Showing 39001 words to 42000 words out of 94348 words
Chapter 14 - GIDAN LIKITOCI BOOK COMPLETE BY AMEERA ADAM.txt
yin haka ba, kada ko wani abin ne ya same shi a ɓanɗakin ba ta sani ba.
"Mai gida lafiya kake kuka a banɗaki?"
Indo ta yi maganar bayan ta samu Yaya Inu har lokacin a tsugunne.
"Indo na haɗu da wani iftila'i, wallahi ina cikin tashin hankali komai ya canza mini, al'amarin ya munana."
Muryar Yaya Inu kaɗai da ta ji ce ta tabbatar mata da tabbas babu lafiya, ta sauke ajiyar zuciya ta ce.
"Me ya faru dai yanzu?"
Yaya Inu ya zauna a kan wani ɗan dandamali da suke zama su yi wanka, ya dubi Indo da shanyayyun idanunsa da suka yi mitsi-mitsi saboda kukan da ya sha ya ce.
"Ku je ku kori yara ɗaki, ki kira mini su Hansatu ku mayar da ni ɗakina. Saboda su kansu jijiyoyin ƙafafuwana sun yi sanyi, ji nake kamar da na wani aka zuba mini ba nawa ba."
Jin haka ya sake ɗaga hankalin Indo, ta ja ƙafafuwa jiki a sanyaye ta samu Hansatu da ke ɗinkin mahuci ta furta.
"Mai gida fa babu lafiya Hansatu."
Da yake har lokacin Hansatu cike take da haushin Yaya Inu, kai tsaye ta ce. "Allah Ya sawaƙe, kowa ma fama yaka da rashin lafiya."
"Wannan fa ba irin rashin lafiyar yau da gobe ba ce, don ya ce a tura yara ɗaki mu je mu ɗauke shi mu mayar da shi ɗakinsa."
Furucin Indo ya sa Hansatu zaro ido, a razane ta ce. "Shi Mai gidan za mu ɗauka mu kai ɗaki? Innalillahi wa inna'ilahir raji'un!"
Da sauri Hansatu ta miƙe, kowacce ta shiga ƙoƙarin tura yaranta ɗaki. Kafin wani lokaci tuni yaran sun shige ciki, Hansatu ce a kan gaba sauran suna biye da ita. A inda Indo ta bar Yaya Inu, a can suka koma suka same shi. Yana zaune ya haɗa kai da gwiwa. Abin da ya sake ɗaga hankalin matan nasa, ganin hawaye shaɓe-shaɓe a fuskarsa yana ambaliya.
"Mai gida! Wai me yake faruwa haka?"
Hansatu ta jefa masa tambaya a rikice, Yaya Inu da muryarsa ta shaƙe can ciki ya ce.
"Ku yi tara-tara ku kai ni ɗaki. "
Da yake Yaya Inu ba mutum ne mai ƙiba ba, ya sa su ukun suka haɗu suka ɗaga shii suka yi ɗaki da shi suka kwantar a katifa. Zani suka janyo suka rufe masa jikinsa, suka yi carko-carko kowacce tana saƙa da warwara a cikin ranta.
"Ɗazu gabanin zan shigo gida na haɗu da wani matsiyacin mai magani, bayan na saya ya ce mini na shafawa ne. Ina shafawa kun ga abin da ya faru!"
Yaya Inu ya ƙarasa maganar yana bankaɗe zanin rufar da suka rufa masa, wannan karon hankalinsa ya fi tashi don ya lura da ci bayan da yake ta samu a jikinsa.
"Innalillahi! Malam mene ne haka a tsotse kamar hanjin ligidi? Wannan wane irin magani ne haka ka shafa?"
Hansatu ta faɗa a ruɗe.
Indo ta jinjina kai ta ce, "Gaskiya wannan abin akwai ayar tambaya, amma babu lambar waya a jiki da sai ka kira shi."
Yaya Inu ya yi zaraf ya ciro robar maganin, cikin sa'a ya ci karo da lambar mai maganin. Yana kira bugu biyu ta yi ya ɗauka, nan take ya zayyane masa duk abin da ya faru. Daga can ɓangaren ya ce.
"Allah sarki Mai gida, na manta ai tun farko ban yi maka wannan bayanin ba. Amma kada ka damu wannan ba komai ba ne, dama a rana ta farko dole za ka fuskanci haka. Amma zuwa gobe war haka komai zai dawo daidai."
Yaya Inu da kamar zai yi kuka ya ce. "Yanzu har sai na kai gobe war haka? Yanzu fa ƙarfe takwas na dare, haka zan yi ta zama a zuƙe?"
"Wannan ba wani abu ba ne, idan har maganin ya game duk jikinka, muna nan da kai sai ka nemo ni ka kawo mini kwastoma saboda kyawunsa."
Kalaman mai maganin kenan da suka ɗan ƙara wa Yaya Inu ƙwarin giwa.
Larai da ke riƙe da haɓa ta jinjina kai ta ce, "Magana ta gaskiya Mai gida lamarin nan fa ya ba ni mamaki, ba yau ka fara amfani da irin wannan maganin ba fa. Wallahi akwai dai magana, ka tuhumi tsakaninka da Ubangiji gaskiya."
Yaya Inu ya zaburo ya ce, "Ke Larai me kike nufi?"
Larai ta murguɗe baki gefe ta yi ƙasa da murya ta ce, "A'a toh, ga dai abu ya bayyana nan tun da har ka haifo zabiya. Ƙila fushin da Allah Yake yi da kai ne ya jarabce ka ta wurin, ba sai a ga ta saɓon Allah ba. Tun da Ubangiji da kansa Ya yi hani da kusantar mace tana cikin jini..."
"Na rantse da Allah zancanki yana hanya Larai, kai duniya jama'a akwai darussa a rayuwar nan fa."
Indo ta furta tana jinjina buwayar Ubangiji.
Kalaman su Larai ba ƙaramin ɗaga hankalin Yaya Inu ya yi ba, yana daga kwance ya tashi zaune ƙirjinsa yana bugawa ya ce.
"Na rantse da girman Allah ban taɓa aikatawa ba, Allah ne shaidata. Na shiga uku Hansatu ku taimaka mini, wallahi ina cikin wani yanayi."
Larai ta yi hanyar waje ta ce, "Wallahi Mai gida ni kam a yanzu ma tsoron taɓa ka nake yi, kada na je ni ma wata hallitar tawa ta tsotse." Daga haka ta yi ficewarta.
Kuka Yaya Inu yake iya ƙarfinsa, ya janyo zanin Hansatu yana ɗago mata hannu. Ba ƙaramin tausayi ya ba ta ba, saboda duk abin da zai saka Yaya Inu kuka ba ƙaramin tashin hankali ba ne.
A sanyaye Hansatu ta zauna ta ce, "Mai gida! Yanzu mene ne abin yi?"
Yaya Inu ya wara mata hannu alamar ba shi da mafita ya furta, "Sai abin da kika ce Hansatu."
Indo ta gimtse dariya ta yi ficewarta, don ita ma a wani ɓangaren ya fara ba ta tsoro.
"A'a kai ne mai faɗa aji ai, tun da kai rana ta ƙwacewa. Laifi dai ka riga da ka aikata, kawai dai ka yi ta isgifari. Sannan sai mu zuba wa sarautar Allah ido, zuwa washegari kamar yadda Mai maganin ya faɗa."
Wata sabuwar soyayyar Hansatu ta mamaye shi, ya riƙo hannunta ya ce. "Hansatu dama haka kike sona, ke kaɗai ce ba ki guje ni ba a cikinsu."
Hansatu ta yi wa Yaya Inu ƙuri da ido, tana tuna soyayyarsu tun ta saurayi da budurwa. Sannan ta tuna irin cin kashin da yake yi musu, musamman na ranar ta ce.
"Ai wannan kalaman da kake faɗa na fatar baki ne ranka shi daɗe, mu da ka ce fuskokinmu kamar na sumammun birarrika? A'a za ka yi aure ai, ni ma abin da ya sa ka ga na tsaya a kanka, ina duba darajar da ka ba ni a cikin matanka da ba ka taɓa sakina ba. Tun da ni ma ka mutumta ni a matsayina na uwar gida."
Shiru Yaya Inu ya yi kunya ta lulluɓe shi, Hansatu ta cigaba ɗebe masa kewa sai da ta fara jin bacci sannan ta wuce ɗakinta. Dai-dai da abincin dare Yaya Inu da ƙyar ya iya ci, haka ya kwana cikin tunani da bacci mara daɗi yana miyagun mafarkai kala-kala.
Lokacin da su Uwale suka samu labarin abin da ya faru ba ƙaramin tashin hankali ta shiga ba, abin sai ya haɗe mata goma da ashirin ga halin da Ɗan Bishir yake ciki, da zargin da ake yi ya kwashi cuta mai karya garkuwar jiki ga kuma halin da mijinta yake ciki. Da yake dawowar Baba Ibrahim kenan daga wurin aiki, ko gidan bai shiga ba ya ce wa Uwale ta koma shi zai je ya ji abin da yake faruwa. Kai tsaye ƙaramin asibitin gwamnati ƙauyen nasu ya wuce, a can ya samu Baba Sale ana yi masa ƙarin ruwa . Da yake an yi masa allurar bacci sai ya zauna a gefensa yana jiran tashinsa. Kusan zaman awa guda Baba Ibrahim ya yi, sannan Baba Sale ya buɗe idonsa.
"Sannu Sale, ya jikin naka?"
Baba Sale ya tashi zaune yana dafe kansa da ya yi masa nauyi, ya dubi Baba Ibrahim murya tana rawa ya ce. "Yaya ka ji abin da ya faru ko?"
Ya gyaɗa masa kai ya ce, "Sale ina son ka saurare ni da kyau don Allah. Na farko dai kai musulmi ne, ka yarda da ƙaddara mai kyau da akasinta. Sannan ka san Ubangiji ne ya ba ka Ɗan Bishir, a lokacin da ba ka yi tsammani ba. Don haka kenan ko a yau Allah Ya yi niyyar ɗauke abinsa zai iya. To me zai sa ka kashe kanka a banza da wofi, ko ka janyo wa kanka ciwo ya kwantar da kai. Lokacin da na zo likitoci sun tabbatar mini ko a asibitin nan ka yi suma ya fi bakwai, don Allah ka kwantar da hankalinka. Yanzu ina son daga nan zan wuce na je na samu Bala Wanzan, da shi Idi Naira na ji yadda aka haihu a ragaya. Idan na ji ta bakinsu sai mu wuce asibiti ɗungurungum a yi haihuwa da hanji, amma babu yadda za a yi a dinga faɗar cuta da fatar baki ba tare da an tabbatar ba."
Da sauri Baba Sale ya riƙo hannunsa ya furta. "Yaya zan bi ka, gara a yi komai a kan idona."
Baba Ibrahim ya sake haɗai rai ya ce, "Idan ka san za ka yi mini hayaniya ko ka je kana sume-sume gara ka yi zamanka a nan."
Cikin sauri Baba Sale ya girgiza kai, Baba Ibrahim ya yi wa lokitocin bayani sannan ya biya su kuɗin ruwa da alluran da ake yi masa; suka wuce Police station.
Bayan sun gaisa Baba Ibrahim ya gabatar da kansa sannan ya ɗora da cewa.
"Yallaɓai zuwa na yi domin na ji kan zancen abin da ya faru, idan da yuwuwar zuwa asibiti a yanzu sai mu wuce gabaɗaya."
Sergent ɗin da ke tsaye ya buɗe wani file ya zaro takarda ya ce, "Alhaji wani mutum mai suna Malam Shehu mai doya shi ya kawo ƙarar Bala wanzan, yana tuhumarsa da cin zarafinsa bayan ya je ƙofar gidansa. Sannan laifin da Bala ya yi har da zagin ɗaya daga cikin ma'aikatanmu, abin da kuma ya sake dagula case ɗin zargin cutar HIV da ake yi wa Alhaji Idi Naira. Yanzu haka shi ma Idi ya kawo Malam Shehu wurinmu, a kan zargin yana ɓa ta masa suna da wannan cutar." Ajiyar zuciya Baba Ibrahim ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Yanzu za mu iya ganin Bala Wanzan ɗin?"
"Gaskiya sai dai zuwa gobe idan Allah Ya kai mu." Ɗansandan ya furta.
Babu yadda suka iya haka suka wuce gida, sai dai kaso talatin a cikin ɗari na damuwar Baba Sale ta ragu, saboda ya ji an ce Alhaji Idi Naira ya yi ƙarar Malam Shehu zai ɓata masa suna.
Mai Yasin tun da ya saka 'Yar gwal a idonsa soyayyarta ta dawo masa sabuwa fil a ransa, haka a ɓangare ɗaya kishinta ya mamaye shi, yana jin tsanar Ɗanladi a ransa don dai kawai yana shakkarsa ne. Yana daga ɗakinsa ya hango ta, ta nufi banɗaki da buta a hannu shi ma ya yi zaraf ya ɗauki buta ya rufa mata baya. Tana shiga banɗaki za ta turo ƙofa ta ji mutum yana ƙoƙarin turowa, suna haɗa ido ta saki murmushi irin na 'yan bariki ta ce.
"Mai Yasin namu, ashe a wannan lungun ka lafe?"
Mai Yasin ya riƙo hannunta ya ce, "Ga ni kuwa kin gani, wai dama 'Yar gwal za ki iya auren wani namijin ba ni ba?"
'Lallai wannan gafalallan tsohon naka wasa ne.' Ta raya a ranta, amma a fili sai ta ce.
"Ka da ka sake kallona a matsayin matar aure, saboda wannan auren nawa shi da babu duk ɗaya. 'Yar gwal ta auri Ɗanladi ne domin ta yi masa tatsar mai, idan ta kwashe albarkar aljihunsa sai ta ƙara gaba."
"Sai da ke 'Yar kunama!"
Mai Yasin ya yi maganar yana dariya, sannan ya yi ƙasa da murya ya ce. "Yanzu ni ya za ki yi da ni?"
"A'a ka ji da tsohuwar da ka samu, idan fa muka bari suka san alaƙarmu na rantse da Allah ni da kai sai dai mu yi biyu-babu. Kawai mu cigaba da sabgarmu, kowa ya wawuri abin da ya wawura ko a fakaice ma dinga haɗuwa."
Guntun tsaki Mai Yasin ya ja, ya ce. "Wa yake ta wata tsohuwa? Ƙila dai a rashinki yau na waiwayi haƙƙina a wurinta."
'Yar gwal ta saki dariya, sannan ta ce ya yi maza ya tafi don kada wani ya gansu.
Bayan 'Yar gwal ta koma a tsakar gida ta ci karo da Laraba tana 'yar carafke, tana shiga ta ɗebo wankin rigunan mama da ɗan kamfai ta wurga mata a fuska. Tsaminsu haɗe da warin man bilicin ɗin da 'Yar gwal take shafawa ya bigi Laraba, ta ture su tana yamutsa fuska.
"Ke! Wanke mini su yanzu, ina son su fita sosai." Da mamki Laraba take kallon ta.
"Ko ba za ki wanke ba? Kika zubo mini ido irin na marasa tarbiyya kina kallo."
Laraba ta tashi ta ɗaga wani wargajejen ɗan kamfai, sai kawai ta tuntsire da dariya. Tun tana dariya a tsaye har ta tsugunna, ta janyo wata warɓeɓiyar rigar mama ta ɗago ta ta sake kwanciya tana dariya.
"Don uwarki dariya ma za ki yi mini? Wato ni za ki mayar 'yar iska?"
Laraba ta tsagaita da dariya tana ɗan tsuke fuska ta furta. "Kambu... Kada ki sake zagin uwata tana ƙasa, ki zagi kowa nawa ban ta uwata wallahi. Ehe, ba dole mutum ya yi dariya ba wannan ai ya isa na yi hijabi da shi."
"Rashin kunya za ki yi mini?" 'Yar gwal ta ƙarasa gaban Laraba a fusace. Laraba ta juya mata baya tana ɗago ɗankwalinta gaba ta ce.
"Faɗa wa ƙeya ɗankwali ya ba ki amsa 'yan mata."
Laraba tana juyowa 'Yar gwal ta wanke ta da mari, a hargitse Laraba ta ɗago za ta yi magana Ɗanladi ya ƙarasa yana faɗin.
"Kin yi mini daidai sanyin zuciyata, wato har yanzu kina nan da iskancinki ko Laraba? Maza wuce ki kwashe su ki wanke kada ranki ya ɓaci." Idon Laraba ya yi ja saboda ɓacin rai, ta harari 'Yar gwal a hankali ta ce.
"Allah Ya isa ban yafe..."
Tun ba ta gama magana ba, kamar haɗin baki Ɗanladi da 'Yar gwal suka make bakinta, nan take bakin ya fashe amma a dole ta kwashe kayan, ta fara wanki saboda yadda Ɗanladi ya ciro belt zai zane ta da shi. Sai da ta yi wa kayan ruwa kusan huɗu kowanne 'Yar gwal tana cewa bai wanku ba, sai a na biyar sannan suka bar Laraba ta fara shanya a lokacin har an fara kiran sallar isha'i.
Jin shirun Laraba ya yi yawa ya sa Inno ta fito daga sashenta, tana zuwa harabar ta ci karo da ita tana shanyar kaya su Ɗanladi suna tsaye a kanta.
"Laraba me kike yi haka da daren nan?"
Murya tana rawa Laraba ta ce, "Wanki."
Inno ta ƙanƙance ido ta ce, "Mene ne wannan kamar ɗan diras? Ke wuce ciki mu je."
Da sauri Laraba ta saki na hannunta ta wuce ciki, Inno ta dubi Ɗanladi rai a ɓace ta ce.
"Ba baiwa aka sayo muku ba, tun da ba ka da mutumci haka matarka ma ba ta gaji arziki ba wallahi ba za ku mori Laraba. Mun kwana a gida ɗaya, amma ban da mutumci da za ku zo ku gaishe ni." Inno ta wuce sashenta a zafafe.
Ran Laraba ya ɓaci sosai, ita kanta ta san a banza ma tana dafa mutum da ruwan jikinsa har ya nuna, ballantana sun taɓo ta da kansu. Don haka ta ci alwashin yadda suka azabtar da ita sai ta rama.
Tun da dare ya fara yi Laraba ta fara zarya, tana saka da warwarar abin da za ta aikata, tana wucewa ta ga 'Yar gwal a ƙofar ɗaki tana dama kunun gyaɗa. Da sauri ta faɗa ɗakin Inno, a can drower madubi ta buɗe ta ciro wani maganin hawan jinin Inno, mai saka bacci ta ɓallo guda takwas. A ƙa'ida Inno ɗaya take sha a wuni guda, kuma a hakan ma bacci yake saka ta sosai. Bayan jininta ya sauka ne aka sauya mata wani, don haka ta daina shansa. A cikin ƙaramar farar leda ta zuba su ta ɗebi ruwa kaɗan ta zuba, sai da ya narke sannan ta fita cikin sa'a kuwa ta ga 'Yar gwal ta shiga ɗaki. Da sauri ta matse maganin a cikin jug ɗin kunun, ta juya cikin sauri ta bar wurin. Tana laɓe a bakin ƙofar Inno tana leƙe ta ƙofa, ta ji lokacin da 'Yar gwal ta ɗauka ta shiga ɗaki. Zuciyar Laraba ƙal da haye katifa ta kwanta, tana shirya irin muguntar da za ta yi musu. A fili ta saki dariya, Inno ta wurga mata harara sannan ta ɗauki furar Mai Yasin ta nufi ɗakinsa.
Saboda Laraba ta taki mugunta haka ta zauna tunkur, har kusan ƙarfe ɗayan dare. Sai da ta fito cikin sanɗa zuwa ƙofar ɗakin Mai Yasin, ta kasa kunne ta ji munsharin Inno da Mai yasin sannan ta saɗaɗa ta fice daga sashensu ta isa ɗakin Ɗanladi. A yadda ta fahimta sun jima da yin bacci, don