Showing 72001 words to 72825 words out of 72825 words

Chapter 25 - RUWA BIYU NA MEENAT A YANDOMA.pdf

Al'ameen aka sa mata SALIMA
suna kiranta (Aymana).
Ranar Suna anci ansha anyi sadaka domin nuna godiya ga Allah, Saro kam sune girjin biki
domin ranar kaya iri ɗaya suka sa da Lubna.

Malam Sule kuwa har hawajen farin ciki yayi jin yadda Lubna ta ɗauke shi a matsayi mahaifi
harta sama yaronta sunan shi.

Duk yadda Al'ameen yaso a bashi Matar shi su koma gida amma Hajiya Salima ta hana domin
ta sanar dashi sai Lubna tayi watanni biyu ta murmuje jariran ta sunyi wayau.

Badan ya so ba sai dan baida yadda zai yi haka ya hakura, Leemcy kuwa duniya ta koya mata
hankali yanzu ta shiryu mijin aure take nema ido rufe, sai ya kasance duk wanda zai zo ta
buƙatar shi ce ta kawoshi, ana cikin haka wani abokin mahaifinta mai mata ukku ya fito, babu
jimawa aka sha shagalin biki tare da miƙata gidan mijinta inda matan shi suke domin gida ɗaya
aka aje su.

Zama kam babu daɗi sai dai haƙuri domin ƴa'ƴan shi zabga_zabga suk sa'annin ta ne, koda su
kaɗai aka barta sun ishe ta gefe ɗaya kuna ga iyayen su, saukin Leemcy ɗaya mijin su na
ƙaunarta san haka ne kaɗai yasa take haƙuri da zaman gidan.

Murja Kuwa bayan gama ta kaba raban gado akayi aka bata nata ta koma wurin danginta, nan
ta samu ta auri wani direba me mata ɗaya, shima kwaɗayi ne ya kawo shi domin yaji labarin
akwai kuɗaɗe hannun ta babu jimawa akayi auren ta tare gidan mijinta.


Kamar yadda Malam Sule yayi alƙawarin ƙara aure haka aka yi domin wata bazawara ya samu
da mijinta ya rasu ita ya aure, Gaje kam tayi kukan fili dana 6oye domin tasan wannan duk
laifinta ne domin tasan halin mijinta yana sonta halin tane kawai yasa ya karo auren amma duk
da haka yana masu adalci.

Mahaifin Lubna Alhaji Jadda shima dangin shi sun taso shi gaba akan dole ya ƙara aure, shiko
har ga Allah yanzu tsoron mata yake domin abinda Murja tayi mashi har yau bai goge a zuciyar
shi ba.

Da kyar aka samu ya auri wata jawara dake cikin family ɗin shi ita ma dan dai an yaba da
halayen ta.

Ta kowane bangare rayuwa tayi daɗi zama ake na farin ciki da jin daɗi, Saro ma ta haihu ɗan na
miji yaci Sunan mahaifin Lubna Sulaiman domin har abada bazata manta da halarcin shi a
garesu ba.

Ayman da Aymana sunyi wayau domin kusan ko yaushe suna gidan su Al'ameen ƙarfi da yaji
Hajiya Salima ta amshe su, Musamman Ayman shi yafi kaunar zama kusa da kakarshi sabanin
Aymana da sai yanzu ta daina kuka in an kawo ta.

Aymana babu wanda ta saba dashi take sakarma fuska kamar Uwar garke sabanin Ayman da
tsoron ta yake ba kaɗan ba, Aymana kuwa ta saba da ita har yazo suke zuwa shiyasa sam
yariyar bata da tsoro ko alama.


Alhaji Sufyan shiya biya ma Al'ameen da Lubna aikin kujerar Hajj ya hada hada bilal da matar

shi, a tare suka keta hazo domin sauke farali.

Uwar Garke ma ba'a barta a baya ba domin ita da fuka_fukanta ta bisu.


*ALHAMDULILLAH ANAN NA KAWO ƘARSHEN WANNAN LITTAFI NAWA MAI SUNA RUWA
BIYU, KURA_KURAN DA NAYINA CIKI UBANGIJI YA GAFARTA MANI, YASA AYI AIKI DA
ABUBAWA MASU AMFANI MU HAƊE A LITTAFINA NA GABA ME SUNA ƘULLALLIYA! DAGA
JIN SUNAN BA'A CEWA KOMI KU DAI KU BIYONI DA 300 ZAKU SAMU WANNAN LITTAFI.*

*TSAKURE DAGA LITTAFIN ƘULLALLIYA!*

"Aisha mi yasa baki son zuwa asibiti? da galihunki da komi Aisha amma kin zauna gida sai ciwo
ya kashe mani ke, ni Yalwa tunda nike ban ta6a ganin inda ciki yayi shekaru biyu ba tare da an
haife shi ba ko a zamanin mu daya shuɗe duk daɗewar ciki bai ta6a haura shekara ɗaya ba tare
da an haife shi ba, amma ke cikin yau kimanin shekarun shi biyu kenan ba tare da kin haife shi
ba, wannan al'amari da ganin shi nasan akwai wata ƘULLALLIYA."
Inna Yalwa ta ƙarasa maganar tare da duban Aisha.

Wadda aka kira da Aisha ce ta ɗago da jajayen idanun ta da kallo ɗaya zakai masu ka fahimci
bata samun bacci ko misƙala zarratun.


"inna Yalwa na roƙe ki da ki dena maganar asibitin nan, a duk lokacin da zaki furta asibiti ji nike
tamkar ana yankar naman jikina, raɗaɗi gami da azaba suke addabar jikina."

Sarƙewa maganar Aisha tayi lokaci ɗaya ta ƙanƙame jikin inna Yalwa tana kurma ihu.

"Gasu nan_gasu nan kin kira sunan asibiti kin ja mani, zasu kasheni , lokaci ɗaya numfashin ta
ya tsaya idanunta suka kakkafe tamkar gawa....

*ƘULLALLIYA!*

Na kuɗi ne akan farashin N300 a tuntubeni ta wannan Number domin naiman ƙarin bayani
08133562798.




*MEEN@RT...✍*
08133562798

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login