Showing 18001 words to 21000 words out of 94348 words

Chapter 7 - GIDAN LIKITOCI BOOK COMPLETE BY AMEERA ADAM.txt

29 Sep 2025

825

zaman yunwa zan ji ko da rashin sutura, kai yanzu ba ka ga yadda na koma ba?"
Yaya Inu ya yi shiru yana bin ta da kallo cike da so, don ta yi shar fatarta har ƙyalli take. Dama ya ji labari an ce a gidan tsohon mijinta ta haɓɓaka uwar gida.

"Ai yanzu wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa na wuce ajinka wallahi Inusa, su dai waɗancan wahalallun matan naka sai su yi ta zama kafin layin saki ya biyo ta kansu."
Tana gama maganar ta yi gaba, ran Yaya Inu ya ɓaci ga rashin samun haɗin kanta da na baƙaƙen maganganun da ta faɗa masa. Ya bi ta da sauri ya ce.

"Banza 'yar wahala an faɗa miki ba zan samu wacce ta fi ki ba, ki zuba ki gani nan da kwanaki kaɗan zan ɓarzo wacce ta fi ki komai." Hajara ba ta kula shi ba ta yi gaba, shi ma Yaya Inu ya ƙarasa gida rai a ɓace.
Tun daga bakin ƙofa ya fara yin ball da kwanika saboda yadda yake a fusace. Hakan ya sa su Larai suka sake shiga taitayinsu, yadda ya ga sun yi tsuru-tsuru ne ya sa ya fahimci abin da ya faru.

"Lafiya kuka yi wani zumu-zumu da idanu kamar an shaƙe zakaru?"
Indo da har lokacin haushinsa take ji, saboda abin da ya yi mata dariya ta kusa ƙwace mata amma sai ta danne ta ce.

"Zakaru kam ai ba shaƙa kaɗai suka sha ba, karo suka yi da wuƙa yanzu ma sun wuce birnin tumbi."
Yaya Inu ya haɗe fuska ya ce, "Abokin wasanki na zama Indo?"

Indo ta fara tafiya irinta ta kai kajiyo, sannan ta sanar da shi abin da Inno ta yi. Jikinsa ne ya shiga karkarwa saboda duk duniya babu abin da yake saurin ɗaga hankalinsa irin a taɓa garkensa. Da sauri ya nufi sashen Inno ya same ta a ɗaki ya ce, "Inno na ji wani zance a kan garkena." Jin haka ya sa Mai Yasin da ya ke zaune a ɗakin Inno ya tauna wani ƙashi wanda ya ja hankali Yaya Inu, wani ƙululun baƙinciki ya tokare maƙoshinsa, ya haɗiyi yawu mai ɗaci yana sauraron Inno.

"Ubanku ne yake marmarin matasan samarin zakaru, shi ne na lalubo 'yan matsakaita uku na yanka masa."

Yaya Inu ya fara huci ya ce, "Amma Inno ko za ki ɗiba ai sai ki sanar da ni."
Mai Yasin ya yi farat ya ce, "Kai Inusa kana neman albarka kuwa? Saboda mahaifiyarka ta ɗebi zakaru uku ka zo za ka yi mana tijara, kai yaro ka shiga hankalinka ka nemi albarkar uwa."
Haushi ya sa yaya Inu ya tunkari Malam yana jin kamar ya murɗe masa wuya, da sauri Inno ta sha gabansa ta ce.

"Ni ka dake ni Inusa ka ji! Ka dake ji na ce."

Shiru Yaya Inu ya yi saboda yadda zuciya ta ciyo shi, sai kawai ya fice daga ɗakin.

Malam ya jima yana zuga Inno ai kuwa ta cika ta yi fam, daga haka ya koma ɗakinsa ya zura doguwar riga ya tafi banɗaki zai yi wanka. Yaya Inu yana daga harabar gidansa ya hango shi, ganin Malam ya shiga wanka ya sa shi faɗawa ɗakinsa da sauri ya ɗauko wani ƙullin yajinsa, ya zura wata doguwar dorina a aljihu ya nufi banɗakin da Malam ya shiga. Sai da ya laɓe ya ji malam ya saɓa sabulu a fuska sannan ya banka banɗakin ya watsa masa yaji a fuska, Malam yana shirin yin magana saboda yadda ya ji an banko ƙofar banɗakin ya ji an zuba masa abu a fuska. Da sauri ya buɗe ido zafin sabulu da na yaji ya haɗe masa a ido lokaci ɗaya, cikin zafin zuciya Yaya Inu ya shiga zabga masa dorina ta ko ina.



07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚

[02/02, 15:02] Ameerah Adam🌚: *GIDAN LIKITOCI*

©®AMEERA ADAM

*FIRST CLASS WRITERS ASSO...*

Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.

*MARUBUCIYAR:*
MARWAN
JARIRI
ASEELA
BAƘAR DAULA
AN YA BAIWA CE?
ƊAN BA ƘARA...
SHU'UMAR MASARAUTA
DUBU JIKAR MAI CARBI
UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA
YAWON SALLAR HAJIYA IYA
ZAUJATU JINNUL-ASHIQ
SANADIN RAGON LAYYA

https://youtube.com/@ameerahaadam9365?si=xyR-pHK5EjkLjQnd

Don Allah duk wanda ya ci karo da wannan page ɗin, ya taimaka ya yi mana Subscribe a youtube channel ɗinmu.👆🏻👆🏻👆🏻

SHAFI NA BAKWAI

Tun da mahaifiyarsa ta kawo shi duniya bai taɓa jin azaba irin wacce yake ji ba, a tsammaninsa aljanu ne suke yi masa wannan izayar don haka Malam ya shiga karanto duk wata addu'a da ta zo bakinsa. Ban da kuka babu abin da yake yi, a zuciye Yaya Inu ya ce masa.
"Wallahi koda wasa idan ka sake cewa za ka ci kaza ko zakaru a gidan nan, sai na yi maka abin da ya fi haka. Munafikin Allah dama ba ka san haushinka nake ji ba, ubanmu ya kwanta dama sama da shekara ashirin Inno ba ta taɓa marmarin aure ba sai a kanka. In sake jin ka saka ta, ta taɓa awakina wallahi sai na lahira ya fi ka jin daɗi."
Daga haka Yaya Inu ya fice daga banɗakin kai tsaye ya wuce ɗakinsa ya sauya kayan jikinsa. Kai tsaye garken awakinsa ya shiga, wani sabon takaici ya mamaye masa zuciya musamman da ya tuna danƙwala-danƙwalan zakarun da Inno ta saka aka yanka.

Tun da ya fara magana cikin gargaɗi Malam ya fahimci Yaya Inu ne, sai da ya ji ya fita daga ɓanɗakin ya yi ƙoƙarin buɗe idonsa ya ji wata azaba ta ratsa shi. Ruwa ya laluba ya shiga kwarawa, ai kuwa ya ji kamar yana zuba wa jikinsa ruwan zafi saboda raɗaɗin da yake ratsa shi. Malam bai wata-wara ba ya fito a guje yana ihu da neman taimako haɗe da faɗin.

"Jama'a taimako, wani marar imanin zai hallaka ni. Jama'a ba kwa ji na ne ku kawo mini ɗauki."

Ihun da Malam yake yi ne ya ja hankulan mutane yara da manya, sai dai manyan da sun yi arba da shi suke komawa a guje. Labaran da Rahina ne suka shigo ba tare da sun san abin da ya faru ba, Rahina da Malam suka yi gware tana yin arba da shi ta kurma ihu suka shige sashensu ita da Labaran a guje. Ɓaɓatun da Malam yake yi ne ya sa Inno ta fito a tsorace ta ce.

"Malam lafiya kuwa?"

Turus Inno ta yi ta zuba hannuwa a ƙirji cikin tashin hankali, shi kuma Malam jin muryar Inno ya sa ya tunkare ta da gudu yana faɗin.
"Inno ki taimaka mini idanuwana za su makance, Innota jikina azaba yake yi mini kamar ana babbake ni."
Inno ta zuba kabbara ta fita da gudu tana faɗin.

"Malam ka yi mini aikin gafara wannan aikin ba nawa ba ne."

Malam Ya rufa mata baya har sashenta yana faɗin.
"Inno a gidan nan ke kaɗai ce kike ƙaunata, ki taimaka mini ki ce iyalina ta gobe."

Inno ta banka ɗaki da yake sashenta shiru yake babu kowa, sai hakan ya sake ɗaga hankalinta ga Malam ya biyo ta a gigice. Ta danna sakatar ɗakin ta ce, "Ka gafarce ni wannan aikin na maza 'yan uwanka ne." Duk bugun da Malam ya yi Inno ba ta buɗe masa ba.
Ana cikin haka Baba Ado ya shiga ya same shi, ko kaɗan bai ji daɗi ba domin tun a ƙofar gida aka fara ba shi labari. Towel ya miƙa masa murya a daƙile ya ce.

"Ka suturce jikinka."

A fusace Malam ya yi warci towel ɗin ya yi wurgi da shi ya ce, "Suturar banza da wofi, kai idan za ka taimaka mini ka ba matsa daga gabana, domin ni kaɗai na san bala'in da nake ciki." Tsaki Yaya Ado ya yi ya ce, "Wallahi idan ba ka ɗaura towel ɗin nan ba, zan tafi na bar ka. Darajar tsufanka na gani shi ya sa na zo taimaka maka, idan ba haka ba wallahi da sai dai ka yi ta zama a haka."

Sanin halin nunkufurcin Yaya Ado ya sa da sauri ya fara lalubar towel ɗin ya ɗauka ya ɗaura a ƙugunsa, kamar ƙaramin yaro haka ya zaunar da shi ya shiga wanke masa fuska da ruwa da sabuli. Zafin ciwukan da dorinar ta ji masa ya sa ya dinga ihu kamar yaro ƙarami, a haka har Yaya Ado ya gama wanke masa sai dai har lokacin wani irin raɗaɗi yake ji. Har ɗaki Yaya Ado ya raka shi ya haye katifa yana rawar ɗari, nan take zazzaɓi ya rufe shi.

Tun lokacin da Bala wanzan ya gama yi wa Ɗan Bishir kaciya ya shiga kiran layin Baba Sale, sai da ya yi ta maza ya ɗauka a nan yake sanar da shi an gana yi masa kaciyar. Jiki a sanyaye ya fita ƙofar gida, yana yin ido huɗu da Ɗan Bishir ya ji wasu zafafan hawaye sun zubo masa.
Da ƙyar ya miƙa hannu ya karɓe shi, har zai shiga gida abokinsa Sani wanzan ya zo wucewa. Ya kalli Baba Saleh sai kawai ya tuntsire da wata irin dariya, wacce shi kaɗai ya san manufar yin ta. Haka kawai gaban Baba Sale ya faɗi, amma sai kawai maze ya wurga masa harara ya shige gida.

Ɗan Bushir ban da yage baki yana kuka babu abin da yake yi. Yana zuwa ya kwantar da shi a kan gado, ya sa gefen rigarsa ya share hawayen ya ce.

"Ɗan Bishiririna! Ɗan Bishiri ka yi haƙuri ban kyauta maka ba ko? Yanzu me kake so na sayo maka?"
Ɗan Bishir ya kalli gabas da yamma, ya kalli mahaifiyarsa da ke gefe a zaune kalli mahaifinsa. Sai ya sake ɓarke baki ya saki kuka.
Ƙirjin Baba Sale ya buga da ƙarfi ya jikinsa yana rawa, ya rungume Ɗan Bishir ya dubi Uwale fuska shaɓe-shaɓe ya ce.

"Uwale tsoro nake ji, wallahi ina cikin tashin hankali."
Uwale ta sauke ajiyar zuciya, saboda ta san za a yi haka ko ma fiye da haka.
"Me ya faru mai gida?"
Baba Sale ya ja gefen ɗan kwalinta ya share hawaye ya ce. "Ina tsoron ko dai an guntule Ɗan Bishir gabaɗaya, Uwale kada fa Bala wanzan ya nakashe mini ɗan ɗaya-ɗayana..."
Kuka ya ci ƙarfinsa.

"Yanzu mai gida duk yaran da ka dinga yi wa shayi, iyayensu ba su ce za ka nakasa musu 'ya'ya ba sai da abin ya zo kanka? Kamar ba ka san yadda Bala yake da ƙware a harkar wanzanci ba? Kar ka manta shi fa ɗan gado ne."
A hassale Baba Sale ya ce.

"Kowa ai nasa ya sani, ni gudan jinina kuma magajina na sani don haka a kansa zan yi magana..."
Ita ma Uwale ta katse shi.

"To ai ɗa na kowa ne, shi ya sa ɗa da dukiya ba a yi musu mugunta. Kuma hausawa suka ka ƙi naka duniya ta so shi, ka kuma so naka duniya ta ƙi shi. Wallahi wannan zazzafar soyayyar da kake yi wa Ɗan Bishir ba za ta kai ka ba. Don ba zan ɓoye maka ba a cikin gidan kowa haushinsa yake ji, ko kaɗan ba shi da farin jini a wurin yara da manya."
Wani irin kallo ya shiga wurga mata, yana jin a ransa yadda ta caɓa wa Ɗan Bishir baƙaƙen maganganu da ace ba a yi masa kaciya ba, babu abin da zai hana bai kora ta gidansu ba. To don dai ya san idan ta tafi babu mai jinyarsa.

"Baaabaaaa!"
Ɗan Bishir ya furta a shagwaɓe, da sauri Baba Sale ya amsa masa sai ya ce.

"Zan ci abincin Rahina, daɗi gare shi. Ni ba zan ci komai ba sai abinci ko shayinta."
Zumbur Baba Sale ya miƙe ya ce, "Ai kuwa yanzu zan karɓo maka, zauna Ɗan Bishiririna ga ni nan zuwa." Ya ƙarasa maganar yana zuwa bakin ƙofa, ya waigo yana jifan Uwale da harara ya ce.

"Shi Ɗan Bishir dai ya zama kabewar kan kabari baƙincikin mai taushe, duk wani mahassadi sai dai ya gan shi ya ƙyale."
Daga haka ya fice daga ɗakin.

Kai tsaye sashen Labaran ya wuce, daga bakin ƙofa ya tsaya yana sallama. A lokacin Rahina ta tsakar gida a zaune tana shan iska, Labaran yana wanka a ta bayan kitchen ɗinsu don ya ce kafin ya samu kuɗin da zai rufa musu banɗakin sashensu, a nan za su dinga wanka saboda abin da ya faru da Rahina.

"Wa alaikassalam."
Rahina ta amsa sallamar tana yunƙurin miƙewa domin ta saka hijabinta, daga can gefe ta ji Labaran ya ce.

"Kada ki sake ki ƙara magana."
Shiru ta yi saboda ta san zafin kishinsa, shi kuma Baba Sale jin an amsa ya saki murya ya ce.

"Amarya mai daɗin tuwo da miya, angon na ki yana ciki?"

Wannan yabon da Labaran ya ji ana yi wa Rahina ya sake ɓata ransa, don haka ya zura gajeren wandonsa ko kunfar jinsa bai wanke ba ya fita fururu ƙofar gida.

"Lafiya Labaran me yake faruwa?" Baba Sale ya furta fuska ɗauke da mamaki.
Labaran ya yarfe kumfar fuskarsa ya ce, "Ita ta kawo haka! Ka san dai abin da ka aikata haramci ne ko? Ka zo ƙofar gida ka zage muryarka kana magana iyalina tana sauraronka, ba ka tsammanin ta ji muryarka ta yi mata daɗi?" Ran Baba Sale ne ya ɓaci, amma da ya tuna Ɗan Bishir ya zo nemarwa abinci sai ya wayance.

"Labaran kenan, yanzu dai duk ba wannan ba. Wallahi Ɗan Bishir ne yake son cin abincin Rahina, saboda zaƙin girkinta kasan na daban ne."
Tun Baba Sale bai gama magana ba Labaran ya hau huci, rai a ɓace ya ce.
"Allah Ya isa, wallahi ba zan yafe maka ba, da wannan yabon. Yanzu saboda Allah abincin Rahina ne wani zindiƙin sankacecen ƙato yake yabawa haka?"
Zuciya ta fara ciwo Baba Sale ya ce, "Kai Labaran kada ka faɗa mini maganar banza da wofi, ban da aska da tasha jinin Ɗan Bishir ka isa na tako wurinka neman abinci ne? Ka faɗa mini ko nawa ne zan biya ka, ka sayar mini abincin nata."

Labaran ya buga tsalle kamar mai shirin tashi sama, saboda yadda kishi ya tirniƙe shi ya ce.
"Ba askar kaciya ba Allah Ya sa abba-tuwa ce a kansa, wallahi ba zai ci abincin Rahina ba. Yanzu ni kake kallo ka ce na sayar maka da abincin Rahina? Ko kasan sayar maka da abincin nan daidai yake da na sayar maka da wani tsagi na daga baiwar da Allah ya ba ta?"
Haush ya sake mamaye Baba Sale sai kawai ya zuciya zai faɗa gidan, da sauri Labaran ya suri wani ƙaton itace. Ganin haka ya sa Baba Sale ya fice, shi kuma ya rufa masa baya yana faɗin.

"Jama'a ku tare ga baƙin kwarto mai lasisi nan."
Baba Sale yana faɗawa cikin gida ya danno ƙofar ya saka sakata, Labaran ya yi bugun duniya bai buɗe masa ba.

Ganin yadda Mahmud ya yi zuru yana nazari ya sa Mudassir ya taɓo shi ya ce.
"Wai me yake faruwa ne?"
Mahmud ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Wallahi Mudassir na haɗu da wani iftila'i a cikin wannan ƙauyen, ina cikin damuwa kuwa matuƙar Mai gari ya gano ni."
Mudassir ya bi shi da kallon mamaki don a iya saninsa da Mahmud, wannan ne zuwansa garin na farko, saboda har yana kan hanya shi ya dinga yi masa kwatance. A tsorace Mahmud ya kwashe duk abin da ya faru tsakaninsa da Laraba ya ba shi labari, tun bai rufe baki ba Mudassir ya dinga sheƙa masa dariyar ƙeta. Haushi ne ya kama shi, ya dube shi rai a ɓace ya ce.

"Ka ma mayar da ni ɗan iska wato ga mahaukaci ko?"
Cikin dariya Mudassir ya girgiza masa kai ya ce, "Wallahi a garin wannan tsoron naka watarana sai ka halaka kanka. Yanzu kai Mahmud aljanu ne za su kai ka su baro? An ma kuwa aljanar gaske ce? Ace aljanu su nemi ya yanka musu zabi su tafi da su? Gaskiya akwai ayar tambaya."
Jiki a sanyaye Mahmud ya ce.

"Wallahi a wannan dajin ba na jin za a samu bil'adama a cikinsa, kai ganin idona na fahimci ba mutum ba ce. Yanzu tun da ka ce dole mu gabatar da kanmu wurin mai gari sai dai ka wakilce mu."

"Kai ka san yadda mutanen ƙauye suka ɗauki mai gari kuwa? Ai dole sai mun haɗu mun gabatar da kanmu ya san da zamanmu a garinsa, wallahi yadda ka ci ubansa shi ma haka zai ci na ka idan ya gano ka."
Mudassir ya furta yana gimtse dariyarsa.
Wata dabara ce ta faɗo wa Mahmud ya saki murmushi a fili ya ce. "Mu je gidan da ka ce za mu sauka, na san yadda zan yi da su."
Mudassir ya shiga kwatanta masa hanyar, suka sauya akalar hanyar zuwa wani ɗan madaidaicin gida mai ɗaki biyu wanda babu kowa a cikinsa.
Mudassir ne ya ɗauko mukulli ya buɗe musu ƙofar suka shiga da kayansu, a kan wani ɗan ƙanƙanin gas da Mahmud ya taho musu da shi suka ɗora ruwan wanka. Sai da suka yi wanka suka sha ruwan tea da Mudassir ya dafa musu, sannan ya ce su

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login