Showing 15001 words to 18000 words out of 94348 words
haka ya sa shi zaro ido, sai kuma ta nuna masa hanyar fadar Mai gari. Shiru ya yi don bai gane abin da take nufi ba, ta ƙare masa kallo tun daga sama har ƙasa ta ga bai yi kama da ɗan garinsu ko maƙotan garinsu ba ta ce.
"Mu gadon gidanmu ba a iya biyansu da kuɗi ko kadara, idan har aka cutar da su. Sai dai a tambaye su abin da suke muradi a yi musu."
Bakinsa yana rawa ya ce.
"Don Allah faɗi abin da kike so ko mene ne zan yi miki."
Laraba ta ja ƙafa da rarrafe ta ce, "Matso kaji don kada aljani Karbu ya ji ka."
Yadda Mahmud ya matso da sauri kamar zai faɗo kanta ya sa dariya ta kusa ƙwace mata. Ta maze a ta fara yi masa raɗa a kunne, da sauri ya zaro mata ido. Laraba ta gyaɗa masa kai sannan ta ce.
"Wallahi idan ba ka aikata son raina ba sai na saka aljani batoyi ya babbake ka, kuma na sa ya bi har gidan iyayenka ya ƙone su ƙurmus. Sannan ya haɗa maka baƙin sharri a garin nan, gara tun wuri ka tafi zan biyo ka ta cikin iska duk abin da za ka yi ina ganinka. Idan ka faɗa ba daidai ba na hukunta ka ba."
Kamar Mahmud zai yi kuka ya nufi hanyar fadar Mai gari da Laraba ta kwatanta masa, su Mai gari tun daga nesa suka fara hango shi don haka suka zuba masa idanu suna kallo. Mahmud yana zuwa ya taka har tsakiyar shimfiɗar Mai gari ya fara bin su da kallo kamar yadda Laraba ta tsara masa, yana yi yana waige don kar ya yi ba daidai ba ta sa a ƙone shi.
Gabaɗaya a tsorace suke don sun yi tsammanin soja ne, Sanƙira ne ya yi ƙarfin hali ya ce.
"Samari daga ina haka? Wa ya ba ku izinin taka shimfiɗar ranka shi daɗe..."
Sanƙira bai gama magana ba, Mahmud ya ɗauke fuskarsa da mari. Saboda tsoro har ji ya yi marin yana yi masa yaji-yaji a fuska.
Lokaci ɗaya suka shiga taitayinsu, cikin Mai gari ya shiga kaɗawa gumi yana keto masa. Malam Bukar ya yunƙura zai tashi ya tafi, Mahmud ya buga masa tsawa.
"Ni da kuka ganni ba mutum ba ne, na zo muku da wannan surar ne domin ku bil'adama ne. Idan na kwashe ku na tafi da ku a can ne za ku yaba wa aya zaƙinta. An turo ni ne daga hukumar kare haƙƙin aljanu, domin na zo na bi diddigin cin zarafin da aka yi wa 'yar cikinmu wato aljanun da ke jikin Laraba."
Mahmud yana gama faɗar haka mutane wurin suka shiga rige-rigen gudu, Mai gari tsalle ya yi ya haye bayan Sanƙira kamar wani ɗan biri. Saboda tashin hankali Sanƙira bai yi wata-wata ba ya damfara Mai gari a ƙasa, ya naɗe babar rigarsa ya take ƙafarsa ya bar wurin a guje. Mai gari yana shirin guduwa, taku ɗaya Mahmud ya yi ya cafko rigarsa. Duk yadda ya so ya ƙwacewa ya kasa, ga shi yawancin mutanen wurin sun gudu sun bar shi. Sai kawai ya taƙarƙare ya fashe da marayan kuka, ta ƙasa kuma gudawa ta ƙwace masa tana zuba.
07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI*
©®AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA
SHAFI NA SHIDA
Wani irin ƙyanƙyami ne ya kama Mahmud jin yadda Mai gari yake ta sakin gudawa babu ƙaƙƙautawa, ya ɗan waiga bayansa cike da tsoro don su kansu da ace ba a tsorace suke ba, da sai sun fahimci tsoron da yake kwance a saman fuskar Mahmud.
Mai gari hawaye da majina da suka gama wanke masa fuska ya dubi Mahmud ya ce.
"Da wanne suna zan kira ka ranka shi daɗe, kuma cikin jinsinku ana iya kiranku da wannan sunan? Ka dubi Allah, ka dubi Muhammadur Rasulillahi ka yi mini rai ka yafe mini."
Mahmud ya tsuke fuska ya ce.
"Kada ka sake yi mini magiya, domin ni ma umarni na karɓa daga sama, a madadin hukumar kare jinsin aljanu ta ƙasa, sun wakilto ni na zo na tafi da kai da taƙadiran mutanenka zuwa fadar majalisar ɗinkin duniya ta aljanu. Amma tun da sun gudu da kai za mu tafi."
Jin haka ya sake ɗaga hankalin mai gari sai kawai ya sake fashewa da kuka, don ba shi da wata mafita da ta wuce haka. Sai da ya yi mai isarsa sannan ya shiga yi wa Mahmud magiya, Mahmud ya tuna yadda suka yi da Laraba ya dube shi ya ce.
"Za mu yi maka afuwa amma da sharaɗi, sharaɗin kuwa za ka ɗebo zabin gidanka guda huɗu ka yanka su a kan waccan bishiyar."
Mahmuda ya nuna masa wata bishiyar tunfafiya, Sanƙira da ke laɓe a bayan katanga ya zaro idanu duk da ba da shi ake ba. Mai gari ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya ya ce.
"Zabin banza ranka shi daɗe, wallahi ko rago ka ce yanka shi zan yi."
Ganin zai yi gaba Mahmud ya ce, "Ba mu gama ba ai, shi wannan jinin da zai sauka a kan bishiyar tunfafiya shi zai goge laifin da ka yi a ofishin shugaban ƙungiyarmu. Saboda ka san haka nan ma aljanu zubar da jini suke yi, gangar jikin kuma ka taho mini da buhu zan kai a kwankwantsa namansu, a madadin naman jikinka da za a yi kwatsa-kwatsa da shi." Mai gari ya shiga gyaɗa kai kamar na ƙadangare. Ya ƙalla wa Sanƙira kira ya ba shi umarnin da ya je gida ya ɗebo zabi guda huɗu. Sanƙira ya yi wuf ya sake ɓuya, don haka aka rasa wanda zai kawo wa Mai gari zabin da zai fanshi kansa sai Sahabi ne ya yi ta maza ya je gidan ya ɗebo. Kamar yadda Mahmud ya ba shi umarni, haka Mai gari ya ƙarasa bakin bishiyar tumfafiyar ya fara yanka zabbin ɗaya bayan ɗaya har ya yanke su duka. Bayan Mahmud ya karɓi zabbin ya cewa Mai gari.
"Abu na ƙarshe da zan faɗa maka shi ne, ka kiyaye ɓacin ran Laraba. Wallahi tun wuri ka haɗa mutanen garin nan su nemi yafiyarta." Mahmud ya sake daidaita baƙin gilashin idonsa ya cigaba.
"Idan ba haka ba sai mun tsotse romon kanka, kuma daga yau duk abin da kuka ga Laraba ta yi to ba yin kanta ba ne. Duk wanda ya yi gangancin sake taɓa ta zai mutu nan take, ko kuma mu ɗauke shi mu yi ta azabtar da shi."
Mahmud ya gama magana ya juya kansa a ƙasa ya cigaba da tafiya, Mai gari yana ganin haka ya fice a guje ya nufi gida ƙafar wandonsa ta yi sharkaf da gudawa.
Ga mamakin Mahmud yana zuwa ya tarar Laraba ba ta nan, a tsorace ya ajiye ɗan buhun zabbin ya yi sauri ya faɗa motarsa ya fisge ta da gudu ya bar cikin dajin.
Tun da Laraba ta hango shi ya tunkaro ta, take ƙyaƙyata dariya tana da saman bishiyar dalbejiya har Mahmud ya ja motarsa ya yi gaba.
Dirowa ta yi ta buɗe buhun tana dariya har da riƙe ciki, sai kuma ta yi shiru tana tunanin yadda za ta yi da zabi har guda huɗu. Mai daban-daban ne ya faɗo mata a rai, wani mai nama da yake can tsallaken ƙauyensu, wanda ya jima da cewa yana sonta. Da sauri ta suri buhun kamar marar gaskiya ta shiga bi ta cikin gonaki ya har ta isa wurinsa.
"Larabayyo 'yar Larabatuwa! Yanzu Laraba sai ki dinga guduna, saboda Allah mene ne aibuna?"
Mai daban-daban ya furta mata cike da so. Laraba ta maze ta ce, "Mai daban-daban ka san shi so makaho ne, to kwanaki shi ya lulluɓe mini idanu a kan wani mutumi amma yanzu ba ya gabana kai nake so!"
Wani irin daɗi ya mamaye shi don haka ya ce.
"Kai amma na ji daɗi Laraba, wallahi yau da ƙyar zan iya yin bacci yanzu faɗi duk abin da kike so a wurin nan a yanka miki."
Laraba ta yatsina fuska ta ce, "Eh wancan balangun za ta yanko mini ko yanka sha biyar ne, amma kafin nan ga zabin Inno nan ta ce a kawo ka gyara ka gasa mata."
Jikin mai daban-daban har karkarwa yake, ya fara yankawa Laraba nama. Ya kalli wani yaronsa ya buga masa tsawa a kan ya karɓi buhun hannun Laraba ya je ya gyara su. Bayan ya miƙa wa Laraba balangun ta ce.
"Na gode sosai masoyina mai daban-daban, yanzu waɗannan zabin idan ka gama gasa su ka ajiye da daddare zan zo na karɓa." Mai daban-daban ya amsa mata yana washe baki. Laraba har ta yi gaba ta waiga ta sake jan kunnensa, a kan kada ya aika zabin gidansu za ta dawo ta karɓa da kanta.
Mahmud bai yi tafiya mai nisa ba, isa bakin wani babban symbol ɗin sabulun wanka da ke gefen titi. Ya ciro waya ya kira abokinsa Muddasir, wanda suka yi da shi za su haɗu a adaidai wurin da ya kwatanto masa. Bugu biyu wayar ta yi ya ɗauka. Daga can ɓangaren ya ce.
"Ga ni nan ina hango ka na kusa ƙarasowa!"
Daga haka Muddasir ya katse. Cikin ƙasa da minti ɗaya mai adaidaita sahu ya sauke shi. Sai da Mudassir ya biya shi kuɗinsa ya ƙarasa wurin motar Mahmud ya ce, "Mutumina ashe ka gane kwatancen!"
Cike da damuwa Mahmud ya ce, "Allah ka yi mana tsari da ƙauye, yanzu saboda Allah a nan za mu yi service?" Mudassir ya yi murmushi yana zama a sit ɗin gaba ya ce.
"Kai kukan daɗi kake yi, da muka samu aka canza mana school zuwa ta garin Gangaren dutse? Da ace an bar mu a garin Rafin gurgu fa? Yanzu ba ga su Haidar can ba suna fama."
Mahmud ya saki guntun tsaki ya ce, "Yanzu ina za mu bi mu ƙarasa garin Gangaren dutsen?"
Mudassir ya nuna masa hanyar shiga garinsu Laraba, gabansa ne ya faɗi amma sai ya basar don ba ya san ya sanar da Mudassir abin da ya faru da shi ya yi masa dariya.
Ganin sun tunkari hanyar garinsu Laraba ya sa Mahmud ya ce, "Wai ina ne garin? Mun kusa zuwa ko da saura. Mudassir ya ce, "Mun kusa zuwa, da ka miƙe za mu bi ta kan doguwar hanyar can har ƙofar gidan mai gari, ka san dole sai mun gabatar da kanmu a wurinsa tun da zama ne ya kawo mu.
A hargitse Mahmud ya taka burki cikinsa yana kaɗawa, Mai garin da ya gama sakawa zawo a wando ne za su je wurinsa su gabatar da kanku?
"Lafiya Mahmud?"
Mahmud da gumi ya gama rufe shi kamar zai yi kuka ya ce.
"Wallahi ba lau ba Mudassir."
Ya ƙarasa maganar yana yin parking ɗin motar a gefen hanya, sai kawai ya kifa kansa a kan sitiyarin motar.
Cike da shauƙi Mai Yasin yake kallon Inno jin amsar da ta ba shi, dangane da sanar da iyalanta a kan maganar aurensu. farinciki fal zuciyarsa ya ce.
"Allah mai haɗa jinin mumini da mumini, Allah kaɗai ya san alkairin da yake ɓoye da silar haɗuwarmu a Saudiyya. Haka kawai na ji kin sake kwanta mini Inno, a gaskiya marigayi ya dace da mace."
Inno ta saki murmushin jin daɗi kanta a ƙasa, ita dai nutsuwar Malam da daɗaɗan kalamansa waɗand ta rasa a baya suna birge ta. Har a cikin zuciyarta tana jin ina ma tun tana budurwa, Allah Ya aiko mata shi cikin rayuwarta, da babu yadda za a yi ta yi rayuwa da tsohon mijinta da ko kaɗan bai iya soyayya da tarairaiyar mace ba. Mai Yasin ya saci kallonta da gefen ido ya ce. "Innota ko ba kya jin daɗin yabon da nake yi miki? Ko da za ki ji babu daɗi sai dai ki ji, amma Allah Ya sani ƙaunarki ta jima da ɗamfaruwa a cikin zuciyata."
Inno ta ɗago ta dube shi ta ce. "Haba Malam, ai duk macen da ta yi dace da kai a matsayi mace ta more a gidan duniya da Lahira."
'An zo wurin, dama nan nake ta jiran mu ƙaraso.'
Malam ya raya a cikin ransa, yana murmushi mai ɗauke da manufa a ransa. Ya ƙanƙance murya cikin yaudara da karuwanci ya ce.
"Wallahi tun da na wayi gari jikin nan yake son dawo mini Inno, ga bakina salam babu daɗi kamar yawun mage. Nace ko zan samu koda kaza ko naman kasuwa?"
Inno ta sauke ajiyar zuciya, tana mamakin yadda Mai Yasin ba ya gajiya da murƙushe cinyoyin kaza, amma da ta tuna a kullum ya ci kazar ya kuma sharɓi romonta ƙara samun lafiya yake sai ta ce.
"To Malam ka ga dai yaran nan ɗazu kusan baram-baram muka rabu da su dutse a hannun riga, kuma dama mai ƙoƙarin sayo maka Iro ne. Yanzu dai ban san cikinsu wa zan tunkara ba, tun da kazar jiya ma shi ya taho da ita."
Mai Yasin yana gama jin haka sai kawai ya fashe da kuka, ya fara jan magina yana matsar ƙwallah. Sororo Inno ta yi jiki a sanyaye ta ce.
"Lafiya malam?"
Mai Yasin ya ja majina ya ce, "Kaico rashin haihuwa, kaicona Allah ka cigaba da ba ni dangana. Da 'ya'yan da na haifa ne ai duk tsiya za su kawo mini duk kuwa yadda muka yi da su, yanzu kamar dai garken wannan yaron Inu har sai na tambaye shi idan na yi niyyar ɗiban kaji ko zabi? Amma tun da ban haifa ba dole na yi haƙuri da rayuwa."
Shiru Inno ta yi tana nazari don ta san mammaƙo irin na Yaya Inu, amma don ta kawar da damuwar Malam sai ta ce.
"Daga yau kada ka sake faɗin yaran nan ba kai ka haife su ba, kai tamkar mahaifinsu ne kuma duk abin da kake muradi, ka yi kanka tsaye ko ka tambaye ni idan kana jin nauyi."
Malam ya hau gyaɗa mata kai, Inno ta miƙe tsaye har ta je bakin ƙofa ta juyo ta ce.
"Kaji kake so ko zabi?"
Malam ya sake narkewa a katifa yana sakin murya a dole shi marar lafiya ya ce, "Idan da so samu ne a samo matasan samarin zakaru masu jini a jika, tun da ai muma a wannan satin ne tariyarmu!" Inno ta saka mayafin ta rufe fuska ta fice tana dariya, tana fita Mai Yasin ya buga tsalle a kan katifa yana rawar oya shake body.
Kai tsaye sashen Yaya Inu Inno ta nufa, a lokacin da ta je ba ya nan sai matansa. Cikin girmamawa suka gaishe ta, bayan ta amsa ta ce su buɗe mata garken awaki da shanunsa. Kusan lokaci ɗaya suka kalli juna, Larai ta yi ƙarfin halin faɗin.
"Inno amma bai ce za ki zo ɗaukar..."
Cikin tsawa Inno ta katse ta.
"Dama ban ce miki na faɗa masa ba, Malam ne ya ce mini yana sha'awar matasan samarin zakaru ni kuma na zo zan bincika masa, idan ya zo ki sanar da shi abin da na sanar da ku." Daga haka Inno ta nufi garken ta hankaɗa ƙofar zagayen da ƙafarta. Safare da Dubu 'ya'yan Yaya Inu ne suka taya Inno ɗiban zakarun guda uku ta fice da su, ta yi wa Malam magana da kansa ya fito zuwa bakin rariya ya yanka su. Inno ta ɗora ruwa ta shiga gyaran kaji, sai ga shi babu jimawa ƙamshin farfesun kaji ya cika gidan, ta zuba a babban food flask wanda ta saba zuba wa Malam ta kai masa. Ta ɗebi ɗan madaidaici ta ragewa Laraba a kai, ƙafa da wuya a cikin tukunya.
Cikin sauri Yaya Inu yake tafe, hannunsa riƙe da baƙar leda wacce take cike da sababbin magunguna da ya taho da su daga bakin kasuwa. Saurin da yake yi La'asar ta ƙarato, ga shi mai maganin sanyin da ya saya ya sanar da shi ba a wuce ƙarfe huɗu na yamma ba tare da an dafa an sha shi ba, saboda ƙa'idarsa kenan. Shi kuma a ranar yake son yin amfani da shi kuma ba ya fatan lokaci ya ƙure, shawo kwanar da zai yi ne ya ci karo da Hajara tsohuwar matarsa wacce ya ji labarin mijin da take aure ya mutu. Dama tun da ya saki Abu zuciyarsa ta shiga wasu-wasi a kan ya dawo da ita.
"Ranki shi daɗe, yau Hajara ce a gari?"
Yaya Inu ya faɗa yana washe baki, Hajara ya ɗan yatsina fuska ta ce.
"Eh ni ce sai aka yi yaya Inusa?"
Yaya Inu ya fara gyara zaman hularsa ta tashi ka fiya naci, ya saka hannu yana gyara wuyan rigarsa yana murmushi ya ce.
"Hajarata tun rannan nake ta so na zo mu gaisa, saboda kin san lamarin duniya komai ɗan haƙuri ne. Wallahi na so na zo na yi miki gaisuwa ma amma Allah bai nufa ba, na ce ƙila ma rabona ne ya yi gaba da marigayi."
Hajara ta ƙanƙance ido cikin masifa ta ce.
"Rabon me? Allah Ya tsare ni da komawa gidanka Inusa, ai ni babbar godiyar da na yi wa Allah da ya sa ban haihu da kai ba. Da