Showing 84001 words to 87000 words out of 94348 words

Chapter 29 - GIDAN LIKITOCI BOOK COMPLETE BY AMEERA ADAM.txt

29 Sep 2025

845

sa Jafar ya kwantar da ita a jikinsa ya sa hannu ya fara bubbuga bayanta, nan take idanunsa suka yi jawur saboda ɓacin rai. Ya dubi mutumin murya a dashe ya furta.
"Ka san wa ka taɓa kuwa? Ka san wanne irin kuskure kake yunƙurin aikatawa. Wallahi sai na nuna maka bakin rijiya ba wurin wasan makaho ba ne." Jafar ya ƙarasa maganar yana yunƙurin cire Uwani daga jikinsa, cikin kuka Uwani ta furta. "Tsoro nake ji Ya Jafar don Allah kada ka sake tafiya."

Ajiyar zuciya Jafar ya sauke ya riƙe hannunta suka fara tafiya rai a ɓace, ganin haka ya sa Alhajin ya zuba a guje ya faɗa ɗakinsa ya datse ƙofa. Ɗakinsu suka wuce sai da Jafar ya sa key ya buɗe suka shiga, ya kai ta kan kujera ya zaunar da ita sannan ya ce. "Ki jira ji yanzu zan dawo." Fuska da hawaye Uwani ta furta.

"Ya Jafar kada ka tafi ya shigo mini."
Sunkuyawa ya yi daidai fuskarta ya ɗan hura mata iska ya furta.
"Ba abin da zai faru da ke yanzu zan dawo kin ji." A hankali Uwani ta gyaɗa masa kai sannan ya fice.

Ɗakin Alhajin ya koma ya yi bugun duniya ya ƙi buɗewa, shi kuwa Alhaji tumbin kuɗi jin ana buga ƙofar ɗakin abokinsa da ƙarfi, ya sa ya ƙara wa tashi ƙofar key sannan ya wuce banɗaki a guje jiki na rawa ya ɓuya.

Ganin ba shi da niyyar buɗewa ya sa Jafar ya zaro waya ya danna lambar DPO ɗin unguwar Zoo road, da yake abokinsa ne. Nan take ya sanar da shi abin da ya faru tsakanin Uwani da Alhajin. Sannan Jafar ya sauka ƙasa ya sanar da ma'aikatan reception abin da yake faruwa da kuma ɗakin da Alhajin yake ciki. Wata mata da ke gefe nan take ta furta.

"Kai malam Allah Ya yi maka albarka. Wallahi ni ma jiya da dare na ɗan fita unguwa na dawo haka wani ya dinga mini ɗan kira, da na shiga ɗaki har buga mini ƙofa ya yi ƙila ma shi ne." Jafar ya furzar da iska mai zafi ya ce. "Daga yau ai ba zai ƙara ba."

"A toh ai wasu mutanen gani suke idan suka ga mutum ya kama hotel kowa ma ɗan iska ne, Allah Ya kyauta."

Ba a ɗauki lokaci ba sai ga motar 'yan sanda ta ƙaraso, lokacin da suka je bakin ƙofar Alhaji sai da ƙyar ya buɗe musu ƙofa. Har ƙasa ya tsugunna yana ba wa Jafar haƙuri amma fir ya ƙi sauraronsa, yaran D.P.O bayan sun saka masa ankwa Jafar ya ce su wuce da shi zai zo daga baya.

A wurin da ya bar Uwani a nan ya koma ya same ta, fuskarta ta kumbura saboda kuka. Tana ganinsa ta yi zumbur! Ta miƙe tsaye. Bai kula ta ba ya koma can gefen gado ya zauna ya dafe kansa, wani irin ɗaci yake ji a maƙoshinsa ya ɗago murya can ƙasa ya ce.

"Ya aka yi mutumin nan ya biyo ki ke da na bar ki a ɗaki?" Zuciyar Uwani ɗaya ta fara masa jawabi.
"Ni fa kasan ƙafata ba ta saba zaman wuri ɗaya ba, gajiya na yi da zama shi ne na fita can ƙasa na sha iska. Da na dawo sai na rasa ɗakin nan, bisa tsautsayi na faɗa ɗakin wani ɗan iska..." Uwani ta kwashe komai ta gaya masa amma ba ta gaya masa irin azabar da ta yi wa Alhaji tumbin kuɗi ba, ta dai ce masa Allah ne ya ƙwato ta bayan ta fito wannan Alhajin ya biyo ta.

Tass! tass! Jafar ya sauke wa Uwani wasu tagwayen mari biyu a fuska, cikin ɓacin rai ya furta. "Uban waye ya ce ki fita? Ba ki da hankali za ki fita da waɗannan kayan?" Ganin yadda Jafar ya hargitse mata lokaci ya sa nan take jikinta ya fara karkarwa, ya rufe ta da faɗa tamkar zai rife ta da duka daga ƙarshe ya faɗa toilet ya bar ta a zaune. Bai jima ba ya fito har lokacin ransa a ɓace yake ya furta.

"Ki shiga ki yi wanka za mu wuce gida yanzu." Zani uwani ta ɗauka ta faɗa ban ɗaki kafin ta fito har Jafar ya gama shiryawa, gefe da gefen fuskar Uwani har ya ɗan kumbura don har lokacin ba ta daina hawaye ba.

Jafar na zaune a gefen gado ya hango Uwani ta fito don ita ta manta ko hula ma ba ta saka ba, a razane yake bin ta da kallo baki sake. Ganin irin kallon da Jafar yake bin ta da shi ya sa Uwata ta sha jinin jikinta, tana sake tunkaro shi Jafar ya zabura a guje ya nufi ƙofa yana faɗin.
"Wayyo Allah! Jama'a ku taimaka mini sun biyo ni nan ma!" Da yake ya manta ya datse ƙofar haka ya yi ta murɗawa ta ƙi buɗuwa. Cikin rashin fahimta Uwani ta ɗan waiga ta ce.
"Wai ya Jafar me yake faruwa ne?" Laƙwas Jafar ya yi ya zauna a ƙasa kamar mutum-mutumi yana kare mata kallon, tamkar ya ga sabuwar hallita. Uwani ta shiga goge kanta da towel ko a jikinta ta ce. "Malam ka fita zan shirya."

Har lokacin Jafar mamakin Uwani yake, ya shiga tariyo abin da ya dinga faruwa a cikin dare. Uwani ta fahimci sarai in da Jafar ya dosa, ta fito da kayan da za ta saka ta sake furta. "Don Allah ka fita zan shirya."

"Uwani ina gashinki?" Cikin halin ko in kula ta ce. "Dada ta aske mini tun rannan."

Miƙewa ya yi ya tako gabanta sannan ya furta. "Wato iskanci ne ya sa kika dinga tsora ta ni ko? Wallahi za ki shiga hannuna da ni kike zancen." Take dariyar da Uwani ke gimtsewa ta suɓuce mata. Jafar ya saki wani malalacin murmushin mugunta yana ayyana irin azabar da zai yi mata cikin ruwan sanyi ba tare da Daddy ya gane ba. Daga haka Jafar ya fice daga ɗakin, Uwani ta saka kayanta sannan ta haɗa ragowar kayanta da ke warwatse ta saka a jaka.

Ba su ɗauki lokaci ba suka shirya suka fito Jafar ya ƙarasa gaban ma'aikatan da ke reception ya biya duk abin da ya suka kashe, sannan ya yi musu sallama suka fita da yake akwai Manajan wurin da shi a ka kai Alhaji can police station. Domin a cewar Manajan Alhajin na ƙarƙashin kulawarsu dole ne su san halin da yake ciki.

Lokacin da su Uwani suka ƙarasa gida mommy ta rako ƙawarta Hajiya Binta bakin gate, ganin su Uwani ya sa Mami ta yi turus tana faɗin.

"Ya aka yi Jafar?" Jafar ya ɗan sosai, sannan ya gaida Hajiya Binta da ke bin sa da kallon tuhuma.

"Ƙawata wai kar dai raɗe-raɗin da nake ji a kan auren Jafar haka ne?" Hajiya Binta ta tambaya tana satar kallon Uwani. Ras! Gaban Mami ya faɗi, ta ɗan basar tana ƙirƙiro murmushin yaƙe ta ce. "Haba Hajiya Binta kina ganin akwai yarinyar da Jafar zai aura a duniyar nan bayan Safna? Ai me aiki ce ya taho mini da ita daga Lagos, a bakin gada take kwana shi ne ta roƙe shi Allah-Annabi wai ta dinga yi masa aiki. Da ya sanar da ni na ce idan zai taho ya kawo mini ita, kin san ɗa na kowa ne ƙawata." Cikin gamsuwa Hajiya Binta ta bi Uwani da wulaƙantaccen kallo ta furta.

"Ban da taɓarɓarewar zamani yanzu wannan yarinyar har ta isa kwanan gada, mtsww Allah Ya sawaƙe." Mami ta furta. "Amin dai, yo yaran da maza ke ba su ɗari biyar suna sa su a ɗaki ina za ki yi mamaki?" Kalaman Mami da ƙarshe da ta jefi Uwani da su ba ƙaramin zafi suka yi masa ba, don haka ko sallama bai yi wa Hajiya Binta ba ya wuce. Ita kanta Uwani kusan daskarewa ta yi a wurin jin irin munanan kalaman da Mami ta jefe ta da shi, tunanin da ta zurfafa ciki ne ya sa Jafar ya wuce ba tare da ta sani ba. A ɗan tsawace Mami ta ce.
"Tsawar me kike yi a gabanmu ne?" Babu yadda ta iya haka Uwani ta ja jaka jiki a sanyaye ta wuce ciki, kai tsaye sashensu ta shiga idanunta cike da ƙwallah.

Sanin Daddy ba ya gidan ya sa Mami kai tsaye ta wuce sashen su Jafar, a falo ta same su duka ta dubi Jafar ta ce.
"Wai fasa tafiyar ka yi ne Jafar?" Bai ɗago ya kalle ya ba ya furta, "Eh Mami." Jim ta yi tana nazartarsa ta furta.

"To haka za ka zauna ana tsorata ka har a sabauta mini kai?" Jafar ya furta. "Ai na biya ta Islama Islamic Center na karɓo magani, kuma ya ce mini za a dace In shaa Allah." Jafar shi kansa ya yi mamaki yadda ya tsara wa Mami wannan jawabin, Mami ta wurga wa Uwani mugun kallo ta ce.
"Wuce mu je akwai aikin da za ki yi mini." Babu musu Uwani ta bi bayan Mami, Jafar ya kwanta a kan doguwar kujewa. Haka kawai ya ji yana kewar Safna, don haka ya zaro waya ya kira ta suka fara hira.

Mami na shiga sashensu ta haɗo wa Uwani wanki duk da a lokacin magriba ta fara kawo kai, bayan gida ta zuba mata wankin ta yadda koda an yi a arashi Daddy ya dawo ba zai ganta ba ballanta ya yi mata faɗa. Kuma dama ta san ba ya gari, don haka za ta ci karenta babu babbaka akan Uwanin.
Cikin wankin da Mami ta haɗo wa Uwani har da labulaye da zannuwan gado, tun Uwani na wankin cikin daɗin rai har ta fara galabaita tun da ko a wurin Dada ba ita take yin wankin kayanta ba. Lokacin da aka kira sallar magriba Uwani wucewa ta yi sashenta don ya gabatar da sallah, tafiyarta babu jimawa Mami ta zagaya ta ga wurin wayam. Sai tsirarin kayan da ta shanya ga waɗansu nan a cikin ruwa.

Uwani na zaune tana zaman tahiya Jafar ya shiga ya zaune yana kallonta, a yadda ya lura da Uwani duk hatsabibanci da ƙiriniyarta ba ta wasa da sallah ko kaɗan. Hakan ba ƙaramin birge shi yake ba, yana nan zaune Mami ta shigo ko shi ba ta yi wa magana ba ta rufe Uwani da duka. Ganin dukan da take wa Uwani ba zai ƙare ba ya sa Jafar ya yi saurin shan gaban ta.

"Lafiya kuwa Mami? Me ta yi miki haka?" Jafar ya furta hankali a tashe.

"Lallai Jafar wannan abar har kake tarewa?" Mami ta faɗa tana sauke numfashi.

Ban da kuka babu abin da Uwani take yi, ga gefen bakinta ya fashe jini na ɗiga. Saboda yadda ta galabaita kukan da take yi ko fita ba ya yi, Mami ta sake zuba mata ranƙwashi a ka tana shirin yin magana Jafar ya ce. "Mami wai me ta yi miki?"

"Wanki na saka ta don iskanci za ta zube mini ta zo ta saka miji a gaba, idan uwarki ce ta saka ki za ki ajiye mata." Mami ta yi maganar tana dungurin Uwani, cikin kuka Uwani ta ce. "Sallah aka kira shi ne na zo na yi..." Da sauri Mami ta sake doke Uwani nan take bakinta ya sake fashewa.

"Haba Mami, ina ce Haladu ne yake yin wanki. Kuma sallah fa ta ce ta zo..." Tas! Mami ta ɗauke Jafar da mari, ba ta tanka masa ba ta figi hijabin Uwani ta fara janta a ƙasa, ba shiri Uwani ta miƙe ta bi Mami. Saboda ɓacin rai tun ba su gama fita ba Jafar ya gegare su ya fice daga gidan zuciyarsa na suya.

"Iyeee Allah Jafar watsa mini ƙasa za ka yi a ido yaushe har ka san zafin mace. Wallahi dole kai ma na ɗauki mataki a kanka." Mami ta yi maganar a ɗan tsorace don ta yi tsammanin ko wuta za ta jefa Uwani sai dai Jafar ya taya ta ba dai ya hana ba.

A cikin duhu ga sauro haka Uwani ta wanke ragowar kayan da ba ta ƙarasa ba, kanta ban da ciwo babu abin da yake yi. Bayan ta gama ne ta nufi sashen Mami har ƙasa ta zube ta furta. "Na gama wankin." A yamutse Mami ta dube ta tana shirin sallamarta Shukra ta shiga ɗakin tana taunar cingam ta ce. "Ke zan saka ki aiki yanzu saura ki yi mini hauka." Uwani ta ɗaga kai a galabaice ta amsa wa Shukra. Auta da ke zaune a gefe duk sai ta ji babu daɗi, tana son ta yi magana amma tana tsoron faɗan Mami.

"Kina ji Shukra na yi miki magana ba za ki iya amsawa ba?" Mami ta yi maganar tana haurin Uwani. Sai da ta goge ƙwallar idonta sannan ta rarrafa gaban Shukra ta tsugunna.

"Ga Salim nan ya faka motarsa a cikin gate, za ki je ki wanke masa kuma wallahi idan ba ta wanku ba sai kin sake." Da sauri Auta ta furta. "Aunty Shukra wankin mota fa?"

Shukra ta sake shan kunu ta ce, "Waya na yi da shi zai kai wankin mota ya ce ba zai samu zuwa yau ba, so don haka na ce ya zo gida za a wanke masa saboda ina son magana da shi." Cikin tausaya Auta ta ce, "To shi kenan zan ta ya ki Uwani..."

"Waye ya gayyace ki? Uwar iyayi da kankanba?" Mami ta katse Auta.

Shukra ce ta yi gaba Uwani ta bi bayanta a lokacin zazzaɓi har ya fara rufe ta, lokacin da suka ƙarasa Salim na cikin mota. Da ya hango su ne ya fito yana sakarwa Shukra murmushi.

"You are welcome dear." Shukra ta furta tana fari da ido.

"Beb an ya zan iya jiran sati ukun nan masu zuwa kuwa? Kin ga yadda kika yi kyau." Salim ya furta cikin shauƙin soyayya, Shukra ba ƙaramin daɗi ta ji ba kin kissa ta ce.

"Well mu je mu zauna, ga 'yar aikin Mami za ta wanke maka mota."
"Za ta iya kuwa Baby? Na ga mata ba sa wankin mota." Salim ya faɗa yana bin Uwani da ke rakaɓe a gefe. Shukra ta dubi Uwani a tsawace ta ce. "Ke ba ki iya gaisuwa ba ne?" Jikin Uwani na rawa ta tsugunna ta gaishe da Salim, sannan Shukra ta ɗan yi murmushi ta furta.

"Ai in gaya maka daga motar Daddy har ta ya Jafar ita take wankewa za ka sha mamaki." Shukra da Salim suka wuce wurin wasu fararen kujeru, daga wurin da suke zauna suna iya hango Uwani da duk abin da take yi.

Sai da ta goge ƙwallar idonta sannan ta ɗauki bokiti ta fara ɗebo ruwa, da yake wurin ɗiban ruwan yana da ɗan nisa da wurin wankin motar a galabaice ta fara wankin motar har ta gama.

Gaban Shukra Uwani ta je ta tsaya ta ce, "Na gama wankewa." Shukra ta bi ta da harara sannan ta ce.
"Matso nan."
Ba musu Uwani ta matsa gaban Shukra, da ƙarfin tsiya ta fisgo Uwani har sai da ta bugu da ɗan ƙaramin table ɗin da ke gabansu ta ce.
"Don ubanki ke ba ki da ladabi ba za ki iya tsugunnawa ba?" Shukra ta ƙarasa maganar tana zuba wa Uwani ranƙwashi.

"Haba Beb da kin ƙyale ta kin san irin yaran nan ba wani tarbiyya suke samu ba, so don sun yi haka ni ba zan yi mamaki ba." Salim ya faɗa a ɗan ƙyamace yana duban Uwani da ta gama jiƙe wa da ruwa sharkaf.

"Dallah tashi ki ba ni wuri kina tafe da baƙi kamar na zunubi." Dariya sosai Salim ya yi jin abin da Shukra ta faɗa ya furta. "Wai yaushe kika koyi masifa ne love?"

"Haba ka rabu da ni na tsani yarinyar nan wallahi." Uwani na laɓe a ta bayan fulawiyin da ke zagaye da harabar gidan, takaici ya mamaye zuciyarta. Wani tunani ne ya faɗo mata don haka da sauri ta zagaya can bayan gidan, ta ɗebo irin manyan bokitan fentin nan guda biyu waɗanda ta gama wanki da su. Sai da ta yagi wata igiya ta haɗa hannuwansu ta ɗaure, sannan ta saki murmushin mugunta. Cikin sanɗa ta fara tafiya ta cikin fulawoyi, a daidai bayan su Shukra ta tsaya ta ji Salim yana faɗin.

"Haba ke dai Baby ba kya mantuwa, wannan fa mahaukacin ma shammatata kawai ya yi amma yadda nake ƙaunarki akwai abin da zan ga zai cutar da ke na gudu ban taimaki rayuwata ba, ke ce fa rayuwata ke ni fa idan za ki rayu da farinciki zan iya sadaukar da komai ciki kuwa har da numfashin da nake zuƙa." Shukra ta rangwaɗa kai cikin farinciki, tana shirin ba shi amsa Uwani ta saki murmushi duk da zazzaɓin da ke jikinta. Sai da ta daidaita saitin kansu sannan ta ɗaga bokitan fentin hannunta, ta kifa musu a kansu ta saka iya ƙarfinta ta danne saman ta yadda ba za su iya fisgewa ba. Salim da abin ya haɗe masa biyu ga zafin hula ga na bokiti ya ware murya cikin ihu ya ce. "Wayyo Allah wuyana!"

"Wayyo kaina, Baby kana ina!" Shukra ta faɗa a ɗimauce. Daga Salim har ita sai ɗaga hannuwa suke cikin neman taimako. Sai da Uwani ta ga sun fara galabaita sannan ta fisgo hannun bokitin ta baya, da yake ƙafafuwansu na ƙasan table ɗin da ke gabansu faɗuwar da za su yi ta baya sai suka taho da table ɗin da ƙafafuwansu. Uwani na ganin za su kai ƙasa ta yi saurin matsawa a guje, sai ji kake rugugum! kacacar kofuna da ruwan jarkar duka sun watso kansu. Ga bokiti ya sarƙafe su ga kuma ƙafafuwasu sarƙafe a cikin table, Uwani ta laɓe a cikin shukoki

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login