Showing 30001 words to 33000 words out of 72825 words
fa ta gama bani wahala a ƙafa na dawo gida a
wahalce na fara bacci sai dai naji anyi ball dani buɗe idon da zanyi naji tana in tattaro gashin ta
daya maƙale a jikina in bata, kai na fa daku ranar ba kaɗan ba."
Wata dariyar suka sake 6a66akewa da ita.
"Ina gaya maku kusha kurumin ku ranar da aka kai wannan almajirar gidan Al'ameen sai dare
yayi mu rufe gida mu naɗa mata bugun bugu."
Cewar Zuly da ta miƙe tana wata girgiza.
Kecewa suka yi da dariya jin shawarar Zuly
Da kyar suka samu feedow ta amince ta shirya tare da binsu.
Ta ko wane bangare shirye_shiryen biki kawai ake, duk da Al'ameen ya hana ayi duk wani abu
daya danganci party amma Leemcy sai da ta tattara ƙawayen ta gogaggun yan duniya suka
kama holl suka gwangwaje.
Tunda Bilal ya kyalla ido yaga Saro duk wata natsuwar shi ya rasa ta, ji yake bazai iya barin
gidan su Al'ameen ba tare daya gabatar da kokon barar soyayyar shi ga saro ba.
Da yake cikin falon suke ita da Lubna da aka gama gyarama jiki, su na hira abinsu.
"Dan Allah Amaryar mu ina da magana da abokiyar ki."
Cewar Bilal yana sosa ƙeya.
Murmushi Lubna tayi tare da tashi ta basu wuri.
"Ƙawar mu barka da safiya."
Kamar ba zata amsa ba domin bata son renin hankali tun ba yau ta lura da take_taken Bilal.
"Ƙawar mu magana fa nike."
Bilal ya katse mata tunani.
"Wai Bawan Allah lafiya nifa na tsani ɗabi'ar naci, bashi ko tara zaka zo ka tasa ni gaba da kiran
ƙawar ku ta ina na zama ƙawar ka?, kaga bani son kalar dangin da wata gantalewa."
Tana ƙarasa maganar tayi gaba tare da barinshi sake da baki.
Wani murmushi ya saki dan ya san koba komi ya samu irin matar da yake so, waɗan nan
shegun yan matan nashi yasan duk zata gyara masu zama, domin shi kaf duniya yana ƙaunar
Mace masifaffciya mara hakuri in an tabo ta sai kuma ga Saro Allah ya haɗa shi da ita.
Ta bangaren Hajiya Mariya kuwa zawo an rasa maganin shi komi tasha yaki tsayawa ta koma
wurin boka amma a banza dan haka yanzu sai dai pampers take sawa, ga kuma hidimar biki da
aka kacame da ita a cikin gidan.
Hajiya Salima tamkar ita ta haifi Lubna haka ta hidima da ita, mussaman ta ɗauko mai gyaran
jiki daga maiduguri ana gyare mata Lubnar ta, kayan ɗaki kuwa dana kitchen ita tayi mata komi
ba tare da gajiyawa ba, domin hajiya Salima ta cika mutum.
Rana bata ƙarya sai dai Uwar ɗiya taji kunya, a yau ne ɗaruruwan jama'a suka shaida auren
AL'AMEEN SUFYAN GARKUWAN TALAKA da amaryar shi LUBNA SULAIMAN sai kuma
HALIMATU MARWAN HARKA akan sadaki kowace dubu Hamsin , ɗaurin aure ne daya samu
halartar manyan mutane ta ko wane bangare yan media da sauran kafafen sada zumunta suma
ba'a barsu a baya ba.
Malam Sule dake cikin manyan kaya na kece raini da mahaifin Al'ameen ya ɗinka mashi ba tare
da sanin kowa ba wasu hawayen farin ciki yaji sun wanke mashi fuska, hannuwa ya ɗaga sama
tare da yima Allah godiya.
"Ubangiji nagode maka bisa ga wannan ni'ima da kayi mani, Allah na sauke nauyi na farko
Ubangiji ka bani ikon sauke nauyin da yafi ko wane nauyi a wurina, ya Allah ka Albarkaci Lubna
ka Albarkaci iyalan Alhaji Sufyan Allah ka saka mashi da sakayya mafi Alkhairi, ya Allah nagode
na ƙara gode maka." Ya karasa maganar tare da share hawayen fuskar shi.
Al'ameen kuwa jin wasu hawaye yayi daya rasa dalilin zubar su, wani nauyi yaji zuciyar shi tayi
mashi, wai yau shine da Aure rayuwa kenan.
Bayan kowa ya gama tafiya mahaifin Lubna dana Al'ameen mota suka shiga domin zuwa gida
yayi Sallama da Lubna.
Duk wani sukuninta yau babu gabanta keta faɗuwa, wani kuka ne ya kufce mata.
"Yau an ɗaura auren ta abinda ko wace Uwa ke gurin taga irin ranar ga ɗiyar ta amma ita
mahaifiyar ta na raye babu damar ta rabeta bare ma ayi maganar samun farin ciki a wannan
rana, ta ɗauki wannan a matsayin ƙaddarar ta."
Ganin tana kuka yasa Saro matsowa tana kwantar mata da hankali.
Sallamar Hajiya Salima ce ta sanyata kara fashewa da kuka domin tasan Mahaifinta ya karaso.
Kama ta tayi tate da nufar part ɗin Alhaji da ita, kaɗan ta hana Malam Sule zubda hawaye
lokacin da yaga an shigo da Lubna.
Nasiha ya fara mata mai ratsa jiki.
"Alhamdulillah godiya ta tabbata ga Allah daya nuna mana wannan rana mai tarin Albarka,
Lubna yau rana ce mai matuƙar amfani a wurin ki ranar da ina fatan kada ta sake maimatuwa a
rayuwar ki, Lubna a yau kin bar hanmuna kin koma hannun mijinki, kinbar gida na kin koma
gidan mijin ki, kiji tsoron Allah a cikin lamuran ki nasan ke mai sauƙin halice, Lubna komi zaki
tarar a gidan mijin ki kiyi haƙuri wata rana zai zama tarihi, a yau a dai_dai wannan lokacin naso
sanar dake wani abu a gaban mahaifiyar ki amma kash! Gaje tayi nisa bata jin kira, Ubangiji ya
albarkace ki ya baki ikon cinye duk wata jarabawa dake fuskantar ki Allah yayi maki Albarka."
Malam Sule ya ƙarasa maganar tare da goge wani guntun hawaye dake neman kuftowa.
Lubna kuwa kuka take tamkar Ranta zai fita mahaifinta ta riƙe gam ta kasa furta koda kalma
daya ce.
Da kyar Hajiya Salima ta 6an6are Lubna a jikin mahaifinta.
Ita ma Hajiya Salima nasihar ce tayi mata sosai.
"Lubna yadda na ɗauki Al'ameen haka na dauke ki ki taimaka duk wata matsala ki sanar dani
kada ki zama mai boye mani abubuwan da suka shafi rayuwar ki Ubangiji yayi maki albarka ya
baki sa'ar shiga gidan miji lafiya.
Da ƙyar aka raba Lubna da Hajiya Salima su duka suna kuka suka rabu.
Nan aka wuce da ita gidan miji.
Leemcy kuwa ita da ƙawayen ta tuni suma suka shige mota sai gidan Al'ameen, gaf da magriba
aka sada su da ɗakunan su.
Masha Allah haɗaɗɗen gida Alhaji Sufyan Ya sai ma Al'ameen daka shiga babban falone
tsakiya sai ɗakunan su Lubna.
Tun bayan kawo Amaren Ƙawayen Leemcy suka jona manyan Sifikun falon suka kunna wata
waƙa ta wasigidi Suna cashewa abinsu, sudai su Lubna daga ita sai Saro cikin ɗaki suna
labari babu wanda ya fito falon.
Bayan sun gama chashewa nan suka hau labari wai Leemcy ce da aure harda kishiya lallai ta
yi sanyi, ita kam jin abinda ƙawayen ta ke faɗa ji tayi kamar ana zuga ta.
"Nikam ina maganar koyama waccan jakar ta ɗaka hankali."
Zuly ta faɗa tare da miƙewa.
"Yana nan babu inda yaje yanzun nan zamu kaddamar mata."
Wata da ake kira Ruwai ta faɗa.
Feedow kuwa ji tayi cikin ta yayi wata katsawa dan tasan aka bigi Lubna yau kashin su ya
bushe.
A ƙalla ƙawayen Leemcy sun kai su goma masu kwana a gidan dan haka dakin Lubna suka
nufa.
Kamar suyi hauka ganin ɗakin kulle, babu yadda suka iya haka suka juyo ɗakin Leemcy cike da
takaici.
Nan suka dawo suna mitar zasu hade da ita gobe ai bata tsira ba, Feedow ce ta nufi Toilet ɗin
da ke cikin ɗakin zata yi fitsari, a guje ta Fito ta tare da bi ta saman waɗan da ke zaune saman
gadon ta haye can ƙurya tana faɗar.
"Uwar Garke wallahi ku shirya Uwar Garke ce a Toilet ɗin.
Zuly da Abun ya ƙuleta masifa ta fara.
"Uwar Garke nan tirken Awakai kika gani da zaki ce kinga Uwar Garke."?
Maganar ta ce ta maƙale sakamakon ƙofar ɗakin data rufe kanta ita kuma ta Toilet ta bude da
karfi.
Uwar Garke ce cikin Mummunar suffa ta fara yo gaba sai wasu jinga_jibgan kadan garu da
girman su yakai girman ɗan akuya, su dai waɗan nan ƙadan garu tsaye suke tamkar mutum
suna tafiya da kafar su ta baya hannuwan su na gaba kuwa riƙe suke da mulmulallen Kulki.
Wata mahaukaciyar dariya suka kece da ita data haddasa ma ɗakin girgiza...
*MEEN@RT...✍*
[8/5, 9:44 AM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*PAGE 2️⃣4️⃣__2️⃣5️⃣*
...iface_iface suka fara ganin wannan bala'i dake tunkaro su, domin tunda Uwar data haife su
basu taba ganin kaɗan gare na tafiya da ƙafafun shi ba ga kuma Uwar Garke da kamanninta
kaɗai sun isa su sanya ka sakin guntun zawo
Sai da suka gama dariyar su mai isarsu kafin su turbune fuska tare da kallo su Ruwai da suka
dunƙule wuri ɗaya jiki na kyarma.
"Madalla da haduwa ta biyu haduwar da jikin ku zai gaya maku zaku gane baku da wayo yau,
wace mara ɗa'a ce tabi ta saman ɗana dana aje ta wuce sauran ma suka take mata baya."?
Uwar Garke ta ƙarasa maganar tare da nuna yan matan da hannu.
"Kwarankwatsi dubu bani bace sai dai ko Ruwai."
Zuly ta faɗa tare da nuna Ruwai.
"Amma Alkah ya isa tsakanina dake ni zaki jona ma masifa."?
Cewar Ruwai tana Ruwai
Kecewa da dariya Uwar Garke tayi.
"Duk ina zuwa kanku, musamma ke mara kunya mai shegen surutu da baƙar aniya, mu kika
kira awaki ko yau zaki gane baki da wayo."
Kafin kace mi wata iska ta fizgo Zuly da Ruwai ta dire su gaban Uwar Garke.
Dauke su aka rika yi da mari ta ko ina, banda ihun su babu abinda kunnuwan ka zasu iya jiyo
maka, dakatawa aka yi da marin su kafin Uwar Garke ta fara magana.
"Kasancewar kune Oganni masu shirya mugunta ga kuma dan Auta da kuka taka hukuncin ku
sai yafi na kowa tsanani."
Wani yagalgalallen jinjiri mai suffar tunku Uwar Garke ta miƙo masu.
"Wannan da kuke gani ɗana ne shine kuka taka, yau kimanin shekaru ɗari cif! Amma baiyi
dariya ba dan haka ku sanya shi dariya ko jikin ku ya gaya maku, duk wasan da kuke muddun
yaki dariya to jikin ku ne zai gaya maku maza ku fara."
"Mun Shiga Ukku mun lalace, yau ni Ruwai na ɗebo ruwan dafa kai na, yanzu wannan Tunkun
zamu yima wasa, amma dai Allah ya isa tsakanina dake Leemcy, kin san gidan ki haka yake
kika sa muka zo."
"Bake kika shiga ukku ba ni zulai nina shiga tara, yanzu wannan halittar zamu saka dariya kiji fa
wani rantalelen kai kamar na Uwar turwa."
Rufe bakin Zuly yayi dai_dai da ƙarasuwar kadangarun inda suke tare da rufesu bugu ta ko ina.
Ihu suke suna kiran ƙawayen su dake saman gado ido ya rena fata, sai da suka yi masu lilis
kafin su miƙe su fara yima na ƙurungu wasa suna hawaye, kallon su yake da ƙwalelen idon shi
gida ɗaya dake tsakiyar goshi tamkar na besfa.
Fashewa yayi da kuka, sai ga Uwar Garke a guje.
"Miya faru ɗan Lele."?
"Tsunkulina suke sam basu iya wasa ba."
Ya fada tare da buɗe bakin shi mai kama da ƙofar gari.
"Tsunkuli, haba shiyasa naga kanata ƙara haɗe rai."
Nuni tayi da hannu sai ga su Zuly anyi sama dasu an ɗaure ƙafadaun su da fanka kan su kuma
yana reto ƙasa, ihu suke tamkar zasu fasa maka dodon kunne ganin azabar da zatayi masu
yasa suka kasa dena ihu, gudun da fankar ta fara ne yasa Feedow sakin wani Guntun fitsari
tare da fashewa da kuka.
"Hhh Faddausi! Kice munyi haɗuwa ta biyu, maraba lale_lale."
Uwar Garke ta faɗa tare da kallon sauran yan matan dake maƙale da juna wasu har sun fara
hawaye.
"Yau kowa sai ta goya ɗan lele kai komi yace sai anyi mashi ko jiki yayi tsami."
"Dan girman Uwarki da Ubanki kada kiyi mani haka, ki kwashi tawagar ki ki bar mani ɗaki."
Cewar Leemcy jiki na ciri.
"Hhh! Mai gayya mai aiki, ai mantawa nayi dake domin ranar nan kinci bashi na baki biya ba,
dan mugunta in kaina ya faɗi sai kin tsukuleni kike ɗauko shi, yau hukuncin ki shine goya dan
lele har gari ya waye.
"Laaah mun shiga Uku mun lalace."
Leemcy da abokan ta suka faɗa a tare.
"Ai yau muna tare daku har gari ya waye, duk sai naga kunyi laushi domun naga har yanzu da
sauran ku."
Leemcy da aka sha kwalliyar Amarci sai ga ta ta bige da goya na ƙurungu, inda zaka san na
Kurungu yafi Uwar Garke mugunta sai an goyashi sai ya ballen zanin goyaon ya faɗo ƙasa da
gangan, nan Uwar Aljanu zata riga gama kan Leemcy da bango tana sa waɗan nan
jibga_jibgan ƙadangaru suna ma Leemcy ruwan kulki.
"Na dawo kanku."
Uwar Garke ta faɗa tare da nufar su Feedow.
Ganin ta nuho su gadan_gadan yasa su tarwatsewa suna ihu kowa yayi wata hanyar suka bar
Feedow kadai data kasa tabuka komi.
"Hhh! Ke ba zani cuce ki da yawa ba, ai nan gaba ƙawance zamu ƙulla dake dan haka taso ki
ƙarasa ƙirgar da baki ƙarasar ba."
Duk da a ƙirgar gashin Uwar Garke Feedow tasha azaba amma tafi ƙaunar ƙirgar fiye da komi
domin ita kaɗai tasan azabar data sha, amma haka ta dage tana kirga gashin uwar garke.
Sauran Kawayen Leemcy dake neman hanyar guduwa tattaro su aka yi wuri ɗaya ƙadangarun
nan suka ci gaba da yi masu ruwan kulakai ta ko ina.
Tabbas ranar ƙawayen Leemcy sunga tashin hankalin da basu taba ganin irin shi ba, wasu har
suma suka yi tsabar azaba ga kuma na saman fanka dake shan tasu azabar su ma.
Leemcy kuwa dake faman goyan naƙurungu jikin ta ya gaya mata domin ji take tamjar ta goya
ƙayoyi haka yake soke mata baya ga wani cizo daya sauke mata a jiki yau kam kowa ya gane
baida wayo.
Haka suka kwana ana abu ɗaya asuba nayi Uwar garke da iyalan ta suka bace bat.
Ruwai da Zuly da aka dora bisa fanka a galabaice suma suka miƙe jiri na ɗibar su
Duk da akwai sauran duhun asuba haka kawayen Leemcy suka riƙa ficewa gidan a guje, ganin
saura su hudu yasa Leemcy tarbe kanyar fita.
"Haba Zuly yanzu kuma tafiya za kuyi ku barni, haka ƙawaye na kada kuyi mani haka."
Leemcy ta faɗa cikin marairaicewar murya.
"Nabi ƙawayen ki da gudu buje a hannu, ai Leemcy nida gidan ki har abada daga yau mun raba
jiha wai mune da hawan fanka kai yau munga tashin hankali."
Ruwai ta faɗa tare da goge guntun hawayen ta.
"Kema kika tsaya bata amsa aini gaf nike da ɗauke Leemcy daga saman hanyar nan in wuce
tun kafin waccan Uwar Garken ta dawo."
Zuly ta ƙarasa maganar cike da jin haushin Leemcy.
"Ni duk kune ku ka jaza mani bala'i, sai da nace bani zuwa harkar bikin nan amma kuka je har
gida kuka tattago ni gashi nan kun yi sanadin da kowa sai da yaji jiki a cikin mu."
Feedow ta karasa maganar tana share hawaye.
Ganin Leemcy ba zata basu hanya ba yasa suka direta wuri ɗaya tare da barin gidan a guje.
Leemcy kuwa ganin saura ita ɗaya cikin ɗaki kamar mayya ya sata fashewa da kuka tate da kifa
kanta bisa gado tana kukan wannan abu da ƙawayen ta sukai mata...
______________________________________
...
Hajiya Murja Kuwa ganin wannan sabon salo da akazo dashi ya sata yadda tabbas yau
kwanan ta sun kare domin duk wata azaba da take sha Hannun Hibba ta yau tafi ta kullum.
Tamkar ana amayo su haka suka riƙa fitowa daga cikin glass ɗin TV suna cika falon.
Wani karfi ne ya zoma Hajiya Murja ji tayi ta mike da gudu ta nihi ɗakin ta a guje ta maido ƙofa
ta rufe.
Wani gumi ne ya shiga wanke mata jiki abinda bata batayi ba shine yau ta samu bakinta ya
ambato wato addu'a, wata irin kara ta riƙa jiyowa tamjar ana tafiya bisa rihin dake ɗakinta,
rikicewa ta karayi amma duk da haka bakinta bai dena furta addu'a ba.
Wata mahaukaciyar dariya taji an kece da ita.
"Yau kinyi galaba a kanmu amma zamu hade nan gaba."
Taji wata murya ta faɗa.
Ajiyar zuciya Hajiya Murja ta sauke tare da sulalewa kasa tana maida numfashi, tabbas tasan
komi ya faru i ta ce sila son zuciya baiyi ba a rayuwa ta salwantar da rayuwar wata wadda ta
kasance mafi kusanci da ita mafi soyuwa a gare ta domin cikar wani burin su yanzu gashi nan
Allah ya bata diyar amma tana ƙoƙarin ganin bayan ta.
"Allah na tuba Ubangiji ka gafarta mamu abinda muka aikata a baya, Allah badan halin mu ba
ya Allah."
Ta karasa maganar tare da fashewa da kuka.
Yinin ranar sam ta kasa koda buɗe kofar ne bare kuma asa ran zata fito, sai gaf da magriba
Abban Hibba dawowar shi ita ce ta yi sanadin buɗe kofar.
Tambayar duniya yayi mata amma amsa daya taje bashi babu komk.
Da haka har ya gaji ya kyaleta, daren ranar sam mahaifiyar Hibba bata