Showing 57001 words to 60000 words out of 94348 words
Chapter 20 - GIDAN LIKITOCI BOOK COMPLETE BY AMEERA ADAM.txt
kwashe mini lalatattun kayan nan kafin ranka ya ɓaci. Ni Kulu uban me zan saka a ciki? An ya Isuhu shaɗanu ba su dafa maka kai a cikin bacci ba?" Uwani da ke uwar ɗaki ta sunne kai ƙasa tana dariya.
"Haba Dada da farar safiya ki cika wa mutane kunne da ihu." Jafar ya faɗa yana sako kansa cikin ɗakin. Uwani da ke ɓoye a ɗaki ta yi ƙasa da murya ta ce, "Kai ma naka ihun yana tafe."
"Ba dole ka ji ihuna ba Jafaru yanzu kamar ni tsofai-tsofai." Sai kuka ya ci ƙarfin Dada sai da ta share hawaye sannan ta watsa wa Jafar rigunan a fuska ta ci gaba.
"Wai Isuhu ya rasa me zai kawo mini sai baraziya wai na saka. Yanzu saboda Allah Jafaru ko uwarka Saratu me za ta yi da baraziyya ballantana kuma ni?" Tun Dada ba ta gama magana ba Jafar ya watsar da rigunan sakamakon wani tsami da bashi-bashi da ya ji ya doko hancinsa.
"Haba Dada me kike yi haka ne?" Jafar ya faɗa a ƙazance.
Kafin Dada ta yi magana mai sunan Malam ya sake tsanyarewa da kuka, Lami ta dubi Jafar ta miƙa masa shi. Kamar Jafar zai yi magana sai kuma ya basar ya miƙa hannu ya karɓe shi, yana bin su da kallon mamaki.
"Don Allah Jafaru ka taimaki yaron nan ka ba shi mama ya sha ko ya yi shiru." Lami ta faɗa a ɗan kunyace. Jafar ya kalli Lami cikin sauri ya ce.
"Wane Jafarun?" Jafar ya tambaya a hargitse.
"Kai mana Jafaru, don Allah ka yi ka ba shi kada ya shiɗe don tun ɗazu yake kuka." Baba Isuhu ya furta. Ran Jafar ba ƙaramin ɓaci ya yi ba, ya haɗe fuska ya dubi baba Isuhu.
"Baba wannan wacce irin magana ce babu tsari, yanzu idan na faɗa maka magana a ce na yi rashin kunya. Idan har ni zan iya shayar da shi me ya hana kai ba ka shayar da shi ba?" Dada ta saki baki da hanci tana kallon baba Isuhu a tsorace, don ita a yanzu ya fara ba ta tsoro shi da Lami. A hankali ya ajiye mai sunan malam a gefe sannan ya miƙe, yana shirin tafiya Lami ta ce.
"Isuhu sai fa mun danne shi..."
Tun Lami ba ta ƙarasa magana ba baba Isuhu ya sa ƙafa ya shatalo ƙafar Jafar sai ga Jafar a ƙasa. Dada na ganin haka ta fara tafiya da rarrafe don ta tabbata yau su Isuhu babu lafiya, shi ya sa ta nemi guduwa kafin ita ma su dawo kanta su danne ta su saka mata rigar mama.
Jafar ya yi mamakin yadda ya gagara ƙwace kansa a hannun baba Isuhu, don haka jin baba Isuhu ya fara ɗaga masa riga sama ya fara kiciniyar kare kansa, garin yunƙurin danne rigarsa sai ga Jafar yana sakin tusa. Uwani kuwa me za ta yi ba dariya ba har hawaye saboda mugunta.
Ganin haka ba zai kai Jafar ba ya sa ya fara ihu.
"Wayyo Dada ki kawo mini ɗauki. Wayyo Allah! Mutanen gidan nan ku kawo min ɗauki su Lami za su haike mini." Uwani na daga ɗaki ban da dariya babu abin da take sheƙawa, saboda tsabar dariya har kwanciya ta yi ƙasa.
Suna cikin haka sai jin muryar Goggo Sala suka yi a bakin ƙofa ta fara lashe baki tana faɗin, "Allah na gode maka da har yanzu lokaci bai ƙure mini ba." A zabure baba Isuhu ya ɗaga Jafar, take jikinsa ya fara karkarwa ta fara tunkaro shi yana ja da baya.
"Wayyo Allah Dada ki zo Goggo Sala za ta sa a cinye ni." A madadin Jafar ya gudu tun da ya samu ya tsira sai ya bi baba Isuhu da kallo, saboda ba ƙaramin mamaki ya ba shi ba. Dada da ke cikin ɗaki ta kai wa Uwani duka tana ce wa.
"Dariyar me kike yi Uwani mu da ya kamata mu fara yunƙurin ƙwatar kanmu." Kafin Uwani ta yi magana suka ji baba Isuhu ya zuba ihu. "Wayyo ta shanye mini ƙafafu, Jafaru, Dada ku zo ku kawo mini ɗauki." Goggo Sala ba ta bi ta kan baba Isuhu ba ta shatalo ƙafafuwansa za ta sunkuta shi a baya sai ga baba Mustafa da baba Idris sun shigo.
"Subhanallahi kai Isuhu lafiya kuwa?" Suka ƙarasa maganar suna ƙarasawa wurin Goggo Sala, baba Isuhu da yake ya gama tsorata sai ji suka yi sharaf ya faɗo jikinsu da alama ya suma. Suka kama shi suka kwantar a ƙasa sai kawai Goggo Sala ta fashe da kuka.
"Yanzu shi kenan rayuwata ta zo ƙarshe."
Da mamaki suke bin ta da kallo, Baba Mustafa ya dubi Jafar da ya yi laƙwas a gefe ya ce.
"Kai Jafar wane sakarci ne haka ake yi kai kuma kana zaune?" Jafar ya sauke ajiyar zuciya ya ce. "Baba ni ma ta kaina nake da tuni sun haike mini, dube ni wai fa ni zan shayar da mai sunan Malam."
"Gara da Allah Ya kawo ku Idirisa, wallahi Isuhu shi da matarsa sun haukace. Ashe ba su kaɗai ba har da Salamatu ita ma, an ya ba gamo suka yi a cikin gidan ba. Ban da haka wai ni Isuhu zai kawowa rigar mama ya ce na saka, sannan su dubi garjejen ƙato kamar Jafaru su ce ya shayar da me sunan malam." Baba Mustafa ya yi farat ya ce.
"Shi Jafarun ne zai shayar da jariri?"
Dada ta wara hannuwa ta furta.
"Ta ya ni ji dai Muɗɗafa, ka ga dai a kan idona aka haifi Jafaru. Kai ƙarshe ma dai ni na yi jinyar shayin da aka yi masa ballantana na ce ko Jafaru ya koma mata-maza, Jafaru ko ka sauya daga baya zuwa mata-maza ne ban sani ba."
A ƙufule Jafar ya ce, "Wallahi Dada kar ki ƙara ce mini mata-maza."
Kukan da mai sunan malam yake tsanyarawa ne ya sa baba Idris ya yi wa Lami magana, sai da ta share ƙwallar idonta ta ce.
"An ce daga jiya kada na ƙara shayar da shi." A daidai lokacin baba Isuhu ya farfaɗo sakamakon ruwan da aka yayyafa masa.
"Waye ya hana ki shayar da shi?" Shiru gabaɗaya suka yi, baba Isuhu ya dubi Lami ita kuma ta kalli Goggo Sala sai kawai suka fashe da kuka lokaci ɗaya. Shiru ɗakin ya yi kowa yana bin su da kallon mamaki, ban da Uwani da ke sakin murmushi a fakaice. Sai da suka yi me isar su sannan aka samu da ƙyar Goggo Sala ta ce.
"Ni kam na san wannan jawabin da zan yi ƙila shi ne na ƙarshe a rayuwata don na san kashe ni za su yi." Baba Isuhu ya yi tsammanin bayanin 'yan ƙungiyar asirin da take ciki za ta faɗa, don haka ya zuba mata ido sai ya ji ta ce.
"Dama dai uwar garke ba..."
Kamar haɗin ba ki Lami da Isuhu suka ta fi da gudu suka toshe mata baki, da mamaki mutanen ɗakin suka bi su da kallo.
"Ƙarya take yi makira haɗa ni da 'yan uwana za ta yi." Baba Isuhu ya faɗa yana haki kamar wanda ya ci gasar tseren gudu.
"Ba ma son shashancin banza da wofi Isuhu, sakar mata baki kada ranka ya yi mummunan ɓaci." Baba Mustafa ya faɗa a fusace. Babu yadda suka iya haka suka koma suka zauna jiki a sanyaye, baba Isuhu ya sunkuyar da kai ƙasa gabansa na faɗuwa. Goggo sala ta fara wassafo jawabi tiryen-tiryen tana hawaye. Tana gama jawabi gabaɗaya ɗakin suka ɗauki salati.
"Kaico rayuwa ni Kulu me na haɗa da sata da Isuhu zai janyo mini mugun hali cikin zuri'ata." Dada ta furta tana zubar da ƙwallah. Malam na Madina da ke gefe ya ce. "An ya Isuhu yanzu rayuwar da ka ɗauko mana kenan? Wallahi ka yi gaggawar yin istigifari kuma ka nemi masu kaya ka mayar musu da abin su. Idan ba haka ba muna cikin Firdausi kana Hawiya, atoh faɗar Allah ce ba ya yafe haƙƙin wani a kan wani." Shiru ɗakin ya yi kunyar duniya ta mamaye baba Isuhu shi da su Lami. Baba Idiris da baba Mustafa suka rufe shi da faɗa sosai, don haka ya nuna nadamarsa a fili. Sannan baba Mustafa ya juyo wurin Dada.
"Dada ki gafarce ni a game da abin da zan faɗa amma tun farko ke ce kika ɓata Isuhu, saboda Isuhu yana ɗan autanki kika ɗauki son duniya kika ɗora masa. Hatta makaranta da Baba Sa'idu ya saka shi daina zuwa ya yi kuma kika goya masa baya, duk cikinmu shi kaɗai ne bai samu karatun arabi da boko mai zurfi ba. Ga shi nan sana'o'in ma wacce ce ba a nuna masa ba amma kullin a tsalle-tsalle yake ba shi da aiki sai kame-kame, tun wuri ka yi wa kanka faɗa domin kullin girma kake ƙara yi." Dada ta sharce ƙwallar da ke fuskarta ta ce.
"Yanzu dama Muɗɗafa ka na da tarin nasihohin nan tutuni ba ka yi mini ba? Ni dai wannan maganar a rufe ta a nan kada Sa'idu ya ji don wallahi sai ya kusa cinye ni ɗanya."
Gabaɗaya suka amsa mata.
"Dama wannan abin kunyar ai ba za mu bari ya fita ba Dada, yanzu dai a tambayi Uwani tun da haƙƙinta ne ta yafe masa?"
Uwani da ke gefe ta saki murmushin ƙeta ta yi saurin cewa, "Ni dai Baba na riga da na yafe musu baba Isuhu ai tamkar mahaifina na ɗauke shi." Da sauri Jafar ya dube ta don haka kawai ya ji bai yarda da kalaman Uwani ba.
"Allah Ya yi miki albarka Uwani, dama ɗa ba sai wanda ka haifa ba kaico rayuwa Allah Ya gafarta wa Yaya Umaru." Baba Isuhu ya faɗa yana sharce ƙwallah.
Uwani ta saki murmushin ƙeta a ranta ta ce, "Za ka ga ɗa ba sai ka haifa ba." Baba Idris ya yi musu nasiha sannan ya ce shi da kansa a ranar zai kira su Aramma na gangare su yi saukar Alƙur'ani a gidan gabaɗaya.
"Baba ni fa gani nake wannan abin da aka yi musu kawai tsoratarwa ne wani ke yi musu, idan aljanun gasken ne ai da tuni sun ɗauki mataki. Kada a yi wasa da hankulan mutane a dai duba lamarin." Jafar ya yi maganar yana zuba wa Uwani kallon tuhuma, don yadda ya ga tana sakin murmushi ya ji sam bai yarda da ita ba.
"Koma dai mene ne ai babu abin da ya fi ƙarfin Ubangiji Jafaru. Allah Ya yi mana maganin wannan masifa." Baba Mustafa ya faɗa, gabaɗaya suka amsa da Amin. Uwani na haɗa ido da Jafar ta sakar masa harara, haɗe da murguɗa masa baki.
07062062624
#Ummou Aslam Bint Adam🌚
[09/06/2024, 12:01] Ameera Adam: *UWANI 'YAR ƘASHIN GWIWA*
©AMEERA ADAM
*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*
Tsokaci: Ban amince a sauya mini littafi ta kowacce siga ba tare da izinina ba, yin hakan na iya kai wa ga matakin Hukuma don haka a kiyaye.
SHAFI NA BIYAR
Kasancewar sunan gidan baba Isuhu ya zo a lokacin hutun zangon karatu ya sa ilahirin zuri'ar gidan sun hallara, musamman da ya kasance baba Mamman ya dawo gida ne gabaɗaya domin lokacin ritayarsa ta kusa. Kuma a wannan kwanakin ne yake shirin tarewa a katafaren gidan da ya gina a nan cikin Unguwar rijiyar zaki da ke jihar Kano. Hajiya Saratu da iyalanta sai shan ƙamshi suke yi suna kallon mutane ɗaiɗai, don ko maganar arziƙi ba ta cika haɗa ta da sauran facalolinta ba. Sanin halinta na raini da wulaƙanci ya sa suma sauran mutanen gidan suke kama mutumcinsu ba tare da sun shiga sabgarta ba.
Asalin Tarihinsu
Malam Haruna mai shanu shi ne ainihin cikakken sun marigayi malam mahaifin su baba Isuhu. Asalinsa mutumin garin Rigana ne da ke cikin ƙauyen lambar ƙunci, ɗaya daga cikin ƙananan ƙauyukan da ke jihar Kanon Dabon Najeriya. Sunan mai shanu ya samo asali ne tun a wurin mahaifinsa kasancewarsa fitaccen bafulani a wannan ƙauyen, duk girman garin Rigana babu mai albarkar shanu da dabbobinsa. Yana da matar aure ɗaya da 'ya'ya biyu sakancewar duka maza, Malam Haruna shi ne babba sai ƙaninsa mai bin sa Sa'idu wanda bayan su mahaifinsu bai sake haihuwa ba. Bayan mahaifiyar su malam mahaifinsu ya auri mata biyu sai dai ko ɓatan wata babu wacce ta taɓa yi. Mahaifiyarsu ta rasu tun suna samari yayin da mahaifinsu ya rasu bayan da kowannen su ya yi aure a lokacin Malam haihuwarsa biyu.
Baffajo tun da ƙuruciyarsa yakan ɗebi shanu da awakinsa su tafi garuruwa kiwo bayan wani lokaci sai ya dawo gida, hakan yake yi har zuwa lokacin da su Malam suka zama samari suma yake nuna musu hanyar kiwon shanu. Sai dai tun suna yara ya fahimci sam ba su da ra'ayin kiwace-kiwacen shanun da yake yi, bayan da mahaifinsu ya rasu sai suka ɗora daga inda ya tsaya sai dai su ba kamar Baffajo ba. Don tun bayan da ya rasu bai fi sau uku zuwa huɗu suka fita da shanu zuwa wasu garuruwan ba.
A wannan lokacin ne kuma watarana bayan malam ya fita da shanun su da suka gada a wurin mahaifinsu, ya yi nisa sosai da garinsu sai ya faɗa tarkon wasu 'yan fashin daji. Kasancewar kuma sarkin yawa ya fi sarƙin ƙarfi sai suka yi masa ƙwacen shanu da yawa, kaɗan ya rage ba su hallaka shi ba ya dawo gida da tsirarun shanun da ko goma ba su kai ba. Wannan yanayin da suka shiga wasu sun dasa zargin har da saka hannun mutanen garinsu, yayin da wasu kuma suka ce jarabta ce kawai daga wurin Ubangiji.
Dalili kenan da ya sa bayan da malam ya warke suka haɗa kai shi da ɗan uwansa suka bar garin gabaɗaya tare da sayar da shanunsu, suka dawo wani ɗan ƙauye a nan garin Kura suka kafa kasuwancin su. Kuma cikin hukuncin Ubangiji sai Allah ya saka musu albarka.
Hauwa kulu Ibrahim mai allo shi ne cikakken ainihin sunan Dada asalinta mutuniyar garin Bauchi ce, baƙar bafulatana ce tana da kyau daidai gwargwado. Mahifinta Malamijo ɗan gidan malamai ne domin a rigarsu gidan su Dada ba ɓoyayyan gida ba ne. Mahaifinta yana da mata biyu da 'ya'ya bakwai. Musa shi ne ainihin sunan malam na Madina, kuma shi ne babban yayansu Dada uwarsu ɗaya ubansu ɗaya. Ya auri matarsa bayan zamansu mai tsawo Allah Ya yi mata rasuwa, sai dai bayan ita ya yi aure-aure da dama bai taɓa samun haihuwa ba. Dada ita take bin shi sai kuma Fatsime take bin Dada sai dai akwai tazara sosai tsakanin Dada da Fatsime. Fatsime ta rasu a wurin haihuwa, ta rasu ta bar 'yarta Abuwa dalilin da ya sa Dada ita da na Madina kaɗai suka rage waɗanda suke uwa ɗaya uba ɗaya.
A lokacin da mahaifiyar su Dada ta haifi Fatsime har ta cire rai da sake samun haihuwa.
Hasiya, Safare, Sule da Gali sune sauran 'yan uwan Dada da suke Uba ɗaya.
Malam ya haɗu da Dada ne a lokacin da suka tafi kiwo garin Bauchi tun mahaifinsu na raye, don haka ba a ɗauki lokaci ba aka tsayar da maganar aure bayan wani lokaci aka ɗaura musu aure. Da yake Dada nesa da garinsu za a kai ta sai mahaifinta ya haɗa ta da ƙanwarta Fatsime, a kan bayan wani lokaci idan Dada ta saba sai Fatsime ta dawo. Sai dai ko da Malamijo ya buƙaci Fatsime ta dawo malam da kanshi ya je har garin Bauchi ya roƙi arziƙin a bar musu Fatsime a wurin su. Ganin yadda malam ke kula da Dada da kuma girman da yake ba shi sai ya kawar da kai ya haƙura ya bar masa ita.
Dada da malam sun haifi 'ya'ya tara bakwai maza sai biyu mata. Baba Yunusa (Soja ne), baba Mustafa (Road safety ne), baba Idris (Malamin makarantar secondry ne), baba Mamman (Ɗan sanda), baba Rufa'i (Likita), Atika, Halimatu, marigayi Umaru wato mahaifin Uwani sai kuma Baba Isuhu (Sayar da itace yake yi).
Baba Sa'idu (Ƙanin malam) Yana da mata ɗaya da 'ya'ya biyar. Biyu maza sai uku mata. Ya auri matarsa ne tun a garin Rigana, kuma tin bayan komawarsu Kura da suka fara kasuwanci shi da ɗan'uwansa, sai ya fara tafiye-tafiye zuwa garuruwa. Sannu a hankali sai nemansa ya fi ƙarfi a garin Zaria, don haka ya ɗauki iyalinsa suka koma can da zama. Cikin ikon Allah kowannensu ya ci gaba da zama da iyalinsa. Da yake Dada kwanika ta dinga yi gabaɗaya 'ya'yanta tazarar su babu yawa, kuma a lokacin da take da cikin Baba Isuhu ne Allah ya yi wa malam rasuwa. Kafin rasuwarsa ne ya biya mata Makka, zuwan farko umara ta je ta yi sai zuwa na biyu da suka je tare suka yi aikin Hajji.
Malam Sa'idu ya kaɗu da rashin ɗan uwansa domin ko mutuwar mahaifinsu ba ta bige shi haka ba, daga nan kuma ya riƙe dukiyar ɗan uwansa da amana yana juya musu. Kuma ya ci gaba da tallafa wa Dada ita da yaranta, ya tsaya musu kai da fata suka samu ilimin addini da na zamani kuma har Allah ya ci da su suka samu aikin yi. Sai dai ba da aikin Gwamnati kaɗai suka dogara ba domin suna harkar kasuwancin kayan robobi da harkar kayan abinci.
Baba Mamman yana da matar aure ɗaya Hajiya Saratu da yara biyar. Jafar shi ne babba, Ibrahim, Shukra, Jidda, sai Mufida wacce suke kira da Auta. Hajiya Saratu 'yar aminiyar mahaifin baba Mamman ce, ba ta da son mutane ko kaɗan. Mace ce mai faɗin rai da taƙama uwa-uba tana da son kanta, ga ta da tsananin kishi sannan akwai ta son hulɗa da matan masu kuɗi. Wannan halin na ta ya sa ko kaɗan ba ta jituwa da Dada, kuma kusan halayenta ne su