Showing 9001 words to 12000 words out of 72825 words

Chapter 4 - RUWA BIYU NA MEENAT A YANDOMA.pdf

ga tayi nan da gudu sai ta dawo ta daka tsalle sai uban tumbinta yayi wata girgiza
kafin su dawo ƙasa.


Ganin yadda ta dage tana ɗirkar rawa yasa Aljanun kecewa da dariya suna fakar idon ta su tofa
mata wani abu data taka zata sul6e ta faɗi haka zata taƙarƙare ta mike taci gaba da ɗirkar rawa.


Ganin irin galabaitar da tayi ne yasa HIBBA daka mata tsawa, "ki dakata, basai na gaya maki
komi ba domin kuwa jikin ya gaya maki, in na ƙara ganin ƙafarki cikin gidan nan gawarki ce za'a
fitar, kada ki kuskura ki faɗama wani abinda ya faru in naji maganar nan wurin wani kashinki ya
bushe, ta ƙarasa magana tare da daka mata tsawa.
"Wallahi naji natuba hanyar gidan nan ma bazani ce nasani ba."


Ƙofar falon ce ta buɗe kanta "tashi ki bar gidan nan kafin mu mufiddaki Ɗan ƙarami kuyi mata
rakiya."


Jin wannan rakiya da za'ayi mata yasa ta zabga da gudu ko gyale ma a hannu yake, tun daga
nesa take kwalama mai gadi kira.

A rikice ya fito da adda domin kiran da take mashi yasan bana lafiya bane.
"Hajiya lafiya, ina zaki babu tufafi."

"Uwarka Nike Ɗan iya, tsirara ka ganni ko nan ubanka ne jikina,Talaka mai muguwar tambaya
ƙurilla shin kana bude mani gida ko sai nabi ta kanka na wuce, Gantalalle baka ganni ba a
gantale a wannan dare har ka tambayi lafiya, bude mani nace, in yaƙi buduwa ka bani tsani yau
kota katanga ne sai na dira nabar wannan baƙin gida." Ta karasa maganar tare da juyawa taga ko masu yi mata rakiya sun ƙaraso.


A rikece jin wannan zagi daya sha ya buɗe get ɗin, ƙafar da zata sa waje sai ji tayi ance "bata
fitaba kuyi mata rakiya."
Sakin gyalen tayi tare da barin wurin a million...

______________________________________
... Wasu hirɗa_hirɗan ƙadangaru ta hango guda biyu sun shaƙe Gaje ta hanyar yi zagaye
wuyan ta kamar tasa sarƙa.


Ganin wannan al'amari yasa Kulu rugawa a guje ta faɗa ɗaki ta rufe tare da barin mahaifiyar ta
tana mai kurma ihu.

A guje Lubna tayo kanta zata kamata, saurin riƙeta Mahaifinta yayi tare da girgiza mata kai.

Mutane kam kamar jira suke sai ga gida ya cika da yan kallo suna ta tofa albarkacin bakin su.

Duk yadda kayi ƙoƙarin raba Gaje da jankwatakayen nan abu yaci tura kana matso inda take
zaka ga sun buɗe baki tare da sakin wuyan ta kai kuma sunyo kanka ba shiri gida ya fara
darewa kowa ya fara ficewa cike da tsoron wannan al'amari.


Wasa_wasa Gaje sai suma take tana farfaɗowa har yamma abu ɗaya ake duk wani mai kama
ƙadangaro an nemo amma abu ya gagara.

Ganin Gaje ta fita hayyacin ta yasa Lubna fara kuka tare da rokon mahaifinta ya barta taje ga
mahaifiyar ta amma furr ya hana.


Abu har dare ana abu ɗaya ƙadangaru sunƙi barin jikin Gaje, baci ba sha Kwana ɗaya amma
duk ta fita hayyacin ta.

Da kyar malam ya bar Lubna ta nufi Mahaifiyar ta, babu tsoro tare da nufi kama ƙadangarun,
abun mamaki kafin hannunta ya isa jikin Gaje sai ga kadangaru sun saki wuyanta a guje sun
haye bango.

Maida numfashi Gaje tahauyi a galabaice, domin ta azabtu, ganin an raba Gaje da ƙadangarun
yasa Kulu ƙoƙarin matsowa inda Gaje take.


Mutanen da abun ya faru gaban idon su sai suka kara tabbatar wa lallai Lubna ba mutum bace.


Shigowar Saratu tayi dai_dai da tashin Lubna aguje suka rungume juna.


Wace ce Saratu
Saratu diya ce ga Malam zailani makwaftan su Lubna, tun tashin su Saratu ke tare da Lubna
duk da ƙoƙarin rabasu da akayi amma abun yaci tuna, Saratu mace ce da bata ɗaukar Reni ko
alama domin tane ma mutanen garin ke rangwantama Lubna saboda bala'i da masifa in kana
son su to ka taba kawar ta tabbas zakaga yadda ake ruwan bala'i domin Saro masifa kamar
yadda suke kiranta bata ɗaukar reni ko alama bata shiga sabgar kowa amma inka shiga tata
akwai matsala, bayan gama karatun su Saro gidan kakarta taje hutu shine dalilin rabuwar su da
Lubna.


Hanun ƙawar tata taja suka shige ɗaki.
"Dawowa ta kenan kaya na kaɗai na aje nace sai nazo na ganki, sai na iske gidan ku cike da
mutane lafiya kuwa."?
Cewar Saratu


Nan Lubna ta kwashe kaf abinda ya faru ta faɗama Saratu


"Hmm duk da mahaifiyar kice amma banso kika cire mata kadangarun nan ba naso ki barta ta
koyi darasin rayuwa."


Bata rai Lubna tayi, "kin san fa banison haka mahaifiyata ce fa."


"To naji mubar maganar."

Ko sallama babu haka Kulu ta faɗo ɗakin tana mai jan dogon Tsoki.
"Babu dai zuciya an yar kare ya ɗauka."

Murmushi Saro tayi domin yau bata da lokacin Kulu ta barta ne zuwa gobe


Bata bar gidan ba sai da aka fara kiran magriba.


Gaje kuwa takai sati tana jinyar wuyan ta daya sha shaƙa, tana karasa warkewa suka ɗora
daga inda ta tsaya.


Sallama akayi da Malam da haka yana fita Gaje ta lallaba tabi bayan shi domin tabbatar da
abinda take zargi.


Babu jimawa tadawo cikin gidan tamkar kububuwa ranta a jagule jira kawai take ya shigo.


"Lubna! Lubna!!."
Malam ya shiga kwala mata kira.

Ita da Kulu a tare suka fito
"Ki fara shirye_shirye na sanya gonata a kasuwa da zarar na sayar zani biya maki kuɗi kici
gaba da karatu."


"A hayye nanaye, yau ake yinta gobe sai labari, yanzu dama abinda kunnena ya jiyo mani ba
gizo bane da gaske gona ka sayar zaka biyama wannan Annobar kuɗin makaranta, wallahi ka
bani mamaki, indai ina raye wallahi kota fara karatun nan saita barshi, in sha Allahu ka sanyata
makarantar nan sai ta dawo maka daɗiya ko ɗa, kai nifa da ace asibiti na haihu babu abinda zai
hana ince musayar diya akayi mani, natsani lubna mai kaunar tama bani ƙaunarshi indai karatu
ne ta fara kagani zakasha mamaki."


Wani nauyi zuciyar shi tayi da ƙyar ya ɗaga hannu tare da nuna gaje idanunshi sunyi jajur
tamkar gauta, amma abinda ya tokare mashi zuciya ne ya sashi dafe ƙirjinshi da sauri, wani tari
ne ya turniƙeshi lokaci daya jini ya fara ambaliya ta hanci da bakinshi sai gani suka yi ya sulae
ƙasa.

A guje LUBNA ta fasa wata ƙara tare da rufowa da gudu kafin ta iso harya kai ƙasa...

*MASOYAN ASALI INA MATUƘAR GODIYA DA NUNA KULAWARKU GARENI� NAGA
KIRANKI DA SAƘON NINKU NAJINA SHURU DA KUKAYI INA MATUƘAR GODIYA ALLAH
YABARMU DAKE YABAR ZUMINCHI* ���


*MEEN@RT...✍*
08133562798
[7/23, 9:04 PM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_



Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma



```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*

*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*�
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________

*PAGE 9️⃣__*
... Kamar yadda yayi niyya hakan ce ta kasan ce domin kuwa sai da ya kwashe mako guda a
waje ba tare da ya nemi mahaifanshi ba, su Haj Salma kuwa hankalinta yayi ƙololuwar tashi
sakamakon rashin ganin tilon ɗan nasu.


Alhaji ne mai kwantar mata da hankali ta hanyar shaida mata duk inda yake zai dawo, shike
sawa hankalinta na ɗan kwanciya, kullum cikin kai kukan ta wurin Allah take.


Tamkar wanda ƙwai ya fashe mawa a cikin lakka haka ya ƙaraso cikin falon inda Mahaifanshi ke
zaune, ratsasu yaso yayi ya wuce sai dai kiran sunan shi da suka yi ne ya sashi dawowa da
baya.


"Barkan ku da safiya."
AL'AMEEN ya futa kanshi a ƙasa.

Cike da zallar mamaki suka amsa domin rabon da ya gaishesu an ɗauki lokaci mai tsayi.

"AL'AMEEN daga ina kake?, yanzu kayi mana adalci kenan katafi kabar gida har tsawon mako
daya baka dawo ba, ka kuwa san irin cikin halin da ka sanya mu."?
Hajiya Salima ta kara maganar cikin bacin rai."


"Kuyi haƙuri."
AL'AMEEN ya furta ba tare daya hada ido dasu ba


Mamakin dake fuskokin su a bayyane yake, yau AL'AMEEN ne ke basu haku, "Alhamdulillah
Allah maji roƙon bawa."


"Alhamdulillah mu fatan mu a kowane lokaci bai wuce Ubangiji ya shirya mana kai ba ka dawo
tamkar sauran mutane, magana ta gaba da nike so dakai i ta ce kafiddo matar aure cikin
ƙanƙanin lokaci nike so ayi bikin ka, shin kanada wata wadda kake so."?
Alhaji Sufyan ya jefama AL'AMEEN tambayar.


"Eh Daddy."
Ya bada amsa


"To wace ce? Waye mahaifinta? Kuma a ina take da zama."?


"Ɗiyar Alhaji Marwan ce ɗan kasuwar nan dayayi fice."
AL'AMEEN yaji bakin shi ya furta ba tare daya bashi izini ba, kwata_kwata ya rasa mi yasa ana
fara mashi waɗan nan tambayoyi sai dai yaji kawai bakin shi ya hau bada amsa bayan shi
kwata_kwata bai fatar LEEMCY ta zama matar shi.


"Alhamdulillah tunda ka samu mata har kun dai_dai ta tomu bamu da matsala, ni zami samu
Marwa zaboda muna da kyakkyawar alaƙa dashi."

Babu yadda hajiya Salima ta iya sai haƙuri domin tasan wace ce Leemcy amma tana fata
wannan auren ya zama sanadin shiriyar su, su duka biyun.


Alhaji Sufyan duban shi ya mai da gasu Hajiya Mariya tare da kiran sunan fadila.

"Kema ki fito da mijin aure domin ina sane da duk wasu abubuwa da kike aikatawa kece fita ki
kwana waje yawo babu inda baki zuwa to duk ina sane da ƙaryar da mahaifiyar ki keyi in na
tambaya a lokutan da baki nan domin ita ke goya maki baya duk abinda kike, cikin samarinki ki
fiddo wanda kike so za'a haɗa auren ku dana AL'AMEEN."

"Wallahi wannan sharri ne ake mata, kawai dan mutum yaga ɗan shi lalatacce ne sai ya ɗauka
ɗan kowa ma haka yake, to Fadila ba haka take ba Alhaji wannan sharri ne ake mata irin na
maƙiya."
Hajiya Murja ta ƙarasa maganar cikin zafi


Murmushin takaici Alhaji Sufyan yayi "domin yasan wannan duk aikin haj Mariya ne, ita ce sana
din lalacewar Fadila.


Kamar yadda Alhaji Sufyan ya fada haka kuwa akayi cikin makon aka sanya bikin AL'AMEN da
LEEMCY wata ɗaya.


LEEMCY kuwa Ganin yadda aikin bokan ta yaci ƙara tashi tayi tsaye tayi domin tayi alƙawarin
raba AL'AMEEN da duk wanda taga suna da kusanci....
____________________________
...Alhaji Lamaru kuwa hankalinshi duk a tashe yake ganin ga zabe ya taho amma babu wannan
halitta da aka sashi nemowa duk yadda ya baza mutane a gari amma shuru har yanzu babu
labari.

Zulfa'u kuwa sam hankalinta ba kwace yake ba tun bayan mutuwar ɗansu mai kimanin shekaru
biyu, da aka wayi gari aka iske gawarshi.


Sam Alhaji Lamaru hankalin shi bai tashi ba da mutuwar ɗan nasu domin shine ya bayar da shi
akayi mashi aiki domin samun duniya shiyasa sam hankalin shi bai wani tashi ba.

Alkawari ya dauka indai yana raye sai ya samo wannan halittar a duk inda take koda kuwa zai
rasa ranshi...

___________________________
...Sanyin Ruwan da ya sauka jikin tane ya sa ta tashi a matuƙar firgice tare da fara waige_waige

"Lafiyar ki kuwa, ace bacci tun dawowa ta kike yi amma har yanzu baki farka ba."
ABBAN HIBBA ya ƙarasa maganar cike da zallar mamaki.

Waige_waige ta hau yi cike da mamaki domin ganin ta tayi kwance bisa gadon ta, " To mi haka
ke nufi, ita da ke falo kwance a sume tun bayan azabar da HIBBA ta gana masu."

"Wai mike damunki kina ji ina maki magana amma kinyi shuru."
ABBAN HIBBA ya katse mata tunanin da take.

"Bakomai zazzabi ne ke damuna amma naji sauki."


"Ok Allah ya karo sauƙi, kada dai ku manta gobe friday tun wuri za'a zo a kwashe ku mUkoma
sabon gida.


Bala'inda take ciki harya mantar da ita tashin da zasuyi, dan haka cikin daren ta haɗa duk wani
abu da take buƙata, cike da tsoron abinda HIBBA ta aikata mata domin har yanzu jin jikin ta
take tamkar ba nata ba.


Unguwar da suka koma yanzu ita ake kira ihunka banza domin kuwa irin unguwannin nan ne
na nesa da gari.


Iya ƙeruwa gidan ya ƙeru domin an ƙawata shi da kayan alatu na more rayuwar duniya.

Abinda suka san suna matuƙar bukata na daga abin amfani dasu kaɗai suka taho amma komi
ABBA HIBBA ya zuba a Sabon gida.


Sai yanzu Hajiya Murja ta tuna da ƙawar ta wato hajiya Turai, waya ta ɗauka tare da kiranta
domin jin lafiyar ta, sai da tayi mata 3 miss call a na hudun ne ta dauka.


"Kai jama'a! Wannan bala'i dami yayi kama, kin kirani ne keda aljanar ɗiyarki ku ƙarasa kashe
ni, to nida ke har abada mun rabu ke hanyar da gidan ki ma yabi nida ita har abada babu ni
babu ke, number kima yanzu zanyi blocking ɗinta, ina zaman zamana kika jawo mani bala'i sai
gani da taka rawar Aljanu sune dayi mani rakiya har gida, babu ni babu ke har abada."

Kafin Haj Murja tayi yunƙurin furta wani abu ji kake ƙit! Haj Turai ta tsinke wayar.

"Yanzu shikenan ni ɗaya ta zaki jazama bala'i ki barni dashi, ni Murja nashiga Ukku na lalace
yau nakai kai na ga halaka saboda son abun duniya."


Hibba kuwa tun bayan dawowar su gidan baka taba gani ta fito da rana sai dai in dare yayi kaji
fitowar ta.

Ganin tun bayan dawowar su gidan babu wani mugun abu daya faru yasa Hajiya Murja sakin jiki
tare da zallar murnar wannan al'amari.


Tun safe ABBAN HIBBA ya bar gidan dumin wata harkar kasuwanci da ta taso masu, dan haka
yau gidan daga HIBBA sai Mahaifiyar ta.


Abinci ma mai aiki ce ta dafa shi ta kaima kowa ɗakin shi dan haka duk yau idon HIBBA bai
haɗu dana Hajiya Murja ba.


Kasancewar Alhaji bai nan yau tun wuri Hajiya ta shige ɗaki ta kulle kanta.


Dare ya raba bakajin motsin komi sai kukan karunuka da kuma mujiya, A hankali ƙofar ɗakin
Haj Murja ta fara buɗe kanta wani baƙin hayaƙi na shigewa ɗakin.

Labulayen ɗakin ne suka fara tashi sama sakamakon wata iska mai tafiya a hankali data fara
kaɗawa, wutar dakin dake kashe ce ta fara kunna kanta tana fafarniya ta ɗauke ta dawo, a
hankali baƙin hayaƙin nan ya fara haɗewa wuri ɗaya tare da koma wa wani dogon hannu mai
farata zaƙo_zaƙo ya tafi luuuw! Ga Haj Murja dake bacci bata san mike faruwa ba...
___________________________________
...Da sauri likitan ya fito yana yarfe zufa, duban su yayi tare da furta.

"Ku same ni office."
Tare dayin gaba abinshi cikin sauri


Gaje ya mutsa fuska tayi cike dajin haushin likitan, ita so tayi ya fito yace SULE ya rigamu gidan
gaskiya.


Baya shigar su office ɗin likitan zaune suka iske shi yana dakon su.

"Kamar yadda na shaida maku halin damuwa da baƙin ciki shine musabbabin wannan almari da
ya tsintsi kanshi, zuciyar shi ta fara kumbura i ta ce sanadin aman jinin daya fara, a tunaninmu
za"ayi ma shi aiki amma Alhamdulillah mun fara shawo kan matsalar tunda ciwon baiyi nisa a
jikin shi ba kuka kawo shi, zamu riƙe shi a hannun mu amma gaskiya zan jima muna kula da
lafiyar shi amma yanzu haka muna bukatar dubu ɗari domin taimakon da zamu rika bashi shine
zai hana ayi mashi aiki."

"Shikenan ka gama likita."?
Gaje ta faɗa tana yatsina fuska.

"Eh wannan sune adadin kuɗin da muke buƙata."


Mikewa tayi tare da furta.
"Sai ka jimu."
Tayi gaba abinta.


"Likita dan Allah mahaifina zai rayu kuwa."?
Lubna ta tambaya hawaye nabin rabin fuskarta.


"Allah shine mafi sanin gaibu, ku dage da addu'a sannan kuyi ƙoƙari samo kuɗin nan da wuri
muke bukatar su."

"Insha Allah zamu kawo."
Lubna ta ƙarasa maganar tare da bin bayan mahaifiyar ta da sauri.


"Mama dan Allah gonar da baba ke magana kanta ki taimaka a sayar da ita azo ayi mashi
magana."
Lubna ta ƙarasa maganar da karyayyar murya.

"Gafara can! Ba za'a sayar ba, da in saida gonar nan dana sama raina kaunar ta ƙara in na
samu mai sayen ki in sayar a bani kuɗin."
Gaje ta karasa yin maganar cike da masifa.

Mugun hali irin na Sailuba da Gaje a nan take suka shirya gidan aikin da zasu kai Lubna a basu
Adadin kuɗin da suke buƙata sai Lubna tayi aiki na adadin kuɗin.


Cikin ikon Allah ashe gidan su Al'ameen aka kai Lubna tayi aiki, a bangaren Hajiya Salima,
sosai Hajiya Salima ke ƙaunar Lubna ganin irin jarabtar da Allah yayi mata, ba wani aiki mai

wahala take sanya ta ba daga wanke wanke sai sharar ɗakin Al'ameen girki ma ba koda yaushe
take yi ba.

Ubangiji yakan jarabci bawan shi ta kowa ne fanni to haka ce ta faru ga Lubna tun bayan sanya
idon ta kan AL'AMEEN taji kaf duniya babu wanda take so sama dashi.


Sabanin Al'ameen da tunda ya hada ido da ita yaji sam bata yi mashi ba da gangan zai sata aiki
da tayi kuskure ya hauta da cin mutumci in bayan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login