Showing 54001 words to 57000 words out of 72825 words

Chapter 19 - RUWA BIYU NA MEENAT A YANDOMA.pdf


🚶🏻â€â™€ï¸Uwar Garke bata bada izinin a bada labarin a wannan page É—in ba🚶🏻â€â™€ï¸ Mu haÉ—e a page na
gaba....



*MEEN@RT...âœí ¼í¿»*
[8/23, 9:25 AM] Meenat A Yandoma: 👽 *RUWA BIYU!!* 👽
_Free book_



Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma



```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` 📚🖊ï¸
*M.W.A*

*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*�
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________

*PAGE 4ï¸âƒ£4ï¸âƒ£__4ï¸âƒ£5ï¸âƒ£*
...Dafarko dai suna na sulaiman sai kuma matata Gaje, asalin mu munaten Lubya ne wata
annoba a kayi ita ta baro mu da garin mu da acan ne kaf dangin mu suka rasu se yar uwar Gaje
guda É—aya da muka tsira tare, mun dawo wannan gari ne ba tare da mun mallaki komi ba.

Farkon shigowar mu wannan gari ba ƙaramar wahala muka sha ba domin sai da muka shigo ne
na fuskancin ba irin rayuwar da muke bace suke, komi nasu na kuɗi ne, nasha baƙar wahala
kafin in mallaki gida nawa na kaina har dako sai da nayi dan ganin na samu abinda zamu
rufawa kanmu asiri.
Ubangiji ya haɗani da makwafci na kirki me matuƙar tausayin jama'a wadda yasan haƙƙin
maƙwaftaka wato Mahaifin Saratu, shine wanda ya jani zuwa cikin kasuwa a hankali ya sanya ni
cikin harkokin su na kasuwan ci, ganin yadda nike da kwazo yasanya shi bani babban jari nima
na fara sana'ar sayar da hatsi.

Ta bangaren Gaje kuwa mace ce masifaffiya marar daɗin zama a ƙalla zuwan mu unguwar nan
tayi faÉ—a da mutanen da suka haura biyar, Sam gaje bata ganin girmana inyi mata Umarni ta
take shi sam ba zata bi ba, bala'i da masifar Gaje harna fara sabawa dasu batun yau ba,kamar
ko yaushe yau ma nadawo daga kasuwa a gajiye amma sam Gaje bata dafa koda kwayar
hatsiba, cike da Zallar 6acin rai na kalleta.
"Yanzu Gaje in je kasuwa in dawo amma ace baki dafa abinci ba yanzu ya kike so inyi da
yunwar dana kwaso."
Na karasa maganar cikie da takaicin a binda tayi mani.


"Nifa mazan hausawa kuna bani mamaki, yanzu Malam da wannan ƙaton cikin zanji ko kuma da
aikin gida, shikenan haka zan tashi in hau aiki ga cikin nan kasan dai wata na ya tsaya harna
fara naƙudar tsattsaye, to ni daga rana me kamar ta yau na gama dafa abinci gidan nan har sai
na sauka." Gaje ta ƙarasa maganar tare da murguda ma shi baki cike da masifar dake cinta.

"In yawo ne Gaje babu inda baki zuwa cikin unguwar nan kullum nadawo se nasa an nemo
mani ke gidaje, amma abinci da zaki É—an dafa daga bakina Sai naki shine yayi maki wahala."
Na ƙarasa maganar ina kallonta.

Miƙewa tayi tare da kallo na.
"In jajen kaza arziƙi ne malam ai sai kayi, ni kaga wucewa ta."
Gaje ta shige É—aki tare da bari na nan tsaye a inda nike.

Ganin ba yau Gaje ta fara yi mani haka ba yasa ni hura wuta tare da sulala taliya domun
saboda halin irin na gaje Babu arziƙi na koyi Girki.

Abinda zai baku mamaki shine sam Gaje bata addu'ar Ubangiji ya bata yaro nagari ko labari
ake sai dai kaji tana faÉ—ar,ita kyakkyawa zata haifa kamarta, ta tsani mummunan jariri.

Wannan maganganu na Gaje suna matuƙar bani mamaki domin ni yara na gari wadan da zanyi
alfahiri da su nike nema ba wai kyawawa ba.

A wani dare, daren da shine a salin faruwar Komi Gaje ta tashi da wata masifaffiyar naƙuda,
ihun da take rarakawa ne tana É—ura mani zagi sune suka tayar dani daga baccin da nike.

Hankali a tashe na rasa shin ina zani nufa da wannan tsohon daren Makwafcina dai Matarshi
taje unguwa shi kaÉ—ai ne gidan, wata zuciyar ce tace inje in kirawo Yayar Gaje, dan haka cikin
hanzari ba tare da tunanin abinda zai iya samuna cikin tsohon daren nan haka na fice gidan
afujajan.
Tafiya nike bakina ɗauke da addu'a domin duhun dare ne sosai bakajin ƙarar komi se kukan

karunuka, ban bar bakina hakanan ba ambaton Allah naci gaba dayi tare da karanto duk wata
Addu'ar da tazo baki na.

Ina gaf da ƙarasawa wurin kwalbatin da ta raba mu da gidan yayar Gaje wano sautin kukan
Jaririya ya dakar mani kunne, razana naÉ—an yi domin nasan badai mutum ba sedai Aljani, a
hankali na tunkari kwalbatin zani tsallaka bakina É—auke da addu'a, kukan Jaririyar ne ya
tsananta tamkar zai fasa dodon kunne na, abinda na lura shine cikin kwalbatin kukan ke fitowa,
tamkar in yi gaba se kuma wata zuciyar tace tsaya in duba, haskawar da zanyi se Ganin abu
nayi cikin kwali yana motsi kuma da gani daga ciki sautin kukan ke fitowa.

Dakewa nayi tare da addu'ar Ubangiji ya bani ikon taimakon abinda ke cikin kwalin, dirawa nayi
cikin kwalbati tare da rarumar kwalin na fidda.

BuÉ—ewar da zanyi se Ganin Jaririya nayi duk jini sai tsala kuka take, abin mamaki rabin fuskarta
ne kaÉ—ai ke kuka rabin kuma a rufe yake da zanin da aka lullu6eta.

Hannu nasa tare da fiddota na riƙe a hannuna cike da Al'ajabin wane marar imani ne ya haifata
kuma ya jefar da ita

Gabas da yamma na duba ko ina amma banga kowa ba, juyowar da zanyi se ganin mace nayi
tsaye gabana, gabana ne yayi mummunar faÉ—uwa addu'ar da nike yi ce na tsanan ta.

Tare da kafe macen dake gabana ido, mace ce da bazata haura shekara Talatin ba sanye take
da baƙaƙen kaya.

"Baiwar Allah mutum ko aljan."?
Na samu bakina da furtawa.

"Ni Aljana ce Amma ka kwantar da hankalin ka ba cutar dakai nazo yi ba, Malam Sulaiman da
farko dai ni suna na Uwar garke, ba komi bane ya bayyanar dani a wajen nan ba se zummar
É—aukar jinjirar dake hannunka domin ni in reneta, wannan jariraya da kake gani iyayenta sun
cuci rayuwarta tun zuwanta duniya zalinci da ban taba gani wata uwa ta aikata ma É—iyarta ba,
abinda nike so in sanar dakai shin zaka iya riƙe wannan jinjira me ɗauke da fuskoki biyu a
jikinta."?
Uwar Garke ta faÉ—a kai tsaye.

Hatta sanar dani da tayi ita Aljana ce bai haddasa mani faÉ—uwar gaba ba kamar yadda maganar
ta ta yanzu ta daki zuciyata; "fuska biyu, to ko mata maza ce É—iyar.
"?
Na tambayi kai na.

"Kada kaba kanka wahalar tunane_tunane, yanzu zani warware maka zare da abawa, ita dai
wannan jinjira da kake gani an haifeta lami lafiya daga baya aka yi sanadin canzawar fuskarta

wato dai ta koma RUWA BIYU rabin mace rabi namiji, shin zaka riƙeta a matsayin ɗiyarka ko
kuwa ni zaka bani ita in riketa, amma ka sani in har ka bani ita tabbas zani reneta da wata irin
guba wato gubar tsanar mahaifanta gubar rashin tausayi da kuma shirin É—aukar fansa, shin
zaka iya ruƙon ta in bar maka ita."? Cewar Uwar Garke tana me kafe Malam Suleman da ido.

Kai na ne ya cushe da tunane_tunane, "anya zan bar ta tareni wannan yarinya kuwa ya kamata
inyi jihadi ni in reneta a matsayin É—iyata, to ya zanyi da Gaje anya zata iya renan wannan
jinjira."?
Na tambayi kai na.

"Kada ka damu da Gaje, in dai ka amince da renan wannan jinjira to zani temake ka, yanzu
haka Matar ka ta sauka lafiya ta haifi mace amma sakamakon wahalar da tasha yanzu haka a
sume take, yanzu zamu É—auki wannan jaririya mu haÉ—a da É—iyar ka a matsayin yan biyu Gaje ta
haifa, ni zani gyara jariran harma da uwar kafin ta farka daga sumar da tayi, kaga koda ta tashi
zata É—auka cewa yan biyu ne ta haifa, kace mata kai ne kayi aikin gyarata da kuma Jariran, in
mukayi haka tabbas jinjirar nan zata rayu ne a matsayi É—iyar Gaje ba tare da wani yayi kokonton
wani abu ba domin dama yan biyu ana haifar wasu ba tare da sunyi kamanni ba, shin wannan
shawarar tayi maka."?
Uwar Garke ta ƙarasa maganar.

"Tabbas wannan shawara tayi mani kuma nayi alƙawarin renon ta tamkar Yadda zan reni ɗiyar
da aka haifa mani babu wanda zaiji wannan sirrin in shaa Allah har se lokacin bayyanar shi
yayi."
Ina gama maganar muka karasa gidana

Kamar yadda Uwar Garke ta fada haka ta kasance ita ce wadda ta gyara yaran tare da Uwar,
abun ka da aiki irin na Junnu hatta ruwan xafi ita ta dora mana tare dayi mani bankwana ta
bace.

Dogon Numfashin naja tare da kallon Jariran dake gefen Gaje suna sharar bacci domin wadda
na tsinto ana cikin yi mata wanka bacci ya É—auke ta.

"Ko ya Gaje zata ji in ta farka taga wannan É—iyar."
Rufe baki na keda wuya Gaje ta farka daga Sumewar da rayi.

Kallo na tayi tare da kallon jariran.
"Ni ce na haifesu."?
Ta jeho mani tambayar fuskarta bayyane da farin ciki

"Eh kin samu yara biyu duk mata."
Cike da murna ta diro daga gadonta tare da nufar yaran da aka shirya cikin kayan sanyi.

Wani ihu ta saki tare da yin jifa da jinjirar data fara É—auka.
"Na shiga Ukku ni Gaje shin Me na haifa haka, yanzu wannan Mummunar halittar diyata ce."
Gaje ta faÉ—a tare da nuna jinjirar data jefar da hannu.

Niko a firgice na É—auki jinjirar dake faman tsalar kuka tamkar ranta ze fita.

"Tabbas Gaje bakida hankali kin kasance marar ilimin addini domin duk me ilimi bazai ta6a
aikata abinda kika aikata ba, Ubangiji ya kamata kiyi ma godiya da saukarki lafiya da yayi tare
da azurtaki da kyautar da ba kowa ne ake yuma ita ba ta haihuwar Ƴan biyu, amma tsabar baki
da hankali shine zakiyi mani jifa da É—iya."? Na karasa maganar rai na a bace ga kuma jinjirar dake tsanyara kuka.

"Wallahi bani son ta bazan taba shayar da ita ba, ya zama dole a barta ta mutu domin wannan
annobace na tsaneta bani ƙaunarta, ka bani ita in murɗe mata wuya kowa ma ya huta."
Gaje ta karasa maganar tamkar zautacciya.

"Baki da Hankali, wallahi koda wasa kika salwantar mani da É—iya se kin gane wane ne ainahin
Sulaiman."
Na faÉ—a cike da 6acin ran kukan da Jinjirar ke tsanyarawa.

"Ka cuceni da baka kira mani yayata ba da nasan tana ganin abinda na haifa kafin indawo cikin
hayyacina zata murÉ—e mata wuya kowa ya huta."
Cewar Gaje dake ƙoƙarin ɗaukar ɗayar jinjirar.

Kukan da take tsayawa yayi ganin kyakkyawar jinjirarta.
"Wannan ita ce ɗiya ta, ta hannunka kuwa na yafe ta bani sonta bani ƙaunar ta."
Gaje ta fada babu kunya bare tsoron Allah.

"Ubangiji ya ganar dake, amma ki sani abinda zani faÉ—a maki ki dawo cikin hankalin ki muddun
kika bari wani abu ya samu diyata zaki gane shayi ruwa ne."

"Kanka ake ji domin ni nagama magana, ka samu wadda zata shayar maka da ita nikam zama
cikin cikina ma da tayi ban yafe mata ba dan haka wannan matsalar ka ce."

Tamkar an watsa mani ruwan darma haka na riƙa ji a cikin zuciyata, dan haka ficewa nayi tare
da ajiye mata jinjirar a gefen ta, kai tsaye kasuwa na wuce tare da sawo madarar jarirai me
matukar yawa wadda zata ishi jaririyar.

Ƴan barka ne suka fara cika gida, nan fa suka fara watsewa ɗaya bayan ɗaya jin wannan halitta
da aka haifi jaririyar da ita, nan fa gari ya hade da an haifi É—iya me fuskar mace da namiji duk
inda na wuce sai an nuna ni ana shine Ubanta, kafin kace mi gari ya haɗe da zantuttukan ƙarya
dana gaskiya, Gaje kuwa ji take tamkar ta hallakar da jinjirar, dawowa ta gida abinda na tarar ya
tayar mani da hankali domin yadda na aje Jinjirar haka na dawo na taras Gaje bata tabata ba,

daukar ta nayi tare da yi mata huÉ—u ba da Lubna, É—ayar kuma nasa mata Hawwa'u.

Lubna kuwa madara na dauko domin nasan yunwa ta gama galabaitar da ita amma sai gani
nayi dana bata sai ta maido ta, tambayar Gaje nayi ko ita ta shayar da ita, a wulakance ta
kalleni tare da fadar Allah ya sawwaƙe ta ba wannan halittar mama.

Ban sake bata madarar ba sai na kyaleta domin a tunanina ƙila wannan Aljana ta bata abinci
ne.

A haka har akayi suna mutane wasu basu sake waiwayar gidan ba, Yaya asibi ita ce yayar Gaje
wadda ke kara tira Gaje kan cewa ta kashe ta kada ta bari ta girma.

Ganin haka yasa na kashe wasu ayyukana dan ganin na lura da yadda Lubna ke rayuwa.

A wata rana da bazan taba mantawa ba lokacin na dan fita kasuwa in sawo ma Lubna madarar
ta data ƙare, tun kafin in gama siyayyar naji gabana na faɗuwa, babu shiri nayo gida affujajan.

ÆŠakin na shige tare da kwalama Gaje kira, zaune na isketa tana ma Kulu wanka.
"Ina lubna."
Ita ce tambayar dana jefama Gaje.

Banza tayi dani tamkar bataji mi nike fada ba, sai da na sake daka mata tsaka kafin ta fara
magana.

"Karfa ka cika mani kunnuwa da surutu, gani nayi ruwan wankan ta ya tafasa kai kuma baka
nan shine na É—auketa na sakata cikin tukunyar kaga in kazo sai ka tsamota ka wanke ta nasan
lokacin ta jiƙu."


Wata mummunar faɗuwar gaba ce tayi mani dirar mikiya, lokaci daya naji jiri na ƙoƙarin kayar
dani.
"Kin sakata cikin tukunyar ruwan zafi fa kika ce."?

"Haka nace ko kunnuwanka sun fara samun matsala ne bakaji magana ta dai dai ba."
Gaje ta fada cikin gadara.

A gigice nayo waje har ina tuntube da tudunka bakina na furta.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un."
Tare da nufar ƙatuwar tukunyar dake saman murhu tana tafarfasa...


*A yi mana Subscribe 👇🏻👇🏻*
https://youtube.com/ channel/UCFefdlP2piaSVv-lAANrzBQ

👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽👆🏽
Idan kuka latsa zaibude saiku latsa inda aka rubuta *SUBSCRIBE da jan rubutu*
*Aslm dan Allah yan uwa ga YouTube channel dina nan kumin subscribe za muna maku posting
na magunguna kala kala da cooking kala kala da karatu tuka da novels masu
zafi.í ½í±í ¼í¿¼í ½í±í ¼í¿¼í ½í±í ¼í¿¼í ½í±í ¼í¿¼í ½í±í ¼í¿¼*





*MEEN@RT...âœí ¼í¿»*
[8/25, 10:22 AM] Meenat A Yandoma: 👽 *RUWA BIYU!!* 👽
_Free book_



Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma



```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` 📚🖊ï¸
*M.W.A*

*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*�
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________

*PAGE 4ï¸âƒ£6ï¸âƒ£__4ï¸âƒ£7ï¸âƒ£*
...Tamkar zautacce haka na rarumi murfin tukunyar tare da jefar dashi gefe, abinda na gani
cikin tukunyar ya matuƙar bani mamaki, Lubna ce kwance saman ruwan tana sharar bacci
abinta, hannu nasa tare da É—aukota ina me yin hamdala ga Allah.

Rumgumeta nayi sosai a jikina bansan lokacin da wasu hawaye suka 6alle mani ba.
"Ubangiji kai kasan mi kake nufi da wannan baiwa taka Allah ka shiga cikin lamuranta ka kawo
mata sauƙin al'amura ya Allah, ka sanya ta cinye wannan jarabawata ta."
Na ƙarasa maganar tare da shigewa ɗakin.

A wulaƙance Gaje ta kalleni cike da mamakin ɗiyar dake hannun na bata ga ta ƙone ba.

"Kina mamaki ne da ikon Allah?, kinga muguntar da kikayi bata yi tasiri ba shine kike mamaki,
to wannan kaÉ—an daga cikin ikon Allah kenan, babu abinda zance maki duniyace Gaje wanda

be zo bama jiran shi take."
Na ƙarasa maganar tare ds Sanya Lubna cikin ɗan ƙaramin Net na jarirai."

"Oho dai in ma mayya ce sai dai ta cinyeka amma ni Gaje jini na yafi ƙarfin nata."
Gaje ta karasa maganar tare da barin É—akin.

Tabbas Gaje tayi nisa batajin kira se dai in bita da addu'a, kayan Jikin Lubna na cire tare da
canza mata wasu, baccin ta take har yanzu bata farka ba.

Bazan manta ba bayan sallar magriba ina daga tsakar gida zaune in ba Lubna madarar jarirai
na fara jiyo ihun Gaje, yunƙura nayi da niyyar in kai mata ɗauki amma kafin in ƙarasa har ƙofar
ta rufe kanta.

Cike da tashin hankali nike hallon ɗakin da gaje ke kurma ihu ga kuma ƙarar sautin bulalai nan
dake tashi ta ko ina.

An ɗauki ƴan daƙiƙu kafin ɗakin ya buɗe kanshi Gaje ta fito a guje tana soshe_soshe jikin nan
yayi jajur sawun bulala kaÉ—ai kake hangowa.

Kallo É—aya nayi mata tare da shigewa É—akin in na barta domin nasan wannan aikin Uwar Garke
ne, ina jinta tana kuka tana surfa bala'in cewa na ga irin bugun da akayi mata ko in tambaya,
kuma tasan wannan mayyar É—iyar dake hannu na ce ta aikata haka.

Shuru nayi da ita domin ni bani biye Gaje in naga tana saida hali, haka muka ci gaba da rayuwa
cikin gidan nan da daÉ—i babu daÉ—i ina tsaye kan iyalina ba tare da Gajiyawa ba duk da irin
rashin mutumci na gaje.

A haka har aka yaye Kulu ita kuma Lubna dama tun tana da wata takwas ta fara tafiya da
ƙafafunta, wannan tafiya fa da mutane suka ga tanayi ta jawo cece kuce nan suka ci gaba da
kiran ta É—iyat Aljannu wasu kuma suce mayyace, ban damu da duk wani abu da mutane ke fada
ba nidai alƙawari na ɗauka duk rintsi zani riƙe Lubna tamkar ɗiyar da nahaifa.
Duk duniya babu wanda Lubna ta yarda dashi daga ni se ÆŠiyar makwafcina wato Saratu,
Saratu na daga cikin mutanen da basu taba nuna kyama ga Lubna ba, duk duniya ita ce

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login