Showing 63001 words to 66000 words out of 94348 words
Chapter 22 - GIDAN LIKITOCI BOOK COMPLETE BY AMEERA ADAM.txt
raɓe a gefe sai raba ido take kamar ƙosan sadaka.
Ganin haka ya sa jikinsu ya sake yin sanyi, don sun tabbata banza ba ta kai zomo kasuwa.
Sai da Na Madina ya kalli Jafar da Uwani sai ya sake fashewa da kuka, ganin haka ya sake raunata zuciyar Dada ta ja gefen mayafi ta fara sharce hawaye sannan ta fara magana.
"Gabaɗayanku na tabbata idan za ku yi mini shaidar Allah da Annabi, za ku yarda da abin da zan faɗa." Suka amsa mata cikin haɗin baki. Dada ta ci gaba da ce wa.
"Wallahi ƙanin mahaifinku Sa'idu ya cuce ni cutar ta har abada, amma ya je ba ni ya yi wa ba zumuncin Allah ya yi wa kuma ranar gobe ƙiyama sai igiyar zumunci ta zarge shi. Ni dai ba zan shiga tsakaninsa da Ubangiji ba amma sai mun tsaya a gaban Ubangiji ni da shi." Sororo gaba ɗaya suka yi hankali a tashe suna kallonta. Baba Yunusa ya ce.
"Dada me yake faruwa haka ne Baba Sa'idu fa? Baba Sa'idu da ya zame mana bango madafa kuma majingina, mutumin da ya maye gurbin mahaifinmu..."
"Inusa wa ya samar maka aikin Sojan nan? Kuma wa ya samarwa ɗan'uwanka Mamman aikin Ɗansanda, shi kuma wancan Rosofti?" Dada ta Katse shi.
"Duka Baba Sa'idu ne ya samar mana Dada wani abu ne ya faru?" Ya tambaye ta a sanyaye.
"Aikin ɗamarar ba shi ya kai Jafaru Lagas ba?" Duka suka amsa mata, jin furucin Dada ya sa Jafar ya ɗago a fusace. Dada ta cigaba da faɗin.
"Silar haka ai ga shi muna shirin samun Iron Alto na biyu a cikin gidan nan." Jin kalaman Dada ya sa gaba ɗaya suka ɗauki salati hankali a tashe. Baba Isuhu ya wurga wa Jafaru wani mugun kallo cike da ƙyama, yana riƙe da haɓa hannunsa ɗaya kuma na riƙe da mai sunan Malam.
Sai da ɗakin ya lafa da hayaniyar da ake yi sannan Na Madina ya ce, "Wallahi ba tun yau ba shi ya sa magana ta a kullin yaran nan a aurar da su, amma da yake nasara ya hure muku kunne sai ku ce yara sai sun yi karatu. Yanzu dubi garsamemen ƙato kamar Jafaru a ce bai yi auren fari ba, ni wallahi ina kamarsa da Allah Ya ba ni haihuwa da na yi 'ya'ya uku. To yanzu me ya fi wannan haushi? Wa ya sani ma a Lagas ɗin ko 'ya'yan ƙedarai ne suka suke buɗe masa idanu, yake wartar ɗaya bayan ɗaya yana sakayewa a gefe. Ga shi nan yanzu ai ya gagara haƙuri ya ja Uwani ɗakin Kulu suna watsa wa sunnar Ma'aiki ƙasa a ido." Kamar haɗin baki gabaɗaya mutanen ɗakin suka furta. "Innalillahi Wa'inna ilahirraji'un."
Duk budurin da ake yi ko a jikin Uwani ita babbar damuwarta ba ta wuce ta samu ta tsira daga horon Jafar ba, don ta san yadda ransa ya ɓaci idan ta shiga hannunsa sai Allah. Ran Jafar ya kai matuƙar ƙololuwar ɓaci don haka a zuciye ya buga tsaki haɗe da miƙewa zai fice daga ɗakin.
"Wallahi matuƙar Jafaru ya fita daga ɗakin nan Mamman sai ka bi ɗanka, tun da ni da ɗan'uwana ba mu isa da shi ba." Dada ta yi furucin rai a ɓace.
"Koma ka zauna Jafar." Mahaifinsa ya furta murya a dashe saboda ɓacin rai.
"Daddy wai ba ka ji me waɗannan mutanen suke faɗa ba ne? Wannan wanne irin abu ne. A ce a rasa ƙazafin da za a yi mini sai na zina, kuma na rasa da wa zan yi sai Uwani yarinyar da ƙazanta ta samu gurbin zama a ilahirin jikinta..." Na Madina ya katse Jafar sakamakon rarrafowar da ya yi, ya dafa ƙafarsa. Kwanciya na Madina ya yi a gabansa sannan ya fashe da kuka.
"Don Allah kada wanda ya hana Jafaru ya rufe ni da duka, dama ɗazu ka so dukana to ka saka bindiga ka tashi kaina a kan waɗannan magangun da kake faɗa mana ni da 'yar uwata." Na madina ya furta ƙwallah na zuba, idan ka ga yadda yake rusar kuka sai ka rantse da Allah wani abin aka yi masa.
"Ba na son sakarci ka koma ka zauna Jafar." Mahaifin Jafar ya buga masa tsawa. Sai da ya haɗiyi yawu mai ɗaci sannan ya koma ya zauna yana wurga wa su Na Madina harara, ya sunkuyar da kai ƙasa cikin ɓacin rai. Baba Inusa da kansa ya ƙarasa ya tashi Na madina ya koma mazauninsa sannan shi ma ya koma ya zauna.
Baba Rufa'i ya gyara zama, sannan ya fara magana.
"Dada duk mun ji abin abin da yake faruwa amma don Allah ku gafarce ni a maganar da zan faɗa."
"Kayya Rufa'i muke wa Ubangiji laifi ma ya yafe mana, ballantana ɗan'adam abin banza." Cewar Dada.
"A iya sanin tarbiyyar da yaran nan suke da ita ba mu taɓa tsammanin haka za ta taɓa faruwa ba, sai dai kuma ɗa ne ka haife shi ba ka haifi halinsa ba." Dada ta jinjina kai jin kalaman Baba Rufa'i yana shirin ci gaba da magana ta katse shi.
"Ai albasa ce ba ta yi halin ruwa ba Rufa'i, wai a rasa wurin da za a yaye wa sunna labulen albarka sai a ɗakina. Kaico ni Kulu." Sai da Dada ta yi shiru sannan ya ɗora.
"Kai Jafar ina maka kallon mai hankali ya aika yi haka ta faru?" Kai tsaye Jafar ya nuna su Dada murya a shaƙe ya ce.
"Baba a tambaye su ni kaina sama ta ka na ji abin da suke faɗa."
"Ba ni da ɗan uwana ka ƙaryata ba, uwarka Saro da ubanka Mamman su ka ƙaryata ka ji Jafaru." Dada ta furta tana wurgawa Jafar taƙuwa.
"Ka shiga taitayinka Jafar? Idan na kuma jin magana mara daɗi daga bakinka sai ranka ya yi mummunan ɓaci, ke Uwani shin yau wannan abin ya taɓa shiga tsakaninki da Jafar ne?" Baba Rufa'i ya jefa mata tambaya.
Zuciyar Uwani ɗaya ta share ƙwalla ta ce, "Wallahi ni kam azalce ta kai ni ɗakin Ya Jafar, ashe Lawan yana laɓe a bayana ban san ya biyo ni ɗakin ba." Cikin haɗin baki duka suka ce, "Waye Lawan?
"Mijin Fanteka ne." Uwani ta faɗa cikin kuka.
"Ashe ba ki da hankali Uwani? Ashe sakarcin na ki da ake faɗa gaskiya ne? A ina Lawan ɗin yake kuma ɗan gidan uban waye a ƙauyen nan? Da har zai shigo cikin gida ya bi ki ɗaki." Baba Yunusa ya yi maganar rai a ɓace.
"Ban gan shi ba Baba, duk neman da na yi ban gan shi ba ma ɗazu, kuma wallahi ganin idona ya fito daga ɗakin ya Jafaru. Sororo suka yi suka gagara gane kan maganar Uwani.
"Shi Lawan ɗin ne zai ɓata a gidan kamar wani zobe? Kin san me kike faɗa kuwa Uwani?" Cewar Baba Mamman.
Ganin duka ba su fahimci inda maganarta ta dosa ba ya sa Dada ta ce.
"Lawan ɗin da Uwani ke faɗa ba kowa ba ne fa face zakaran da take kiwo, ko ba Lawan mai wake-wake ba Uwani?" Da sauri Uwani ta gyaɗa kai.
"Ba maganar zakara muka yi miki ba, muna magana ne akan tsakaninki da jafar." Baba Yunusa faɗa.
Jin haka ya sa Uwani ta kwashe duk abin da ya shiga tsakaninta da Jafar ta faɗa musu, shiru duka suka yi Dada ta dubi Na madina ta ce.
"Yaya wai haka ne abin da ta faɗa? Don gaskiya shedar zir haramun ce kar Mamman ya fusata ya ce mun yi wa ɗansa ƙazafi ya kaimu kotu, alƙali ya yanke mana bulala tamanin mu shiga uku."
Jikin Na Madina ya yi sanyi don shi kasan ya san zargin ne yake yi idanunsa ba su gani ba. "Ni dai Allah Ya sani ban kama Jafaru da Uwani turmi da taɓarya ba, amma na ji waɗansu kalamai da suke yi a cikin ɗakin Kulun. Don Allah me zai sa su keɓe idan ba warware mutumcin sunna suke ba?" Sai a lokacin iyalan wurin suka fahimci gabaɗaya inda maganar su ta dosa.
"Amma dai Yaya ka ci zarafin zuri'ata, yanzu saboda Allah wacce ƙiyayya kake yi wa Jafaru da Uwani da za ka nemi ka haɗa su da hali irin ta'adar Iron Alto, ni dai ku zama shaida ta daga yau ba zan sake haɗa inuwa ɗaya da Yaya Musa ba." Dada ta yi maganar cikin kuka, ta mayar da kallonta wurin su Jafar ta ci gaba da cewa.
"Ban da ƙarfin alƙawari ma me zai haɗa Uwani da Jafaru? Yarinya kyakkyawa kamar Uwani a ba ta Ɗansanda, Ɗansandan ma kamar Jafar mai zuciyar masifa. Ni tsorona ma kada watarana Uwani ta yi masa laifi ya sa bakin bindiga ya bindige ta..."
"Allah ya tsare ni, ni kuwa me zan yi da Uwani wallahi ko a ƙafa aka ɗaura mini ita ba zan ja ba, kai ko abokina ba zan yi wa hanyar aurenta ba, haka kawai a ce na yi sanadin auren ƙazama kamar Uwani." Jafar ya faɗa a ƙazance kamar zai yi amai.
"Idan kai ba ka so ba ai tuni alƙwari ya ba ka aurenta Jafaru, shafa Fatiha kaɗai ya rage muku. Amma fa wallahi faɗi kanka tsaye Jafaru ƙazantar uwani tun da na zo duniya ban taɓa ganin ƙazama irinta ba." Jin tonan asirin da Dada take mata ya sa Uwani tura ba ki gaba.
"Rigar mama wannan Uwani ba ta san ta canza ba sai dai idan na tilastata ta sauya, ban da ma Allah Ya kawo mu zamani yaushe yarinya za ta fara saka rigar mama a gaban iyayenta? To haka take zama da tsamin hammata, rannan ina kwance a saman kaina na ji tsami ya cika min hanci wallahi ina dubawa na ga ashe ɗan diras da kanfanta ne a ajiye. Ni ina tsoron ma kar a aurar da Uwani ta shafa wa Jafaru kwarkwata, don wallahi ko gorin kwarkwata aka yi wa Uwani sai haka. Amma dai tun da Hajiya Saro (Mahaifiyar Jafar) ta daina ƙazanta Uwani ma za ta daina, don bara war haka sai da na roƙa wa Uwani addu'ar yayewar ƙazantar nan a Harami." Dada ta mayar da kallonta wurin su Baba Rufa'i sannan ta cigaba.
"Yanzu dai ba za mu tashi daga wurin nan ba sai mun kammala maganar yaran nan. Kun dai ga yadda Uwani ta zama budurwa ni tsorona ma kada ta fara baƙon wata a gabana na shiga uku..."
"Subhanallah wannan wanne irin mummunan fata ne haka Kulu? Yanzu saboda Nasara ya gama wanke wa su Mamman hannu a ka sai su bar yaran nan haka?" Jafar ya saki murmushin takaici don shi gani yake duk sokiburutsun tsofaffin ne.
"Don Allah ku dubi fuskar Jafaru washar yadda yake sakin murmushi, ko wannan miskilancin da yake yi fa aure yake so, kuma yanzu ya samu an soso masa wurin da yake yi masa ƙaiƙayi." Na Madina ya ƙarasa maganar yana sakin murmushi.
Baba Rufa'i ya yi gyaran murya sannan ya furta.
"Dada dama ba mu ƙi ta ku ba, amma gaskiya shekarun Uwani sun yi ƙanƙanta a aurar da ita yanzu Ina laifin ta gama sakandire ma..."
"Sakandi me? Kana nufin zan zauna ina ganin Uwani a gabana har tsawon shekara biyar? Wallahi da kunci amanar zumunci, yanzu saboda kun ga ƙasa ta lulluɓe idon mahaifin yarinyar nan shi ne za ku watsa mata ƙasa a ido. Kaico mutuwa mai yankan ƙauna. Allah Ya jiƙanka Umaru, ni na san da Umaru ne ba zai taɓa yi wa bayanku haka ba."
Shiru suka yi Baba Mamman na shirin magana Na madina ya katse shi, "Amfanin me karatun bokon zai yi mata? Aure fa shi ne sunnar Ma'aiki. Yanzu Dada ba ga su Safare nan ba kowacce tana ɗakinta da 'ya'yanta, ina ce firamare kawai suka yi. Ko kuma mu iyayenku da ba mu yi yi bokon ba sai a ce ba mu ji daɗin rayuwar aure ba?"
Dada ta ware hannuwa cikin gamsuwa ta ce, "Gane mini hanya Yaya, so suke yadda fitsararrun yaran can suka rasa miji ita ma ta gandame mini a gabana."
"Dada domin fa mu inganta rayuwar Uwani muke son mu tsaya mata ta yi karatu kamar yadda sauran yara suka yi, amma ba don wata manufa ba. Don Allah ku fahimce mu Uwani yarinya ce, har yanzu fa ba ta cika sha biyar a duniya ba duk fa girman jiki ne."
"Ni dai Baba kawai a aura mini Ofisana, kar na je Furaira ta riga ni gabatar da kanta a wurinsa. Don wallahi Furaira masifar son shi take. Ka ga ni ma sai na dinga gayu irin nasa, Allah ko su Fanteke sai sun zama 'yan gayu..." Da sauri Jafar ya katse Uwani.
"Ke ba na son shashanci da rashin hankali an gaya miki ni sa'anki ne? Tun wuri dama ki nemi mijinki don ni tuni akwai wacce zan aura a Lagos..."
"Lagas? Yanzu Jafaru ka rasa wacce za ka auro sai ƙedarun Lagas, wallahi ni kam dole na je Zariya na samu Sa'idu." Dada ta faɗa cike da damuwa.
"Jafar wannan daɗaɗɗan alƙawari ne da na ƙulla shi shi tun ranar da Uwani ta zo duniya, kamar yadda ka sani mahaifinta ya rasu tun tana ciki sakamkon hatsarin da ya yi. Ba ta taɓa sanin fuskar mahaifinta ba sai mahaifiyarta. Tausayinta ya sa na ɗauki alƙawarin aura maka ita matuƙar kuka kai munzalin aure, tun da a lokacin ba ka fi shekara goma sha uku zuwa sha biyar a duniya ba. Daga kai har ita mu muke da iko a kanku babu wanda ya isa ya bijire wa umarninmu." Baba Mamman ya yi wa Jafar jawabi fuska a haɗe.
Dada ita da na Madina suka washe baki cikin farinciki ya ce, "Wallahi ka jima ba ka faranta mini rai irin na yau ba Mamman."
"To yanzu dai duk ba wannan ba, abu ɗaya zan yarda da shi. Ba zan zuba wa Uwani ido ba a yi mata aure ba har nan da shekara biyar ba. Watan Maulidin nan me zuwa ne bikin su Shukra ko?" Baba Mamman ya gyaɗa mata kai.
"Nan da watan maulidi nake son a ɗaura musu aure idan ya so nan da wani lokaci sai a yi maganar tariya. Ko dai mutuwa na yi kafin lokacin na sauke nauyin da muka ɗauka, ko ba haka ba Yaya?" Dada ta furta tana kallon Na Madina, cikin gamsuwa ya amsa mata. Duk yadda su Baba Mamman suka so shawo kan Dada don ɗaga maganar fir ta ƙi amincewa. Don haka suka haƙura suka tashi daga taron, Jafar tun ba su kai ga tashi ba ya fice fuuu daga ɗakin. Ganin haka ya sa Malam na Madina ya saki murmushi ya furta.
"Ja'irin yaro wannan doron da ya yi yana yin aure zai miƙe, na san yau kwanan farinciki zai yi yoo aure wasa ne." Dada ta bushe da dariya.
07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
[11/06/2024, 13:08] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
SHAFI NA BAKWAI
Kamar Jafar zai tashi sama haka ya nufi sashen mahaifiyarsa saboda ɓacin rai ko gabansa ba ya gani sosai, da ƙarfi ya doka ƙofar falon Mami da su Shukra na zaune. A zabure duka suka miƙe Mami ta dube shi ta ce.
"Hankalinka ɗaya kuwa Jafar? Saurin me kake yi haka?" Jafar bai tanka mata ba ya wuce kan kujera ya zauna yana furzar da iska mai zafi. Sai da ta ƙare masa kallo sannan ta ƙarasa kusa da shi ta furta.
"A kullin ina gaya maka ka dinga rage wannan baƙar zuciyar taka. Me aka yi maka?"
"Mami me ya sa Daddy ba ya son farin cikina ne?" Shi ma ya jefa mata tambaya.
"Me ya sa ka faɗi haka?"
"Yanzu Mami da girmana ni ba ƙaramin yaro ba a ce za a wani nemar mini matar aure, saboda Allah an yi mini adalci kenan? Atleast ko shawarata ai sai a nema." Nan take Mami ta haɗe fuska sai da ta sauke ajiyar zuciya ta furta.
"Ina tunanin dai wasa yake yi maka, amma kuma ban da abin ka Jafar ka sani ko 'yar manya ce ita ma. Duk da dai na san kun gama daidaitawa da Safna ai ita ma wannan sai mu ji waye ubanta."
Tun da Mami ta fara magana wani ƙululun baƙin ciki ya tokare masa maƙoshi, "Mami ko 'yar gidan uban waye ni fa idan ba na sonta ba zan aure ta ba. Kuma Daddy ya rasa wa zai haɗa ni da ita sai waccen kucaka, sakarya kuma ƙazamar yarinyar can Uwani."
A zabure Mami ta miƙe tsaye har ba ta san lokacin da wani ashar ya suɓuce mata ba. "Uban waye zai haɗa ka da wata Uwani? Yarinyar da ko a mai aiki ba zan ɗauke ta ba. Ba zai taɓa yuwu ba wallahi, wannan ma ai shiga haƙƙi ne ina kai ina wata jakar yarinya Uwani." Jin haka ya ƙarfafa gwiwar Jafar nan ya kwashe duk yadda aka yi ya sanar mata, tun ba ta gama jin jawabinsa ba ta dakatar da shi tare da faɗin.
"Bari na je na samu Dada wallahi ba zai taɓa yuwu ba wankan kuturu da sabulu." Fuuuu Mami ta wuce su Shukra na daskare mamaki ya mamaye su.
"Waye haka mai ƙirar samudawa ya yi mini gandandan a tsaye?" Dada ta furta tana ƙare wa Mami kallo da ta yi tsaye a bakin ƙofa. Mami ba ta amsa ba ta wuce ta zauna a kan hannun kujerar Dada, tana cika tana batsewa.
"Sannu da gida Dada."
Mami ta furta a daƙile. Dada ta bi ta da kallo sai da ta taɓe baki sannan ta ce.
"Sannunmu dai."
"Dada a gaskiya ba a yi mini adalci ba, saboda Allah wai a rasa da wa za a haɗa Jafar sai da wata Uwani. Yaron nan fa namiji ne ko mace ba za a yi wa dole ba,