Showing 51001 words to 54000 words out of 72825 words
kimanin watanni huɗu maganar Umma nayi mani yawo cikin kai, duk na canza nayi
sukuku hatta aminiyata hajita Turai ta fuskanci halin da nike ciki. Ita ce ta ƙara zugani cewar
bakomi bane face bankwana, nan na shashantar da maganar naci gaba da hidimomina.
Ƙalubale na farko dana fara fuskanta shine kwata_kwata Jadda bai da ilimin addini irin mutanen
nan ne masu zallar boko da suka daɗe cikinta, sai naga duk rashin ilimina to na fishi sau dubu.
A wata safiya da bazan taba mantawa ba a cikin tarihin rayuwata, shine tunda asuba Jadda ya
tayar dani mukayi sallah abinda bai taba yiba, bayan gama sallar naga ya kafe ni da ido da
yaga zamu hade ido sai ya kauda kanshi.
"Ki shirya muje gida."
Wannan ita ce maganar daya faɗa mani tare da ficewa.
Ban kawo komi a raina ba ganin tunda nayi aure banje gida ba na dauka gaida su Umma
zamuje yi, da murnata na shirya gari nayin haske muka dauki hanyar gida.
Tunda muka shawo santar gidan mu nike ganin mutane jifa_jifa suna kallon mu tare da girgiza
kai, ban ƙara tsinkewa ba sai da muka shiga farfajiyar gidan mu naga mutane cike sunyi
jigum_jigum suna alwala.
Cike da mamaki na fito na nufi hanyar dakin Umma domin sanin mike faruwa, wani wawan birki
naja ganin mahaifiyata an nannaɗeta cikin likafani fuskarta ce kaɗai a buɗe.
Tamkar zautacciya haka na fara girgizata ina kiran sunan ta.
"Umma ki tashi bazaki mutuba ki barni, karya kuke Umna bacci take ya za'ayi ma ta mutu ta
barni umma ki tashi ki gaya masu baki mutu ba."
Na karasa maganar tare da fashewa da kuka.
Matan dake cikin ɗakin kuwa banda kuka babu abinda suke, ganin tamkar na fita a hayyacina
yasa ƙanwar Umma janyeni.
"Murja sai hakuri wanda ya fimu ƙaunar Sa'adiyya ya ɗauki abinshi, Ubangiji Mungode maka
Sa'adiyya Allah yasa can ta fiye maki nan."
Wannan maganar da inna Hassu tayi ji nayi kaina yayi wata sarawa nan na yanke jiki na faɗi.
Kai tsaye asibiti aka wuce dani, ban farka daga sumar da nayi ba sai da aka dawo daga kai
mahaifiyata.
Jikina naji yayi mani wani irin nauyi wani abu ne ya tokare mani zuciya wasu hawaye ne suka
balle a fuskata.
"Dan Allah Murja ki kiyi hakuri kodan abinda ke cikin ki likita yace jininki ya hau,ga kuma Juna
biyu dake gareki har na kimanin watanni huɗu."
Cewar Inna Hassu ita ma hawaye nabin fuskarta.
Kwana na biyu a asibiti aka sallameni, tashin hankalin da nike ciki ba karami bane domin gani
nike tamkar Umma bata mutuba da naje gida zani ganta amma ina wanda ya mutu bai taba
dawowa har abada.
Sai da akayi sadakar bakwai mahaifina yace in koma gida domin laulayim da nike.
Tun bayan mutuwar mahaifiyata nike cikin wani irin ƙunci marar misaltuwa kewar ta nike matuƙa
tare da tariyo maganganun da take gaya mani ashe da gaske wasiyyace daga ita ba zamu sake
haɗuwa ba."
Koda yaushe hawaye ne ke gudana a fuskata ga laulayin ciki da nike fama dashi, Jadda shine
me kwantar mani da hankaki a duk lokacin da yaga ina cikin damuwa domin ya kwallafa ranshi
akan cikin nan dake jikina.
Haka kwanaki suka yita shuɗewa har yau cikina nada kimanin watanni takwas.
Kiran mahaifinane ya shigo wayata da sassanyar marecen lahadi.
Jin yace in same shi gida ko drive ban ɗauka ba haka naja mota sai gida.
Ganin halin damuwa da mahaifina ke ciki yasa ni fara tambayar shi.
Dogon Numfashi yaja tare da zama bisa kujera ya fara magana.
"Sanin kanki ne kece ɗiya kwalli ɗaya da muka mallaka, na soki fite da komi a rayuwa ta, na
nuna maki gata wanda ba kowane ɗa bane ke samun irin shi,a yanzu ina da yaƙinin duk abinda
nace ina so zaki iya mallaka mani domin ba zaki so in fadi wannan kujera da nasa gaba
ba,buƙata ce nike da ita wadda duk duniya kece me iya yi mani ita a matsayinki na ɗiyar da nike
gani inji sanyi a cikin raina."
Mahaifiya ya ƙarasa maganar tare da kafe ni da ido.
Cike da zaƙuwar jin buƙatar mahaifina na amsa mashi komi ye zanyi.
Abinda naji ya faɗa ne yayi sanadin Miƙewata tsaye ba tare dana shirya ba a matuƙar firgice,
ƙaton cikin dake gabana ne yayi wata murɗawa tamkar ɗan dake ciki zai faso ya fito waje,ba
shiri na sanya hannuwa na biyu tare da dafe ciki na....
Kada a manta da yi mana subscribe
https://youtube.com/channel/UCFefdlP2piaSVv-lAANrzBQ
KAINUWA TV DON NISHADINKU PLS KUYI LIKE & SUBSCRIBE
*MEEN@RT...✍*
[8/21, 12:12 PM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*PAGE 4️⃣2️⃣__4️⃣3️⃣*
...Ƙafafun na danaji sun kasa ɗauka tane yasa ni saurin zamewa bisa kujera amma har yanzu
abinda ke ciki na be daina motsiba.
Wannan magana da mahaifina ya gaya mani tayi masifar tayar mani da hankali domin a kona
mafarki banyi tunanij jin makamancin abinda naji yanzu ba.
"Alfarma guda ɗaya dana nema a wurinki ita ce ba zaki iyayi mani ba Nurjanatu."?
Mahaifina ya fada tamkar zai zubda hawaye.
"Ka gafarceni abinda ka nema ba me samuwa bane rayuwa ce sunkutukum kake nema in
salwartar, yakai mahaifina idan na mallaka maka abinda ke ciki na ya zanyi da mahaifin shi
wato Jadda, kace in babu shi tabbas bazakaci zabe ba, Shin kasan tsayin lokacin da Jadda ya
ɗauka yana tanadi kuwa muddin muka salwantar da rayuwar ɗashi ko kuma ɗiyar shi wallahi
baba ina cikin tashin hankali."
Na karasa maganar tare da fashewa da kuka.
"Yanzu Murja wannan ita ce sakayyar soyayyar dana nuna maki, da abinda zaki saka mani
kenan, jinin ki ɗaya da zaki salwantar saboda ni amma ba zaki iya ba tabbas kin bani kunya, to
ki sani muddun kika ce ba zaki mallaka mani abinda ke cikin ki ba Murja daga yau na datse duk
wata alaƙa dake tsakanina dake." Mahaifina ya ƙarasa maganar rai a matuƙar bace.
Cike da tashin hankali naji gabana yayi wata mummunar faɗuwa lokaci ɗaya hawayen dake kai
kawo a fuskata suka tsaya.
"Na rene ki tun daga yarintarki har girmanki amma ni zan nemi buƙata a wurin ki kihana, yau na
fahimci baki ƙaunata Murja."
"Zanyi komi kake so, amma ya zamuyi da Jadda daya kwallafa rai a kan wannan cikin."?
Na faɗa cikin hanzari domin a lokacin zuciyata ta bushe na yarda in sadaukar da jaririna domin
mahaifina ya cika burin shi.
Wani farin ciki marar misaltuwa ne ya ziyarci mahaifina ji yayi tamkar ya goyani domin yasan
burinshi ya gama cika.
"Ina Alfahari dake Murjanatu, idan watan haihuwarki ya tsaya zani bukaci jadda ya barki ki dawo
gida zan samo cikin dangina wata ta riƙa kula dake domin in kina kusa dani ne kaɗai burin mu
zai iya cika, in aiwatar da abinda nasa gaba batare da munfuskanci wata matsala ba."
Jin wannan jawabi na mahaifina se nayi na'am dashi lokaci daya naji ƙaunar da nike ma abinda
ke ciki ta kau domin nasan yana zuwa duniya rayuwarshi zata shiga cikin haɗarin da mutuwa ce
kawai hutu a gare shi, gida na koma cike da shirya irin ƙaryar da zani shiryama Jadda.
Kasancewar shi mutum ne ɗan boko bai wani ƙiya ba lokaci daya ya yarda inje gida in watan
haihuwata ya kama, nikam jin ya amince wani farin ciki ne ya lullubeni.
A kwana a tashi babu wuya wurin Allah domin yanzu watan haihuwata ya kama inda na rika
wata irin rashin lafiya tamkar me naƙuda, haɗa kaya na nayi Jadda ya miƙani gida cike da farin
cikin magajin nashi ya kusa zuwa duniya, tsohon ɗakina da nayi rayuwa cikin shi lokacin ina
budurwa nan mahaifina yasa aka gyara mani, nida wata tsohuwa da bansan inda mahaifina ya
samota ba.
Kulawa ta musamman mahaifina ke bani domin ganin na sauka lafiya ya, Nikam banida burin
daya wuce in sauka lafiya in rabu da wannan cikin domin nasan indai haihuwa ce yanzu na fara,
dan nayi kyauta da wannan ta farko ba wani abu bane.
Wani yammaci nida mahaifina muna zaune muna hira nike cewa
"In na sauka lafiya, shin ya zamu yi da Jadda idan ya buƙaci ganin abinda aka haifa."?
Dogon Numfashi mahaifina yaja tare da fara magana.
"Na gama shirya komin domin hatta gawar jariri tuni nasa anyi mani booking kina haihuwa za'a
kawota domin wannan al'amari ba ƙaramin shiri nayi mashi ba kedai Ubangiji ya sauke ki lafiya."
Mahaifina ya faɗa.
Ba'a ɗauki wani lokaci me tsayi ba ciwon naƙuda ya kamani, wannan tsohuwa ita ta kula dani
tare da bani duk wani temakom gaggawa da ake buƙata, tun safe nike abu ɗaya har la'asar, na
wahala tamkar bazan rayu ba, hankalin mahaifina yayi matuƙar tashi ganin yadda ake abu ɗaya
tun lokaci me tsayi, kamar yadda ya buƙata ina haihuwa tsohuwar nan me kula dani ta gyarani
jaririyar kuwa kamar yadda ya gargaɗeta bata taba ta ba.
Wani tunani ne ya rika yi mani yawo cikin kwalwa.
"Ke Murja yanzu ɗiyarki wadda kika sha wahalar haihuwar ta ita zaki salwantar saboda abin
duniya, abinda kike ƙoƙarin aikatawa yanzu fa matsayin kisan kai yake, shin kinada tabbacin
zaki sake haihuwa idan kin salwantar da wannan, haƙƙin Mahaifinta zai barki ki zauna lafiya
kuwa."? Naji wata zuciya na gargaɗi na kada in aikata haka.
"Allah me tausayin bayin shin shi ne, ki aikata daga baya baya seki tuba."
Wata zuciya ta fada mani, shigowar Mahaifina ce ta katse mani tunanin da nike.
Ganin ga Jinjirara nan cikin jini ko gyarata ba'ayi ba yasa Mahaifiya sanya hannu ɗaya ya
dagota, wani sabon kuka ne jinjirar ta ƙyaƙyace dashi, kukan da kana jinshi kasan kukane da
take buƙatar jin gumin mahaifiyar ta take bukata a shayar da ita tamkar yadda ake ma ko wane
jariri, amma ita tun bayan zuwanta duniya haka aka barta cikin jini a ƙasa a yashe sanyi na
shiga jikinta.
Saman wani ƙaramin benci Mahifina ya sanya jinjirar tare da daukar wani zane ya rufeta.
"Kina da buƙatar ganin ɗiyar ki kafin ƙaddararta ta risketa."?
Naji Mahaifina ya faɗa.
Samun kaina nayi da dirowa daga saman gadon tare da nufar jinjirar na buɗe fuskarta,
kyakkyawa da ita sak Ni ta biyo wurin kyau amma baƙin mahaifinta ne ta ɗauko ,kururu take
tamke tamkar taci babu hannun ta ɗaya yana cikin baki tana ta tsotsa, abin mamaki idanunta
bude suke tar! ganin wani abu na ƙoƙarin ɗarsuwa a zuciyata yasa nayi saurin barin wurin tare
da hayewa saman gado wani abu me kama da nadama na ƙoƙarin ɗarsuwa a zuciya ta.
Wata farar Kwalba naga mahaifina ya fiddo daga cikin Aljihu tare da nufar Fuskar jinjirar.
Cikin ɗaga murya naji mahaifina ya fara magana.
"Yakai Hatsabibin baƙin Aljani kayi sani cewa mun cika maka burinka wannan jinjirar ta zama
mallakin ka, muma ka cika mana namu burin."
Yana kaiwa nan ya buɗe kwalbar tare da danna bakin ƙaramar kwalbar cikin hancin jinjirar, wata
mahaukaciyar ƙara jaririyar ta kwala tamkar ana yankan naman jikinta, idanun tane suka rufe
lokaci daya barin Fuskarta ya fara rikiɗewa yana komawa na maza.
Murmushin Farin ciki mahaifina ya saki domin yasan wannan alamace ta Aljanin ya koma
ƙarƙashin ikon su, yanzu zasu milke shi.
"Taso kiyima ɗiyar ki kallon ƙarshe, domin kana daga cikin mutanen da keda damar ganin
fuskarta a halin yanzu.
Wata mummunar faɗuwar gaba ce ta ziyar ceni sa'in da nayin arba da Fuskar jinjirata data
koma rabi ta namiki rabi ta mace, saurin ja da baya nayi tare da furta.
"Baba mi hakan ke nufi."?
Murmushi yayi
"Yana nufin daga yanzu har zuwa karshen rayuwar ta a haka zata rayu, ba zata taba warkewa
ba."
Ya karasa maganar tare da kafeni da ido.
"Bani sonta dan Allah kada ka bari ta rayu, a jefar da ita inda ba zata taba rayuwa ba."
Na fada a rikice domin a lokacin na tsorata matuƙa.
A gabana mahaifina ya kira wani amintaccen yaron shi ya miƙa masu jinjirar da Ke faman bacci
ne ko suma domin jikinta tamkar ta mutu nike gani, ficewa suka yi da ita, nan mahaifina ya
ɗauko gawar jariri sabuwar haihuwa tare da mika mani a matsayin wadda zamu mikama Jadda
cewa abinda na haifa ya mutu.
Koda su Cika aiki suka fito da jinjirar kai tsaye, wata babbar kwalbatin dake cikin wata Unguwar
da mazauna cikin ta akasarin su talakawa ne naga sun nufa, kwalin suka jefa cikin kwalbatin
tare dayin gaba abinsu.
Jadda kuwa Jin ɗanshi ya mutu seda ya zubar da hawayen baƙin ciki domin ya kwallafa ma
ranshi soyayyar yaron.
Mahaifina kuwa duk da beda wasu masoya masu yawa cikin al'umma amma shine wanda ya
lashe zaben shugaban ƙasar, munyinfarin ciki mara misaltuwa da wannan mataki da mahaifina
ya taka.
Ban koma gida na ba seda nayi kwana arba'in sannan nakoma gidan Jadda, Rabo me gaggawa
Rabon da shine har gobe nike kira Rabon wahala shine samun cikin Hibba da nayi ban yima da
komawa gidan Jadda ba.
A wannan karon hattani wata irin soyayyace nike nuna ma cikin domin duk wani buri namu to ba
shakka yana kan cikin nan, tun yana da wata bakwai muka bar ƙasar n muka nufi India domin
can nace zan haihu.
Zuwan mu india shine asalin faruwar komi shine mafarin labarin, kamar yadda muke zaune a
hotel tun bayan zuwan mu ƙasar, zaune nike bisa kujera ina cin tuffa, Jadda kuwa ya fita ya
dawo.
Ƙofar da naji ana kwankwasawa ce ta sanyani tashi domin a tunani na Jadda ne ya dawo, turus!
nayi sakamakom tozali da nayi da wata mata wadda kana ganinta kasan haifaffiyar kasarce,
kallo daya nayi mata naji gabana yayi wata mummunar faɗuwa domin wani irin gashi ne da ita
tun daga saman kanta har kasa yana jan ƙasa, ga wasu fararen kaya jikin ta tamkar fatalwa
idanunta kuwa jajur tamkar garwashin wuta.
Bankaɗeni tayi tare da shigowa dakin tana me fashewa da wani irin kuka daya haddasa ma
ɗakin fara girgiza.
"Kece wadda ta rabani da farin cikina, kece wadda tayi sanadin zamana cikin kaɗaici ita kuma
take rayuwa cikin farin ciki, na dauki alƙawari daga yanzu har zuwa ƙarshen rayuwarki zaki yita
ne cikjn tashin hankali da kuma zullumi."
Matar na kaiwa nan kafin in an kara ta zama hayaƙi tare da shigewa jikina, daga lokacin ban
sake sanin mike faruwa ba sedai ganina nayi kwance Jadda na jero mani sannu.
Tun daga wannan lokaci na daura aure da mafarkin matar nan tana zo mani zata kashe ni.
Babban tashin hankali shine zuwan Hibba duniya, jaririyar da tasha banban da sauran jarirai,
likitocin da suka amshi haihutawa suma sun sha manakin ganin jinjirar da aka ɗora a jikin
mahaifiyarta lokacin zuwan ta duniya amma se gani akayi ta mulmulo ta faɗo kasa duk buguwar
da jaririyar tayi bai sa ta buɗe baki da niyyar kuka ba, a rikice likitoci suka dauketa tare ta bani
ita domin in shayar da ita, nan ma ta datse bakinta taƙi sha tare da kafeni da ido.
Hankalin malaman asibitin nan fa ya tashi matuƙa ganin wanan irin jaririya da aka haifa masu,
nikam a halin yanzu na tsorata matuƙa da ganin wannan al'amari.
Madarar shanu ita ce ta zama abincin hibba na tsawon rayuwar ta har i zuwa girman ta, tun
tana jaririya take azabtar da rayuwa ta duk duniya mahaifinta kaɗai ke ganin dariyar ta.
Dakatawa tayi da maganar tare da fashewa da kuka, duk wani me rai dake cikin falon jin irin
zaluncin da suka aikata seda ya zubar da hawaye, Alhaji Jadda kuwa mutuwar zaune yayi
idanunshi ne kaɗai ke zubar da hawaye domin yasan Murja ta gama cutar shi.
"Innalillahi wa'inna ilaihiraji'un."
Ita ce abinda Malam Saif ke memetawa.
"Kun tafka babban kuskure, son duniya yasa kin biyema mahaifinki kun aikata abinda Allah yayi
hani dashi, duk saboda mulki wanda yanzu harya gama mulkin gashi nan yana girbar abinda ya
shuka, babu tausayi bare imani haka kika salwantar da ɗiyarki da kika haifa, duk dan saboda
cikar wani burinku na duniya, Ubangiji ya kiyashemu da aikata makamancin abinda kuka
aikata."
Malam Saif ya ƙarasa maganar cike da zallar bacin ran wannan rashin imani da suka aikata ma
Lubna.
Mahaifin Lubna sam ya kasa magana hawaye ne kaɗai ke zuba a idanunshi.
"Yau shine aka salwantar da ɗiyarshi aka tarwatsa mata jin daɗin ta aka zama sanadin rasa
wani sashe na jikinta, tabbas Murja tayi ma shi cutar da har abada bazai taba yafe mata ba."
Mahaifin Murja kuwa kuka yake tamkar ƙaramin yaro domin yau abinda suka binne yau ya tonu
a bainar jama'a.
"Ina me roƙonka da girman Allah Alhaji Jadda kada kayi magana, mu jira muji ta bakin Mahaifin
Lubna wato Malam Sule taya ya samu Lubna ya akai ta zama ɗiyar Gaje ba tare da Gaje tasan
ba ita ta haifeta ba wannan abu akwai ɗaure kai, gashi dai kowa ya shaida Lubna ɗiyar Gaje ce,
dan haka muna saurarenka ka warware mana wannan ƙulli muji gaskiya abinda ya faru shekaru
ashirin da biyu da suka shuɗe."
Malam Saif ya karasa maganar tare da kafe Malam Sule da Ido.
Yaƙe Malam Sule yayi wanda ake kira kafi kuka ciwo ya kalli Gaje dake faman Zubda hawaye,
girgiza kai yayi cike da takaici ya fara bada labari kamar haka....