Showing 66001 words to 69000 words out of 72825 words
Murja ke sawa su rika Allah wadai da abinda ta aikata, babu wanda yakai
mahaifan Alhaji Jadda farin cikin ganin Lubna da suka yi mahaifiyar Lubna kuwa tasha zagi
gami da Allah wadai rantsuwa suka yi kan cewa babu ɗansu babu maido Murja koda mata sun
ƙare a duniya.
Wannan magana tayima Lubna ciwo ba kaɗan ba domin mahaifi a duk inda yake mahaifine, ko
alama bata so taga mahaifanta a ware basu tare amma babu yadda zatayi ƙaddara ta riga fata.
Sun ɗauki kimanin mako guda tana wurin dangin mahaifinta inda ake nuna mata zallar gatan da
bata taba ganin irin shi ba, amman duk da wannan bai hanata tunanin Mijinta da kuma Malam
sule.
A wani yammaci suka Alhaji Jadda yazo ya ɗauki Lubna da kuma kakannin ta suka nufi gidan
Malam Sule domin su miƙa godiyar abun arziƙin da yayi ma jikanyar su.
Tunda suka karyo kwanar gidan Lubna ke kallo gidan nasu daya canza suffa ya koma wani
haɗaɗɗen Flat house wanda kaf area wurin babu tamkar shi, ita ce farko buɗe kofa ta fito tare
da shigewa gidan cike da zumuɗin ganin mahaifin nata, sallamar da tayi ce ta sanya Gaje dake
ba Kulu ruwa a baki juyowa da sauri, shi kuma Malam Sule dake cikin tamfatsetsen falon jin
muryar yar Lelenshi ya sanya shi fitowa da hanzari.
Faɗawa tayi jikin mahaifin nata cike da kewar shi da tayi, Malam sule kuwa wani farin ciki ne ya
ziyarci zuciyarshi domin yayi kewar Lubna matuƙa.
Murna da farin ciki basu bar malam Sule ya lura da su Alhaji Jadda ba sai yanzu, a tare suka
rankaya suka shige ɗakin, bayan sun gaggaisa ne Mahaifan Alhaji jadda suka riƙa kwararo
godiya gami da addu'ar fatan alkhairi ga Malam sule domin sun shaida ba kowane mutum bane
zai iya irin abinda yayi masu.
Shi kan shi Malam Sule godiya ya riƙa yi ta irin taimakon da Alhaji yayi mashi, ya gyara mashi
gida ya bashi jari me matuƙar gwabi, tsakanin shi da mahaifan Lubna sai godiya, koda Alhaji
Jadda zai tafi nan Lubna ta buƙaci da su barta tayi wasu ƴan kwanaki gidan Malam Sule, basu
matsa mata ba nan suka barta tare da yima Malam Sule sha tara ta arziƙi.
Mutanen Unguwa kuwa tururuwa suka riƙa yi dan gane ma idon su shin da gaske ake Lubna ta
warke, sunyi matuƙar yin mamaki cike da Kunyar abinda suka riƙa yi mata haka suka riƙa fitowa
daga gidan, sai gashi wadda suka tsana suke kyara ita ce wadda tayi sanadin da aka gyara
masu Unguwar su domin a halin yanzu babu mutum me wadatar Kamar Malam Sule Kaf
unguwar, duk da halin da suka nuna mashi a baya hakan baisa ya guje su ba domin Malam
Sule mutum ne me hannun kyauta ba shi da Rowa ko a lama.
Gaje kuwa dake jinyar Kulu kuka take cike da nadamar abinda ta aikatama Lubna domin tasan
indai Lubna bata yafe masu ba suna cikin tashin hankali.
Zaune suke cikin Falon Gaje na ba Kulu abinci a baki, juyowa tayi tare da kallon Lubna sai
kuma wasu hawaye suka shiga wanke mata fuska.
"Tabbas Alhaki kuikuyo ne, Lubna basai na faɗa ba nasan na cuceki amma dan girman Allah ki
yafe mani ashe rayuwa zata iya juya mani baya har haka, sai gashi abinda na shuka duk ya
dawo kai na."
Gaje ta ƙarasa maganar hawaye nabin fuskarta.
Ita ma Lubnar kuka take domin tunda tazo taga Halin da Kulu ke ciki take zubda mata hawaye.
"Dan Allah mama ki dai na faɗar haka domin ni tuni na yafe maki nima Allah ya yafe mani."
Lubna ta ƙarasa maganar tare da kamo hannun Kulu.
Da kyar kulu ta tashi zaune da ƙaton cikin ta haihuwa ko yau ko gobe.
"Lubna nasan na cutar dake mafi munnin cuta, alhakin kine ke ɗawainiya dani, na roƙe ki dan
Allah ki yafe mani nasan lokacin mutuwa ta ya gabato yafiyarki ita nike nema."
Kulu ta ƙarasa maganar tana hawaye.
"Na yafe maki , ki daina cewa zaki mutu, Kulu ba zaki mutu ba in shaa Allah zaki haihu ki gyara
rayuwarki."
Lubna ta ƙarasa maganar cikin ƙarfafa mata guiwa.
Murmushin da ake kira yaƙe Kulu tayi domin ita kaɗai tasan azabar da take ji a jikinta, domin
duk wani maganin cutar da ake sawo mata ba tare da sanin kowa ba ashe bata sha sai dai ta
boye shiyasa cutar tayi mata mummunar illa a jiki.
Saro ma da yake kullum sai ta shigo duba jikin Kulu nan ta iske Lubna.
A wata safiyar laraba ne Kulu ta tashi da matsananciyar na ƙuda, Malam Sule mota ya ɗauko ya
kwashe su sai asibiti, da yake sun san lalurar Kulu nan suka hau bata taimakon gaggawa amna
ina jini ne ya fara yo gaba haihuwarta tazo da matsala, duk wani taimako da zasu bata amma
ina abun ya fi ƙarfin su,dan haka dole suka shirya yi mata C.S cikin gaggawa, ganin Kulu ta
buƙaci a kira mata mahaifanta tayi bankwana dasu yasa likitocin kiranta mahaifan Lubna, suka
faɗa Emergency a gigice, kallo ɗaya suka yi mata Lubna ta hau kuka, Gaje kuwa nadama da
tausayin tilon ɗiyar ta ne suka sata zubar da hawaye.
Da kyar Kulu ta buɗi baki ta fara magana kamar haka.
"Ba kuka zaku yi mani ba addu'ar ku nike nema, a halinda nike ciki yanzu babu abinda nike
buƙata wurinku kamar addu'a, Baba ka yafe mani domin nasan na cutar dakai cutarwa me tarin
yawa na sa6ama umarninka, naja maka zagi wurin mutane, dan Allah ka yafe mani ko zan
samu rangwame ." Ta ƙarasa maganar a galabaice.
"Na yafe maki Hawwa'u Ubangiji ya tashi kafaɗunki kinji."
Malam Sule ya fada da karyayyar murya.
"Ba zaki mutu ba Kulu, ki daina kiran mutuwa dan Allah."
Lubna ta ƙarasa maganar tana kuka tare da kamo hannun kulu.
"Lubna ke mutuniyar kirkice kina da halacci, Ubangiji ya dawwamar da farin ciki a rayuwar
Aurenki, Lubna sai wata rana..."
Tana kaiwa nan jikinta ya riƙa wata jijjiga lokaci ɗaya idanunta suka kalli sama.
Ihu Gaje ta kurma tare da zubewa ƙasa a sume, Lubna Kuwa a guje ta fice ta kira likitoci, ganin
sun tattaba ko ina amma ina Kulu ta amsa kiran Allah, farin kyalle suka jawo tare da rufe mata
jikinta dashi, suka fice daga ɗakin jiki a sanyaye.
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun!"
Ita ce kalmar da suka ci gaba da mai_maitawa.
Cikin ƙanƙanin lokaci mutuwar Kulu ta karaɗe ko ina, Malam Sule da kanshi ya sanar da
surukan Lubna da kuma Mahaifin ta Alhaji jadda.
Gida fa ya cika sai koke_koke akeyi tare da jimamim wannan al'amari, da misalin ƙarfe biyu aka
kai Hawwa'u gidanta na gaskiya, Gaje kuwa ta koma tamkar zautatta babu magana sai dai
hawayen dake bin fuskarta.
Hajiya Salima tare suka iso ita da Alhaji Sufyan, fadawa jikinta Lubna tayi tana me sakin wani
kuka me tsuma zuciya.
"Hakuri zakiyi Lubna, lokacin ta ne yayi a halin yanzu babu abinda take buƙata sai addu'ar ku."
Nan ta shiga kwantar ma da Lubna da hankali.
Kira ne ya shigo wayar Alhaji Sufyan, mikewa yayi tare dayin nesa da jama'a sannan ya ɗauka,
jikin shi me ya hau tsuma yana gama wayar a gaggauce ya kira Mahaifiyar Al'ameen kai tsaye
asibiti suka wuce, duk tambayar da Hajiya Salima kema mahaifin Al'ameen amma bai bata
amsa ba dan haka taja bakinta tayi shuru.
Emergency taga sun nufa tare da shigewa wani ɗaki, ganin wadda ke kwance saman gadon
yasa Hajiya Salima karasawa wurinta cike da farin ciki ta furta "Yaya!"
Jin muryar Hajiya Salima yasa Hajiya Mariya ɗago kanta a firgice.
"Yaya ina kika shige, mun neme ki ruwa a jallo amma bamu ganki ba, kin tafi kin barmu cikin
tashin hankali."
Kuka hajiya Mariya ta fashe dashi tare da kallon su.
"Nagode ma Allah daya sanya kafin in bar duniya na sake haɗuwa daku, yau zani warware
maku ƙullin da ni na kullashi da hannu na amma komi zaku ji na roƙe ku yafe mani domin ina ji
a jikina lokacin mutuwata ya kusanto ni, tun bayan kawo ki a matsayi Amaryar Alhaji nike
ƙulle_ƙulle dan ganin na fitar dake daga cikin gidan amma Allah bai rubuta ba sai ma ya
kasance duk abinda nayi sai ya dawo kai na, koda na haifi Fadila banso ace mace bace na
haifa naso ace ɗa namiji ne na haiho, a kwana a tashi har kika haifi Al'ameen inda tsabar baƙin
cikin da naji tamkar in haɗiye zuciya in mutu, nida ke cikin gidan na riga ki jimawa na haifi mace
ke kuma daga zuwanki kin haifi ɗa namijj, nan fa na duƙufa bin malamai da bokaye ganin na
kashe Al'ameen sai ya kasan ce duk wurin malamin da naje ceman yake basu iya kashe shi sai
dai abi wata hanyar, na bada maƙudan kuɗaɗe ganin an lalata mani rayuwar Al'ameen in da
kuma cikin ikon Allah sai ga al'amuran Al'ameen sun fara tabarbarewa amma duk da haka ni
banso ba domin ba irin wannan lalacewar naso yayi ba, duk wani ƙulli da zanyi akan Al'amen a
banza domin basu kama shi, in taƙaice maku magana har bayan auren Al'ameen ban daddara
ba duk da bacewar ɗiyata da ta shiga duniya, anan nayi niyyar raba al'ameen da kowa nashi
nayi magani dan ya shiga duniya, amma sai ga maganin ya koma kai na nice na shiga duniya,
nasha wahala shigata duniya abinda zanci ma gagarata yake nayi bara na kwana a titi daga
karshe na samu aikin gidan wani me kuɗi ina masi shara da wanke_wanke suna biyana tare da
bani abinci, a wani dare da bazan taba mantawa ba, ina cikin bacci a ɗakin masu aiki muka jiyo
ƙarar bindiga, a firgice muka farka muna niyyar guduwa amma ina tuni yan fashin sun fiddo mu
tare da mai gidan da matanshi, maƙudan kuɗaɗe suka buƙaci a basu Alhajin na rawar jiki ya
kwaso masu kuɗaɗe, nikau da jikina ke ciri a hankali na ɗago kai na karaf idona ya sauka ka
Fadila da ta koma tamkar ƙato kannan anyi mashi askin yan fashi riga da wando ne jikinta
hannunta ɗauke da bindiga ta auna ni da ita.
Cikin rawar la66a na fara magana
"Fadila kece kika zama haka? Innalillahi wa'inna ilahirrajiun, tabbas sharri ɗan aike ne yau gashi
ya dawo kai na, kallo na Fadila tayi a fusace tare da tambayar miya kawoni gidan, Ogan sune
daya lura an gane su shida kanshi yasa Fadila ta harbeni a ciki, daga nan bansan mike faruwa
ba sai farkawa nayi naga an yi mani aiki tare da sanar dani in kwantar da hankalina domin aikin
DA akayi mani me haɗari ne bolet ɗin ya shiga jikina ciwon ya harbi hantata abu ne me matuƙar
wahala in rayu, sam a lokacin ba rayuwa ta bace me amfani domin hankalina yana wurin Fadila,
koda na tambaye su ceman suka lokacin da Fadila ta harbe ni ƴan sanda sunyi nasarar kawo
ma gidan ɗauki inda mafi akasarin ƴan fashin suka gudu macen kaɗai akayi nasarar harbi
loKacin taka ƙoƙarin guduwa."
Kukan da Hajiya Mariya keyi ne ya haddasa mata kasa ci gaba da magana.
Cike da tashin hankalin jin wannan labari Mahaifiyar Al'ameen ji tayi ƙafafunta sun kasa ɗaukar
ta, kujerar dake gefen gadon ce ta yi sauri janyo wa tare da zama.
Alhaji Sufyan kuwa banda kallo tsana babu abinda yake aikama Mariya dashi.
Shar6e majina tayi tare da cigaba da magana.
"Nayi kukan baƙin ciki tare da nadama wadda bantaba yiba domin nasan ƙaiƙayi ne ya koma
kan masheƙiya, abinda na aikata ne ya dawo kaina, sai gashi nida naso Al'ameen ya zama
ajalinki sai ya kasance ɗiya ta ce ta zamo ajalina, ganin halinda nike ciki yasa na bada address
ɗin ka domin in nemi yafiyarku koda zani samu sassauci a wurin Ubangiji, nasan na cutar daku
amma dan girman Allah ku yafe mani."
Ta karasa maganar tare da dafe cikin ta da taji tamkar ana yankar hanjinta.
"Mariya kin cutar damu, kin sanyani cikin tashin hankali na gur6acewar tarbiyyar yarona, sai ga
shi tun duniya Ubangiji ya fara nuna maki iyakarki,shin miye aibun ɗiya mace dan ka haifeta
kace kai dole sai namiji, dukkansu Allah ne ke badawa Fatanmu shine a bamu na gari amma
kika manta da wannan kike ƙoƙarin kashe mani yaro, amma babu komi na yafe maki Ubangiji
ya yafe mani nima."
Mahaifiyar Al'ameen ta karasa maganar tare da goge guntun hawayen ta.
Mahaifin Al'ameen ne ya kalli Hajiya Salima rai a matuƙar bace.
"Kece har zaki buɗe baki kice kin yafe ma wannan maciyiyar amanar? Matar da ta cutar damu
ta tarwatsa mana farin ciki sannantayi sanadin mutuwar ɗiya ta, Mariya na tsaneki ban yafe
maki ba, Na sakeki! Na sakeki!! Na sakeki!!"
Mahaifin Al'ameen ya karasa maganar a fusace tare da ficewa daga ɗakin.
Ihu Mariya ta riƙa kurmawa sai kuma ta fashe da dariya.
"Ƙarya kake ban saku ba, kai yama za'ayi ka sakeni, nida keda bokaye da malamai, niface nasa
Al'ameen ya lalace."
Sai kuma ta fashe da dariya, tare da ci gaba da tona mata kanta asiri, duk wani abu data aikata
nan ta rika fallasa kanta tana wurgida duk wani abu dake saman gadon, ganin yadda ciwon
hauka ya sameta dole aka ɗaure ta Alhaji Sufyan ya sanar da danginta kaf abinda ya faru, nan
suka shiga tashin hankali tare da nufar asibitin, sai da Murja ta share wata ɗaya tana hauka
daga nan kuma tayi mutuwar wulaƙanci.
Gaje kuwa nadama ce ta risketa a lokacin da bata da amfani domin tasan yanzu Malam Sule
haushin ta yake ji ga kuma ɗiyarta data rasa saboda son zuciya irin nata, rayuwa kenan yau ga
ɗiyar da ta wulaƙantar ita ce ta tallafi rayuwar su ita ce gatan su.
Malam Sule kuwa bazai iya sakin Gaje ba domin inya sake ta wurin wa zata je, amma alƙawari
ne ya ɗauka dole ya ƙara aure.
Wayewar garin yau Malam Sule da Gaje sun shiga matsanancin ruɗani da tashin hankali domin
kuwa sun nemi Lubna sama ko ƙasa sun rasa, bai kira ya sanar da bacewar Lubna ba sai da
yaga abun na neman fin ƙarfin shi domin har azahar tayi babu lamarin Lubna, Mahaifan
Al'ameen ya kira domin jin ko Al'ameen ne yazo ya dauke ta, amma sai ce mashi suka yi bata
zo ba, nan fa hankali ya tashi, bangarorin biyu suka shiga neman Lubna amma basu sanar da
Alhaji Jadda halinda ake ciki ba.
Koda Al'ameen yaji batan Lubna jiki ya yanke ya faɗi jini ya fara zuba ta hanci da baki, a gigice
suka kwashe shi aka nufi asibiti domin a yadda suka ga jikin shi ya saki abu ne me matuƙar
wahala Al'ameen ya rayu, tashin hankali biyu ya haɗema Hajiya Salima kuka tare tana
mai_maita innalillahi wa'inna ilaihirraji'un Allahumna ajirni fiymusibati wa'akhlifini khairan minha,
tana yi hawaye na kwarara a fuskarta.
*A YI MAN UZURI NA JINA KWANA BIYU DA AKAYI SHURU, ASKI NE YAZO GABAN GOSHI
♀️♀️*
*MEEN@RT...✍*
08133562798
[9/7, 6:39 PM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*PAGE 5️⃣6️⃣__5️⃣7️⃣*
Ku tanadi ɗan gajeren tsumman ku na goge hawaye da majina.
...Al'ameen dai tun bayan kai shi asibiti da akayi har yanzu baisan inda kanshi yake ba, ga
Lubna ita ma har yanzu shuru bata bayyana ba.
A bayanin da likitoci suka ma mahaifan Al'ameen sun sanar dasu cewa zuciyar shi ce ta fara
kumburi sakamakon wani abu da yake so amma bai samuba damuwar da yake ciki ita ta ƙara
haddasa mashi ciwon, jin wannan bayani ya ƙara tayar da hankalin Mahaifan Al'ameen
musamman Hajiya Salima.
Bangaren Malam Sule kuwa rokon Allah yasa aketa ti har Allah ya bayyana Lubna, Gaje kuwa
duniya ta koya mata Hankali domin kuka ta rika yi Allah ya bayyana mata Lubnar ta.
A yau ne suka shirya Sanar da Alhaji Jadda halinda ake ciki madamar basu ga Lubna ba,
Malam Sule da Gaje ne suka ziyarci asibitin da yammacin marece, bayan gama jajanta ma juna
ne suke tambayar jikin Al'ameen.
"To! Da sauƙi za'a ce domin har yau bai farka ba."?
Hajiya Salima ta faɗa murya na rawa.
"Ubangiji ya bayyana mana Lubna, shi kuma Allah ya tashi kafaɗun shi."
Gaje ta faɗa.
A hankali suka ji ƙarar turo ƙofar ɗakin tare da shigowa da Sauri, hankalin sune ya koma ga mai
ƙoƙarin shigowa ɗakin, a tare suka miƙe tare da furta "Lubna!"
Lubna da jikinta ya ƙara kyau sai sheƙi take yi, ta yi ƴar ƙiba kallo ɗaya zakai mata ka fahimci
irin ni'imtaccen kyawun data ƙara, cikin Hanzari Lubna ta ƙarasa jikin gadon Al'ameen tamkar
zatayi kuka.
"Lubna ina kika je, kin barmu cikin tashin hankali ga Kuma Al'ameen dake cikin wani mawuyacin
hali sakamakon 6atanki."
Mahaifiyar Al'ameen ta ƙarasa maganar tare da kamo lallausan hannun Lubna.
Malam Sule kuwa da kyar ya iya furta.
"Lubna Allah yasa ba wani mugun abu bane ya faru dake, 6atanki ya tayar mana da hankali."
"Ku gafarceni ni ce nan na ɗauki Lubna, ba da nufin in bata maku ba."
Jin me maganar Juyawa suka yi da kallon Uwar Garke dake ƙoƙarin shigowa ɗakin.
"Na ɗauki Lubna ne domin ayi mata yan dabaru irin namu na jinnu wanda ba zasu cutar da