Showing 6001 words to 9000 words out of 72825 words

Chapter 3 - RUWA BIYU NA MEENAT A YANDOMA.pdf

gefen ta ya kafe ta da ido domin jiran ta yaje
ta farka yaji mike tayar mata da hankali har jinin ta ya hau haka.


"Sannu."
Daddyn Hibba ya fada tare da kafeta da ido.

Kai kawai ta ɗaya domin magana ma batason yi.

"Mike faruwa dake, mikika nema kika rasa da har zaki sama kanki damuwa jinin ki ya hau har
haka."?
Cewar DADDYN HIBBA.


"Alhaji bani son gidan nan a canza mana wani dan Allah."
Ta fara murya na kyarma.


"Shine damuwarki kuma baki sanar dani ba, har kika bari jinin ki ya hau haka, ku fara shiri friday
zamu koma sabon gida."
Ya karasa maganar tare da ficewa daga ɗakin.


Binshi tayi da kallo zuciyar ta na kuna, ba tada wata hanya da zata rage mata abinda take ji sai
wannan domin a tunanin ta i ta ce mafita in sun koma wani gida kila aljanun jikin HIBBA su fita.


Bacci ta samu tayi har zuwa yammaci, wata shawara ta zo mata, wayar ta ta ɗauka tare da

kiran Babbar aminiyar ta wato turai.


Ba'a dauki dogon lokaci ba sai ga Hajiya turai ta bayyana a gidan domin jin abinda yasa take
mata kiran gaggawa.


"Yanzu ke da wannan abubuwan ke faruwa dake amma baki tashi neman magani ba kina nan
zaune, in tambayeki Baba yasan da wannan maganar."?


"Bani so in tayarma da mahaifina hankali kinsan tun bayan rasuwar Hajiya har yau jikin shi babu
daɗi."


"To a yanzu ba sai an jima ba ki shirya akwai wurin Malamin da zan kai ki."


"Turai yanzi fa magrib ta kusa."


"Ke dalla can wace magriba, kina tashi muje a kawar maki da matsalar ki ko kuma zaki zauna
ne ki mutu a banza."?


Ko Alhaji bai sani ba ta kama hanya suka nufi gidan boka, domin dama shi rayuwar gogaggun
yan boko yake tana da izinin zuwa duk inda take so ba tare da ta nemi izini a gareshi ba.


Wajen garine anyi nesa da mutane sosai suka shige cikin Bukkar.

Hajiya Turai ce ta budi baki da niyyar korama boka bayani.

"Kada ki wahakar da kanki, tun kafin kuzo an sanar dani komi, ɗiyarki na bincika tauraronta
amma banga komi ba in takaice maki magana babu tauraron ta a jinsin mutune kuma banga ta
a jinsin jinnu ba, tabbas a kwai wani boyayyan al'amari dake tattare da ɗiyar ki, ku amshi
wannan maganin a tabbatar an turara shi a yau, kada kuyi kuskuren barin ta taga wannan
maganin,hhh in kuka bari ta ganshi kashin ku ya bushe."
Ya karasa maganar tare da jefa ma Hajiya MURJA.

Kuɗi suka zazzage a gabanshi tare dayin godiya suka dauki hanyar gida.

"Jikina yayi sanyi, wallahi tsoro nike ji."
Hajiya Murja ta fada da karyayyar murya.


"Ke fa a kwai ki da saurin karaya, miye na wani jin tsoro, muje ayi komi a gabana dan na lurabin
nabarki tabbas sai kinyi kuskure."


Basu isa gidan ba sai gaf da Magriba duhu yayi, ba batun Sallah turaren suka ɗauko aka mai da
shi cikin jikkar Turai.

Sai da suka tabbar Sun kulle ɗakin HIBBA kafin su dawo falo su ɗauko garwashin.


"Kai! Murja ke kika ɗauki maganin nan? Yanzu fa muka barshi a cikin jikkata mukaje mu ɗauko
garwashi."
Turai ta ƙarasa maganar tare da kafe Murja da ido.

"Tare fa muka fita dake."

"Ga abinda kuke nema na kawo maku."
Hibba dake ratsowa ta cikin bango ta fada hannunta riƙe da maganin.


Tsabar firgita da suka yi wani guntun fitsari ne ya kubce ma Turai....

_____________________________
...Sanyin asuba da Kuma sassanyan ruwan da aka sheka mata ne ya sa ta mikewa a firgice
tare da kiran sunan mahaifin nata.


"Ishasshiya basarakiya kin hakimce kina bacci, maza ki tashi ki ɗebo ruwa, ko wani kike tunanin
zai ɗebo maki."
Gaje ta fada cike da masifa dake cinta.

Duk da jikin ta babu kwari, haka ta ɗauki ƙaton bokitin tayi waje, a guje ta dawo gidan tana haki,
tuna abinda ya faru jiya dasu Goga.

Babane ya shigo gidan ganin LUBNA yayi tsugune tana haki.

Ganin jikin mahaifin nata da raunuka ya tabbatar mata cewa jiya ciwon ta ya tashi.

Cikin kuka ta ƙarasa gaban mahaifin nata .

"Baba ka yafe mani nasan ni naji maka waɗannan ciwukan, mi ya sa ka tsaya a lokacin da
hankalina ya gushe."

Zaunar da ita yayi domin yasan jikinta babu kwari, "ki kwantar da hankalinki, miya fiddaki waje
bayan jikin ki babu kwari."


"Ruwa zani ɗeboma Mama."

"Ruwa!"
ya maimata kalmar cike da zallar mamaki."

"Gaje! Gaje!!."

"Wai lafiya da sanyin safiyar nan kake kwala mani irin wannan kiran."
Gaje ta fada tare da tsayuwa bisa kanshi ƙerere.

"Yanzu tsabar baki da imani yarinyar nan bata lafiya amma kika aiketa ɗibar ruwa, ita Kulu aikin
mi take a cikin gidan nan da bazaki aike ta taɗebo ba."?


"Kaga Malam ina fa ganin girman ka, ah to kada fa ta kaimu ga haka nida kai a cikin gidan nan,
ita Lubna ba i ta bace babbab akan mi zani tayar da Kulu tana bacci alhali ga Lubna."

"Baza ni gajiya da fada maki kiji tsoron Allah ki haifi ɗiya amma ki rika nuna mata tsana, ko mi
kika yi Gaje keda Allah."

"Yo dama ai dole ka fadi haka tunda ka ɗaure mata gindi a cikin gidan nan."
Ta karasa maganar tare da turo kallabi gaba.


"Baba!."
Lubna ta kira sunan.

"Baba Su Goje fa."?
Ta jefa mashi tambayar.

Cike da mamaki yake kallon ta "Miyasa kike tambayar su Goje, yanzu haka ana can ana shirya
jana'izar su."


Wata zabura tayi tare dayin baya, "kada kace mani suma sun mutu, Innalillahi wa'inna
ilahirraji'un."

"LUBNA ki kasan ce mai daukar kaddara a koda yaushe ke kuma taki kaddarar kenan, ki maida
lamuranki ga Allah komi lokaci ne wata rana haƙurin da kikayi zai zama riba a gare ki."


Hawayen dake fuskarta ta share.
"Baba nagode insha Allah zanyi amfani da abinda ka fada mani."

"Allah yayi maki albarka."
Da Amin ta amsa tare da shigewa ɗaki ta faɗa bisa katifa ta cigaba da kuka mai ban tausayi.

Mirrow ɗin ɗakin ta nufa tare da yaye gyalen da ta rufe fuskar ta dashi, nan fuskarta ta bayyana,
fashewa tayi da kuka tare da shafar fuskar ta.

Abinda zai baka mamaki bangaren fuskar macen shine ke kuka sa6anin bangaren fuskar namiji
daya kasan ce dariya yake.


Ihun Gaje taji yi tana neman temako take tamkar zata tarwatsa dodan kunnen mutum, a guje
Lubna ta zari mayafin ta tayo waje jin ihun da mahaifiyar tata keyi.


binda taga ya faru da Gaje ne yasa ta jin wani jiri namen kayar da ita, anya kuwa abinda idonta
ya hasko mata gaskiya ne...




*MEEN@RT...✍*
[7/22, 6:19 PM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_



Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma



```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*

*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine

ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*�
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________

*PAGE 7️⃣__8️⃣*
...Gudu yake tsalawa saman titin tankar zai tashi sama, ganin tuƙin gagancin da yake yasa
mashina da motoci bashi hanya da sun ga ya nuho inda suke tare dayi mashi addu'ar shiriya.


Tsarewar Ubangiji ce kaɗai ta isar dashi gidan Bilal lafiya, ko ƙarasa kashe motar biyi ba ya fito
tare da afkawa gidan.


Kamar yadda ya zata kuwa hakane, yana shiga ya iske bilal zaune a falo shida budurwar shi,
kota kansu bai bi ba a fusace ya haye sama.


Cike da mamaki suka bishi da kallo, "Jira kiga in bishi nasan yau halin ya motsa, mutumin nawa
akwai matsala."
Cewar Bilal tare da miƙewa zai haye sama.


Bata fuska tayi tare da cuno baki.
"Ɗan wahala kawai, kai yanzu daga shigowar shi har ka wani mike kaji lafiyar shi, nifa wannan
guy ɗin bai wani burgeni hasalima nafishi ranshin darajar da yake ji da ita."
Cewar Amna


"Kee! Wallahi ki shiga hankalin ki wancan guy ɗin ya fiki iya bariki, kwaro ne da kike ganin shi."
Ya ƙarasa maganar tare da hayewa sama.


Saman gadon ya ganshi zaune yana sauke ajiyar zuciya, "ayya mutumi na ran maza ya baci,
lafiyar ka kuwa naga ka shigo kana shirin yin ball damu."
Cewar BILAL.


"Kai na ya ɗauki zafi, bani son dogon surutu, ina LEEMCY take."?
AL'AMEEN ya fada a taƙaice.


"Nikam ina zani san inda LEEMCY take, ka kirata mana kaji."

Turo ƙofar da akayi ne ya dakatar dasu daga maganar da yake, LEEMCY ce ta shigo cikim
muguwar shiga irin ta gogaggun yan duniya, domin tun bayan shigowar Al'ameen Amna ta
sanar da LEEMCY.


Ganin shigowar tane yasa BILAL ficewa daga dakin.


"Honey! Mike damunka miya bata maka rai."?
Cewar LEEMCY.


"ki bari kawai gida kowa bai sona babu mai kaunata, yanzu haka na baro masu gidan su bazani
koma ba har sai sun nemeni."


Wani irin daɗi ne ya lullube zuciyar LEEMCY, domin koba komi ta samu damar da zata cika
burin ta.


WACE CE LEEMCY?
Ɗiya ƙwalli ɗaya ga Alhaji Marwan da kuma Hajiya Nusaiba, Alhaji Marwan mutum ne mai
matuƙar kuɗi babban ɗan kasuwa wanda duniya tasan da zaman shi domin har kasar waje
yana da hannun jari.


Tun tasowar Ɗiya ɗaya a garesu wato Halimatu wadda ake kira leemcy yarinya ce mara ɗa'a
gatan da suke nuna mata shine yayi sanadin ta ida lalacewa, zata iya fita tayi kwanaki bata
dawo ba kuma babu wanda ya isa ya tanka mata domin ta samu daurin gindi ga mahaifin ta,
hatta karatun ta a kasar waje tayi shi haɗuwar su da AL'AMEEN ce tasa a ka maidota ƙasar ta
taci gaba da karatu, tun bayan haɗuwar su LEEMCY babu yadda batayi ba ganin taja ra'ayin
AL'AMEEN sun aika zina amma bata samu dama ba, domin kuwa duk iskancin AL'AMEEN
gyamar Zina yake yi, wannan yasa yau ta ɗana tarkon ta ganin AL'AMEEN ya baro gidan su.


"Honey!.?"
Leemcy ta faɗa.


"Na'am Baby na."

"Yaushe zamuyi aure."?


Jin tambayar yayi wani banbara kwai, shifa duk lalacewar shi yaba taba fatan ya auri LEEMCY,
yafi so inya tashi aure ya samo wata natstsiyar ya aura.


"Kayi shuri."
Leemcy ta jefa mashi tambayar.

"Shi aure yana buƙatar natsuwa kibari mu dai_daita da mahaifana sai mu yi auren mu hankali
kwance."


Kallon shi tayi tare da saƙa wani abu a zuciyar ta.
"Karya kake AL'AMEEN, sai ka aure ni koda baka so, duk duniya babu namijn da nike so sama
dakai, dole ne in koma gidan boka a sake sabon shirina kan ka."


"Mi kike tunani haka."
Al'ameen ya katse mata zancen zucin da take.

"Babu komi rayuwar auren mu nike haskowa wadda zamu gudanar."


"Sakara! Baki da hankali, ni zani auri yar bariki.a matsayin matar aure na, ai sai dai kiji ana
ɗaura mani aure da wata."
Ya ƙarasa maganar cikin zuciyar shi.


"Duk ka gama guje_gujen ka lokaci na baka, domin Boka ya shaida mani sai ka aureni, indai
nice zaka zo hannu."
Ta karasa maganar cikin zuciyar ta.


Tun bayan barin AL'AMEE Haj Salima ke kuka sakamakon cin mutumchi da ta sha wurin
MARIYA.


"Salima!"
Alhaji ya ambaci sunan shi.

Ɗago kanta tayi da idanunta da sukayi jajur tsabar kukan da tasha.

"Ko wane bawa da kike gani da tashi ƙaddarar, ki daina zubda ma AL'AMEEN hawaye domin
hakan babban tashin hankali ne a gareshi, kiyi hakuri mu dage da addu'ar wannan ita ce
ƙaddadarar mu, addu'a ita ta kamace mu ba kuka ba."


Fadila kuwa tun bayan ficewar Al'ameen baƙin ciki ne cunkushe a zuciyar ta domin taso ta
haɗashi da jami'an tsaro amma sai ga mahaifin su ya shigo, dogom tsoki taja tare da ɗaukar
key ɗin motar ta tabar gidan.


Ɗakin Wizee ta nufa domin yau tayi alƙawarin bazata kwana gida ba inta huce zata dawo...
_____________________________________
...Dakin ne ya fara girgiza ga kuma dariyar HIBBA dake tashi cikin amo mara ɗaɗin sauti tamkar
kukan jaki gamida kukan jarirai ya hade wuri daya ya bada wani rikitaccen sauti.


"Ba yanzu ya kamata ki fara fitsari ba, ki bari ki amshi sakamakon ki."


"Wato ku yan ɗaɗi zuwa wurin boka ko, hada kulle ni a ɗaki, cikin ku wace ce ta kulleni a ɗaki."?


Caraf Hajiya Turai ta nuna Hajiya Murja.
"Kin ganta nan i ta ce wadda tace a kulle ki."

Cike da mamaki haj Murja ke kallon Turai ganin zata jaza mata wani bala'in.

"Turai! Waya kawo shawarar a kulleta inba ke ba."


"Ƙarya kike mani, ke nifa Murja kin cuce ni kin jaza mani bala'i miyasa baki shaida mani gidan ki
a kwai aljanu har haka ba, Allah ya isa tsakani na dake wayyo Allah aljana da girman uwarki da
Ubanki ki gafarce ni.


Falau! Taji an Gwabre mata baki da wani basamuden hannu.
"Niki ke zagi Uwata da Ubana kike zaga, ni sheɗaniya kike zaga, hhh yau zaki gane kurenki.


"Na tuba sheɗaniya ki gafarce ni a buɗe mani gida in Fita wallahi ko hanyar gidan nan bazani
sake kallo ba."

Tuntsirewa HIBBA tayi da dariya tare da fara shawagi a sama domin har yanzu bata sauko ƙasa
ba.


"Yau zaki ga ƙarshen sheɗanci sai kin gane kinyi kuskuren shiga faɗan dan da babu ruwanki."
Ta gama faɗar haka ta nuna TURAI da hannu sai ga wani iska ya kwasheta sunyi sama, duk
ƙiba irin ta Turai haka iskan nan yayi sama da ita ya ɗaure kafar ta jikin fanka.


Ihu kawai take kurmawa tare da tsinema Boka da Kuma Haj Murja, fankace ta kunna kanta tare
da kece wa wani irin gudu tare da Turai dake jikin ta maƙale.


Hajiya Murja kuwa ganin abinda ya faru da Turai jikin ta babu inda bai kyarma.


Tamkar giftawar ido haka HIBBA ta dira gaban Haj Murja.
"Mai gayya mai aiki nadawo kanki, kina tunanin boka zai iya raba wannan faɗan dake tsakanin
mu, gabar dake tsakanina dake ta fara ne tun kafin zuwabna duniya, kin rabani da farin cikina
rayuwata wanda ya kasance shine rayuwa ta domin cikar burin kun, ta karasa maganar
hawayen jini nabin fuskarta."

"HIBBA! kin san kuwa abinda bakin ki ke furtawa, minayi maki dawa na rabaki a rayuwar nan."
Rufe bakinta keda wuya Hibba ta Nunata da hannu take wasu hannaye suka shiga ɗauke Haj
murja da lafiyayyun maruka.


An ɗauki sa'o'i sun kai biyar kafin a daka ta
"Kamar yadda na rabu da farin ciki kema har abada a haka zamu tabbata dake daga ƙarshe
kuma in kashe ki."


Murja bata san mike faruwa ba domin marukan da tasha sun rikita mata kwalwa ta koma ganin
mutane bibbiyu.


Hannu HIBBA ta ɗora a goshin murja lokaci ɗaya wani farin abu ya shiga jikin murja tamkar
wadda aka jona ma shokin ɗin nepa haka Murja ta riƙa kyarma idanun ta suka kafe ta dena
motsi.

Turai dake saman fanka ma jeho ta akayi ƙasa tim, komi ya juye mata sakamakon gudun da
fanka ta riƙayi da ita, dan haka zafin faɗowar da tayi ne yada ta shiga kurma ihu tana neman
temako.


"Zaki rufe mana wannan rubabben bakin naki ko sai mun farke shi."


Ba shiri Turai tasa hannu biyu ta toshe bakin ta gudun kada kukan da take ya fifo, ganin Murja
kwance ƙasa shirim! Ba karamin tayar da hankalin Turai yayi ba da sauri ta kara toshe bakin ta
ganin kukan na neman sake kubce mata.


HIBBA kuwa wasu ƙananun yara masu suffar tane suka bayyana, kawunan su kuwa sun linka
girman jikin su sau biyu.

A tare suka tuntsire da dariyar da ta sanya ɗakin amsa kuwwa.

"In an yanka nike son kai."

"Ni kuma tumbinta nike so."

"Kafafun za'a bani."


"Ni kuma kan nike so."

Jin abinda halittun gaban Hibba ke fada yasa Turai fashewa da kuka tana kiran sunan mai gadi.


"Na tuba kuyi man rai ku barni da rayuwa ta, nida gidan nan ko kuma shiga sabgar Murja har
abada, kada ku cinye ni wayyo ni Turai yau naɗebo ruwan dafa kaina."


"Kina so kibar gidan nan lami lafiya."?
Cewar HIBBA.


"eh."
Ceqar turai tare da yayumar gyale ta miƙe tsaye.

"Indai kina son barin gidan nan sai kinyi mana rawa irin wadda aljanu keyi."

"Nashiga ukku ko kiɗan aljanu ban taba jiba bare kuma rawar su dan girman iyayenki kiyi mani
rai bani iya rawa bakiga yadda nike ba a dunƙule kamar giwa."

Mari aka ɗauke ta dashi sai gata ƙasa warwas.

Kafin rai na ya baci ki miƙe ki fara taka mana rawar aljannu.


Lokaci ɗaya ɗakin ya ƙaure da wata rikitacciyar waƙa maradaɗi sautin ta kaɗai ya isa ya sumar
da mutum.


"Ruum_ruum dumdumarun, shuuuw,ƙuuuw duuuw, rumdumdum ruuuw, ƙuuuuwduuuw."
Amon waƙar ya cika dakin


Miƙewa tayi ta fara taka rawa in tayi gabas sai tumbinta yayi yamma haka take rawa tana
gantsarewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login