Showing 81001 words to 84000 words out of 94348 words
Chapter 28 - GIDAN LIKITOCI BOOK COMPLETE BY AMEERA ADAM.txt
kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
SHAFI NA TARA
Sai a lokacin Uwani ta fahimci ashe ba iya su Yaya Ƙarama ce kaɗai idonsu biyu ba, hatta mutanen da ke cikin uwar ɗakin lakur suka yi sai da suka ji Uwani ta yi sufa za ta faɗo uwar ɗakin suka fara ihun neman ceton rai. A daidai bakin ƙofar uwar ɗakin Uwani ta tsaya sai ta hango wata wuƙa a gefen randa, ta janyo ta ta fara wasawa. Naziru ɗan wurin Sa'a da a lokacin ya wartsake ya kafe Uwani da kallo, ganin haka ya sa Uwani ta kalle shi tana zare ido ta ce.
"Ga wani ɗan ƙwage da shi za mu fara." Uwani ta ƙarasa maganar tana fusgar hannun Naziru da bai wuce shekara huɗu ba.
"Wayyo Iyata! Wayyo Iyata." Ya fara ihu hankali a tashe don ƙiri-ƙiri ya ga wuƙar hannun Uwani. Sa'a na ganin haka ta fara jan hannun Naziru Uwani na jan ɗaya, Sa'a ta waiga wurin su Yaya ƙarama ta ce. "Ƙarama don Allah ku kawo mini ɗauki Naziri zai tafi."
Yaya ƙarama da ke ƙuryar uwar ɗaki ta ce. "Sa'a ki haƙura da Naziru tun da ba wuce haihuwa kika yi ba, wallahi a yanzu ko Habibu (Shi kaɗai ne ɗanta) suka ja sai dai na bi shi da addu'a." Sa'a na shirin magana Uwani ranƙwala mata ludayi a ka, a guje ta saki hannun Naziru cikin kuka ta faɗa uwar ɗakin tana faɗin.
"Wayyo Naziru."
Shi ma Naziru sai tirjewa yake yana faɗin. "Iyata wayyo Iyata." Yaya ƙarama ce ta yi sauri ta banka ƙofar ɗakin ta danna sakata tana sauke ajiyar zuciya.
"Idan kun rufe ƙofa za mu ɓullo ta ƙarƙashin ƙasa, mu dama ai daga kabari muke. A wannan lokacin babu buƙatar mu yi muku bayanin mu su waye, domin hukunta ku muka zo yi ɗaya bayan ɗaya, a kan cin zarafin da kuke yi wa mahaifiyar 'yar uwarmu da kishiyarta. Mu tawagar fatale sai mun saɓule fatar jikinku sannan mu tsotse romo da ɓargon jikinku. Amma za mu ɗaga muku ƙafa zuwa nan da ɗan wani lokaci, don mun lura kun fara nadama. Sai dai muna mai tabbatar muku babu wanda zai tafi gidansa sai an yi sadakar uku, idan kuma mutum ya yi kuskuren tafiya gida gobe, to a daren ranar sai dai ya kwana a ƙiyama."
Uwani ta furta a lokacin da ta fita da Naziru tsakar gida da ke ƙwala ihu. A yadda ta lura kusan ilahirin mutanen gidan duka sun tashi, wata dabara ce ta faɗo mata don haka ta buga tsalle a tsakar gidan ta ce.
"Waɗanda kuke leƙenmu muna gano ku, ke wato har da ke ko. Wallahi ɗaya bayan ɗaya za mu bi ku mu ƙwaƙwale idanunku idan ba ku koma kun kwanta ba." Ta saki hannun Naziru ai kuwa da gudu ya faɗa ɗaki yana ihu, sai ta tafi da gudu ta nufi ɗakin mahaifiyarta, a guje ta ji mutanen ɗakin suna shigewa uwar ɗaki wasu na hantsilawa. Nan ma ta nufi ɗakin kishiyar mahaifiyarta ta razana su, sai da ta tabbatar da sun gama tsorata kowa ya shige uwar ɗaki sannan ta lallaɓa ta isa banɗaki ta wanke fuskarta. Ta duƙunƙune hijabin Inna Suwaiba ta soke a hammata, sai da ta shirya sosai sannan ta nufi ɗakin mahaifiyarta da gudu tana faɗin. "Wayyo Allah! Ku taimaka mini za su ƙara janye ni." Tana shiga ɗakin ta tarar falon mahaifiyarta babu kowa an banke uwar ɗaki sai ƙananan yara da ke kuka suna buga ƙofa, saboda kada a gano Uwani ita ma ta fara bubbuga ƙofar tana ihu. Da ta lura ba za su buɗe mata ba sai ta janyo ƙofar falo ta datse.
Har aka yi assalatu babu wanda ya yunƙurin fitowa daga ɗakin, duk da duka baƙin gidan a zuciyarsu kowa ya ayyana gari na wayewa tafiya zai yi. Amma da sun tuna kashedin da aka yi musu a kan kada wanda ya bar gidan har sai an yi sadakar uku sai jikin kowannensu ya yi sanyi. Sai da gari ya yi tangararan sannan Indo ta yi ƙarfin halin buɗe ƙofa, kamar sababin munafukai haka mutane suka dinga leƙowa ɗaya bayan ɗaya suna fitowa suna yin alwala suna sallah. Duk wannan abin da ya faru bayan da gari ya waye babu mutum ɗaya da ya jajantawa kowa, domin kowa a tsorace yake. Su Uwani suna zaune sai ga Aramma ya shiga ɗakin kansa ya yi waɗansu ƙulalai sun fi biyar, daidai tsakiyar hancinsa har wani ja ya yi yana maiƙo. Da mamaki suka bi shi da kallo, Aramma ya zauna daɓar jikinsa zafi zau da zazzabi. Gaishe shi mutanen ɗakin suka yi, suna son jin abin da ya faru da shi suna tsoro. Hannu ya sa a aljihu ya zaro kuɗin ya ce. "Ungo wannan Maryama, kuɗinki na jiya ne. Wannan kuma kyautar dubu hamsin ce na ba ki ita ma Indo zan miƙa mata nata." Baki sake Maryama ta bi shi da kallo, ta ce.
"Malam dubu hamsin fa? An ya ba mantawa ka yi ba?" Aramma ya dube ta a fusace da ya tuna gargaɗin fatalwa sai ya wayance ya sassauta murya ya furta. "Maryama shaidar da za ki yi wa mijinki kenan? Kyautatawa ce kawai ta sa na ba ku." Maryama hannu na rawa ta sa ta karɓa tana zuba masa godiya, Aramma har ya miƙe zai fita Inna Suwaiba ta ce. "Aramma ungo shafa-shafa sai ka shafa a malolon nan na ka, Allah dai ya sawaƙe sanyi haka yake lokaci ɗaya ka ga wuri ya luluye. Ko kuma bige wa ka yi ne da dare?" Aramma da ba ya son a ja doguwar magana ya karɓa ya yi gaba ba tare da ya amsa mata ba, ɗakin Indo ya faɗa ita ma ya sallame ta ya koma ɗakinsa don ilahirin jikinsa ciwo yake masa. Aramma na shiga ɗaki sai ga Indo jiki na rawa ta shiga wurin Maryama suka fara tattaunawa cikin mamaki, ba su ƙara nutsa wa a tekun mamaki ba sai da suka ji Aramma ya ce a yi shinkafa da miyar dage-dage da rana. Wannan sabon sauyi da suka samu daga wurin Aramma ba ƙaramin daɗi ya yi musu.
A na gobe Uwani za ta koma gida wurin ƙarfe goma sha biyu na dare ana zaune ana ɗan hira, ta hangi Aramma ya suri buta ya yi banɗaki. Sai da ta tabbatar da hankulan mutane ba ya kanta ta saci jiki ta nufi banɗaki, da yake banɗakin ya yi nesa da ɗakuna don haka ta laɓe a can kusurwar bango ta fara magana.
"Baba ga tawagar 'ya'yanka sun dawo. Kada ka tsorata mune dai fatalen nan." Aramma da ke tsugunne a kan masai sai abin ya yi masa a daidai, saboda wata sabuwar gudawa ce ta tsarge shi. Gumi ya fara tsattsafo masa ya ce. "To 'ya'yana don Allah kada ku taɓa lafiyata, wallahi har yanzu ban warke ba."
"Ba za mu sake cutar da kai ba, domin ƙawarmu wato matacciyar 'yarka ta ce ta ga irin kyautatawar da kake yi wa iyayenta da 'yan uwanta. Ki yi masa magana ya ji sabuwar muryarki ta cikin jinsin fatalwa." Uwani ta yi maganar tana wani fuffuka, sannan ta maƙale murya ta furta.
"Baba ni zan tafi da kai na fi so na dinga ganinka." Tamkar an buɗe fanfo haka cikin Aramma ya birge, ya ci gaba da sakin gudawa babu ƙaƙƙautawa. Cikin tashin hankali ya ce. "Na yafe don Allah ki je ki ɗauki mahaifiyarki."
"Shi kenan Baba zan dai dinga kawo muku ziyara a ɓoye duk dare ina ganin rayuwar da kuke yi, idan na ga saɓanin abin da ka fara yi wallahi cikin tumbinka zan shiga, na kannaɗe hanjinka ita kuma kodarka na fansarwa shugaba." Uwani ta furta tana gimtse dariyarta.
"Wallahi komai zan ci gaba da yi idan na saɓa ki mini duk abin da za ki yi mini."
"Mu zamu tafi Baba sai mun sake zagayowa." Uwani na gama faɗar haka ta fara wata fuffuka tana gurnani sannan ta saɗaɗa ta bar wurin. Saboda yadda Aramma ya razana bayan da ya gama uzurinsa a duƙe ya dinga tafiya, saboda yadda ya ji ƙafafuwansa sun yi sanyi har sun gagara ɗaukar nauyin gangar jikinsa.
Ranar da aka yi sadakar uku dai tun da safe wasu daga cikin 'yan gaisuwa suka fara watsewa, domin dama wasu tamkar a kan ƙaya suke. Ita ma Uwani sai da aka yi sallar la'asar sannan Aramma ya zo ya sanar da Maryama an zo ɗaukan Uwani, ta so Uwani ta ƙara kwanaki amma babu yadda ta iya haka ta danne. Wasu daga cikin 'yan uwan mahaifiyarta sai tsokanarta suke suna amarya sai sun zo biki. Kafin Uwani ta fita sai da Maryama ta sata a gaba ta yi mata nasiha sosai.
Fakare Uwani ta yi tana sauraronta kamar nasihar na shigarta, sai gyaɗai kai take tana amsawa. Sai da ta gama sauraron mahaifiyarsa sannan ta ce. "Ni kam Inna don Allah zan faɗa miki wata magana amma don Allah kada ki faɗa wa kowa." Take gaban Maryama ya faɗi amma sai ta basar ta ce. "Ina jin ki babu wanda zai ji Uwanina." Duk abin da ya faru tun daga farko har ƙarshe ta sanar da ita tana dariya, ita kanta Maryama dariya take sheƙawa sanna ta riƙe baki ta furta. "Allah Ya shirye ki Uwani ni dai wallahi ban san halin wa kika ɗauka ba, mahaifinki dai har ya fi ni sauƙin kai. Allah Ya shirya ki ko ba komai kin samar mana 'yanci." Suna cikin haka suka ji ƙarar horn da sauri Uwani ta sungumi jakar kayanta, ta ɗauko hijabinta ta saka. Sai da ta yi wa mutanen gidan sallama da Aramma sannan ta ƙarasa bakin motar cikin murna, don tun daga nesa ta hango motar baba Mamman. Don haka da saurinta ta buɗe motar tana faɗin.
"Daddy wallahi na yi kewar Dada, ƙila ma ita tana can ko a jikin..." Kalamanta suka maƙale a maƙoshi sakamakon ido biyu da suka yi da Jafar. Wata uwar harara ya banka mata, ta yamutsa fuska tana ƙare masa kallo ta ce.
"To kai kuma ina motarka ka ɗauko ta Daddy?" Jafar bai tanka mata ba ya fisgi motar da gudun gaske har sai da wasu yara suka matsa a guje.
Suna cikin tafiya babu wanda ya tanka wa wani sai Uwani ta fashe da dariya har da ƙyaƙyatawa, a fusace Jafar ya waigo ya zuba mata manyan idonsa. Sai kuwa Uwani ta sake kwashewa da dariya, gangara motar ya yi ya faka ya ɗauke kai gefe a daƙile ya ce. "Fice mini daga mota."
Uwani ta gimtse dariyarta sannan ta ce. "Kamar ya na sauka ai ba motarka ba ce."
"Uban me kike wa dariya?"
Uwani ta yi murmushi ta ce, "Wallahi dariya ka ba ni, ni dai ba baƙuwa ba ce a wurinka atoh. Kuma dai komai na ka Dada ta ba ni labari tun kana jariri har fa tunbiɗin da ka dinga yi kana yaro. Sai kuma na ga ka fafaki mota kana yin wani irin tuƙin 'yan Kaduna-Zaria, to wai ni birgar me za ka yi mini?" Jafar ya haɗiyi wani yawu mai ɗaci haɗe da fusgar da iska mai zafi, jin irin maganganun da Uwani ta faɗa masa. Yana shirin yin magana Uwani ta sake sakin wata dariyar tana faɗin.
"Kasan Allah yadda ka iya fafakar motar nan da Inuwan Toyota zai ganka tsaf zai ɗauke ka kwandasta, saboda wataran idan ya gaji ya ba ka ɗani..."
"Fice mini a mota." Ya furta mata cikin tsawa.
"Wallahi ba zan fita ba ai motar Daddy ce, malam kada ka yi mini gori ni nan gaba ma jirgin sama zan tuƙa." Kalamanta na ƙarshe suka kusa ba shi dariya. 'Yarinyar da cikakkun sentence na hausa ma ba ta iya haɗawa ba ita ce za ta tuƙa jirgin sama.' Ya raya a ransa. Ganin za ta ɓata masa lokaci ya sa ya fisgi motar ya ci gaba da sharara gudu, har suka ƙarasa gida wani bai sake kula kowa ba.
Tun Jafar bai gama faka motar ba Uwani ta suri jakar kayanta ta ɓalle murfin motar ta fice a guje ko rufe motar ba ta tsaya yi ba, tun daga soro ta fara ƙwalla wa Dada kira tana washe baki. Mami da ta rako aminiyarta Hajiya Falmata ganin Uwani ya sake tado mata da wani malolon baƙin ciki.
"Ƙwata wannan abar ce fa aka aura wa Jafar, imagine a ce wannan ce sirikata." Hajiya Falmata ta ƙare wa Uwani kallo sannan ta saki wani malalacin murmushi ta furta.
"Haba ƙawata wai da wannan 'yar abar ce ke barazana da aurenki? Tun da ƙuruciya ba ki yi yaji ba sai yanzu? Babu inda za ki, matuƙar kin bi duk tattaunawar da muka yi wallahi na faɗa miki da ƙafarta za ta kori kanta babu boka babu malam." Sai a lokacin Mami ta ƙara jin ƙwarin gwiwa, Hajiya Falmata ta ci gaba da biya mata miyagun shawarwari sannan suka yi sallama.
Da murna Dada ta tarbi Uwani don ita kanta ba ƙaramin kewarta ta yi ba, dalilin da ya sa tun safe ta sa baba Mamman ya ɗauko ta. Shi kuma ya ce a bari zuwa bayan azahar sai Jafar ya ɗauko ta. Kuma ya yi haka ne domin so yake kafin lokacin tariyarsu su ƙara samun fahimtar juna.
Sai da aka yi sallar Margriba kamar yadda Baba Yunusa ya ce za a zauna ya tara 'yan uwansa, Dada, na Madina, Uwani, Jafar da kuma Mami. Sai da ya buɗe taron da addu'a bayan kowa ga gama sannan ya fara magana.
"Alhamdu Lillah! Na san wasu daga cikinku sun san dalilin wannan zaman yayin da wasu kuma ba su sani ba. Maƙasudin zamanmu a kan kai Jafar da kuma ke Uwani ne." Jafar ya sunkuyar da kai ƙasa rai a bace. Tsabar takaici ya sa Mami yin ƙwafa a fili, Dada ta dube ta haɗe da taɓe fuska ta ce.
"Aure dai Allah Ya haɗa duk mai hassada sai rabo ya kashe shi, yara su haihu kuma a mayar da sunansa." Mami ta shiga aika wa Dada harara a fakaice.
"Jafar a yanzu wani nauyi ya hau kanka domin aure ba wasa ba ne, ka riƙe yarinyar mutane amana don a yanzu da kake gani komai nata ya dawo ƙarƙashin ikonka. Ke kuma Uwani wannan da kike gani aljannarki na ƙarƙashin ƙafarsa, ki bi mijinki sau da ƙafa yi na yi bari na bari. Duk abin da kika san zai faranta ran mijinki shi za ki yi, abin da ba ya so sai ki haƙura da shi don zaman aure ɗan haƙuri ne." Sai da Baba Yunusa ya numfasa sannan ya ci gaba.
"Mun tattauna ni da 'yan uwana a kan za ku tare tare da Mahaifinku tun da an riga an ɗaura aure babu fa'idar a ce za a zauna har sai nan da wata biyu idan auren su Shukra ya zo. A don haka idan Allah Ya kai mu ranar Laraba mai zuwa ne mahaifinku Mamman ya ce za a ƙarasa gyara komai da saka komai na gidan, tun da akwai wadataccen wuri za ku zauna a ƙaramin part ɗin da ke gefen na Maminku." Wani irin tuƙuƙin zafi ne a zuciyar Mami har za ta ƙi amimcewa da hakan sai kuma ta tuna da huɗubar ƙawarta Hajiya Falmata.
"Saboda haka muka yanke shawarar idan Allah Ya kai mu juma'a mai zuwa ne tariyarku, kuma bayan nan za a nema wa Uwani wata makarantar za ta ci gaba da karatunta. Idan ya so bayan sun yi hutu sai ka ɗauki matarka ku wuce wurin aiki." Jafar ya yi shiru ba tare da ya amsa ba. Wannan maganar ta ƙarshe ba ƙaramin daɗi ta yi wa Mami ba, don a wannan lokacin ne za ta ci karenta babu babbaka a kan Uwani.
"Ni iya abin da zan iya ce wa kenan, Dada kafin mu zo kan ki ko akwai mai magana a cikin?" Gabaɗaya suka girgiza kai ban da Baba Mustafa da ya ce yana da abin cewa.
"Sannu da ƙoƙari Yaya Allah Ya ƙara girma, duk bayananka a kan tsari suke. Amma abin da nake gani me zai hana a ɗaga tariyar ta su zuwa nan da kamar sati biyu zuwa uku, duba da yanayin ragowar shirye-shiryen da ya kamata a yi musu. Daga haɗa lefe har zuwa wani shirye-shirye na su na mata, sannan a wannan lokacin mahaifiyar yarinyar na cikin halin rashin 'yarta. Amma bayan wannan lokacin ita kanta za ta samu nutsuwar gudanar da bikin yadda ya kamata." Dada ta jinjina kai sannan ta furta.
"Wallahi Mustafa ka yi kyan kai, saboda Allah kamar gajiya na yi da Uwanin da za a ce nan da kwana huɗu a kai ta ɗakin miji." Baba Yunusa ya yi murmushi ya furta. "Wannan haka ne, Dada me za kike ganin ya dace bayan haka." Dada ta yi jim sannan ta furta.
"Ni dai kam nasiha ce zan yi wa Jafaru da ita Uwani, amma kam ba yanzu zan yi musu ba sai ranar da za su tare. Don ina gudun na tofar da yawun bakina a banza, su barbaɗar da nasihar da na yi musu tun kafin tariyarsu." Tambayar Mami aka yi ko tana da abin faɗa ta ce babu, don haka suka ƙarƙaren zaman tun ba a gama addu'a ba Mami ta sa ƙafarta ta fice rai a ɓace.
07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
[21/06/2024, 12:32] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
SHAFI NA SHA UKU
Jin yadda jikin Uwani yake karkarwa ya