Showing 18001 words to 21000 words out of 72825 words
yayi wani kwakkwaran motsi tuni sun haje jikinshi masu yakushi nayi masu cizo
nayi, ihu yake tsalawa koda za'a jishi a kawo mashi dauki amma a banza suru kake ji
domin,Duk ihun da zai yi ba za'a taba jin shi ba.
Babban abinda ke kara ruɗar dashi bai wuce a jikinshi inda jini ke fita ba haka magunan nan ke
lasar wurin suna kara girma.
Cak ƙatuwar magen nan ta ɗageshi sama kanshi na reto a ƙasa ta rika hajijiya dashi tammakar
yadda fanka ke sharara gudu.
Sakin shi tayi yayo kasa inda shi kuma idanun shi suka hasko mashi wani ƙaton rami da
gefenshi yaya mulmulawa zai faɗa ciki.
Kanshi ne ya bugu lokaci daya idanunshi suka rufe saman girarshi jini ya fara fita, kecewa tayi
da dariya tare da lasar jinin shi ta lumshe ido domin tunda take yau ne karo na farko da ta
ɗanɗani jinin da bata taba ɗanɗanar irin shi ba.
Rikiɗewa tayi tare da komawa sak Lubna, ta cikin bangon ta rika ratsawa harya karasa ɗakinta,
bisa gadon ta zube wani nannauyan bacci yayi awon gaba da ita.
A hankali wani ruhi mai kama da hayaki ya fara fita daga jikin Lubna, har ya fice tas! Shidai
wannan abu tamkar hayaki haka yake, suffarshi kuwa namiji ne tsaye.
A hankali ya zo dai dai saitin fuskar Lubna tare da fashewa da kuka mai firgitar da ruhin
bil'adam.
"Ban kamaci ratuwa jikin kowa ba amma haka suka mayar dani tamkar bawan su sun rabani da
kowa nawa banida sauran gata a wannan dunuyar, taya zani barki kiyi rayuwa cikin farin ciki
bayan mahaifanki sune silar komi, zani rayu dake ne har ƙarshen ratuwarki domin a wurina
tamkar hadaya kike an mallaka mani ke tun shuɗaɗɗan lokaci."
Ya gama faɗar haka ya ratsa ta cikin bangon tare da shigewa ɗakin Fadila dake faman bacci.
Tun tana jin kukan awakin sama_sama har yayi ƙarfin da yayi sanadin tashin ta daga bacci.
Farkawar ta tayi dai_dai da ganin wasu baƙaƙen akuyoyin masu kai irin na kadangaru idan su
ɗata rak a tsakiyar goshi,cike da ɗakin sun buɗe bakuna suna mata ihu.
"Kan uba!."
Fadila ta furta tare da dirowa daga saman gadon.
"Miya kawo awaki cikin ɗakina? Kodai wani ya bude gidan gonar dady ni kuma suka shugo
mani daki, ni gidan nan an rena mani wayo awaki har cikin ɗakina dole in iske dady yanzu
kuwa."
Ta karasa maganar tare da miƙewa.
"Ni zaki aika ƙafafuna takwas zani fiki saurin kai wa."
"Aa ke baki da gudu nita cikin bango nike bi zani fiki saurin karasa wa."
"Ni uwar garke har ku fada mani sauri yanzu nan zani bace in sanar da Ubanta abinda take
faɗa."
A wakin dake gaban Fadila suka hau gardama, a firgice tayi wani wawan tsalle da nufin fadawa
bisa gado sai jinta tayi tabar ƙasa.
Kecewa suka yi da dariya tare da yin kuka Meeeeeeyyy!
Ƙara rikicewa tayi domin sai yanzu ta fahimci irin halittar dake jikin su, ihu ta fara tana neman
temako.
"Keyi mana shuru ko kema yanzu halittarki ta koma irin tamu."
Zakaƙurar cikin su ta faɗa.
"Na tuba nabi Allah na biku akuyoyi, kuyiwa girman iyayenku ku bar mani ɗaki, wallahi ɗakina
ba garken akuyoyi bane."
Ta karasa maganar tana mai sakin kuka.
Garam! Suka gwabje mata baki da kofato.
"Masu daraja kike kira da awaki, maza ɗauko makilin da borosh ki wankema kowa baki in kin
ƙiya yanzu jikin ki ya gaya maki."
"Na shiga ukku na lalace tunda nike ban taba gani an yima akuya borosh ba yanzu wannan
kawunan naku na ƙadangaru zani wanke wayyo uwata da ubana Hajiya kina ina."?
"Ba zaki fasa kiranmu da akuyoyi ba, Uwar garke ku hora ta."
Tamkar yadda ake buga ball haka awakin suka rika jifa da Fadila in wannan ya bugo tanan sai
wannan ya bugo tanan.
Sai da suka yi mata lilis kafin su fara magana.
"Zaki fara wanke mana bakin ko sai jikin ki ya gaya maki."
"Kuyi mani rai zani wanke."
Ta faɗa a gabaice
Haka ta rika bin Awakin nan tana wanke masu baki, da ta fara wanke wa zataji kaf haƙoran sun
fara ficewa suna zubowa a hannunta.
Ko kuma tana zura hannu zata fara wanke masu bakin taji sun lafta mata cizo sun datse bakin
ga hannunta ciki.
Bata gane bata da wayo ba sai da tazo kan uwar Garwake, tana fara wanke bakin ta hada da
hannuwan ta cije, ihu Fadila ta fara tana sakin kuka.
Azaba ranar babu kalar wadda bata sha ba jikinta duk sawun bugu ne fatar ta duk ta farfashe.
Shugabar su ce ta fara magana.
"Wannan hukuncin kadan ne kika gani muddun baki fita sabgar Lubna ba nan gaba yanka ki
zamuyi mu tsotse jinin jikin ki kinaji kina gani."
"Ni da ita har abada kai in ma kince ba su kada in sake hada ido da ita to daga yau na dena."
Kecewa suka yi da dariyar da ta haddasama ɗakin girgiza tare da bacewa bat.
Fashewa tayi da kuka tare da fadawa kan gado jikin ta na mata raɗaɗin azabar da tasha.
Lubna kuwa
Kamar yadda ta saba duk safiya sai taje ta gaida su Hajiya Salima yau ma haka taje suka gaisa
tayi mata gyaran ɗaki sannan ta nufi kitchen.
Har 12:00 amma sam hajiya bataga gilmawar Al'ameen ba, tunani tayi ta aika Lubna sai kuma
wata ziciyar tace taje da kanta ta gani.
Bakinta ɗauke da sallama ta tura ƙofar ɗakin, turus taja ta tsaya tare da rafka salatin daya jawo
hankali Lubna da Daddyn Al'ameen suka shugo ɗakin a rikice.
Kuka Hajiya Salima keyi iyakar karfinta tana ambatar sunan Allah, waya Alhaji ya zaro a rikice
tare da kinran family doctor nasu, Lubna kuwa wani kuka ne ya kubce mata ganin Al'ameen
yashe babu alamun rai a tattare dashi...
____________________________________
...A wani ƙasurgumin jeji Hibba ta bayyana fuskar nan a turniƙe
Yanayin jejin kadai ya isa ya firgita Ruhin bil'adam amma Hibba ko ajikinta sai ma kara ƙaimin
kutsawa da take cikin jejin.
Bakin wata bishiyar Kuka ta tsaya tare da Nuni da hannu ƙasan bishiyar take wata guguwa ta
taso ta turniƙe wurin lokaci ɗaya wani rami ya bayyana a ƙasan bishiyar.
Cikin ramin ta shige tare da dauko wani katon akwati da aka ƙera da zallar karfe, direshi tayi a
kasa tare da rungumeshi tana mai fashewa da kuka lokaci daya jejin ya fara girgiza tsuntsaye
na tashi sama.
"Sun azabtar da ruhinka sun salwantar da rayuwar ka sun mai dani mareniya bani da kowa a
wannan duniyar sai kai daya,alƙawari ne na ɗauka sai naga bayan duk wanda keda hannu cikin
wannan al'amarina ne."
Ta karasa maganar hayaƙi na fita a bakin ta.
Hajiya Murja kuwa ganin yadda goshin ta ya fashe ga jini kaca_kaca yasa mutanen daukar ta
tare da nufar asibiti mafi kusa
Emergency aka shiga da ita domin wasu ma suna kyautata zaton ta mutu ganin yadda suka
dauke ta.
Jikkar ta aka duba nan aka ga wayar ta cikin,sunyi sa'a wayar a bude take bata sa password
ba, Hajiya Turai shine kira na ƙarshe a cikin wayar ta dan haka nan suka kira amma
kwata_kwata wayar bata shiga, Abban Hibba shi suka kira, ta can bangaren shi anyi sa'a yana
kan hanya dan haka Hibba ya kira ta iso kafin ya ƙaraso.
Kashe wayar Hibba dake makale saman fanka tayi tare da fashewa da dariya, ƙafarta ita ce
sakale jikin fanka inda kanta da hannuwanta suke reto a kasa.
"Ko baka kirani ba yanzu zani wuce asibitin, Burina shine in ganta cikin masifar da sai ta
kwammace mutuwa da rayuwar da zatayi."
Tana karasa maganar tamkar tsuntsuwa haka ta diro daga saman fankar, komi nata tsayawa
yayi domin Jikinta ya bata akwai wani a la6e a inda take.
Kanta ne ya juyo tare da kallon bayan ta, Uwani dake labe jikin Window ihu ta saki tare da
ƙoƙarin guduwa.
Kwatsam! taga Hibba ta bayyana a gaban ta, "Hhh ni zaki ha'inta Uwani ni zaki tonama asiri,
wanda duk ya shiga hanyata kauda shi nake, domin ni ruwa ce in na taho babu mai tare mani
hanya."
Jiki na ciri ta bude baki da nufin yin magana.
"Ki gafarce, kiyi mani rai babu wanda zai san da wannan maganar nayi maki alƙawari."
Kecewa da dariya Hibba tayi.
"In kin rayu ne har zakiyi ƙoƙarin tona mani asiri."
Tana karasa maganar tayima Uwani wata shaƙa lokaci ɗaya idanunta suka fara firfitowa jinin
jikinta ne Hibba ta fara tsotsewa sai da ta gama tsotseshi tas fatar Uwani ta koma fara sol kafin
ta saketa ta faɗo ƙasa a ma ce.
"Duk wanda yayi ƙoƙarin tona mani asiri mutuwa ita ce sakamakon shi."
Tana karasa maganar Ta ratsa ta cikin bango ta nufi asibiti...
*MARASA COMMENT DUK WANI HAKURI NAYI AMMA TABBAS YAU A WAJE ZANI
TATTARA KU IN WATSA KUMA ALƘUR'AN KADA WADDA TA BIYONI PC DOMIN NASON
MASU COMMENT, KUMA NASAN YAN ZAMAN KASHE BUJE*
*MEEN@RT...✍*
[7/30, 11:44 AM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*PAGE 1️⃣8️⃣__1️⃣9️⃣*
...Kamar yadda tayi niyya haka ta bayyana kwatsam cikin asibitin, duk inda ta wulga dole ne a
bita da ido wasu ma harsai ta bace ma ganinsu, domin Hibba mace ce mai matukar kyau kana
iya ma tunanin bata cikin jinshin mutane kyawunta yayi yawa.
Ba ta tambaya ba bare ace dama can tasan ɗakin da mahaifiyar ta ke zaune, kai tsaye ɗakin ta
tura babu ko sallama haka ta afka ɗakin, mahaifinta tagani zaune bisa kujera kusa da
mahaifiyar ta.
Ɗago kanshi yayi tare da kallon ta, "Hibba duk mi kike har haka ace nida ke nesa sai da na
rigaki zuwa wurin nan, shin wai bisa mima kikazo domin lokacin da na kiraki ina cikin asibitin
nan yanzu kuma ko minti goma ba'ayi ba amma gaki kin karaso."?
"Kana buƙatar sanin abinda ya kawo ni ne."?
Hibba ta faɗa murya ƙasa.
"Mikika ce."?
Abban Hibba ya tambaya.
"Ni Abba bani son yawan tambaya dan wata rana in dai kana ƙure ni da tambayoyi tabbas zamu
samu matsala dakai dan haka yanzu dai gani ya jikin Umma."?
Hibba ta karasa maganar tare da matsawa gafda gadon mahaifiyar tata.
Cike da zallar mamaki Mahaifin nata ke kallon ta.
"Kwata_kwata kwanan nan ya rasa mike damun Hibba bata jin nauyi tayi mashi abinda taga
dama ga rashin nuna kulawar ta ga mahaifiyar ta amma ya dauki laifin faruwar haka ya dora a
kan su domin su suka yi mata tarbiyya a haka, ganin irin yadda jikin Hajiya Salima yayi laushi
yau ta matuƙar jigatuwa yasa Alhaji kiran mahaifinta ya sanar dashi halin da ake ciki.
Kafin kace mi karar jiniyar motocin jami'an tsaro ta cika asibitin, wanda suka yo ma tsohon
Shugaban kasa rakiya, yana fitowa jami'an tsaro suka take mashi baya cike da girmamawa.
Kallon daya zaka yima irin tafiyar da yake ka fahimci irin saurin da yake na ganin tilon ɗiyar
tashi data rage mashi a duniya.
Karo yaci da Hibba tana fitowa daga ɗakin da Hajiya Salima take, ko kallon inda yake bata yi ba
ta raba shi zata wuce.
Ganin jami'an tsaro sunyo kanta zasu kwasheta daga hanyar yasa Alhaji mamman dakatar
dasu.
"Hibba ya jikin mahaifiyar taki."?
"Ba gaka a kofar dakin ba zaka iya shigewa ka gani."
Hibba ta faɗa tana mai aika mashi da mugun kallo.
Tuni masu tsaron lafiyar shi suka yi kanta a fusace, tsawar daya daka masu ce ta dakatar dasu,
domin inda sabo ya saba da kiyayyar da jikar tashi ke nuna mashi tun tana ƙarama dan haka
bai bi ta kanta ba ɗakin suka shige.
Hibba kuwa jikin ta wata iriyar tsuma da yake ji tayi inama ace ba a bainar jama'a take ba da
babu abinda zai hana ta salwantar da rayuwar mutumin can.
Ciki ya iske Abban Hibba, bayan sun gama gaisawa ne Hajiya Murja ta farka, ba karamin daɗi
taji ba da ganin mahaifin nata wani kuka ne ya kubce mata domin harga Allah mahaifinta kaɗai
take raba taji sanyi a ranta.
"Murja miya fito dake ba tare da driver ba, shin bana hanaki fita ke ɗaya ba, kina so ki salwantar
mani da rayuwar ki ne in rasaki kamar yadda na rasa mahaifiyar ki."
Mahaifinta ya karasa maganar cike da kaunar ɗiyar tashi.
"Kayi hakuri gani nayi in zani je gida har sai na tafi da wani driver, amma nayi alkawari hakan ba
zata sake faruwa ba.
"Mi likitoci suka ce game da lafiyar ta, ko akwai matsala mu fiddata kasar waje."?
Mahaifin Hajiya Murja ya tambaya.
"Aa Alhaji likita yace buguwar da tayi ce kanta ya fashe amma jikinta Alhamdulillah tana samun
sauƙi zuwa gobema za'a iya sallamar ta."
Duk da basu buƙatar kuɗi amma haka mahaifin murja haka ya aje masu maƙudan kuɗi tare da
barin asibitin.
Idanun Hajiya Murja na ga ƙofa ganin ko Hibba zata shigo amma shuru, rashin shigowar ta ba
karamin daɗi yayima Hajiya Murja ba.
Hibba kuwa duk asibitin ta isheta domin kwata_kwata basu rayuwa cikin asibiti yanzuma ƙarfin
hali ne kawai ya sanya ta zama.
Ganin duhun dare ya fara yasa Hibba fitowa harabar asibitin zata fice, karo suka ci da wata
mata mai tsohon ciki da aka kawo lokacin, suna haɗa ido da hibba mai naƙudar nan tayo kanta
tamkar yunwataccen zaki.
Shake Hibba tayi tana kururuwar "ku riƙeta kada ku bari tabar asibitin nan, ku samu igiyoyi ku
ɗaure ta nace ku rike ta kada ta tsere."
A gigice mutane suka banbare matar mai tsohon ciki suna yima Hibba sannu.
Tamkar mahaukaciya haka matar nan tarika ihu tana su sake ta sai ta kashe Hibba, mutane da
dama sun tausayama matar nan mai naƙuda domin sun dauki wanan abu daya faru a matsayin
zafin nakuda.
Da kyar likitocin suka shige da wannan mata labour room, Hibba kuwa Murmushin gefen baki
tayi tare da kallon gabas da yamma sai da ta lura hankalin mutane bai kanta kafin fara magana.
"Karya kike ba zaki tona mani asiri ba, duk wanda yayi ƙoƙarin shiga gona ta kauda shi nike
daga hanya ta."
Tana gama fadar haka ta rufe idonta tare da karanto wasu ɗalasimai kamar ƙiftawar ido wutar
Nepar asibitin ta dauke wani matsanancin duhu ya mamaye asibitin...
_________________________________
...Bayan likitan ya gama duba lafiyar shi cewa yayi kowa ya bashi wuri domin ana buƙatar ya
ƙara hutawa kafin ya tashi, ɗakin suka jawo mashi tare da fatan samun lafiya.
Yau Fadila da Lubna sune da haɗuwa wuri ɗaya amma Fadila babu alamun bakar magana bare
habaici sai nan nan take da Lubna.
Wannan abu ba karamin ƙona ma Hajiya mariya rai yayi ba dan haka jan Fadila tayi suka shige
ɗaki.
"Mi nike gani haka, yau kece da wani shisshige ma Lubna anya kuwa kanki ɗaya."?
Hajiya Mariya ta fada a fusace
"Ni fa Hajiya ki kyale ni ki daina shiga Gonar Lubna wallahi kuwa, shin Hajiya tunda kike kin
taba yima awaki Brush."
Fadila ta tambaye mahaifiyar tata.
"Ke bani son zance banza, ke tunda kike kin taba ganin inda aka yima dabba wankin baki."?
"To Hajiya ki kiyayi ranar da za'a baje maki garken Awaki ace ki wanke masu baki, musamman
uwar garke duk ta fisu baƙin hali,ni bala'in da nagani ba kaɗan bane, nifa kada ma ki jaza mani
wani bala'in kinga tafiya ta."
Fadila ta karasa maganar tana barin ɗakin mahaifiyar tata da sauri.
"Awaki da Uwar Garke kuma, to ko dai ita ma Fadilan ta fara shaye_shaye ne."
Hajiya Mariya ta tambayi kanta.
Lubna kuwa yinin yau banda kuka babu abinda take, ita dai tasan tun sa'in da Al'ameen ya zuba
mata Coffee akai bata sake sanin mike faruwa ba sai dai ganin ta tayi bisa gado kwance" ya
Allah kasa bani bace sanadin fadawar shi wannan yana yi."
Kaf abinda Lubna keyi a kan idon Hajiya Salima dan haka wani irin tausayin ta ne taji ya kara
shigar ta ba kaɗan ba.
Kiran da ake ta yima wayar Al'ameen ce ya sanya Hajiya Salima dauka tare da Sallama, ashe
ma sirikar ta ce wato Leemcy jin Al'ameen ba lafiya nan Leemcy tace gata nan zuwa, Feedow ta
kira domin ta raka ta, basu ma tsaya ɗaukar mota ba Napep suka hau domin dama suna da
aikin da sabon bokan su ya basu suyi a cikin gidan su Al'ameen sai gashi kuma anyi a sa'a zasu
samu damar shiga gidan...
________________________
...Mahaifin Lubna kuwa jiki yayi sauki domin suna sanya ran sallama anan kusa.
Gaje kuwa baƙin hali sai ma gaba da yayi domin babban baƙin cikin ta bai wuce gidan hutu da
Mahaifin Lubna ya bada auren ta ba.
Alƙawari ne ta ɗauka indai tana raye baza'a ɗauran auren nan ba Sai tayi yadda tayi aka fasa
auren nan.
Kulu kuwa wannan zaman asibiti ribane a gare ta yawon banza sai abinda yayi gaba, da Malam
Sule ya tambayi inda take Gaje