hali da haƙuri. Duk wanda ya santa idan ya san Uwani dole zai ce albasa ba ta yi halin ruwa ba. Aramma jikinsa har rawa yake ya sa aka sayo musu ruwa, ba su jima sosai ba Dada ta kawo kuɗin sadaka dubu biyar ta bata. Sauran sirikan Dada kuma mai ɗari biyar mai dubu ɗaya duk suka haɗa mata, lokacin da za su tafi ne Dada ke ce wa Maryama Uwani za ta zauna har sai an yi sadakar uku za ta tafi. Har ƙofar gida Maryama ta raka su, su Baba Idris suka yi mata gaisuwa, suma suka kawo abin sadaka suka ba ta da shi ma Aramma. Har sun ɗauki hanya za su tafi Dada ta dawo ta ja Maryama gefe tana yi mata raɗa.

"Dama kuɗin da aka ba ki ko da wasa kada ki ba wa wannan mijin naki kin ji Maryam!" Maryama ta gyaɗa kai jiki a sanyaye sannan ta raka Dada bakin mota tana ɗaga musu hannu.

"Dada gaskiya zan yi kewarki kwana biyu an ya ba biyo ku zan yi ba?" Uwani ta faɗa tana tura ba ki gaba.
Dada ta watsa mata harara sannan suka wuce.

Tun da suka koma cikin gida Uwani ta lura da mahaifiyarta sam ba ta da nutsuwa, suna nan zaune sai ga Aramma ya shigo.
"Ke Maryama kawo abin sadakar nan da aka ba ki zan haɗa a yi abincin rana." Tamkar kazar da ƙwai ya fashe wa a ciki haka Maryama ta miƙe jiki ba ƙwari ta kunto kuɗin wurin su Baba Idris ta miƙa masa. "Ke ba na son shashanci da rainin hankali, kina nufin su matan ba su ba ki komai ba? Wai Maryama me ya sa kin fiye baƙin halin tsiya ne." Ran Maryama ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ganin irin tozarcin da Aramma yake yi mata a gaban Uwani da kuma sauran mutanen da suka zo gaisuwa. Don haka rai a ɓace ta ce.

"Wai Aramma ya kake so na yi ne? Me ya sa..." Tun ba ta gama magana ba Aramma ya ɗauke ta da mari, yana shirin kai mata duka Uwani ta shiga tsakaninsu ta furta.
"Baba bari na miƙo maka kuɗin a cikin jakar can ta ajiye dama na ji ta ce za a auno garin masara a yi tuwo, amma bari na miƙo maka." Jin haka ya sa Aramma ya washe baki ya ce. "Ka ji yarinya mai hankali maza miƙo mini, ke dai kin yi asarar hali Maryama."

Babu musu Uwani ta zuge jakar da ta ga mahaifiyarta ta zuba kuɗin a ciki, ta ɗebo su duka ta miƙa masa.

"Kai Allah wadaran naka ya lalace wallahi Maryama kin ji kunya ace wai har 'yar cikinki ta fi ki hankali." Wasu daga cikin ƙannen Aramma suka bi mahaifiyar Uwani da baƙaƙen maganganu. Ba ta tanka musu ba sai ma ruwan hawaye da ke tsiyaya daga fuskarta. Uwani na daga gefe ta ci gaba da kallonsu ɗaya bayan ɗaya, kowanne tana zana gashin azabar da za ta yi musu daga baya.

Sai da mutane suka ragu a ɗakin sosai daga Maryama sai 'yan uwanta ta dubi Uwani ta ce. "Me ya sa za ki ɗebi kudina ki ba shi." Ta ƙarasa maganar fuska a haɗe.

"Gobe da safe zai dawo miki da su Inna rance na ba shi!" Uwani ta furta cikin rashin damuwa.
"Rance fa? Ta ya ya zama rance bayan a kan idona kika ba shi?"
"Allah Inna kada ki damu zai dawo miki da kuɗinki har ma ya ƙara miki wasu." Jin sokiburutsun Uwani ya sa Maryama ba ta sake bi ta kanta ba saboda takaici.

"Maryama yaya aka yi kika bari har ya ga lokacin da aka ba ki kuɗin nan? Kin fa san halin mutumin nan sarai, ba shi da tausayi ko kaɗan." Indo kishiyar Maryama ta furta ƙasa-ƙasa.
"Ai kin san tun da ya gan su ya san za su ba ni wani abu, kuma ragowar ma ba ni na ba shi ba yarinyar nan ce ta ba shi." Maryama ta furta. Suka gama jajantawa juna, don zaman da suke yi sam babu kishi a ciki saboda dukkansu ba wani daɗin zama da shi suke ji ba.

Wuni ɗaya da Uwani ta yi a gidan ta fahimci irin zaman ƙuncin da mahaifiyarta da kishiyarta suke yi a cikin gidan, a kan idonta ta ga Aramma ya yo cefane har da nama ya ce a yi masa jar miya da shi. A yadda ta lura hatta abinci ma daban ake yi masa, su kuma duk kwamacalar da ya ga dama sai su dafa. Don abincin dare sai da ƙyar Uwani ta iya cin miyar kukar da aka kaɗa, saboda haka ta ci alwashin gyara masa zama kafin ta bar gidan.

Tun da doshin magriba Uwani ta hangi wani ludayin silba a kwandon wanke-wanken mahaifiyarta, a fakaice ta ɗauke shi ta ɓoye sai da dare ya tsala kowa ya yi bacci sannan ta saci jiki a hankali. Har za ta fita ta hangi wani zumbulelen farin hijabin Inna Suwaiba, wani tunani ne ya faɗo mata da sauri ta saki murmushi. Ta figi hijabin a hankali ɗayan hannunta ɗauke da ludayin sulba, can hanyar soro ta nufa da yake a baki-bakin ƙofa turakar Aramma take, daga ɗakinsa kuma sai ɗakin da suke ajiye kayan abinci. Toka ta ɗiba ta bursune fuskarta da ita sannan ta saka zumbulelen farin hijabin, ta leƙa ɗakin ta hango Aramma a kwance ya sharɓe sai sakin munshari yake yi daga shi sai gajeren wando. Da yake irin mutanen nan gajeru masu ƙiba ga uban tumbi. Tana shiga ɗakin ta tsaya a kansa, sai da ta gimtse dariyarta sannan ta daidaici gefen goshinsa ta ba shi raaaal da ludayin hannunta. A firgice Aramma ya miƙe yana dafe da goshi, "Wane ɗan iskan ne a tsohon daren."

"Tawagar fatalwar 'yan iskan lahira ne!" Uwani ta faɗa da wata irin murya, ta sa hannu ta cikin hijabin ta buɗa shi, sai ta ƙara faɗi ta cikinsa. A razane Aramma ya ja da baya ganin hallitar da ke tunkaro shi.

"Mu sababbin ƙawayen 'yarka da ta baƙunci lahira ne. A cikin fatale ma mu tawagar shaiɗanu ne domin fatattaka ɗan adam muke yi da kulkin lahira. Ita da bakinta ta gaya mana irin zalincin da kake yi wa iyalinka, don haka muka zo domin mu tsintsinka hanjin cikinka, ko kuma mu gayyato 'yan uwanmu mu yi daga-daga da kai." Uwani ta yi magana tana wani miƙa wuya gaba.

Jin kalaman Uwani ya sa Aramma ya fashe da wani irin kuka mai cin zuciya, cikin tashin hankali ya ce.
"Ku dubi Allah ku yi haƙuri wallahi zan daina duk abin da nake yi..." Da sauri Uwani ta katse shi.

"Zo nan maza-maza, matso nan."

"Don Allah ku yi mini rai." Aramma ya faɗa fuska haɗe da hawaye da majina.

"Za fa ka taka ɗan tsiti a bayanka, wallahi tawagarsa ta fi ta mu bala'i ka matso na ce maka." Da sauri Aramma ya matsa tiɓi-tiɓi sai haɗa gumi yake. Yana zuwa ya tsugunna a ƙasa, hannun Uwani mai ɗauke da ludayin da ke cikin hijabi ta ɗaga da sauri ta sake ba shi raaal a ƙeyarsa. A zabure Aramma ya miƙe sai da ya yi tsalle uku ya faɗi a can gefe cikin azaba.

"Fatalwar 'yarka ta gaya mana duk abin da matanka suke samu karɓe musu kake yi, a jiya ma ka karɓe wa uwar marigayya kuɗaɗenta to ko ka mayar mata da abin ta ko kuma mu mayar da kai kuɗi. Domin muna cikin irin fatalwar da ke yi wa 'yan ƙungiyar asiri aiki, za ka zama kuɗi wayyo kuɗi, kuɗi masu daɗi." Uwani ta yi maganar tana wani tsalle tana ɗaga hannu ta cikin hijabi kamar mai shirin tashi sama.

"Na rantse da Allah ko wasu aka ce na ƙara mata yanzu zan ƙara mata su." Uwani ba ta bi ta kansa ba ta ce.

"Da ma ga hantarka da zuciyarka nan muna gani manya ne, ko su kaɗai muka tsaface za ta kawo mana miliyoyi." Da sauri Aramma ya dafe cikinsa da hannuwansa biyu, ya sake ɓarkewa da kuka.

"Idan ka sake ka tona mana asiri wallahi a yanzu za mu hallaka ka." Jin haka ya sa Aramma ya haɗiye kukansa, ya sa hannu biyu ya toshe bakinsa. Uwani ta sake jingina da bango ta furta. "Ganin yadda muka ga ka yi nadama za mu ɗaga maka ƙafa na kwana biyu mu ga idan za ka sauya halinka, kuma ka gaggauta mayarwa da mahaifiyar 'yar uwarmu kuɗinta. Sannan ita da kishiyarta dole ne ka ƙara musu dubu hamsin-hamsin. Kuma ya zama wajibi duk sati ka dinga ba su dubu uku-uku na kashewa."

"Duka na ji kuma na yi alƙawari zan yi yadda kuka ce, na gode muku Allah Ya biya ku." Aramma ya yi maganar yana rissinawa.
"Ba ma buƙatar godiya, yanzu dai za mu tafi da kai ka je ka ga makwancin 'yarka, sai mu baro ka a can bayan sadakar uku sai mu dawo..."
Tun Uwani ba ta gama magana ba ya katse ta cikin kuka.

"Wallahi na haƙura da ganin ta, Allah ba sai na ga halin da take ciki ba. Na san mai sunan Iya tana da halin na gari."

"To kuwa ya zama wajibi ka zaɓi ɗaya, ko mu ɗauke ka ta ƙarfin tsiya mu tafi da kai. Ko kuma ka zo ka ku yi sallama da shugabar tawagar 'yan iskan fatale." Jin haka ya sa jiki na rawa ya matsa gaban Uwani ya ce.

"Zan gaisa da ita..." Maganar bakinsa ta katse sakamakon jin saukar ludayin da ya yi a gaban kansa. Wannan karon kasa motsi ya yi ganin haka ya sa Uwani ta sake sauke masa na biyu aka sannan ta ɗora da cewa.

"Yanzu haka za mu fita mu ba ka wuri, sauran tawagarmu na tsakar gidan nan. Kuma duk abin da ka ji ko kuma duk hukuncin da ka ji muna aikatawa matuƙar ka leƙo to zai dawo kanka. Sannan saura idan gari ya waye ka ce ga abin da ya faru da kai." Daga haka Uwani ta fice tana wani shagiɗewa gefe tana tura wuya gaba.

Kusan duk abin da ya faru tsakanin Uwani da Aramma, Yaya ƙarama da su Rahane 'yan uwan Aramma sun ji, sakamakon ɗakin da suke kwance a jikin na Aramma yake. Da yake dama idan wani abin taro ya kama a gidan to duka danginsa a wannan ɗakin suke sauka. Kowannensu na daga kwance cikinsa ya ɗuri ruwa ko motsin kirki babu mai yi, babban abin da ya ɗaga hankalinsu yadda suka dinga jiyo kukan Aramma ƙasa-ƙasa, da ita kanta saƙon fatalwar da take faɗa. Suna nan kwance suka ji motsin Uwani a ƙofar ɗakinsu tana ɗan wani gurnani, take fitsari ya jiƙe zanin Yaya ƙarama. Uwani na ɗaga labulen ɗakin ta hango yadda aka jere yara a ƙasa, ɗaya bayan ɗaya haka ta dinga jidar yaran tana kai wa tsakar gida. Yaya ƙarama na daga kwance ta ji Uwani ta dafa ƙafarta, jiki na rawa ta ce.

"La'ilaha'illahu Muhammadur Rasulillah."

"Ba za ki mutu yanzu ba sai mu fafe ƙwayar idonki." Uwani ta faɗa da wata irin murya, har ta juya za ta fita ta ce. "Su kuma waɗancan yaran zan ba wa ƙananan fatalenmu umarni su gama da su." Uwani na ƙarasa magana ta wuce wurin yaran da ke kwance a tsakar gida, idan ta ɗauko yaro ɗaya sai ta gasa masa mintsini ta tura shi cikin ɗaki. Ganin yadda yaran ke shigowa a firgice cikin kuka ga magagin bacci ga kuma zafin mintsini, ya sa su Yaya ƙarama suka banka uwar ɗaki a guje. Uwani ta yi wata irin sufa ta rufa musu baya tana faɗin. "Ya Ahalul fataleeee ku zo ga nama mun samu."


07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
[13/06/2024, 13:37] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*

©AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login