Showing 63001 words to 66000 words out of 72825 words
mashi zuciya.
"Matar da yake aure ita ce A hotel ita da wani suna gantalewa? Nikan mi ma ya kai ni na auri
Leemcy."?
Ta tambayi kanshi.
Mahaifin Al'ameen ne ya fara magana.
"Amma Halima bata kyauta ba ta cuci rayuwar ta, domin ba kowa ta cuta ba sai kanta, shiyasa
ake so a duk inda kake ka kasance mutumin kirki yanzu da mutuwa Halimatu tayi a halin da
take ciki tace ma Allah mi, ta mutu tana zina alhali da auren ta wa'iyazubillah! Ubangiji ka
tsaremu da aikata duk wani abu daya sa6a maka, kun yi sa'a domin kuwa wancan da kuje gani
Malami ne in da rabo Halimatu zata iya warkewa."
Mahaifin Al'ameen ya ƙarasa maganar tare da kallon Malam Saif.
Umurtar mahaifiyar ta yayi da ta matso kusa ta riƙe ɗiyar ta.
"Malam kada ka wahalar da kan ka domin nice nan na bigeta."
Uwar garke ta ƙarasa maganar tare da matsowa kusa da Leemcy, hannu tasa ta shafi fuskar
Leemcy, jikin Leemcy ne ya fara motsi kafin ta fara atishawa sai kuma ta Buɗe idanunta ta fara
bin mutanen falon da kallo ɗaya bayan ɗaya, tozali tayi da Uwar garke dake gabanta zaune,
wata irin zabura Leemcy tayi sa'i ɗaya ta fara kurma ihu tana ƙoƙari bangaje mahaifiyar ta ta
fice ɗakin.
"Innalillahi, la'ilaha illalahu, Amanar rasulu, li'ilafi ƙuraishi, Uwar Garke yau ni na shiga uku
jama'a kuzo ku cece ni wayyo Uwar garke zata sabauta ni wayyi hu_hu jama'a."
Leemcy ta cika falon da ihu tamkar zata tarwatsa dodon kunnen jama'an dake falon.
"Ki natsu ki dawo cikin hankalin ki, waye ya aike ki yawon banzar ki da had zaki cika ma
mutane kunnuwa da iface_iface."
Mahaifiyar Leemcy ta faɗa rai a matuƙar bace.
"Aljana ce, wallahi Aljana ce ku taimake ni ku barni in fice daga gidan nan, baku san wace ce
uwar Garke ba ne."
Leemcy ta ƙarasa maganar jiki na kyarma.
"Baiwar Allah ki kwantar da hankalinki, a yanzu Uwar Garke ba zata cutar dake ba domin tana
cikin jerin mu na musulmai."
Malam Saif ya faɗa.
"Wannan ya zama darasi a gare ki domin da ace da ƙarar kwana da tuni kin mutu bayan gama
sabon Allah da kika yi alhalin kina da auren ki, wannan wane irin bala'i ne shiyasa ga mu nan
fitintunu sun addabi Al'ummar mu ta ko ina, kina musulma ɗiyar musulmai amma kina aikata
abinda ko wasu marasa addini ba zasu aikata shi ba." Nan malam Saif ya shiga yima Leemcy nasiha me shiga jiki da ma duk wanda yake zaune a
wurin.
Kuka sosai Leemcy keyi domin tunda take bata ta6a jin nadama makamanciyar wannan ta
shigewa ta ba, juyowa tayi da runannun idanun ta tare da zubewa bisa guiwowin ta, tana me
fuskantar Al'ameen.
"Ni me matuƙar laifi ce, laifin da in dai baka yafe mani ba tabbas zani haɗu da fushin Ubangiji,
na roƙeka da Girman Allah ka yafe mani ko da zani ga da kyau a rayuwata, tabbas nayi
abubuwa da dama dan ganin na aure ka, bani so ayi tone_tone nidai yafiyar ka nike nema."
Leemcy ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka.
"Na yafe maki, muma Ubangiji ya gafarta mana, amma zama tsakani na dake ya ƙare domin
bazan iya ci gaba da zama dake ba, ko da ace na zauna dake tofa zargin ki zan riƙayi kuma shi
zargi yana kashe aure, dan haka kije na sake ki saki Uku."
Al'ameen ya ƙarasa maganar tare da Kallon Leemcy.
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun."
Ita ce kalmar da mahaifan Leemcy suka furta cike da tashin hankali.
Leemcy kuwa taji daɗin sakin nan domin koba komi sun rabu da Uwar garke rabuwa ta har
abada.
Cike da jimamin wannan ɗanyen hukunci da Al'ameen ya yanke Hajiya Salima ta fara magana.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Al'ameen har saki har Uku a gaban idon mahaifan ta."?
"Kiyi haƙuri, wallahi bazan iya ci gaba da zama da Leemcy ba."
Al'ameen ya ƙarasa maganar kanshi a ƙasa.
"To alhamdulillah domin ta wannan hanyar sakin shine maslaha, muddun zargi ya shiga
tsakanin ma'aurata yana kashe aure ne, sai dai muce Ubangiji yasa haka shine mafi alkhairi."
A tare suka amsa da Ameen.
Mahaifin Hajiya Murja kuwa tuni ya fara zabga ihu yana tona ma kanshi asiri duk wasu abubuwa
daya aikata nan ya riƙa bayyana su yana zabga ihu.
Mutane da dama sun tausaya mashi amma da suka tuna ance kowa ya sai rariya yasan zata
zubda ruwa, Murja kuwa kuka take tamkar ranta zai fita cike da nadamar abubuwan da suka
aikata.
Mahaifan Leemcy bankwana suka yi tare da ficewa daga gidan, Malam Saif magungunan da
za'a riƙa ba Lubna ya sanar dasu, tare dayi masu fatan alkhairi shima ya fice.
Idanuwanta ne suka fara motsi kafin ta fara ƙoƙarin buɗe su, tamkar wata baƙuwar duniya haka
ta riƙa jujjuya idanun ta tana sauke su ga mutanen falon.
Cikin hanzari Hajiya Salima, Alhaji Jadda da kuma Malam Sule suka ƙarasa wurin Lubna dake
ƙoƙarin tashi.
Masha Allah ita ce kalmar da duk jama'ar wurin suka furta yayin da suka yi tozali da Lubna da
ainahin kyawunta ya bayyana, baƙa ce amma ko cikin baƙaƙen ita me kyau ce, fuskar nan
ubangiji ya ƙawata mata ita da dukkan wani nau'i na kyau abun sai da ace masha Allah.
Al'ameen kuwa mutuwar zaune yayi domin kyau irin na Lubna tabbas bai ta6a tunanin za'a
samu wata mace a cikin matan ma baƙaƙe da irin wannan kyau ba.
Yadda taga sun tunkaro ta ne yasa ta fashewa da kuka tare da faɗawa jikin Hajiya Salima,
domin kaf abinda ya faru Lubna naji, taji komi taji yadda mahaifiyar ta tayi mata.
"Lubna yanzu ba lokacin kuka bane lokaci ne na farin ciki da miƙa godiyarki ga Allah daya nuna
maki samun lafiyar ki, kuka ba naki bane."
Malam Sule ya fada cike da kaunar Lubna.
"Zo gare ni ɗiyata, zo in ji gumin jikin ki, kin rayu ba tare da ni ba, an rabamu tun kina jaririya, in
ba yanzu ba bantaba sanin cewa ina da wata ɗiya a duniyar nan ba."
Alhaji Jadda ya karasa maganar tare da goge guntun hawayen da yaji sun gangaro mashi.
Daga ita har Jadda kuka suke cike da so da ƙauna wanda ke tsakanin ɗiya da Uba.
Murja ko tamkar ta6a66iya haka ta zube a gaban Lubna tana roƙon ta cewa ta yafe mata.
"Na cutar dake, nasan da wuya ki kalkeni a matsayin mahaifiyarki saboda irin cutar da nayi maki
babu wata mahaifiya a faɗin duniya da ta ta6a yima ɗiyarta irin ta."
Kasa karasa maganar Murja tayi sakamakon kuka da yaci ƙarfin ta.
"Ke mahaifiyata ce kuma na ɗauki wannan abun a matsayin ƙaddara ta, na yafe maki Ubangiji
ya yafe mana."
Cewar Lubna tana kuka.
Jikin Murja ne ya sake yin matuƙar sanyi, cike da zallar nadama ta kama mahaifinta dake ta
hauka suka fice tana zubda ruwan hawaye.
Gaje Kuwa roƙon Lubna ta riƙayi hawaye na bin fuska.
"Nasan bani da bakin da zan roƙeki akan ki yafe mani domin na cutar dake mafi munin cutarwa,
Ubangiji ne ya fara nuna mani sakayya keda na banzatar nike ma fatan lalacewa sai gashi nan
ɗiya ta ce ta lalace,dan girman Allah ki yafe mani badan halina ba."
Lubna me matukar sanyi hali ce dan haka babu bata lokaci ta yafe masu.
Malam Sule shida iyalin su bankwana suka yi zasu fice, nan fa Lubna ta tubure sai ta bisu, da
kyar malam Sule ya shawo kanta ta haƙura ba zata bisu ba.
Alhaji Jadda ma koda zai tafi baiyi yunƙurin tafiya da Lubna ba nan ya barta wurin Hajiya
salima.
Hajiya Salima kuwa tamjar zata maida Lubna cikin ciki haka take ji, ƙaunar yarinyar na ƙara
shigarta.
Duk yadda Al'ameen yaso su haɗu da Lubna amma abun yaci tura, sa'ar daya samu ita ce
Lubna na shiga kitchen yayi saurin tare ƙofar kitchen ɗin.
Juyowa tayi cike da mamakin wannan sabon hali daya bullo dashi.
"Amincin Allah ya tabbata ga matar Sunnah."
Al'ameen ya faɗa yana me jingina da bango
Lubna kuwa mamaki me ya kasheta
"Ko ba matar Sunna ba? Shin wai kama manta da wadda kake tsaye gabanta ne, Baƙa
mummuna me mafi sunin halintta wadda ka tsana mafi munin tsana, shin mi kazo yi wurin
wannan Baƙar halitta kuma mummuna, kamar yadda ka gujeni lokacin da nike cikin mummunar
halitta haka nima yanzu zani murtsuke wannan auren naka in je in aure kyakkyawan namiji Fari
sol kuma santalele."
Lubna ta karasa maganar tana me Yin fari da ido.
Wani mahaukacin kishi ne ya lullu6e zuciyar Al'ameen ji yayi tamkar ana zuba mashi ruwan
darma a zuciya, a fusace ya haɗe Lubna da bango tare da shaƙe mata wuya.
"Ƙarya kike, a gaba na kike ambatar zaki murtsuke mani aure kije ki auri wani banza, ƙarya kike
yi Lubna."
Ka karin wahala Lubna ta fara, Hajiya Salima kuwa a guje tayo kanyar kitchen ɗin ita da Uwar
Garke da ta bayyana yanzu suna rige_rigen shigewa kitchen ɗin...
*MEEN@RT...✍*
[9/5, 9:16 AM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*PAGE 5️⃣4️⃣__5️⃣5️⃣*
....Fizga ɗaya Uwar Garke tayi ma Al'ameen ta fincike shi daga shaƙar da yayi ma Lubna.
Cike da zallar mamaki Hajiya Hajiya Salima ta fara magana.
"Al'ameen anya kana da hankali? Ɗiyar mutane zaka shaƙe ka haɗe da bango shin kisan kai
kake so kayi? Mi ya haɗaku har haka."?
Hajiya Salima ta ƙarasa maganar cike da 6acin rai.
Lubna dake hannun Uwar Garke numfashin wahala ta riƙa medawa.
Al'ameen kuwa har lokacin idanun shi jajur suke tamkar gauta, ga wani ɗaci da yaji yana taso
mashi ya haɗe ilahirin maƙoshin shi dan haka ya kasa furta koda kalma ɗaya ce.
"Za kayi mana bayani ko sai ranka yayi mummunan 6aci."?
Hajiya Salima ta fada a fusace.
Lubna ya kalla da har yanzu bata ƙarasa dawowa cikin hayyacin ta ba sannan ya fara magana.
"Har ni yarinyar nan zata kalla tace zata murtsuke aure na taje ta auri wani, ina matsayin
mijinta."
Ya ƙarasa maganar a fusace.
"Amma tabbas baka da hankali, to in ma Lubna tace haka ai dole ka aiwatar yarinyar da taci
wuyarka dama can ba sonta kake ba sai yanzu zaka wani shaƙeta, to ka bude kunnen ka da
kyau kaji in dai Lubna tace ta gama zama da kai dole ka sawwaƙe mata."
Hajiya Salima ta karasa maganar tare da wurga ma shi harara.
Uwar Garke ce ta kar6e zance.
"A wane daliline zaka shaƙe mani ɗiya kana neman rabata da duniya? Kai Al'aminu tsaya kaji
har yanzu a Uwar Garke ta nike yanzu ma kawai kawaici nayi maka amma da jikin ka ya jima da
gaya maka, haka kawai kasamu Lubna ka shaƙe, to kayi na ƙarshe dan kaɗan daga cikin
aikina ne in maka kamun kazar Kuku a wurin nan, Al'ameenu ka fita idona in rufe." Uwar Garke ta ƙarasa maganar tare da ficewa da Lubna daga kitchen ɗin.
Take masu baya Al'ameen yayi a fusace yabar gidan, rarrashin Lubna suka hau yi domin cewa
tayi gidan Malam sule zata koma da kyar suka shawo kanta ta amince zata zauna.
Jim kaɗan Sai ga Saro ta bayyana a gidan, a ranar sunyifarin cikin da basu taba yin irin shi ba
domin saro tayi murna sosai da samun lafiyar Lubna tamkar ta zuba ruwa ƙasa tasha.
Ko kaɗan Lubna bata yi gigin sanar da Saratu abinda ya faru yau tsakaninta da Al'ameen ba,
Sai ma saratun ce kece mata ita dole ne yanzu taja aji ta dan gasa Al'ameen ta yadda zai gane
kuskuren shi na baya.
Murmushi Lubna tayi domin harga Allah tana matuƙar ƙaunar Al'ameen shiyasa ba zata iya
bashiwata wahala ba sakamakon son da take mashi, kauda maganar Lubna tayi tare da yima
Lubna batun Bilal.
"Baba ya amince ma Al'ameen yanzu haka an kawo kuɗin Aure na, nan da wata hudu, amma ji
nike anya zani iya rayuwa da Bilal, yaro ne mara natsuwa sam kanshi rawa yake."
Saratu ta ƙarasa maganar.
"Saratu ke shaida ce, yadda rayuwar ta baya ta kasance da Al'ameen amma yanzu komi ya
canza, Saratu haƙuri zakiyi domin Bilal na matuƙar ƙaunar ki, zaki iya canza shi ta hanyar yi ma
shi addu'a tare da kuma nuna ma shi hanyar gaskiya da kuma nusar dashi abinda bai da
amfani, mai haƙuri shike dafa dutse."
Jikin Saro ne yayi sanyi nan taji tabbas zatayi iyakar ƙoƙarin ta wurin ta canza Bilal, yinin ranar
haka suka yini suna fira Ta yaushe gamo, sai gaf da magriba saro ta tafi.
Bayan tafiyar ta ne Hajiya Salima ta iske Lubna har daki, ganin ta da tayi ne yasa Lubna
matuƙar jin kunyar ta domin tasan sam bata kyauta ba abinda tayi ma Al'amin domin koba komi
ya kamata ace yaci darajar mahaifiyar shi.
Zama Hajiya Salima tayi kusa da Lubna tare da fara magana a hankali.
"Lubna!"
Hajiya Salima ta kira sunan ta a hankali.
Lubna kuwa kanta a ƙasa ta amsa.
"Banji daɗin abinda ya faru ɗazu ba, Lubna keda Al'ameen duk ɗaya na ɗauke ku, in kina da
matsala ni mahaifiyar ku ce kada ki boye mani komi wallahi koda ace baki son Al'ameen saki
kike buƙata nice wadda zani tilasta shi ya sake ki, Lubna ina maki soyayyace ta tsakani da
Allah, shin kina buƙatar Al'ameen ya sawwaƙe maki."? Hajiya Salima ta karasa maganar tare da kafe Lubna da ido.
Lubna kuwa gabanta ne yayi mummunar faɗuwa domin har ga Allah tana son mijin ta bata fatan
rabuwa dashi, sake tambayar ta da Mahaifiyar Al'ameen tayi a karo na biyu ne yasa tayi saurin
girgiza ka alamun tana son mijin ta.
Murmushi Hajiya Salima tayi tare da kamo hannun Lubna.
"Ke yarinyar kirkice wadda bata da butulci ko kadan, duk da kin samu lafiya amma baki guji
ɗana ba, sabanin shi da ya nuna maki zallar kiyayya, Lubna nagode Ubangiji yayi ma rayuwar ki
Albarka."
Jim kaɗan sai ga Alhaji Jadda yazo gida tare da buƙatar shi ta abashi Lubna domin dangin shi
su ganta, babu musu Hajiya Salima ta shirya Lubna tare da haɗa mata kayanta tayo masu
rakiya har bakin mota, mahaifin Al'ameen kuwa bai bar wurin ba sai da Jadda ya bar harabar
gidan, cike da kewar Lubna Hajiya Salima ta koma falo ta zauna tayi jugum, wani murmushi ne
ya subuce mata domin ta samu hanyar da zata hora Al'ameen ya gane cewa Lubna tana da
gatanta.
Al'ameen kuwa duk da suna tare da Bilal amma hankalin shi na wurin Lubna burin shi ɗaya
shine ya ganshi ya bayyana gida koda zai yi tozali da Lubna.
Kai tsaye ɗakin mahaifiyar shi ya tura gabanshi na dakan uku_uku, bayan ya gaidata har zai
nufi ɗakin Lubna yaji mahaifiyar tashi ta kira sunan shi, dawowa yayi tare da zaunawa kai a
kasa yana susar ƙeya.
"Yanzu Al'ameen abinda kayi ka kyauta kenan? Yarinyar da tayi maka halaccin da ba ko wace
mace bace zata iya irin shi ba, amma ace ita zaka shaƙe kana neman nakasa ta? To kayi
dai_dai domin na lura baka son farin cikina a gidan nan sai bacin raina, nagode Al'ameen."
Ta karasa maganar tare da haɗe girar sama data ƙasa.
"Dan Allah ki yafe mani Mommy, wallahi banyi da nufin ranki ya baci ba, nayi ne sakamakon
bacin rai da kuma kishi daya ziyarce ni, amma bazan kuma ba."
Al'ameen ya ƙarasa maganar tamkar zai yi kuka.
"Ni na haƙura, amma ka sani mahaifin Lubna yazo cikin daren nan ya ɗauki ɗiyar shi ya tafi da
ita domin bazai taba bari ka nakasa mashi ɗiya ba, sai ka rubuta takardar ta ka aje mata."
Hajiya Salima ta karasa maganar cikin daga murya.
Wata mummunar faduwar gaba gami da firgici ne suka ziyarci Al'ameen, lokaci daya zufa ta riƙa
keto mashi tamkar yana gaban wuta.
"Lubna rayuwata ce Mommy bazan iya rabuwa da ita ba, na roƙeki kada ki bari a rabani da
Lubna, na tuba bazan sake aikata abu makamancin wannan ba."
Ya karasa maganar tare da kama ƙafar mommyn ta shi.
Hajiya Salima kuwa wata dariya ce ke neman kubce mata ganin yadda ɗan nata ya kamu da
soyayya lokaci ɗaya.
"Dan Allah sakar mani kafa kada ka karya ni, babu abinda zance maka sai kaje ka dage da
addu'a domin ran mahaifinta ya 6aci matuƙa."
"Zani yi amma dan Allah ki tayani, kada a rabani da Lubna ta Mommy."
Al'ameen ya ƙarasa maganar kamar zai yi kuka.
"Zani taya ka Amma kaje ka kwanta kaga dare ne yanzu."
"Bani iya bacci Mommy yau kwana zanyi ina sallah ko Allah zaiji ƙai na yasa Lubna ta dawo
gare ni."
Hajiya Salima kuwa cike da mamaki take kallo shi, yaron da rabon da taji yace zai yi sallar dare
harta manta amma yau shine da faɗin zaiyi sallar na fila, lallai soyayya tana sauya mutum.
A ƴan kwanakin sam Al'ameen bai cikin natsuwar shi domin kallo ɗaya zaka yi mashi ka
fuskanci yana cikin damuwa, Uwa da ɗa sai Allah, Hajiya Salima tausayin ɗan nata ne ya kama
ta matuƙa.
Tun bayan tafiyar Alhaji Jadda ɗaya bayan ɗaya ya riƙa bin dangi yana nuna masu Lubna, su
kuma takaicin Hajiya