Showing 42001 words to 45000 words out of 94348 words
Chapter 15 - GIDAN LIKITOCI BOOK COMPLETE BY AMEERA ADAM.txt
lokacin da ta ɗaga labulen ɗakin a ƙasa ta gansu sun ɓingire suna bacci, 'Yar gwal tana jingine da bango da kofin kunnu a hannunta. Sai da Laraba ta saka ɗankwali ta rufe fuskarta, sannan ta ɗauki sauran kunun ta juye mata a fuskar. Wani tunani ne ya faɗo mata ta fita da sauri, ta ɗauko jarkar ruwa irin ta 'yan-ga-ruwa ta tuttule musu ruwan gabaɗaya a ɗakin. Ta janyo galan ɗin man gyaɗarsu ta sheƙa a ƙafafuwan 'Yar gwala da Ɗanladi, ta kai jarkar man ta saƙala mata a hannu. A hankali ta lalallaɓa ta ja ƙafar Ɗabladi sai ta ji ya tafi yaraf, daga shi da ma sai gajeren wando da singlet. Ta ɗauko ƙaton omonsu ta zazzage masa a jiki zuwa fuska, har ta je za ta fita ta hango belt ɗinsa da sauri ta ɗauka ta fara zabga musu ɗaya bayan ɗaya. Sai da ta ga sun fara motsi sannan ta fice daga ɗakin da sauri, ta nufi ɗakin Inno. Tana zuwa ta shige bargo ta kwanta tana dariyar ƙeta, babu jimawa bacci ya yi awon gaba da ita.
Mai Yasin tun da ya sha fura suna hira da Inno ya ga bacci ya ɗauke ta, bai tashe ba don shi ma ba son tafiyarta ɗakinta yake ba. Yana gama shan furar babu jimawa shi ma bacci ya ɗauke shi, ba shi ya farka ba sai kusan uku saura na dare. Inno cikin bacci ta fara jin alamun ana lalubar mamanta, da yake bacci ya sha kanta cikin magagi ta ce.
"Laraba wani wulaƙanci ne kike ji da shi haka?"
Shiru Mai Yasin ya yi ya ci gaba da sabgar gabansa, Inno ta gyara kwanciyarta jin har lokacin ba a daina lalubarta ba, kuma har lokacin idonta a rufe yake da sauran bacci a kanta ta furta.
"Laraba zan ci mutumcinki fa."
Mai Yasin ya kashe murya, shi a dole yana son lallamar Inno don kar ta ba shi matsala ya ce, "Wannan Ɗanlami ne ba Laraba Innota." Firgigit Inno ta yi ta ware idonta, a rikice ta ce. "Malam mene ne haka?" Mai Yasin ya kashe mata ido ɗaya ya ce, "Haba Innoniyata, kamar wata 'yar sha uku duk kin firgice. Sharuɗɗan aure ne fa nake son cikawa." Inno tana shirin ture Mai Yasin ya murɗe 'yan hannuwanta, ta yi mamaki matuƙa yadda ta ji ta kasa kataɓus. Don ba ta taɓa tsammanin yana da ƙwari haka ba, Inno babu yadda ta iya haka ta zubawa sarautar Allah ido. Tun tana tsine wa Mai Yasin a zuciyarta har ta fito fili, don shi da ita sun yi yarjejeniyar auren ɗauko mini buta suka yi.
In Shaa Allahu wannan shi ne shafi na biyun ƙarshe, gobe zan gama free pages.
Littafin kuɗi ne 500 ta Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
*GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd
Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻
SHAFI NA SHA UKU
Inno har gari ya waye ban da hawaye babu abin da take yi, da ta kalli Mai Yasin ban da kallon tsana babu abin da yake wurga masa. Shi kuma Mai Yasin ban da juyi a katifa babu abin da yake yi, saboda wani bacci da ya samu mai cike da kwanciyar hankali. Jin shasshekar kukan Inno ce ta farkar da shi, ya ɗago cike da shauƙi ya ce.
"Innota! Haba Innota, me ya sa kike son ɗaga mini hankali da farar safiya haka? Maimakon ki zo na ninke ki a bargo, mu cigaba da baccin cikar fariciki amma sai ki ɓa ta ranki a banza. Ko me na yi miki ai soyayya ce, haba Innaniyota!" Inno ta share hawaye, a hankali Mai Yasin ya dinga fasa mata kai yana yabonta tare da nuna mata zallar soyayya. Saboda ya lura da abin da Inno ta fi so, ya kuma fi saurin sace zuciyarta da shi. Nan take ta saki jikinta, sannan ta miƙe za ta fita da sauri ya ce.
"Inno me za ki fita ki yi, kina fama da kanki?"
Inno ta jingina da jikin ƙofa ta ce, "Abin kari zan haɗa mana..."
"Allah Ya sawaƙe ki fita ki haɗa kayan abinci, da kanki kina fama da ɗanyan jiki."
Murmushi Inno ta saki har cikin ranta ta ji daɗin kulawar da yake ba ta.
"Bari ki ga na je wurin Sule mai shayi, na kaso mana dubu biyar ɗin nan."
Da sauri Inno ta ce, "Malam dubu biyar fa?"
Cike da son nuna burga Malam Ya ce, "Dubu biyar ɗin banza, ni duk yawan kuɗi ba kin fiye mini su ba Innota." Kan Inno ya ƙara girma, za ta fara magana wayar ta ta fara ringing. Malam ne ya miƙa mata, sai da ta ɗauka ta kai kunnenta sannan ta gane muryar aminiyarta ce, kasancewar sabuwar wayar da Fadil ya sauya mata, ba a iya saving da shaidar mota ko jirgi da a baya ake yi mata.
"Assalamu Alaikum, Hajiya Goggo barka da safiya."
Daga can ɓangaren Goggo ta ce, "Wa alaikissalam, barka dai amarsu. Inno ga mu nan a tasha yanzu motarmu za ta taso."
Cike da farinciki Inno ta ce, "Kai amma dai gaskiya kin yi mini bazata, Allah Ya kawo mini ke lafiya."
Goggo ta amsa da Amin sannan ta furta, "To agaida mana angonmu kafin mu zo, don na ji muryarki ta sauya amarci ya karɓe ki tsohuwar nan."
Inno da Goggo suka saki dariya lokaci ɗaya, daga haka suka yi sallama. Ba tun yau ba Mai Yasin yake jin labarin Goggo a wurin Inno, a lokacin aurensu ma ta so zuwa wani jikanta ya rasu don haka ta ɗaga zuwan sai daga ba ya.
Tun bayan fitar Laraba sama-sama suka dinga yunƙurin buɗe idonsu, amma fatar idanunsu ta yi wani irin nauyi don haka suka gagara buɗewa. Sai dai wasu abubuwan da suka faru gani suke yi kamar a cikin mafarki ne. Ɗanladi da 'Yar gwal ba su suka farka ba, sai kusan ƙarfe tara na safe. Ɗanladi ne ya fara farkawa ya ji jikinsa duk ya yi tsami, a hankali ya buɗe idonsa ya ci karo da ɗakin ya yi jaga-jaga. Ransa ne ya ɓaci da ya ci karo da mai ya yi luntsum a tsakar ɗakin, ga jarkar man a hannun 'Yar gwal ta yi share-share a ƙasa tana munshari. A fusace ya ƙarasa wurin da take yashe, ya tsinka mata mari wanda ya sa ta miƙe tsaye a gigice.
"Tsabar iskanci dama ba ki daina shaye-shayen da na hana ki ba? Dubi irin rashin mutumcin da kika yi mana?"
Da mamaki 'Yar gwal take bin jikinta da ɗakin da kallo, ta dafe kumatu ta ce. "Ni ka mara?"
A harzuƙe Ɗanlami ya ce, "An mare ki ko za ki rama? Da yake har lokacin maganin bai gama sakin ta, ta yi luuu da idanu ta furta. "Wallahi ba ka mari banza ba sai na rama."
"Ashe kuwa zan yi miki ɓarin makauniya, tsabar rashin mutumci in saka sama da dubu goma sha na sayi jarkar mai ki rubar a ƙasa. Wallahi yau sai kin gane ke ƙaramar ƙwaya kike sha." A zabure 'Yar gwal ta miƙe tsaye tana kaɗa ƙugu ta ce, "Ƙwayar ma ai mataki-mataki ce, billahillazi sai na nuna maka ko a gidan giya akwai babba. Kai ba wani shege fa." Daga haka ta cakumi wuyan Ɗanladi, ganin haka ya sake ɓa ta ransa don haka ya shiga kai mata duka ita ma tana ramawa. Kasancewar ƙarfin namiji da mace ba ɗaya ba, ya sa 'Yar gwal ta fara laushi. Wannan ya sa, ta ɗauki wani burugali a bayan ƙofa ta ranƙwala masa a goshi, nan take goshinsa ya yi wani tsororo ya kumbure suntum. Azaba ta sa Ɗanladi ya kai mata naushi a ba ki, sai ga bakin 'Yar gwal ya fashe har haƙorinta ɗaya na gaba ya faɗo. Kafin wani lokaci tuni bakin ya kumbure sai sheƙi yake yi. Sai da suka jigatu don kansu sannan suka faɗi gefe, ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba. 'Yar gwal ta fara tattara kayanta tana kuka, hakan ya sa jikin Ɗanladi ya yi sanyi. Ya tsugunna a gefenta cikin tattausan lafazi ya furta. "Me kike yi haka 'Yar gwal?"
Ba ta tanka masa ba, ta cika akwatinta, ta fizgi mayafi ko wanke fuskarta ba ta yi ba saboda ɓacin rai za ta fita. Da sauri ya janyo ta, ta faɗo jikinsa ya ce. "Haba 'Yar gwal, don Allah ki yi haƙuri kin san dai ba zan iya rabuwa da ke ba. Wallahi ɓacin ran abin da kika yi mini ne ya sa haka, ke ma kin san ba ki kyauta ba." Har a ranta ta ji daɗi saboda ita ma dama ba ta yi niyyar tafiyar ba, ta yi hakan ne don ta tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro. Ta janye hannunsa fuska a haɗe ta ce, "To ai gara na ba ka wuri tun da hakan shi ya fiye maka, da ka dinga tuhuma ta a kan abin da ba ni da masaniya."
Shiru ya yi yana nazari, don shi ma a iya saninsa dai 'Yar gwal ta daɗe ba ta shaye-shaye, kuma ko ta bugu ba ta irin wannan ɓarnar.
"Yar gwal jiya bayan mun sha kunu me ya faru?"
Ba ta ba shi amsa ba, ta taɓe baki. Wani irin tsoro ya kama shi, don ya ga jikinsa da na 'Yar gwal duk sun yi ruɗu-ruɗu.
"An ya ɗakin nan babu aljanu kuwa?"
Ya yi tambayar cikinsa yana kaɗawa, 'Yar gwal ta ce, "Ah to gidanku ne dai, ka fi kowa sanin yadda yake ai." Ɗaladi ya jima yana rarrashin 'Yar gwal, daga ƙarshe dai ta haƙura. Shi da kansa ya shiga gyaran ɗakin, don 'Yar gwal cewa ta yi ba za ta taɓa komai ba.
Washegari tun da farar safiya Zuly matashin kai ta dokowa Yaya Inu waya, cike da kissa take yi masa kalaman tausasawa domin tana son sake karɓar kuɗi a wurinsa. Yaya Inu duk damuwar da yake ciki lokaci ɗaya ta yaye, ya miƙe a hankali ya saka wata jallabiyyarsa ya fice. Ƙofar gidansu Zuly ya ƙarasa, ya kai mata dubu goma sha biyar kamar yadda ta buƙata. Ta kashe masa ido ta ce, "Yanzu fa nan da awa biyu zuwa uku na zama taka. A gaskiya duk macen da ta yi sa'ar samunka ta yi dacen miji." Yaya Inu ya saki murmushi ya ce, "Waɗannan kalaman na ki suna sake birkita ni Zulyta. Yanzu dai bari na wuce gida na sallami waɗancan mutanen, na fara shirin tafiya ɗaurin aure." Zuly ta ɗan yamutsa fuska ta ce, "Tun yanzu baby?" Yaya Inu cikin tausasa lafazi ya ce, "Sai yadda kika ce." Zuly ta yi wani far da ido ta ce.
"Ni na isa, Allah Ya taimake ka aje ayi yadda ya dace. Don na fi son mijina ya zama adali."
Yaya Inu sai da ya yi da gaske sannan ya tafi daga wurin Zuly, yana tafiya ta wuce gidan Hajiya zuma mai magungunan mata. Ta kai mata dubu biyar cikon kuɗin magungunan da take bin ta. Saboda ba ƙaramin haɗi ta yi mata ba, don ta ci alwashin kafin ta fito daga gidan Yaya Inu sai ta tatike shi tsaf, domin ba da niyyar zama ta je ba. Don haka ta je aka saka mata inplan, don ma kada ta ɗauki ciki.
Tun da hantsi ya yi suka ga shiru Mai gari bai fito ba, Azeema ce ta shiga ɗakin saboda dama girkinta ne. A zaune ta samu Mai gari ya haɗa kai da gwiwa yana hawaye, hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali ya yi ba. Jiki a sanyaye ta zauna kusa da shi ta ce, "Ranka shi daɗe lafiya? Me yake faruwa da kai a farar safiyar nan kake kuka?"
Mai gari ya ja majina yana sharce hawaye, ya saka hannu ya dafe saitin zuciyarsa da yake bugawa da sauri ya ce. "Azeem ina cikin wani yanayi mara musaltuwa, zuciyata tana cike da muradin da ban san lissafin da mutane za su lissafa a kaina ba."
Azeema ta sauke ajiyar zuciya ta ce, "Tun shekaran jiya na fara lura da sauyinka ranka shi daɗe, amma na yi maka tambayar duniya ka ce mini babu komai. Mene ne a zuciyarka da yake damunka?"
Kai tsaye Mai gari ya ce, "So ne, so ne yake nuƙurƙusar zuciyata kuma ban san a lokacin da ya yi mini kamun kazar kuku ba. Yanzu haka na takure kaina a ɗakina ne, saboda kada na fita fada zuciyata ta fisge ta zuwa gidansu."
"Wace ce ita?"
Ta wurga masa tambaya.
"Laraba ce Azeema, wallahi zuciyata har wani tartsatsi take a kanta."
A razane Azeema ta ce, "Laraba tsidigu dai? Eh lallai dole ka ce jarabta. Ranka shi daɗe ko dai mafarki kika yi, ka rasa wacce za ka so sai waccan sheɗaniya hatsabibiyar yarinyar Lara..." Ba ta gama magana ba, Mai gari ya gwaɓe mata ba ki ya fashe.
"Kada ki sake danga ta mini Laraba da shaiɗanu, idan ba haka ba ranki zai yi mummunan ɓaci."
Tsoro ne ya kama Azeema, jikinta a sanyaye ta fice daga ɗakin domin ba ta tantama akwai ciwon da ya samu mijin nasu.
Kamar yadda suka tsayar da magana, a washegari Baba Ibrahim da Baba Sale har da Ɗan Bishir suka sake komawa police station.
"Alhaji na yi mamaki ƙwarai da na ji an ce case ɗin naka ne? Me ya yi zafi haka?" Baba Ibrahim ya tambayi Alhaji Idi Naira.
Alhaji ya furzar da iska mai zafi ya ce.
"Wani zance ne ya fara yawo a cikin garin nan, wai ina ɗauke da cuta mai karya garkuwar jiki Dr, ni kuma a iya sanina ba ni da ita. Da na bi diddigin maganar, sai aka ce an samo zancen daga wurin Malam Shehu, don haka na kawo shi ƙara. Sai bayan na zo na ci karo da Bala wanzan a nan , ni kuma ba zan laminta ba har sai an bi mini haƙƙina. Daga nan ma kotu nake son a tura mu."
Malam Shehu ya yi fiƙi-fiƙi cike da tsoro ya ce. "Wallahi tallahi ni ma ba ni na faɗa, jita-jita na ji ana yi kuma sai aka yi sara a kan gaɓa. Ni kuma ina ganin kamar Bala wanzan ya sani, amma ya munafurce ni."
Bala wanzan ya zaburo yana faɗin, "Amma ai kai ka kawo hukuma har gida suka tafi da ni, ka ce na yi maka aski wai kai ma kana zargin ka kamu."
Jin hayaniya tana neman kacamewa wani Sergent ya buga musu tsawa yana faɗin.
"Ba ma son hayaniya, kai Bala tun da kai aka fara kawowa ka yi musu bayani."
"Ni dai tun da nake ban taɓa yi wa Alhaji Idi Naira aski ba sai wannan karon, ya kira ni har gidansa na yi masa aski da gyaran fuska. To bayan na fito daga gidansa, sai na wuce gidajen iyayen yara da dama na yi wa 'ya'yansu kaciya, wasu ma har aski na yi wa iyayensu. Sai kuma jarirai biyu da na cirewa hakin wuya. Bayan kwana biyu, sai na fara jin surutun wai Alhaji Idi Naira yana ɗauke da cutar ƙanjamu. Kwatsam! Ina zaune sai ga jami'an tsaro su zo da Malam Shehu, su ka tattaro ni suka yi awon gaba da ni."
Sergent ɗin ya gama rubuta jawabin Bala wanzan, sannan ya dubi Idi Naira.
Idi Naira ya shiga wurga wa Malam Shehu harara ya ce. "Yallaɓai wannan mutumin ya ci mutumcina, ta hanyar yi mini ƙazafin da ban ji ba ban gani ba. Kawai saboda kwanaki na yi fama da rashin lafiyar farankama, shi ne aka fara yawo da ni wai ina da ciwon ƙanjamau. Har wasu suna cewa ƙurajenta sun fito mini." Ƙuri Baba Sale ya yi wa Alhaji Idi Naira yana kallo, saboda irin ramammun mutanen nan. Idi Naira ya ɗora da cewar.
"Dr kai ne likita, saboda Allah ina haɗin cutar farankama da ƙanjamau? Ko saboda kullum sun ga ina lalacewa kamar ɗibana ake yi? Ni lafiyata ƙalau, masifar uwar gida da amaryata ne suka saka ni a gaba."
Sai a lokacin Baba Ibrahim ya numfasa jin musu da hatsaniya ta fara kacamewa ya ce.
"A'a gaskiya babu haɗi ma tsakanin cutar ƙanjamau (HIV) da cutar farankama/ƙarambau (CHIKENPOX).
Tun da ita cutar ƙanjamau wato HIV (Human Immunodeficiency virus), cuta ce da take karya garkuwa da kariyar jikin ɗan'adam. Ta yadda za ta ba wa ƙwayoyin cututtuka damar shiga jikin salin-alin, ba tare da wata kariya ba. Alamomin cuta mai karya garkuwar jiki sun haɗa da: Ɓarkewar zawo, yawaitar kaluluwa, matsanancin zazzaɓin da ya ƙi jin magani har zuwa lokaci mai tsawo, ciwon maƙoshi, yawaitar fitowar ƙuraje babu dalili, gumin dare koda lokacin sanyi ne, ramewa da rashin cin abinci, tashin zuciya da amai sai tari mai ɗaukar lokaci ba tare da ya ji magani ba."
Cikin Alhaji Idi Naira ya kaɗa sosai, saboda yana jin kusan kaso mai yawa na alamomin da ya ji Baba Ibrahim ya lissafa.
"To amma wani hanzari ba gudu ba, koda mutum ya