Showing 15001 words to 18000 words out of 72825 words
ta ɗakin tare da jawo mata ƙofa kasan cewar dare yayi sosai.
Zaune tayi bakin gado zuciyar ta cunkushe da abubuwa da dama a zuciyar ta.
"Bake daya bace zai aura akwai wata da yake so ɗiyar Alhaji Marwan wato Leemcy, Lubna
nasan auren nan ƙaddara ce ta haɗa shi kiyi ƙoƙari ki haɗa da hakuri ki so Al'ameen ki fiddo shi
daga cikin duhun da yake, ni nasan abun akwai wahala amma hakuri zakiyi ki dage da addu'a
Halimatu da kuke gane kowa yasan ba yarinya bace mai jin magana nasan zaman ku ba daɗi
zai yi da ita ba amma kiyi hakuri komi ya faru ki ɗauka ubangiji ne ya jarabce ki ta wannan
hanyar."
Maganar Hajiya Salima ta riƙa yima Lubna yawo a cikin kai.
Zamewa tayi tare da kwanciya bisa gadon.
"Ya Allah ka ƙara mani hakuri da juriya akan duk wani al'amari da zai same ni, na rungumi
ƙaddara ta da hannu bibbiyu."
Alwallah ta tashi tayo tare da tada Sallah.
Bayan ta gama kwanciya tayi domin wani bacci da taji yana fizgar ta.
Bakin wani wawakeken rabi ta ganta tsaye ga wani iska mai ƙarfi dake neman jefa ta cikin
ramin, wata bishiya ta ƙama ta riƙe gam tana am ambatar sunan Allah.
Wata bakar hallitta mai mummunar suffa naga ta fara tunkaro in da Lubna ke maƙale tana
neman taimako.
Ilahirin jikin halittar gashi ne bazagar_bazagar tamkar wani dodo, idonta guda ɗaya ne sai
hannuwa rututu, baki ta wangale tare da kecewa da dariya.
Sai da tayi mai isarta kafin ta turbune fuska tare da nuna Lubna da yatsa.
"Kamar yadda suka tarwatsa farin ciki na na zama bawa gare su nike masu duk wani aiki da
suka sani, kema alƙawari ne na ɗauka ba zaki taba farin ciki ba a rayuwar ki damuwa da bacin
rai sune Abokan zaman ki, bashin da suka ci kece wadda zaki biya shi ba zani bari a so ki ba
bare kuma aure ki dole ne koma waye sai nayi yadda nayi kuka rabu, matsayin baiwa kike a
wurin na ke mallakina ce tun shuɗaɗɗen lokaci aka mallaka mani keee."
Yana karasa maganar ya fizgeta suka fada cikin ramin.
A firgice Lubna ta farka daga wannan mummunan mafarki da tayi, Rabin fuskar ta ne taji ya fara
motsi, gyalenta ta sanya ta rufe wurin tare da shigewa toilet tayi alwalla ta tayar da sallar asuba.
Bata koma bacci ba domin jin abun tayi wani banbarakwai domin ita a gidan su da asuba Tayi
take tashi ta hau aiki kwata_kwata bata baccin safe.
Haka taita yan tunane_tunane na wannan mugayen mafarkai da suka aure ta kwanan nan.
Hajiya Salima ce ta turo ƙofar hannun ta ɗauke da breakfast, saurin sauko wa tayi tare da gai
sheda Hajiya Salima cikin girmamawa.
"Lafiya lau Alhamdilillah ya kika tashi."
"Alhamdulillah ta amsa kanta a ƙasa."
"Lubna!."
Hajiya Salima ta kira sunan ta.
Amsa wa tayi kanta a kasa tana wasa da yatsun hannun ta.
"Kada ki dauke ni a matsayin sirika, ni matsayin ɗiya ta na ɗauke ki, duk wata damuwar ki kada
ki boye mani dake da Al'ameen duk ɗaya na ɗauke ku a wuri na."
Kanta a kasa ta furta.
"Nagode mommy."
Ba karamin daɗi Hajiya Salima taji ba da kiranta da Lubna tayi da Mommy.
Hajiya Mariya kuwa jin abinda ya faru nan ta shiga yan haibace_habaice tana sakin magana.
Hajiya Salima mace ce mai haƙuri da kawai ci dan haka ba ta bi ta kan ta ba bare kuma suyi
rigimar da Mariya ke nema.
Fadila kuwa indai zata ga Lubna yanzu zata fara kiran ta da karuwa anzo an biyo abokin iskanci
an nanike masu a gida.
Hajiya Salima ita ke kwantar ma da Lubna hankali tare da karfafa mata guiwa
Saratu kuwa jin kawar tata shuru bata sake dawowa unguwar ba kuma taje asibiti bata ganta ba
yasa yau ta yanke shawarar zuwa gidan su Al'ameen koma mi zai faru sai dai ya faru.
Lubna na kwanceba cikin dakin ta taji Saratu ta turo kofa da zallar farin ciki suka rungume juna
tare da zama bakin gadon.
"Lubna kinga kuwa yadda jikin kinya koma kinyi fresh rama ce kadai naga kin ɗan yi, shi wai
mima kike yi a cikin gidan nan."
Nan fa Lubna ta kwashe kaf abinda ya faru ta sanar da Saratu.
Guda ta yi tare da furta Alhamdulillah.
"Buri na zai cika zakiyi aure a gidan da koda wancan gantalellen Al'ameen ɗin bai sonki to
iyayen shi na sanki, ita kuma waccan da kika ce kina tsoro ni har kin bani kunya ita ɗin banza,
ke tsaya kiji wallahi ki cire ma kanki tsoron wata kishiya yadda take matsayin matar shi kema
haka keda ma kike da digi Mahaifan shi na matuƙar ƙaunar ki akan wane dalili zaki sama kanki
tsoron wata banza, cikin hidimar bikin nan ni sai na kimtsama duk masu yi maki wargi zama
ɗaya bayan ɗaya, kai ayyiriririreeee."
Saro ta sake guda.
Fadila da tazo giftawa ta ƙofar dakin Lubna jin guɗar ne ya sanya ta turo ƙofar.
"Uban waye ke yima mutane guɗa cikin gida kamar na iyayenshi."
Cewar Fadila tana ƙoƙarin shugowa dakin.
"Uwar ki ce keyin gudar ko akwai yadda za'ayi dani."
Saro ta fada tare da turo ɗan kwali gaban goshi.
Jin wannan zagi da aka maida mata ne ya sanya ta shigowa ɗakin da sauri.
Turus taja ta tsaya tare da ƙarema Saro kallo.
"Wace marar kunyar ce a cikin ku nayi magana ta zage ni."
Cewar Fadila tana mai riƙe kugu.
Saurin riƙo Saro Lubna tayi tana ƙoƙarin hanata magana magana.
"Ke ar! Uwar yan tsoro ni sakar mani hannu domin dai_dai nike da zamaninta, nice nan na baki
amsa ko akwai yadda zakiyi dani."?
Cewar Saro
"Ke ni kike kallon idona kike fadama magana."
Cewar Fadila tana mai nuna saratu da yatsa.
"Naga dai ke mutumce a cikin mutanen ma kuma mara tunani gallaƙeƙiyar banza, ko zamu
gwada ƙwanji ne a fidda reni."
Ganin yadda Saro tayo kan fadila, kuma fadila taga lallaifa inta tsaya tana ruwa domin Saro ba
irin Lubna bace da suke cin zalinta tana kyalewa.
"Ke ɗin mi, akan wane dalili zani hada jiki da ɗiyar talakawa ai sai ƙimata ta ragu, gayyar tsiya
anzo an addabi mutane."
Fadila ta karashe maganar tare da barin ɗakin cikin sauri.
"Ai da kin tsaya yau dana gwanje wannan bakin inga gobe damu zakiyi ma wani rashin daraja,
ke kuma ki zauna kowa ya riƙa taka ki kinji."
"Tashin hankali ke bani so."
"Nabi rashin san tashin hankali a guje buje a hannu, ke ki saurara kiji wallahi tun yanzu ki miƙe
ki zama mai kwatar ma kanki yanci in kika zauna haka kuwa to kowa ma zai ci gama da taka ki
kina nan zaune sasakai."
Saro ta karashe maganar tana jifa ma Lubna harara.
Sai gaf da magriba Hajiya Salima tasa driver yakai saratu har gida.
Al'ameen kuwa abun duniya duk ya isheshi domin yanzu jin soyayyar Leemcy yake tamkar ta
kashe shi.
Kai tsaye gidan Bilal ya wuce.
Jin wanna jawabi na Al'ameen yasa Bilal yi ihu tare da ba abokin nashi hannu.
"Shegen sama, kace kai auren gata iyayen ka zasu yi maka, kai wallahi su Hajiya na ƙaunarka
ba kaɗan ba, Mata biyu a rana ɗaya."
Ganin yadda Al'ameen ya bata rai yasa Bilal kecewa da dariya.
"Kaga angon mata biyu, miji ga Leemcy da kuma Lubna, wannan haɗi shi ake kira riba biyu."
Bilal ya karasa maganar tare da kecewa da dariya.
Rai bace Al'ameen ya mike tare ds furta.
"Sai kayi da wani kuma, ni na bar maka gida."
Ya karasa maganar tare da ɗaukar key yayi gaba abinshi.
"Kaga aboki yi hakuri dawo mu karasa irin shagalin da zamu sha nan da kwanaki uku."
Ko juyowa Al'ameen bai yi ba ya Tayar da mota yayi gaba.
Ganin shigowar Al'ameen ne yasa Hajiya Salima kiran Lubna tare da bata Coffee ta kaima
Al'ameen.
Jiki a sanyaye ta furta, "Mommy!"
"Kin ga Lubna ban san ki da gardama ba amshi kawai ki kai ma shi."
Babu musu ta amshi Coffee ɗin tare da nufar part ɗin Al'ameen gabanta na faɗuwa, kasan
cewar magriba ce bata iske kowa falo ba kai tsaye ɗakin ta nufa.
Tura ƙofar tayi bakin ta ɗauke da sallama.
Ba tare daya amsa ba ya ɗago tare da kallon ta.
"Kee! Wane tsautsayi ne yasa kika kwaso wannan mummunar fuskar taki kika shigo mani ɗaki."
Cewar Al'ameen yana mai dirowa daga saman gadon.
"Mommy tace in kawo maka Coffee."
Ta fada murya na kyarma.
"Ok! Jira ki gani."
Amsar zazzafan Coffee ɗin yayi tare da juye mata shi akai
Cikin rashin sa'a Coffee ɗin ya zuba a bangaren fuskar namijin.
Wata ƙara ta saki tare da dafe fuskar ta, lokaci daya ƙofar ɗakin Al'ameen wani iska mai
matuƙar ƙarfi ya rufe ta ji kake garam!
Wutar dakin ce ta dauke wata mahaukaciyar dariya aka kece da ita cikin mabanbantan
muryoyi...
___________________________________
...Murja dake ta sharar baccin ta ba tare da sanin abinda ke faruwa ba haka wannan hannu ya
rika sulalowa tare da wanka mata mari.
A firgice ta farka daga baccin tare da kallon abinda ke gabanta, ihu ta saki ganin gundulmim
hannu babu gangar jiki a gabanta.
A gigice ta diro daga saman gadon ta fada Toilet tare da banko ƙofa ta rufe tana maida
numfashi.
Rashin dabara da rabon wahala yasa ta nufi gaban mirron dake manne jikin bango da nufin
duba inda aka wanka mata mari.
Saurin waigawa tayi bayan ta ganin sak wata Hajiya murjar irinta ta cikin Mirror tana mata
dariya.
A gigice ta juya bayan ta dan ganin koda gaske ne abinda ta gani cikin Mirron.
Wayam! Babu kowa bayan ta babu kowa, sake juyowa tayi ta kalli mirror nan fa taga da gaske
mai suffar ta ce.
Ja ta fara yi da baya cike da zallar firgici, caraf Murjar cikin mirror ta zuro hannu tare da shaƙe
Hajiya Murja ta ainahi.
Idanun ta ne suka fara firfitowa waje, daga cikin Mirror ta riƙa fitowa har sai da ta fito gaba ɗaya.
"A tunanin ki duk inda kika je ba zamu iya binki ba."?
"Muna tare dake ruhinki bazai taba samun salama ba kamar yadda muma kika salwantar da
farin cikin kinmu."
Dagata tayi da hannu biyu ƙafar ta na wutsil niya a sama.
Sakin ta tayi ta faɗo kasa tare da bace wa bat, wuyan ta take shafawa cike da tashin hankali
domin ba karamar shaƙa akayi mata ba.
Da kyar ta miƙe tare da dafa ƙofa da nufin ta bude, kafin hannunta yakai ka ƙofar ji tayi ƙofar
Toilet ɗin ta bude da kanta.
Falon ta saka kafar ta cike da tsoro tana sanda zata koma ɗakin ta, da gudu taji an gifta ta
bayan ta, saurin juyiwa tayi cike da fargabar abinda zata gani.
Wayam! Bata ga kowa ba, ajiyar zuciya ta sauke tare da dafe kirji, ƙit! Taji ƙaruwar plasma dake
manne jikin bangon ɗakin ta kunna kanta.
Jariri ne karami ya bayyana cikin Tv ɗin yana mata dariya, tsabar firgita kasa motsawa tayi daga
inda take sai jikin ta dake kyarma tamkar mazari.
Wani jaririn ne ya sake bayya suka ci gaba da dariya, "Mama suka furta a tare."
Suna masu nuna ta.
"mu fito zuwa gareta."
Taji jariran sun furta.
Kafin tayi wani ƙoƙari gani tayi jariran sun fara fitowa daga cikin Tv ɗin tamkar ana amayo su
kwatsa_kwatsa, ganin yadda dandazon jaririran suka yo kanta yasa ta sulalewa kasa.
Ba ita ta farka ba sai da gari ya waye tangaram, tsamin da jikin ta yayi mata ne ya sa ta dafe
bayanta dake mata matuƙar ciwo.
A gogon dake manne jikin falon ta kar ƙarfe 12:30 da rabi dai_dai cike da mamaki take kallon
tsayin lokacin da ta kwashe a sume.
Mikewa tayi tare da nufar Toilet turus! taja ta tsaya sakamakon tuno abinda ya faru jiya.
Ganin bata da wata mafita Yasa ta fada Toilet ɗin tare da yo wanka ta yo ta fara rama sallolin da
ake binta.
Mai aikin ce ta kawo mata abinci tare da juyawa zata fita.
"Uwani."
Hajiya Murja ta kira sunan mai aiki.
"Na'am ranki shi dade."
Uwani ta amsa tare da dukawa.
"Hibba fa kin kai mata nata."
"Aa Hajiya yau Hibba tun safe ta fita."
"Je kici gaba da aikin ki."
Hakiya ta faɗa tare da sauke ajiyar zuciya jin Hibba ta fita ba karamin daɗi yayi mata ba.
Bayan gama cin abincin shiri ta hauyi domin yau dole taje ta sanar da mahaifinta abinda ke
faruwa, wajen karfe uku na yamma ta shirya tare da nufar gidan tsohon shugaban ƙasa wato
Alhaji Mamman wada.
Bata yadda driver ya bita ba domin yau tana so ne suyi sirri bata so kowa yaji.
Gudu take tsalawa tamkar zata tashi sama, zuciyar ta cunkushe da abubuwan da dama.
Abinda ya shude shekara da shekaru ne ya fara dawo mata tamkar a lokacin ya faru, firgigit ta
dawo daga duniyar tunanin da ta afka sakamakon ganin Hibba da tayi tsaye gabanta tana
niyyar taka ta da mota, a firgice Hajiya Murja tayi niyyar kauce mata ta hanyar ɗibar wata hanya
daban kafin tayi ƙoƙari taka birki motar ta kwace mata tare da kai ma wani iccen bedi dake
gefen Hanyar karo, a cike da tashin hankali mutanen da abun ya faru kan idon su suka yo
kanta...
*MEEN@T...✍*
[7/29, 5:55 PM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*TALLAH!*
Ina mata yan kwalisa , mata masu aji ,KASAITATTUN mata masu mallakan zuciyan me gida
kuzo ga ummu Abdullah tazomuku da mayikan gyara jiki,kala kala,da sabulai na gyaran jiki, da
turarreka wuta da na jiki Dana kaya da na tsuguno,da humra kala kala da shi'umar humra, da
kayan chemical,irin su liquid soap, perfume,air freshener,, Hair cream,Shampoo etc tana
kuyawa tana hada kaya ,domin Neman Karin bayani Sai kutuntibi wanna lambar 07046858716.
*PAGE 1️⃣5️⃣__1️⃣6️⃣*
...Ƙarar buguwar ƙofar ne ya sanya shi kallon ta raina 6ace, "Ki Bace mani da gani na ce maki."
Al'ameen ya faɗa raina matuƙar 6ace.
Ita kam dafe take da fuska ga kuma hasken nepa dake ɗaukewa yana dawowa.
Da yake bala'in cinshi yake ganin hasken ɗakin na ɗaukewa touch light ya zaro tare da
haskawa yaga shin ina take.
Wayam babu kowa ɗakin sai shi kaɗai, hannun shi daya ta6a jikinta ya kalla ya wani 6ata rai
tare da nufar Toilet ɗin domin wanke hannunshi.
Abun mamaki wutar Toilet ɗin lafiya lau take sabanin ta dakin dake ɗaukewa tana dawowa.
Kai ya tura tare da shigewa ya sakarma jikin shi ruwa tare da rufe idanunshi, ruwan Coffee ɗin
daya juyema Lubna akai ne photon yadda abun ya faru ya fara dawo mashi sabo fil.
Saurin buɗe ido yayi tare da nufar Mirror ɗin yana gyara gashin gemonshi, wuƙil! yaga wata
baƙar mage ta wulga ta cikin mirror ɗin, a razane ya ɗan juya domin shi kaf duniya babu halittar
daya tsana kuma yake tsoro kamar mage.
Dube_dube ya hau yi amma wayam babu mage babu dalilinta, ci gaba da aikinshi yayi tare da
watsar da tunanin magen.
Ɗago kan da zai yi ƙatuwar mage ya gani da girmanta ya kai na jaririn maraƙi ta buɗe baki tana
babbaka dariya.
Wani gumi ne yaji yana wanke ilahirin jikinshi lokaci daya wata kyarma ta kwace mashi a
hankali ya far juya akalar shi domin yaga koda gaske i ta ce,karo yaci da wata mummunar
mage da ilahirin jikinta wasu dogayen gashi ne masu matuƙar tsayi, kanta kuwa rabi fuskar
Leemcy rabi kuma ta mage.
Kecewa tayi da dariya tare da nuna shi da hannu.
"Kayi kuskuren aikata abinda kayi, ni zaka ƙonama fuska, ka ko san hukuncin wanda ya taba
fuskata, ka taba marin fuskar amma na gyaleka amma yau zaka ɗanɗana kuɗarka."
Ta karasa maganar bakinta na fidda wani irin tiriri.
Zubewa yayi bisa guiwar shi, "dan Allah dan girman Allah ki taimaka ki yafe mani, ko kallon inda
kike bazani sake ba, anti Lubna na roƙe ki wallahi bansan ke Aljana bace."
Bugun da magen ta kawo mashi a baki ne yayi sanadin hadiye sauran maganganun shi.
"Bani yafiya bani afuwa hukuncin kisa naso yanke maka, amma naga bazani iya kasheka ba
duk ƙoƙarin da nayi amma zan Kyale gane ba kowa ake tabawa ba a zauna lafiya."
"Na tuba Lubna ki gafarta mani, ina sonki ina kaunar ki wallahi kece ma Uwar gida ki ceci
rayuwata kada ki illata mijinki na roƙe ki."
Kecewa tayi da dariya tare da kallon shi a fusace
"Zaka rayu saboda wani dalilina ba zani kasheka ba amma zaka ɗanɗana kuɗarka.
Tana karasa maganar wasu kananun maguna masu kawuna rututu suka bayya tare da baibaye
Al'ameen, kafin