Showing 93001 words to 94348 words out of 94348 words
Chapter 32 - GIDAN LIKITOCI BOOK COMPLETE BY AMEERA ADAM.txt
su a cikin jakarta kai tsaye ta nufi sashen Uwani ita da ƙawarta Fatima. Kuma ko Fatima ba ta san da plan ɗin su Mami ba. Tun da Uwani ta tare sau ɗaya Shukra ta taɓa shiga sai a wannan ranar ta yi na biyu.
Shiru ta ji falon babu kowa, sallama ta rangaɗa daga cikin ɗaki ta ji Uwani ta amsa. Ita ma Uwani dawowarta kenan daga sashen Mami don tun da Dada ta zo kusan wuni guda a cen take yi, idan ta dawo ɓangarenta sai dai ko wani uzurin ne ya dawo da ita. Uwani na fitowa Shukra ta ɗan saki fuska tana murmushi ta ce, "Ki je Mami tana kiranki. Sannan kuma ƙawata Fatima za ta yi Sallar Walha, sashenmu hayaniya ta yi yawa shi ya sa na ce ta zo nan." Uwani sakato ta yi tana mamakin yau rana ɗaya da har Shukra ta sakar mata fuska, a sanyaye ta amsa mata sannan ta wuce kiran da aka ce Mami tana yi mata. Uwani na fita Shukra ta faɗa ɗakin Uwani bayan da Fatima ta fita yin alwala, ta janyo drowar madubin ta saka kuɗin a ciki ta mayar ta rufe. Ba su wani jima sosai ba suka fice daga ɗakin bayan Fatima ta idar da Sallah, a ɓangaren Shukra dama kuma buƙatar maje Hajji Sallah tun da buƙatarta ta biya ba ta ga amfanin zaman nasu ba.
Uwani na zuwa ta samu Mami a falo ta tsugunna har ƙasa, a lokacin Mami zaune take da matan Baba Mustafa sai ƙawarta Hajiya Falmata.
"Uwani ku je ke da Auta ki taimaka mata ku ciro mini wayata ta faɗa bayan gado." Babu musu Uwani ta yi wa Auta magana suka shiga ɗakin Mami, sun sha wahala sosai kafin su samu damar ɗauko wayar tun da can ƙarshen gado ta faɗa. Abu ɗaya ne ya tsaye wa Uwani a rai, a iya sanin ta tun ranar da ta zo gidan Mami ba ta taɓa saka ta aiki tare da Auta ba. Amma sai ta sa a ranta ko don ganin mutane ne ya sa Mami ta yi hakan, don kar a ce har yanzu ba ta ƙaunarta.
Wurin sallar Azahar bayan Mami ta yi sallah ta fito falo ta fasa kukan an sace mata maƙudan kuɗin da Daddy ya ba ta ajiya har kimanin raina miliyan biyu da rabi, nan da nan hankulan mazauna gidan ya tashi. Dada na jin haka ta fara sababi rai a ɓace.
"A gaskiya ni kam idan aka kwashe kuɗin nan an cuci Mamman, saboda Allah a tara mutane domin harkar arziƙi su ɓige da harkar tsiya? Shi dai ɓarawo bai ji daɗin halinsa ba, ba don sai Hajji zan je Saudiyya ba da babu abin da zai hana na kai ƙarar ɓarawon nan wurin Ubangiji a ɗakin Allah ba."
Haka dai kowa da abin da ya dinga faɗa, daga ƙarshe aka ce su waye suka shiga ɗakin Mami a ranar su za a bincika, nan take aka bada shedar Uwani ce da Auta suka ɗauko waya. Kiransu aka yi aka tambaye su kowacce ta ce ba ta ga kuɗi ba, Mami ta bada shawarar a duba ɗakunan kowaccensu, haka aka kasu gida biyu wasu suka yi ɗakin Auta wasu suka wuce ɗakin Uwani. Falonta aka fara dubawa har da ƙasan kujeru, sannan suka wuce ɗakinta, masu duba drower saka kaya na yi, wasu kuma har da leƙa ƙarƙashin gado suke. Kwatsam ana duba drower madubi sai ga kuɗi, nan take mutane suka ɗauki salati. Aka wuce wurin Mami da kuɗi, saboda tashin hankali Uwani jikinta har karkarwa yake yi.
Duk yadda Uwani ta so fitar da kanta abin sai ya gagara, ta yi kuka ta yi rantse-rantse babu wanda ya yarda da ita. Hatta Dada a wannan karon ba ta yarda da ita ba, Uwani ta rarrafa gaban Dada tana kuka cikin takaici Dada ta wanke ta da mari sannan ta hankaɗa ta gefe. Daddy ne kaɗai da ya zo ya lallashi ta, a ransa yana wasu-wasin wannan abin da ya faru.
Lokacin da Jafar ya dawo ya ji labari ransa ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, nan take kuma Mami ta birkice a kan sai Jafar ya saki Uwani a cewarta ba za ta zauna a ɓata mata tarbiyyar yara ba. Shi kuma Daddy ya sake jaddada wa Jafar umarninsa na ko bayan ransa bai amince ya rabu da Uwani ba.
Abin duniya goma da ashirin ne ya haɗe wa Uwani don haka ta koma sashenta, ta faɗa kan gado ban da rusar kuka babu abin da take yi. Lokacin da Jafar ya shiga ya same ta kallon tsana ya wurga mata sannan ya ce.
"Wallahi ni dai an gama cutata, a ce wai matata ta rasa wa za ta yi wa sata sai mahaifina, me aka rage ki da shi ci ko sha? Ƙanƙanuwar yarinya da ke ko a ina kika san kuɗi da har za ki sa hannu ki kwashe miliyan biyu da rabi. Ni kam na yi dana-sanin aurenki, ni dai aurenki wallahi bai amfane ni da komai ba sai tsiya. Ya zame mini dole na yi gaggauwar auren Safna, don ba zan zauna ɓacin rai da takaicinki ya kashe ni ba. Shashasha ɓarauniyar banza da wofi." Jafar ya yi tsaki ya fice daga ɗakin.
Uwani ta ci kuka kamar babu gobe, tana nan ɗaki Auta ta je ta same ta.
"Uwani Allah Ya sani har yanzu ba na jin ke kika ɗauki kuɗin nan, tare fa muka yi komai muka gama." Rai a ɓace Uwani ta ce. "Auta fice mini a ɗaki kada na sauke fushina a kanki."
"Don Allah ki saurare ni kada ki yi mana jama'u..." Cikin tsawa Uwani ta katse ta.
"Ki fice mini a ɗaki na ce."
Auta ta tsorata sosai da yadda ta ga Uwani ta birkice lokaci ɗaya, bayan fitar Auta Uwani ta fara nazarin shigowar Shukra da kiran da Mami ta yi mata. Murmushi ta saki ta share hawayenta a fili ta furta.
"Wallahi wannan ƙwallar da na zubar ba za ta tafi a banza ba. Ni Uwani za ku laƙa wa sharri, ai ko kura ta rame ta fi ƙarfin gawurtattun karnuka." Daga haka Uwani ta shiga banɗaki ta wanke fuskarta, ta koma can sashen su Mami. Yadda mutane ke bin ta da kallo ita ma Uwani sai ta murje idonta ta fara bin su da kallo, hatta Dada fushi take yi da ita don haka ita ma ta yi kamar ba ta san da Dada a wurin ba. Duk in da Uwani ta gifta sai dai ka ji ƙus-ƙus na tashi.
Auta ta nema ta ba ta haƙurin abin da ta yi mata, ita ma dama Auta ba ta ga laifin Uwanin ba don idan ita ce ma za ta yi fiye da haka. A cikin dabara Uwani ta tambayi Auta Event ɗin da za a yi kamu, Auta ta nuna mata ai sai su tafi tare tun da ba ta san wurin ba.
Yamma liƙi jama'ar gidan ana ta hada-hadar tafiya wurin kamu, Uwani ma atamfarta ta saka da mayafi sai dai tun rana Auta ta hana ta yin wannan ɗige-ɗigen kwalliyar. Ita ta biya musu kuɗin make up aka yi muku kwalliya sai ga Uwani ta fito shar kamar ba ita, lokacin da Uwani ta saka ƙafa a cikin hall ɗin ne ta saki murmushin ƙeta da mugunta. Ta zura hannu cikin aljihun doguwar rigarta ta ji fakitin sabuwar rezar da ta saya tana ciki a fili ta furta.
"Uwani ce fa 'yar ƙashin gwiwa, ai yanzu za mu fara wasan da ku tun da haka kuka zaɓa."
AlhamduLillah a nan free pages na wannan labarin ya ƙare🫠 idan kina buƙatar ci gaba za ki turo 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 First bank sai shaidar biya ta wannan lamber 07062062624
Sai mun haɗe a shafin gobe idan Allah Ya kai mu domin mu ji tsiyar da Uwani za ta shuka, Fakitin Reza a cikin Hall ɗin kamu na san akwai ƙura.😂
#Ummou Aslam Bint Adam🌚