Showing 1 words to 3000 words out of 72825 words
[7/17, 10:04 AM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*PAGE 1️⃣__2️⃣*
...Gagarumin hadarin da yayi ma garin ƙawanya ne ya haɗe da duhun dare ya sake haddasa
ma garin wani irin matsanan cin duhu mai matuƙar ban tsoro.
Mace ce yar kimanin shekaru talatin da wani abu, amma sam yanayin jikin ta bai nuna
shekarun ta sakamakon hutu daya ratsa jikin ta, Zaune take ita da HIBBA yarinya yar kimanin
shekaru goma sha bakwai kallo suke ita da mahaifiyar ta ta.
Iskar da taji ya fara kaɗawane alamun ruwa zai sauko ya sake ɗaga hankalinta, gashi dai
Abban hibba bai dawo gida ba ga kuma hadari da ke kara ɗaga mata hankali.
"Umma bacci nike ji nidai sai da safen ki."
Hibba ta fada tare da nufar ɗakin ta.
Wata ajiyar zuciya Haj Murya ta sauke, domin harga Allah tana matuƙar ƙaunar Hibba ɗiya ɗaya
rak da suka mallaka, son da bata taba yima wata halitta ba, amma yanzu tsoron Hibba take
tamkar yadda take tsoron mutuwar ta, saukar ruwan ne da mugun ƙarfi ya sanya ta wata iriyar
zabura ta miƙe tare da shiga dakinta ta haye gado tana waige_waige.
"Alhaji! Alhaji dan Allah kadawo, innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, ka ƙi yarda dani kaƙi gasgata
maganar da nike fada maka akan HIBBA."
Wutar ɗakin ce ta fara farfarniya.
Blanket ta bude tare da shigewa jiki na kyarma, taku taji an farayi alamun ana nufo inda take ga
kuma ƙarar ruwan da ake sheƙawa da ta cika ɗakin.
Addu'a ma ta kasa zufa ce kawai ke tsiyaya a jikin ta ga wata kyarma da take tamkar gadon zai
karye.
Cak taji komi ya lafa sai dai ruwan da ake shekawa har yanzu kamar da bakin kwarya.
Wani bacci taji yana fizgarta bata san lokacin da ta fara gyangyaɗi ba.
"HIBBA karki kasheni, kin manta nice na haifeki, ashe dama ɗiya zata iya kashe Mahaifiyar ta."?
Haj Murja ta karasa maganar tana kara shigema bangon ɗakin domin sun kawo inda babu
yadda za'ayi ta gujema HIBBAH.
"Hahaha Umma! Bani da wani buri daya wuce inga na rabaki da rayuwarki, Umma abinda kika
shuka shine zaki fara girba dole ki mutu, musha jininki."
HIBBA ta karasa maganar tare da nufar mahaifiyar ta da wuƙa tsirara.
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun."
Haj MURJA ta furta domin mafarkin yau ya kazanta fiye da na baya.
"Alhaji kana ina yau har yanzu baka dawo ba."
Miƙewa tayi da nufin barin ɗakin.
Ƙafafunta aka wawura tare da bugata da bed side kanta ya bugu, tsabar ruɗewa da kwalwar ta
tayi ƙokarin shigewa karƙarshin gado ta fara.
"Kul! Kika ce zaki guje mana."
Ta jiyo wata murya wadda ko tantama batayi muryar HIBBA ce, kanta dake mata wani
matsanancin raɗaɗi ta ɗaga tare da kallon HIBBA dake zaune da wasu jajayan kaya ta juya
mata baya.
"Hib...bba..."
Bakin Haj MURJA ya kasa ƙarasa sunan illa jikin ta dake kyarma.
Dariya aka kece da ita dakin ya ɗauki amsa kuwwa, garam! ƙofar ɗakin ta rufe kanta.
Juyowar da HIBBA zatayi Haj MURJA tayi arba da abinda bata taba gani ba, domin rabin fuskar
HIBBA ya ru6e tsutsotsi ne ke fita suna cin naman fuskar ga wasu idanu kwala_kwala kaf suffar
ta ta juye ta koma abin tsoro.
"Hahaha kin gama mafarki na yanzu kuma gani nazo maki a zahiri."
Cewar HIBBA cikin wata iriyar murya mara daɗin saurare.
"HIBBA mi nayi maki kike azabtar da rayuwata, kin manta ni nayi dakon cikin ki na haife ki nayi
renonki har kika kawo lokacin nan kike ƙoƙarin kashe ni, mina aikata maki."?
"Ke ba abin tausayi bace Umma ko baki so sai na kashe ki sannan zani samu salama, babu
wanda nike ji na tsana kamarki Umma, dan haka yanzu zaki bakunci Lahira."
Tana kaiwa nan ta shaƙi wuyan MURJA da hannu ɗaya tayi sama da ita.
Sai da ta tabbatar ta daina numfashi sannan ta sake ta tare da barkewa da mahaukaciyar
dariya ta bace 6at.
Turo kofar yayi tare da yarfe jikinshi da ruwa yayima duka, cak! Ya tsaya ganin matar tashi baje
tamkar gawa, a guje yayo kanta yana mai ambatar sunanta.
Ganin shuru yasa shi kwalama HIBBA kira, a guje tayi cikin dakin domin tasan wannan kiran da
Mahaifinta ke mata bana lafiya bane.
HIBBA kam a rikici take jijjiga mahaifiyar ta tare da kiran sunan ta "Umma...
________________________________________
"Mama da Allah dan Girman Allah kada ki yanka mani hannu, Mama miyasa baki sona dan
Allah in laifi nayi maki ki sanar dani in baki hakuri ki yafe mani dan Allah."
Cewar LUBNAH tana mai sanya ɗayan hannun ta tare da rufe gefen fuskar ta dake barazanar
bayyana.
"LUBNA nina haifeki amma na tsaneki, bani sonki bani kaunar ki, tun lokacin dana ga halittar
dake tattare dake, badan kada in kasan ce Uwa ta farko data data kashe diyar ta ba LUBNA da
wukar nan a cikin ki zani caka maki ita kowa ya huta, na aikeki dibar ruwa kin fasa mani bokiti in
ban yankeki ba yau raina bazai mani sanyi ba." Cewar GAJE dake rike da wuƙa ta saka ɗiyarta a kona.
Dayan hannun ta tasa tare da dafe Rabin fuskarta dake rufe da kallabin dake kanta.
"Mama indai zakiji sanyi a ranki na yadda ki yi mani hukumci."
Ta karasa maganar tare da fashewa da kuka.
"Ko baki ce ba LUBNAH sai nayi maki hukunci."
Ta karasa maganar tare da yanka damtsen hannun LUBNA.
ƙara ta saki lokacin da taji kaifin wukar ya ratsa tsokarta ya rabata biyu.
"Gobe ma ki kara fasa mani bokiti, kuma maza ki dauki bokiti keje fanfo ki dauko mani ruwa."
LUBNA azabar da hannunta ke mata kasa tashi tayi hawaye suka ci gaba da zuba ta gefen
fuskar ta inda bata rufe ba, da kyar ta mike tare da shigewa matsakaicin dakin nasu mai dauke
da katifar kwanansu sai kuma wani miro da buhun nan kayan sawar su.
LUBNA ba zata haura shekaru sha bakwai a duniya ba, baka taba gane shin tana da kyau ko
akasin haka domin kullum rabin fuskarta a rufe yafe da gyale.
Gaban miron taje ta tsaya tare da fashewa da kuka tayi wurgi da gyalen dake saman kanta nan
fuskarta ta bayyana.
INNALILLAHI WA'INNA ILAIHIRRAJI'UN shine abinda na furta lokacin da nayi arba da fuskar
LUBNA, Rabin fuskarta ta mata ce Rabi kuma fuskar namiji ce, a taƙaice dai fuskar ta an daga
tsakiya an rabata bangare daya ta mace bangare daya kuma fuskar namiji ce.
Hannuwan ta biyu tasa tare da shafar fuskar tata tana mai fara wani sabon gunjin kuka.
"Ya Allah banyi butulci ba ina godiya da wannan halitta da ka yi ni da ita tun farkon tashi na
bansan daɗin uwa ba an haifemu mu biyu amma abokiyar tagwaici na kadai mahaifiyar mu ke
nuna ma soyayya, uwata ta tsane ni mutanen gari sun tsaneni Allah nagode maka da wannan
baiwa da kayi mani." Ta kasa karasa maganar sakamakon wani kuka daya tokare ta.
Kallon miron take bangaren fuskar macen na zubda hawaye, bangare fuskar bamijin ce taga ta
fara mata murmushi, wani sabon kukan ta sake fashewa dashi.
"LUBNA in na iske ki cikin dakin nan wallahi kashe ki ne kaɗai baniyi."
GAJE ta faɗa daga waje.
Gyalenta ta maida tare da rufe rabin fuskar ta tare dayo waje, "ki fara share gidan nan kafin ki
ɗebo ruwan"
GAJE ta faɗa a tsawa ce.
Kasan cewar gidan na masu karamin ƙarfi ne tsakar gidan ko shafe babu sai jar kasa dake baje,
daga bakin baranda kuma a shafe yake.
Tsintsiyar kwakwa ta dauka tare da fara sharrar gidan hawaye nabin rabin fuskarta.
Kammala sharar tayi da hannunta dake ɗigar jini domin har yanzu yankan da mahaifiyar ta tayi
mata bai bar zafi ba, bokiti ta dauka tare da nufar Fanfon dake cikin unguwar su.
Tana fita yara suka fara kiranta Ruwa biyu suna shigewa gidajen su a guje.
Abokiyar tagwaicin ta ce ta hango suna tafe ita da ƙawayen ta.
"Kulu dan Allah ki amsa ki ɗebo mani ruwa hannu na bani iya wa."
Cewar LUBNA
Wani kallon wulakanci Kulu tayi ma Lubna.
"Ke dalla gafara ki bani wuri, har ni zaki kalla kice in ɗebo maki ruwa, to koda kina ganin tare
aka haife mu wallahi na tsane ki LUBNA, ke nifa ina ji a jikina zani iya kasheki kowa ya huta."
Kulu ta karasa maganar cike da nuna zallar ƙiyayya.
Sauran Ƙawayen KULU kecewa suka yi da dariya.
"Nikam Kulu, wai wannan yayar taki kodai mata maza ce? Ace mutum fuskarshi rabi ta mace
rabi ta namiji."
Sake kecewa suka yi da dariya.
Wata hatsabibiya ce ta fara magana.
"Ke nifa Kulu duk da wannan halittar yayarki ce bazai hana mata rashin daraja ba."
Bangaje ta suka yi tare da barin ta nan kasa, ganin bata da mafita yasa ta mike dafe da hannun
ta dake mata raɗaɗi.
A hankali tsokar jikinta ta rika haɗewa ciwon na haɗe kanshi, kallon hannun take domin hakan
ba yau aka fara ba.
"Ba zani bari kowa ya taba sonki ba, duk wanda ya soki mutuwa ce hukuncin shi "
LUBNA taji an rada mata a kunne.
Kafin ta ƙarasa wurin fanfon haka yara suka rika janta suna kiran ta RUWA BIYU.
Inda sabo ta saba da ƙiyayyar da kowa ke nuna mata, amma ita ƙiyayyar da tafi damunta i ta ce
wadda mahaifiyar ta ke nuna mata, tunda take bata taba samun soyayya ba daga mahaifiyar ta,
makaranta ma kowa ya tsane ta, mahaifinta kaɗai kesonta
Zuwanta bakin fanfon tayi sa'a bata iske kowa ba, dan haka duƙawa tayi domin ɗibar ruwan,
"yar baƙa ruwa biyu"
Wani yaro ya faɗa tare da yin boll da bokitin da take ɗibar ruwa nan take ruwan ya bare shi
kuma ya ruga a guje.
Kasan cewar yanayin fatar ta baka ce wadda ake kira black beauty, cike da damuwar wannan
abu da kowa ke mata ta ɗauki bokitin tare da sake ɗora shi ta shiga buga monon.
Su Goga ne suka zo wucewa ta wurin monon kasan cewar inda take ba cukowar mutane.
"Kai! Goga kamar fa yarinyar can ce nike gani."
Ɗan taure ya faɗa cikin muryar yan daba.
"Ahh! Alƙur'an i ta ce, kai tsuntsu daga sama gasasshe, Alafiya dai Goga ya kace ne."?
Wanda aka kira Goga ɗaga kai yayi tare da ƙare mata kallo, gefen 6aren fuskar ta da ta rufe ne
yaji yana muraɗin ganin abinda ta rufe.
"Ku zo muje."
Goga ya faɗa tare da yin gaba.
Tsattsaye ta gansu gabanta sun kewaye ta, nan fa jikin ta ya hau ciri.
"Dan Allah kuyi hakuri, kuzo ku ɗiba ni na gama."
"Dillah gafara can, munafUka wannan lullu6in da kika yi zaki bude muga wace uwar ce kike
rufewa."
"Innalilahi wa'inba ilaihirrajiun Baba kana ina."?
Ta karasa maganar tana mai ƙara sanya hannu tare da danne 6arin fuskar ta.
"Ah! Kajifa Goga wai Cus ɗinta take kira, izininka nike jira Goga yanzu in ƙaddamar mata."
Ɗan taure ya karasa maganar yana tangaɗi.
"Kubar munafuka yau sai ta bude wannan lullu6in munga mi take rufewa."
Goga ya faɗa tare da Sanya hannu ya fizge gyalen da ta rufe fuska.
Wata ƙara ta saki wadda ta haddasa masu faduwar gaba, ba shiri suka sanya hannayen su
suka toshe kunnuwan su.
Kafin su yi wan kwakkwaran motsi ta zube ƙasa tayi ruf da ciki tana wani kurnani tamkar
yunwatacciyar zakanya.
Burinsu dai kam bai cika ba domin dai LUBNA a ruf da ciki ta faɗi basu samu ganin fuskarta ba.
"Mu zaki yima akuyan ci, Oga mu ai munfita zama yan akuyoyi, ku jira ku gani."
Ɗan taure ya karasa maganar tare dayin inda taka kwance.
Ɗaga kafar da zaiyi sai ji suka yi an kece da dariya Mahaukaciyar dariya da ta haddasa ma
wurin amsa kuwwa...
_Ina dai ƙara tuni, kibi littafin nan tun yanzu kada inyi nisa a rika pls daga farko_
*MEEN@T...✍*
08133562798
[7/18, 6:19 PM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*PAGE 3️⃣__4️⃣*
...Tun daga bakin Get babu abinda kaje ji face amon waƙa daya karaɗe ilahirin gidan, abinda zai
baka mamaki shine yadda Volume ɗin waƙar yayi matuƙar yawa.
Hajiya Salima dake bacci sakamakon ciwon kan daya addabeta firgigit ta farka tare da nufar
ɗakin ɗan nasu dan tana da tabbacin shine ummul aba'isin faruwar haka.
Turus! Taja ta tsaya jikin ta har ciri yake, lokaci ɗaya ciwon kan dayafi na ɗazu ya sake yi mata
dirar mikiya.
Da sauri ta dafe kanta dake mata barazanar tarwatsewa, tare da jingina da bangon ɗakin
sakamakon wani jiri da taji yana ɗibarta.
Ba komi bane ya haddasa mata haka face AL'AMEEN da ta gani tare da wasu kyawawan ƴan
mata da basu da marasa da karuwai kusan su huɗu sun baje suna ta shan shisha, kayan jikin
su kaɗai zaka kalla ka tabbatar da ko a cikin Karuwai to su sun shahara.
"Innalillahi wa'inna ilaihirrajiun, AL'AMEEN!."
Sunan shi data kira ne ya ankarar dasu cewar wani ya shigo, bata rai yayi domin har ga Allah in
yana huta da bebs ɗinshi hatta wayar shi kashewa yake.
"Mom ya zaki shigo mana wuri babu Sallama, bayan ke kike kwa6ata akan indai na shiga wuri
ba Sallam."
Ya ƙarasa maganar tare da shuno baki gama.
Cike da tsabar baƙin ciki Haj Salima taji wasu hawaye nabi fuskarta.
"AL'AMEEN mi kake son ka zama, yanzu har takai ka riƙa kawo mana mata cikin gida,
AL'AMEEN kana so baƙin cikin ka ya kashemu kowa ya huta."?
Ta karasa maganar wani tuƙuƙin baƙin ciki na taso mata daga cikin zuciya.
Ƙasa da kai yayi yana gunguni, su kuma matan sunyu fiƙi_fiƙi da ido, "zaku fice daga gidan nan
kosai na haɗaku da security."?
Cewar Hajiya Salima rai a matuƙar 6ace.
Sumi_sumi suka tattare kayansu tare da rabata suna wucewa sai wata daya da ta tsaya kusa
da AL'AMEEN wadda daka kalli idon ta kasan ta shahara.
Kallon AL'AMEEN tayi tare dayin farrr da ido. "Baby sai mun haɗe muyi waya kawai."
Ta karasa maganar tare da jifar Mahaifiyar Al'ameen da mugun kallo tare da ficewa.
Binta yayi da kallo dumin duk cikin yan matan shi yana masifar ƙaunar LEEMCY saboda irin
fararen matan nan ne da suka haɗa da bleaching har yellow fatar su keyi, shi ko a duniya farar
mace duk yadda take mugun ƙaunar ta yake sabanin baƙar mace da yayima wata iriyar
muguwar tsana duk kyawun ta kuma.
"AL'AMEEN!."
Mom ta kira sunan shi, "Ka iske ni ɗaki."
"Nifa fisabilillahi Mom bacci nike ji in na gama zaki ganni."
Bata tsaya saurarar wannan kayan takaici ba barin ɗakin tayi rai a matuƙar bace.
Bakin gadon ta ta zauna tare da fashewa da wani irin kuka mai tsuma zuciya.
"Ya Allah kana gani Allah kai ne sheda tun yana yaro tarbiyyar daka koyar damu mu tarbiyyanci
yaran mu da ita muka tarbiyyance shi, Allah kai shedane bamu saki rayuwar AL'AMEEN sakaka
kamar yadda masu kuɗi ke sakin yaran su ba, munyi iyakar yinmu iyakar ƙoƙarin mu, amma tun
tasowar shi yaro ne dabai jin magana tarbiyyar da muke bashi tamkar bashi muke bawa ba,
Ubangiji ka shirya mana mana AL'AMEEN domin shiriya taka ce, ya ALLAH mun ɗauki wannan
jarabawa da kayi mana da hannu bibbiyu ba zamu yi butulci ba ALLAH kai mai gafara ne
ALLAH ka shirya mana shi dama sauran yara na Al'ummar musulmi."
Kukan daya ci ƙarfinta ne yasa ta kasa ƙarasa maganar.
Cike da tausayin matar tashi ya ji wasu siraran hawaye sunyi nasarar kubce mashi, tun
shugowar ta dakin yake bakin ƙofar tsaye, halinda take cike ne ya hana ta ganin shi.
Gefen gadon ya zauna tare da share mata hawaye, "Mu muka ma Ubangiji lamurranmu kada
muyi garaje mU kasa cinye wannan jarabawa, Hajiya nasan kina haɗiyar gubar AL'AMEEN a
cikin gidan nan, amma mu ƙara haƙuri tare da dagewa da addu'a, komi lokaci gareshi."
Jingina tayi da mijin nata da take kallon shi a matsayin Uwa da kuma uba agareta.
"Ni dakai ƙuruciyar mu mai kyau mukayi ba muyi abinda AL'AMEEN keyi ba, amma shi..."
Saurin rufe mata baki Alhaji yayi tare da girgiza mata kai.
"Mu ƙara haƙuri, komi lokaci ne, nasan ki da hakuri da kuma juriya."
Nan ya shiga rarrashin ta har ta daina kukan sai kuma ajiyar zuciya da take saukewa.