Showing 39001 words to 42000 words out of 72825 words

Chapter 14 - RUWA BIYU NA MEENAT A YANDOMA.pdf

tarar kayi
mussai."
Hibba ta faɗa da wata mummunar murya.

Kecewa da dariya Hibba tayi tare da nuna Mahaifinta da hannu sai gashi iska tayi sama dashi
ana juya shi tamkar waina a tanda.

Ganin yadda ake hajijiya dashi ya sa shi fashewa da kuka yana kururuwar Hajiya ta kawo mashi
dauki, iyakar galabaituwa Yayi ta sai da idanunshi suka fara gano dishi_dishi kafin suyo ƙasa
dashi.

Nan ya baje yana nishin wahala domin yau ya fidda rai da sake rayuwa, har ya hango ta yadda
Hibba zata gama dashi, ashe dama haka Hajiya keji amma yake ƙaryata ta yake katseta aduk
lokacin da ta fara mashi bayanin halin da take samun kanta, Allah sarki ashe Aljanu shegune
sai yau ya tabbatar da haka, inda ya samu ya kubuta daga hannun Hibba motar gida Zoo zai
dauko a kwashi Hibba domin ta zama halitta abin tsoro ga bil'adama.

Tsawar da Hibba ta daka matace ta haddasa mashi dakatar da tunanin da yake.
"Wannan ya zama na ƙarshe da zaka shiga harkata ina kaunar ka shiyasa ma kaga na yi maka
hukunci mai sauki amma karka bari muyi haɗuwa ta biyu dakai tashi fice mani a ɗaki kafin insa
ayi maka rakiya."
Da gudu ya 6a66aka ya fice a ɗakin tare da bi ta sakan Mahaifitar Hibba yana ƙoƙarin shigewa

bayan gadon amma tumbin shi ya maƙale, a firgice ita ma hajiyar ta miƙe tare da barin gadon ta
buɗe toilet ta shige tare da maido kofa ta rufe.

Ta ɗauki lokaci mai tsayi a cikin Toilet ɗin kafin ta buɗe ta fito tana rarraba ido.
"Abban Hibba lafiya ka kusa latse mani yan hanji ka kai ni lahira ban shirya ba, wai dan Allah
mima ya faru ina kaje cikin daren nan."?
Cewar Mahaifiyar Hibba tana kafe shi da ido.

"Ke ar! Kina nan kina baccin asara ana can za'a kashe maki miji, anya Murja kina neman
Aljanna kuwa? Ace ina can ana neman halaka ni kina nan kin saki le6e kina bacci."
Abban Hibba ya fada a ƙule.

"Alhaji nifa ka sanya ni a duhu miya faru haka na ganka a birkice bangane inda maganganunka
suka dosa ba."
Hajiya Murja ta ƙarasa maganar cikin ruɗu.

"To yau dai kaɗan ta hana Hibba ta kasheni wahalar duniya yau nashata ba kaɗan ba ashe
abinda kike faɗa mani gaskiya ne ban yarda ba sai yau."
Abban Hibba ya karasa maganar yana mai saurin kallon ƙofa.

Murmushine ya Kubcema Hajiya Murja ganin yau shima da gani ya faɗa hannun Hibba.

"Ayyo! Murja ni kike ma dariya, Murja Mijin Sunna kikema dariya lallai Murja."


"Yi hakuri Alhaji ba dariya nike ba jimami ne nike tayaka."
Ta karasa maganar tare da gumtse dariyar dake neman kubce mata.

"Na yanke shawarar Gobe gidan Zoo zamu kai Hibba domin wannan yarinyar ba mutum bace,
barin ta cikin mu ba karamin haɗari bane ga rayuwar mu."


A firgice Hajiya Murja ta kalli mahaifin Hibba.
"Alhaji gidan Zoo fa kace?, yanzu ɗiyar mu zamu kai gidan zoo kamar wata dabba, Alhaji
kamata yayi fa mu nemi malamai ayima Hibba magani."
Cewar Mahaifiyar Hibba.

"Eh to sai mu nemo malamai ayi mata magani amma ni yanzu tsoro take bani, na tsorata da
Hibba."
Cewar Alhaji.


"Yanzu ka kwanta ka koma bacci kafin gari ya waye mu bazama neman malamin addini ko

zamu dace."

"Ni zani koma bacci murja! Kice so kike Hibba ta la6a6o ta karni, to bazani kwanta ba kedai in
kina kwanciya ki kwanta."

Ganin Abban Hibba a tsorace yake bazai kwanta ba ita kwanciyar ta tayi, mahaifin Hibba kuwa
yadda yaga rana haka yaga dare, safiya nayi yafice neman malami.


Haj murja na kitchen wurin haɗa breakfast mahaifinta yayi mata 5 miss call, tana ganin wannan
kira tasan ba lafiya dan haka kiranshi tayi domin jin mike faruwa, abinda ya sanar da ita ya sata
sakin cup ɗin Tea dake hannunta ya fadi ƙasa ya tarwatse a guje ta dauki gyalenta da key ɗin
mota ta bar gidatamkar zata tashi sama... _________________________
...Fizgota yayi yana ƙoƙarin janye gyalen da ya rufe mata fuska.

Tsoron Lubna bai wuce ganin fuskar ta da Al'ameen ke ƙoƙarin yi ba, bata an kara ba taji ta
wanke Al'ameen da wani mahaukacin mari, wasu taurari Al'ameen ya gani suna yi mashi
shawagi cikin idon kafin duhun daya rufe mashi ido ya fara yayewa.

Dafe kumci yayi cike da zallar mamakin shine yau mace ta ɗaga hannu tare da ɗauke shi da
mari lallai yau in bai ɗauki mataki akan wannan yarinyar ba tabbas bai cika Al'ameen ba, Lubna
kuwa kuka ta fashe dashi tare da zubewa akan guiwowinta domin harga Allah tasan bata marin
Al'ameen ba kaf duniya bata iya ɗaga hannu ta mari wani ba re kuma mijinta na sunna da take
matuƙar ƙauna.

A matuƙar fusace Al'ameen ya fice daga ɗakin yana dube_dube, Lubna kuwa kuka ta fashe
dashi tana tunanin irin abinda Al'ameen zai aikata a gareta yau.


Al'ameen kuwa yana fita ɗakin Leemcy ya shige tare da neman inda ya aje bindigar shi domin
yau babu abinda zai hana shi harbe waccan halittar Al'ameen ya fada cike da zallar 6acin rai.

Jin maganar Al'ameen Leemcy tayi tamkar rugugin aradu, babu shiri ta duro da gurmuɗaɗɗiyar
ƙafar ta da bata gama warkewa ba.

"Wallah ba zaka harbe taba ka haɗa mana bala'i da masifa da Uwar Garke, Al'ameen kana
hauka zaka kashe Lubna kuwa."?
Cewar Leemcy tamkar zararriya tana tarbe hanyar da Al'ameen zai bi ya fice.

"Zaki bani hanya ko sai na fara harbe ki."
Al'ameen ya faɗa a matuƙar fusace.

"Wallahi sai dai ka Harbe ni, daka haddasa mani bala'in Uwar Garke ƙara in mutu ta hanyar
Harbin bindiga da dai in mutu hannun Uwar Garke."
Ta ƙarasa maganar tare da riƙe ƙafar Al'ameen.


A matuƙar fusace Al'ameen ya harbar da Leemcy ta bugu da bango, duk da azabar zafin
buguwar da tayi amma haka ta mike ta take mashi baya a guje.

Yana fitowa ya iske Lubna zaune tana kuka, kafin ya aunata da bindiga tuni Leemcy ta shiga
tsakani tana ihu.

"Wallahi ƙarya kake, ba zaka ja mani baƙin bala'i wurin Uwar Garke ba, Al'ameen ka fara ta
kaina kafin kaje wurin ɗayar minahikar, Lubna kin cuce ni kin kulla mani mummunar alaƙa
tsakanina da Uwar Garke."
Ta karasa maganar hawaye nabin fuskarta ga majina da hawaye sun haɗe mata a fuska.

Lubna kuwa ganin bindiga tsirara a hannun Al'ameen kuka me sauti ta fara tana ƙoƙarin
guduwa.

Al'ameen kuwa tsabar baƙin ciki auna Leemcy da bindiga yayi.
"Zaki kauce ko sai na tarwatsa maki kwalwa."?
Al'ameen ya fada cikin tsawa.

"Ba zani kauce ba, wayyo ni aure ya zame mani bala'i, Uwar garke Billahil azeem babu ruwa na
wayyo Uwar Garke."
Leemcy ta shiga kurma ihu.

Fizgo Leemcy Yayi a fusace yashi wanka mata mari, duk da faduwar da tayi sai da ya bita har
ƙasa ya shiga Bugu, ihun Leemcy kadai kake jiyowa cikin gidan.


Ganin irim bugun wulaƙancin da yake ma Leemcy a guje Lubna ta shige ɗaki ta kulle ita tana
nata ihun tare da neman temakon jama'a.

Tun Leemcy na surfama Al'ameen zagi har bakin ya mutu murus, Bayan Lubna yabi a matuƙar
fusace ga bindiga a hannu.

Bilal ne yayi sallama tare da shigowa falon, a firgice yayi kan Al'ameen dake ƙoƙarin karya
ƙofar ɗakin Lubna.

Ga kuma Leemcy dake kwance kallo ɗaya zakai mata ka gane ta bugu.
"Mi kake koƙarin yi haka Al'ameen ko yan fashi ne suka ziyarci gidan naku, duba kaga Leemcy
yadda ta bugu fuskarta duk ta fara kumburi."

Cewar Bilal

"Ka rabu dani yau duk sai sun gane kurensu, harni Lubna zata daga hannu ta wankama mari."
Al'ameen ya ƙarasa maganar jijiyoyin kanshi sunyi burɗin_burɗin.

"Mari fa kace."?
Bilil ya faɗa cike da zallar mamaki.

"Yau sai na harbe halittar can in yaso nima a kashe ni."

A razane Bilal ya rike bindigar yana roƙonshi yayi haƙuri kada ya biyema zuciya amma ina
Al'ameen ya fusata da yawa.

Da kyar Bilal yayi nasarar amshe bindigar dake hannun Al'ameen.

Hakurin duniya ya bashi amma kamar ƙara tunzura shi ake, ganin Bilal zai kira su Hajiyar nan
Al'ameen ya ce ya hakura amma sai ya sauke haushin shi kan Lubna dole ne ita ma jikinta ya
gaya mata.

Leemcy kuwa ganin ita ma Allah ya kawo masu wani cikin gidan miƙewa tayi a guje ta faɗa daki
ta kulle.

Juyin duniya sunyi amma sam Lubna taƙi ta buɗe ɗakin kukan ta kawai take tamkar ranta zai
fita.


Lubna kuwa bata buɗe ɗaki ba sai bayan da Al'ameen ya tahi yima Bilal rakiya.

Falon ta zube tana maida numfashi domin yau ta azabtu da kukan da ta sha.

Ko kallon inda take baiyi ba haka ya tsallae ta ya shige ɗakin ta, Lubna kuwa alƙawari tayi koda
zai yanka naman jikin ta sai ta sa me shi ta bashi haƙuri.

"Dan girman Allah kayi hakuri wallahi bani bace na mareka wannan ba halina bane, ka gafarta
mani ba zani iya marin wani ba bare kuma kai."
Ganin irin kukan da take cizga tamkar ranta zai fita ya sashi kallon ta a fusace.

"Bani son renin wayo in baya ga Kin rena mani wayo ki daga hannu ki mareni yanzu kina fadar
bake bace, mi kika mai da ni."?

"Bani bace."
Ta faɗa tana kuka tamkar zata shiɗe.
Ficewa yayi yabar mata ɗakin rai bace.

Sake fashewa tayi da kuka domin tasan wannan aikin na rabin fuskar ta ce, kecewa aka yi da
dariya "Da sannu sai nayi sanadin rabuwarki da kowa domin ni bani yafiya bani afuwa."

Ɗif maganar ta tsaya lokaci ɗaya tamkar anyi ruwa an ɗauke.

A yanzu hawayen fuskar tama sun dena zuba sai dai ajiyar zuciya da take saukewa kawai.

A cikin yan kwanakin Lubna tasha azaba wurin Al'ameen tamkar ba gobe, bugu dai ba wani abu
ba tasha shi tamkar zai kasheta, Leemcy kuwa ta tsorata domin yanzu ta gane wata aura dan
haka yanzu takardar saki take nema ido rufe, ga babban abinda ke damun ta kawayen ta da har
yanzu sun ƙi daukar wayarta ko ta kira su, wannan abu ba karamin tayar da hankalin Leemcy
yayi ba, domin ita yanzu ta tsorata da lamarin Uwar Garke, bata da burin daya wuce Al'ameen
ya sawwaƙe mata ta rabu da masifar da take ciki.


Hajiya Mariya kuwa zawo sai abinda yayi gaba, amma bata da burin daya wuce taje gidan
Al'ameen ta aiwatar da aikin dake gabanta.

Ba karamin mamaki Hajiya Salima tayi ba jin mariya zata gidan Al'ameen,amma sanin zargi
baida kyau kauda zargin da take tayi tare da yima Mariya fatan fatan dawowa lafiya.


Shigar Hajiya Mariya gidan Al'ameen ba ƙaramin mamaki tayi ba domin taga yadda Alhaji
yayima ɗan lelen shi 6arin kuɗi ita kuma ɗiyar ta na can ta shiga duniya.

Ƙutawa tayi tare da fiddo maganin, ganin , Lubna ta shiga ta kawo mata ruwa maganinta ta
fiddo tare da nufar ƙofar shigowa falon tasan dai dole in Al'ameen ya dawo zai tsallaka
maganin.

Cike da farin ciki ganin ta aiwatar da aikinta ta miƙe zata koma mazaunin ta.

"Baki baɗa maganin da kyau ba domin can ga wuri can maganin bai je ba."
Hajiya murja taji wata murya ta faɗa.

A firgice ta juyo dan gane ma idonta me wannan murya, Uwar Garke ta gani rike da wani
jibgegen Kulki tsaye gabanta.

Wani miyau Mariya ta haɗiya ji kake ƙuttt! zawo ne ya kubcema Mariya ra6a6a yana bin
kafafunta, ba shuri tayi zaman yan bori ta6ar!....

*MEEN@RT...✍*[8/13, 6:37 PM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_



Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma



```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*

*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*�
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________

*PAGE 3️⃣2️⃣__3️⃣3️⃣*
...Gudu Hajiya Murja ke sheƙawa tamkar zata tashi sama, Ubangiji ne kawai ya kaita gidan
mahaifin nata lafiya.

Ko parking bata gama yiba ta fito a guje ta afka gidan mahaifin nata, tamkar zautacciya haka ta
hau neman shi tsakanin falo da kuma ɗaki, ganin ya fito a wani ɗaki ne ya sanya ta zubewa bisa
guiwowinta tana mai da numfashi.


"Baba ashe babu abinda ya sameka, na tsorata matuƙa da abinda ka faɗa mani."
Ta ƙarasa maganar a firgice.

Matsowa yayi tare da zama gefenta.
"Murja gani na tsaye da kikayi da ƙafafuna ba shi bane tabbacin lafiyata lau, ki kwantar da
hankalinki kiji abinda zani faɗa mani
"Murjanatu muna cikin gagarumin tashin hankali wanda a binciken da akayi mana asirinmu na
gaf da tonuwa, bala'in dake tunkaro mu ba ƙarami bane, yanzu haka rayuwar mu na cikin garari,
dama hausawa sunce abinda ka shuka shi zaka girba."
Alhaji Mamman ya ƙarasa maganar cikin karyayyar murja.

"Dama na sani Hibba ita ce ajalina, baba mutuwa zanyi Hibba sai ta kasheni."
Murja ka ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka.


"Kiyi haƙuri yanzu haka Boka nacan ya dage aiki babu dare ba rana, kedai ki kiyayi haɗuwa da

Hibba cikin yan kwanakin nan."
Cewar Mahaifin nata.


Kasa magana tayi domin tasan kwanakin barin duniyar ta sune suka ƙaraso, mahaifinta ne ya
katsema ta tunanin da take tare da miƙo mata yar ƙaramar laya

"Wannan ita ce ƙarshen magana, ki maƙalata a cikin gashin kanki kada ki kuskura ki rabu da ita
duk rintsi."
Ya ƙarasa maganar tare da jaddada mata.


"Baba In ta faɗi mi zai iya samuna."
Cewar Hajiya Murja.

"Kada ma kiyi kuskuren bari ta faɗi domin in ta faɗi akwai gagarumar matsala."
Cewar Mahaifinta.

Jin yadda mahaifinta ke nanata akwai matsala cikin tsakiyar gashi ta tura layar, ganin mahaifin
Hibba ya tafi nemo Malamin da zai yi mata rr
rukiya, ya sanyata yin bankwana da mahaifin nata.

Tafiya take amma sam hankalinta bai kan driving ɗin da take, Ubangiji ne kaɗai ya kaita gida
lafiya, ko parking bata gama ba ganin motar Alhaji yasa ta fito tare da shigewa gidan da sauri.

Zaune ta ganshi shida wani mutumin da kallo ɗaya zakayi mashi ka shaida Malami ne ga dai
wani rafkeken rawani a kanshi ya dage sai zazzare ido yake shiga malami.

Hajiya Murja ce ta ƙarasa wurin Alhaji.
"Wannan ne malamin."?
Hajiya Murja ta tambaya murya a ƙasa_ƙasa.

"Shine mana ko bai yi maki kama da malamai ba, to wannan da kike gani shahararren malami
ne mai faɗa da duk wasu hatsabiban Aljani da suka gagara."
Cewar Alhaji.

Alama tayi ma Abban Hibba da suje ɗaki akwai magana, dan haka nan suka bar malamin cikin
falo.

"Alhaji anya wannan malami ne? Ni fa ina ga kamar malam nan ne masu ci da addini masu
karyar malumta alhalin suba malamai bane."
Cewar Hajiya Murja.

"Ki rufe mani baki!."
Abban Hibba ya faɗa a tsawace.

"Kin san iyakar wahalar da nasha kafin a haɗani da Gwari, ki fita idona in rufe bani son shirme,
ina hibbar take ."
Ya ƙarasa maganar a fusace.

"Allah ya baka haƙuri, Yanzu na dawo gidan Hibba na can ɗakin ta kaje ka duba."


"Yanzu Murja ni zaki aika? In aikeki ki aike ni, maza kije ki kira Hibba kafin raina ya baci."

Jiki sukuku cike da zullumin shiga ɗakin Hibba Hajiya murja ta nufi kiran ta.

Malam gwani kuwa ganin haɗuwar wannan gida da tsaruwar shi ya sashi sakin baki yana
kalle_kalle.
"Kuji fa inda kuɗin mu suke, aikam a kawo itama yar banzar yarinyar in same ta in zane raɗau
domin ni nan ko cikakkiyar addu'a ban iyaba, yau dawa tayi nam gani zani samu kuɗi a sama."
Gwani ya ƙarasa maganar tare da gyara tanƙamemen rawaninshi.

Abban Hibba ne ya fito yana mai yima Malam Gwani sannu, babu jimawa sai ga Hibba ta fito
tamkar mutuniyar kirki ta neme wuri gefen gwani ta zauna.

Abban hibba ne ya fara magana.
"Ya Malam ga marar lafiyar nan."
Cewar Abban Hibba.


Ɗaga kai Gwani yayi yana kallon Hibba.
"Keee! Ɗaga idonki ki kalle ni bani son sheɗanci ko kuma yanzu in saba maki kamanni domin in
ana gaban mu biyayya ake."
Jin abinda Malam Gwani ya faɗa yasa Hibba sakin Wata Shu'umar dariya tare da Kallon Gwani.

"Alhaji wannan sheɗanun jikinta baƙaƙen ne aikin su akwai wahala amma kafin mu fara karatu
da bugu zamu fara domin sai sun ji jiki zasu fita."
Gwani ya ƙarasa maganar tare da fiddo wata jibgegiyar dorina irin wadda dogarai ke bugun
doki da ita.


"Ai indai zasu fita kada kaji komi ya shehi kaci gaba da aikin ka."
Abban Hibba ya faɗa yana gyara zama domin ganin yadda za'a cirema Hibba Aljanu.

Ganin zasu fara cire Aljannun Hajiya Murja ɗaki ta shige.

Karkace kai Gwani yayi tare da aje rawani gefe ya cire babbar riga itama ya ajiyeta gefe ya
ɗauki zabgegiyar doriya ya nihi Hibba dake zaune ta ƙura mashi ido.

Iyakar ƙarfin shi ya ɗaga bulakar nan ya shiga sauketa a jikin Hibba ji kake taaaa!

A ƙalla yayi mata bulala takai Goma amma ko gezau bata yiba sai ƙura mashi ido da tayi tana
murmushi.

Tamkar walƙiya haka Hibba ta fizge Bulalar dake hannun Gwani ta kece da wata mahaukaciyar
dariyar data haddasama ɗakin girgiza, a guje Abban Hibba ya take ma Hajiya Murja baya suka
maido ƙofa suka rufe.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login