Showing 45001 words to 48000 words out of 94348 words
Chapter 16 - GIDAN LIKITOCI BOOK COMPLETE BY AMEERA ADAM.txt
ji irin alamomin da na lissafa ba zai ce kai tsaye yana da cutar ba, har sai ya je asibiti an gwada shi kuma an tabbatar."
Jin furucin Baba Ibrahim ya sa Alhaji Idi Naira ya sauke ajiyar zuciya, Bala Ibrahim ya cigaba.
"Amma ita cutar farankama/ƙarambau (CHIKENPOX), ƙwayoyin virus na varicella-zoster ce take haifar da ita, cutar tana iya kama yara da manya. Kuma ana iya ɗaukarta ta hanyar shaƙar numfashin mai ɗauke da ita, cin abinci, makwanci ko wasanni tare.Tana saka ciwon ciki, zazzaɓi mai zafi, firgita, jajayen ƙuraje masu ɗurar ruwa, da matsanancin ƙaiƙayi. Mafita ɗaya ce a kiyaye haɗa mai cutar da wanda ba shi da ita, yin gaggawar zuwa asibiti domin bada agajin gaggawa. Killace mai fama da ita, da karɓar rigakafi."
Baba Ibrahim ya dubi Idi Naira ya furta, "Ka ga kenan babu alaƙa tsakanin cutar ƙanjamau da farankama Alhaji, amma duk ba wannan ba, yanzu ku tashi sai mu wuce asibiti gabaɗaya a yi muku gwajinta domin kowa ya fita daga zargin."
Cikin Alhaji Idi Naira ya ɗuri ruwa saboda shi kansa ba shi da tabbacin rashin cutar, sakamakon idan ya tafi Lagos har ya dawo da matan banza yake mu'amala. Ya haɗe fuska tamau ya ce. "Dakata Dr, babu inda zan je ni lafiyata ƙalau." Ganin borin kunyar da Idi Naira yake yi ya sa kowa ya aminta da tabbas biri ya yi kama da mutum, domin rashin gaskiya ya bayyana ɓaro-ɓaro a fuskar Alhaji Idi Naira.
Yaya Inu yana komawa gida daga wurin Zuly matashin kai ya samu Hansatu da Larai sun riƙo Salame ranga-ranga za su tafi da ita asibiti.
"Subhanallah! Hansatu lafiya?"
Yaya Inu ya furta a razane.
"Wallahi Mai gida jikin ne ya rikice ina jin haihuwar ce ta zo."
"Allah Ya ba ta lafiya, yanzu ina za ku kai ta?"
Kai tsaye hansatu a ce. "Asibiti, saboda jikin ya ba ni tsoro."
A gwasale Yaya Inu ya ce, "Yanzu haihuwar ce har sai kun yayime ta zuwa asibiti? A can ɗin rage mata zafin ciwon za su yi?" Haushi ya sa Hansatu ta yi gaba ba tare da ta kula shi ba. Shi ma daɗi ya ji saboda ya san ƙarshen zance a ce ya kawo wani abin.
Fadil ne ya ɗauke su a motarsa ya wuce da su asibitin ƙwararru na Malam Aminu Kano (AKTH). Kasancewar a can yake aiki, kai tsaye ɗakin haihuwa aka wuce da ita domin a duba ta. A gwaje-gwajen likitocin ne suka tabbatar da ba ciki ba ne, sai dai ba sa ganin komai a cikin nata. Hankali a tashe Hansatu ta kira Yaya Inu, a lokacin ya ci babbar rigarsa zai tafi ɗaurin aurensa.
"Mai gida akwai damuwa ciki dai na jikin Salame ashe ba ɗa ba ne."
"Mene ne idan ba ɗa ba? Hansatu kada ku janyo mini masifa a farar safiyar nan. Ni fa ba na son damuwa, yanzu haka ɗaurin aurena da Zuly zan tafi." Baƙin ciki ya sa ƙwalla ta zubo wa Hansatu a ƙufule ta ce, "Yanzu abin da za ka ce mini kenan? Mai gida kana nufin Zuly ta fi 'yarka Salame?"
"Hansatu kada ki ɓata mini rai, kin san dai jiya a yadda na kwana. Auran nan da za a ɗaura ne kawai yake ba ni ƙwarin gwiwa, har kika ga ina walwala. Ke bari na wuce kada ki ɓa ta mini lokaci, saboda matashin kai ta ce mini waliyinta wutar ciki gare shi zai iya tafiya idan na makara." Daga haka Yaya Inu ya katse, ya tura waya a aljihu ya rufe ɗakinsa sannan ya fice.
Yana kai kansa zai fita a ƙofar gida ya ci karo da Mai gari shi da su Sanƙira, cike da girmamawa mai gari ya russuna ya ce.
"Barka da fitowa!"
Hannuwa biyu Yaya Inu ya kai ya fara shafa idonsa, a ransa yana ayyana ko dai gizo idonsa ya yi yake nuna masa Mai gari ne yake tsugunna masa.
"Ranka ya daɗe ya haka kuma?"
Mai gari ya russuna ya ce, "Duk girmanka ne ai, ga wannan a rage da abincin yara."
Sanƙira shi da Muzammil, suka shiga kiciniyar sauke buhunhunan kayan abincin daga cikin kura sannan suka tafi. Mai gari har zai juya da sauri Yaya Inu ya tsayar da shi.
"Ranka shi daɗe ni fa ka saka ni a duhu, waɗannan ɗin na mene ne?"
Mai gari ya shafa kai ya ce, "A da dai ban yi niyyar sanar da kai yanzu ba, amma na ga kana neman ƙarin bayani ne Baba. Magana ta gaskiya Allah Ya jarabce ni da son Laraba, kuma aurenta nake son yi." Yaya Inu ya bayyana mamakinsa a fili, saboda duk cikin yaransa babu mai baƙin jini da samari ba sa kulawa kamar Laraba. Amma ganin irin rawar ƙafar da Mai gari yake yi masa, da tarin arzikin da zai samu ya sa ya ce.
"Idan ma yanzu a shirye kake, ka wuce mu je masallaci domin yanzu haka ni ma ɗaura mini aure za a yi!" Cike da shauƙi Mai gari ya ce, "A yi haka kuwa?"
Yaya Inu ya washe baki ya ce, "Me ya rage Mai gari? Ni ma ai an sauƙaƙa mini wannan bidi'ar wunin bikin, da mata za su zo su yi ta cinye abinci." Godiya sosai Mai gari ya yi, ya ce zai je ya sauya kayansa sannan ya ƙarasa. Hakan kuwa aka yi, Mai gari yana zuwa masallaci ana gama ɗaurin auren Yaya Inu da Zuly matashin kai. Yana zama ya miƙa wa Malam Liman sadaki ya zama waliyinsa, aka ɗaura aurensa da Laraba a kan sadaki naira dubu ɗari.
Fitar Yaya Inu daga gida babu jimawa Goggo ta ƙarasa, almajirai ne suka shiga da ƙullin kayanta. Inno tana hango ta, ta ƙarasa wurinta cikin farinciki ta rungume ta tana faɗin.
"Lale marhabun yau ga mutanen Jibiya." Goggo ta saki murmushi ta ce, "Ga mu Allah Ya kawo mu, wai ina Laraba ban ji motsinta ba?"
"Idan kika bibiya ta fita ta ɗauko mini magana, yarinya yadda kika san rainon ifiritu." Goggo ta saka dariya cike da zolaya ta ce, "Ni kam wai Inno hala yaron ciki gare ki? Irin wannan ƙyalli da kike yi haka."
Inno ta saki guntun tsaki ta furta, "Wuce mu je ku gaisa da Malam, kafin mu shiga ki fara zuba mini labari."
Tun shigar Goggo gidan da Mai Yasin ya ji muryarta, ƙirjinsa ne ya yi wata irin bugawa da ƙarfi. Haka kawai ya ji gabansa yana faɗuwa, jin muryar matar da ko a duniyar mafarki ba zai manta da ita ba.
Da sallama ɗauke a bakin Inno suka shiga ɗakin, Mai Yasin yana ɗaga ido karaf ya sauka a kan Goggo da ta daskare a wurin.
"Malam Jafaru! Dama tsawon shekaru a nan ka laƙe bayan ka halake mini dukiyar marayu? Allah na gode maka, tabbas addu'a ba ta faɗuwa ƙasa banza. Azzalumi maha'inci, ka ci amanata kuma ka tafi ka bar ni da ƙallagaggen aurenka a kaina."
Mai gari ya jima bai yi farincikin da yake ciki a wannan ranar ba, saboda mallakar Laraba da ya yi ji yake kamar ya mallaka faraincikin duniyarsa gabaɗaya. Yaya Inu ne ya sanar da shi tariyar Laraba, za ta kama sati mai zuwa saboda 'yan saye-sayen kayan ɗaki da za a yi mata.
Bayan sallar Isha'i Zuly matashin kai da wasu fanɗararrun ƙawayenta biyar, suka yi mata rakiya zuwa ɗakin miji. Dama da rana ma tare da ita aka yi jere, don haka da za a kai ta suna tafe suna hira. Zaune take a ɗakin ta, tana jiran shigowar Yaya Inu hayaniyar yaran ta cika mata kunne. Cike da izza ta fita tsakar gidan a gadarance ta ce.
"Ku waɗanne irin dabbobi ne, ku da yaranku da za ki dinga tunɓele da dare?"
Indo da dama zuciyarta take cike da kishi fal ta ce, "Yadda muka zama dabbobi, sannu a hankali ke ma za ki zama dabbar, har ki haifo balami a ciki gaba da yin tamɓelen da shi." A daidai lokacin Yay inu ya shigo, yana shigowa duka yaran suka nustu suna yi masa sannu da zuwa, ko ƙurarsu bai kalla ba ya wuce wurin Zuly ya kamo hannu ta suka wuce ɗakinsa. Sabuwar hira suka dasa suna ƙyalƙayala dariya, zuciyar Indo kamar za ta buga, tun tana tsakar gida tana jin hirarrakinsu har dare ya yi ta shige ɗaki ta kwanta.
Ganin Yaya Inu ya ja filo da abin rufa ya sa Zuly matashin kai ta ce, "Yaya haka ne masoyi? Ban gane ba an yi gabas da kare." Ƙirjin Yaya Inu ya buga amma sai ya basar ya ce, "Na gaji ne kin san fa yau na sha baƙi." Zuly ta ɗan tsuke fuska ta ce, "A'a ai kuwa haka za ka yi haƙuri ka tashi, don ni in saluɓe namiji ba abu ne mai wuya a wurina ba." Tsoro da kunyar Zuly ya mamaye shi, saboda tun da yake aure bai taɓa auro fitsararsiyar mace irinta ba. A ɓangare ɗaya kuma bai san me zai ce mata ba, hasali ma wata irin kunyarta yake ji. Yana cikin nazari, ya ga Zuly ta miƙe tsaye tana warware ɗankwalin kanta ta ce. "Na ka wasa ne Malam Inusa, ai ni ba na sanya. Ba ka ji ma laƙabin sunana ba matashim kai? Bari ma ka gani."
Zuly ta ƙarasa maganar tana fisgo siraran ƙafafuwan Yaya Inu.
Ya auren Yaya Inu da matashin kai zai kasance? Shin Yaya Inu yana warkewa ko ya tafi kenan? Wacce badaƙalar za a yi a gidan Mai gari da Laraba? Shin za ta so Maigari ko shi yake wahalarsa? Ina matsayin auren Inno da Mai Yasin? Yaya Mai Yasin zai yi tun da asirinsa ya tonu? Zai zauna da Goggo da Inno ko yaya? Mene ne a cikin Salame idan ba ɗa ba? Ya matsayin gwajin da za a yi wa su Ɗan Bishir? Yar gwal da Ɗanladi zaman su zai ɗore?
Duka waɗannan tambayoyin da ma waɗansu, amsarsu tana cikin cigaban littafin GIDAN LIKITOCI.
AlhamduLillah, a nan na kawo ƙarshen free pages ga me son ci gaba za ta biya ta 500 Acc Aisha Adam 3090957579 Firstbank shaidar biya ta wannan no 07062062624
Ummou Aslam Bint Adam🌚
[05/06/2024, 16:52] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
SHAFI NA ƊAYA
Cikin karayar zuciya da ɗacin rai wasu tagwayen hawaye suka fara 'yar tsere a saman dakalin fuskar Baba Isuhu, ya kai kallonsa wurin mai sunan malam da ke wutsul-wutsul a hannun Lami ya ce. "Mai sunan malam ba zan iya rabuwa da kai ba, don Allah Lami kada ki azabtar da ruhina da rashinku." Kuka ya sake ƙwace wa baba Isuhu da ya sauke idanunsa a kan ƙullin kayan Lami da ke ɗaure a ɗankwali.
Sai da ya sharce majina da gefen rigarsa sannan ya sake kwantar da murya yana faɗin.
"Lami kin san irin so da ƙaunar da nake yi miki? Ko so kike ki mayar da ni marayan ƙarfi da yaji? Matuƙar za ki tafi gidanku sai dai ki tafi da ni Lami, domin ni na fi maye maita indai a kanki ne." Baba Isuhu ya janyo hannun Lami ya haɗa da na mai sunan malam ya rungume a ƙirji sai ya sake ɓarkewa da kuka.
"Don Allah ki haƙura da yajin nan da za ki yi Lami. Matuƙar naman ƙauri ne zai datse igiyoyin so da ƙaunar da ke tsakaninmu ko sayar da kaina zan yi, amma na yi miki alƙawari duk inda zan shiga zan yi koma me ye na nemo miki abin ƙaurin nan Lami."
Lami ta taɓe ba ki sannan ta ce.
"Wallahi Isuhu ba abin da zai hana ni tafiya a daren nan, don in gaya maka na ce wa Goggo Sala ko awa guda ba za mu ƙara a gidan nan ba. Saboda Allah kamar a kaina tsiya ta ƙare, haihuwar fari a ce yau kwana biyu cir babu kajin ƙauri ballantana na saka rai da ɗan akuya ko tinkiya. Kai tir da halinka Isuhu, wallahi da Isa mai tsire na aure na san nama har sai na ci na ture..." Cikin sauri Baba Isuhu ya katse ta.
"Me aka yi aka yi Isa ne Lami? Wai ko kin manta Isuhun Lamisuwa mai hadarin naira?" Lami ta sake taɓe baki ta furta. "Ai a banza man kare, tun da a haihuwar ɗanka na fari guda a ce abin ƙauri ya gagara, kenan haka zan zauna har hakikar sunan ita ma ta gagare ni. Wallahi ba za ta saɓu ba bindiga a ruwa."
Jin haka ya sake tsuma Baba Isuhu ya zabure haɗe da ɗaga hannu sama ya ce. "Sai ni isuhullen Lamisuwa mai hadarin nairori, sai ni Isuhun da ya sha gaban zaratan mazaje ya samu Lamisuwa." Lami ta ɗan saki murmushi sannan ya kalle ta ya ce.
"Wai ina Lami take?" Da sauri Lami ta amsa. "Ga ni mana."
"A yau ba sai gobe ba zan kayar miki da tinkiya." Sai da ya kalli hagu da dama ya yi ƙasa da murya sannan ya matsa saitin kunnenta ya ce. "Kin san Allah yau uwar garke zan girke miki." Da sauri Lami ta washe baki cikin zumuɗi ta furta. "Uwar garke fa..."
"Ki yi ƙasa da murya mana haba Lami, ko so kike asirina ya tonu?" Baba Isuhu ya katse ta da sauri.
"Ɗan Isuhullena ai sai yanzu na fahimce ka, Allah Ya ba ka sa'a kada hatsabibiyar yarinyar nan ta ganka lokacin da za ka ɗauke mata uwar garken nan." Lami ta yi maganar murya can ƙasa zuciyarta fes.
"Ai maso abin ka ya fi ka dabara Lamisuwata, dare zan bi na san yadda zan yi da ita. Ke dai kawai ki zuba wannan ki sha kallo." Baba Isuhu da Lami suka kwashe da dariya.
"Lami! Ke Lami ki fito mu wuce kin shanya ni ke 'yar daɗi miji, kin san dai idan ana jego ko kyakkyawan zama a wurin miji ba a yi ballantama wannan mijin na ki..." Lami ta yi saurin katse Goggo Sala, "Goggo zo mu je ciki ai tuni mun riga da mun gyaro ta ni da shi." Baki sake Goggo Sala ta bi ta da kallo sannan ta ce. "Hmmm namiji kenan! Ke yanzu daɗin bakin namiji har zai sa ki zauna..." Lami ta yi saurin yi wa Goggo Sala raɗa a kunne, da sauri Goggo Sala ta washe ba ki ta furta.
"Ke 'yar nan da gaske?" Lami ta gyaɗa kai tana murmushe.
"Haba ko da na ji wannan ita ce harkar arziƙi, ko ni ƙanwar uwarki ai na samu na lasa wa a bakin salati. Ni fa kin san ni dama na fi kwarkwasa kwaɗayi, duk wurin da ake samun mai maiƙo-maiƙo a nan na fi ƙarfi." Lami ta yi gaba tana tafiya cikin ƙwambo tana jin ita ma ta isa, kuma ta tabbata matuƙar aka wayi gari da an yi mata ƙauri da tinkiya ta san daraja da ƙimarta ta ƙaru a idanun facalolinta.
CIKIN DARE
A hankali Uwani ta buɗe idonta sakamakon jin fitsarin da ya zame mata kamar farilla cikin talatainin dare, sai da ta gama murtsike idanu sannan ta fara tashin Dada.
"Dada! Dada don Allah ki tashi ki raka ni fitsari nake ji." Dada cikin takaici ta saki dogon salati sannan ta ce. "Ni kam wallahi Dijen Iro ta cuce ni da ba ta gashe miki mara tun kina zanin goyo ba, wallahi Uwani ki kiyayi haƙƙin tashina tsakiyar dare da kike yi..."
"Dada kamar kukan uwar garke nake ji." Uwani ta katse Dada cikin sauri tana sake kasa kunne, don sama-sama take jin kamar kukan dabbobinta kasancewar suna da ɗan nisa da sashen Dada. Dada ta yi mata shiru saboda takaici. "Dada don Allah ta shi mu je ko wani abu ne yake damun su..."
"Ai wallahi ko Umaru ne ya dawo daga Lahira bai isa ya fid da ni waje ba, tun wuri ki kama 'yan matan ƙafafuwanki ki yi gaba." Jin takaicin abin da Dada ta faɗa ya sa Uwani tashi fuuu ta suri buta ta yi waje.
Tamkar sabon munafiki haka Baba Isuhu yake tafe cikin sanɗa yana waige har ya ƙarasa sashen da awakin Uwani suke, sai da ya karkace maƙogaro ya maƙe murya kamar yadda Uwani ke yin magana sannan ya ce. "Uwar garkeruruna tayya maza mu je ki ci dusa." Shiru ya ga uwar garke ta yi babu alamin za ta motsa, ganin za ta ɓata masa lokaci ya sa ya ɗago ta ya fara ja a hankali. Sai da ya ƙarasa bakin katanga sannan ya taka turmin da ke jingin, sama-sama ya ɗan fara jiyo motsi don haka ya yi kasake. A ɓangare ɗaya ƙirjinsa na bugawa don kada uwar garke ta yi kuka asirinsa ya tonu. Yana raɓe a gefen katanga ya ga Uwani ta wuce da buta a hannu sannan ya sauke gwauruwar ajiyar zuciya, tirmi ya taka a hankali ya leƙa ya hango Mai gari da ke tsaye yana jiransa.
"Haba Isuhu tun ɗazu ɗauko tinkiya ya gagare ka, ko so kake asirinmu ya tonu mutumcina ya bi rariya ya tsiyaye tas a garin nan ina matsayin mai garin garin nan." Baba Isuhu ya yi ƙasa da murya ya ce. "Kai Talle ka san dai fita da uwar garke ta ƙofa ba zai yuwu ba saboda tsaro, yanzu ga ta ka matso zan cicciɓo maka ita." Da sauri Mai gari Talle ya matsa jikin katangar. Baba Isuhu ya koma wurin Uwar