Showing 3001 words to 6000 words out of 72825 words
"Ya kamata ka tafi wurin Mariya kasan kwanan tane kasan halinta ka tafi kada tazo ta tayar
msna da hankali."
Cewar Haj Salima.
Harga Allah Alhaji Sufyan yana matuƙar ƙaunar fiye da Mariya, Salima mace ce mara haƙuri
hatsabibiya.
"Mar'atu saliha, kullu yaumun ina kara godiya da Ubangiji ya mallaka mani ke a matsayin mata,
sam baki barina inyi rashin adalci a tsakaninku."
Murmushi tayi domin inda sabo ta saba da wannan yabo da mijinta ke mata.
Hajiya MARIYA dake la6e bakin ƙofa tana jin duk wata magana da suke wani murmushin
mugunta ta saki.
"Dani kuke magana, ni in haifi mace a cikin gidan nan daga zuwan ki ki haifa namiji, fata shine
AL'AMEEN ya ƙara lalacewa fiye da haka in so samu ne ma ya zama ajalinki."
Ta karasa maganar tare da barin wurin sakamakon tafiyar Alhaji da taji.
AL'AMEEN kuwa yana gama baccin shi wanka yaje yayi tare da shiryawa kota kan Mom dake
jiran shi bai bi ba ya dauki key ɗin motar shi tare da fitowa, saurin yin baya tayi ganin sun kusa
yin karo da juna.
"Kee!"
Ya furta rai a bace.
Hannu ya daga tare da zabga mata wani lafiyayyan mari da yayi sanadin ɗaukewar ganin ta na
wicin gadi, ruɗewa tayi tare da faduwa kasa.
"Hanne ni zaki kusa bankewa kin taho kai sama kamar tunkiya, bana ce kada ki sake in ƙara
haɗa hanya dake ba, banza bakar mace kazama dake in kika sake na sake hada hanya dake
jikin ki ne zai gaya maki."
Ya karasa maganar tare dayin Boll da ita yayi gaba
Inda sabo Hanne mai yima hajiya Salima hidima ta saba da halin shi.
Abinda zai baku mamaki shine fatar jikin AL'AMEEN ba fara bace baƙace irin ta mahaifin shi
domin bai biyo mahaifiyar shi data kasan ce fara ba, amma minahikin ya tsani baƙar mace.
A fusace yaba motar wuta, da gudu mai gadi ya buɗe get dan yasan ba wuya yasha mari wurin
ɗan masu gida, tamkar zai bi ta kan mai gadi haka ya fice da motar a guje.
____________________________________
..Duk wata dabara da taimako da ake ba mutum inya suma to Abban Hibba ya yima Hajiya
Murja amma shuru kake ji.
Tun abun bai fara bashi tsoroba har yazo ya fara tayar mashi da hankali, saman gadon suka
mai data.
"Kina ina wannan abun ya faru da mahaifiyarki."
Cewar Abban Hibba.
"Abba ina daki na, tun kafin tasowar hadari nayi bankwana da ita nata fi na kwanta, kiran da ka
kwala mani ne nazo naga halinda take ciki."
A jiyar zuciya ya sauke domin harga Allah kwanan nan ya rasa gane kan Matar shi, ganin irin
ruwan da ake tsulawa ne yasa bai kira likita ba ya jinkirta gari ya waye.
"ABBA ni bacci nike ji sai da safe."
Hibba tayi gaba ba tare da bi takan Mahaifiyar ta dake kwance batasan wanda ke kanta ba.
Cike da mamaki yake kallon abinda Hibba ta aikata, kasanceqar shi ɗan boko sai kuma wata
zuciyar tace mashi lokacin bacci ba'a hadashi da komi."
Dan haka sai ya dena ganin laifin HIBBA, shi ya kwana kan Hajiya har gari ya waye bata farka
ba.
Bayan dawowar shi masallaci yana zaune kusa da ita domin harya kira Family doctor.
A firgice ta farka tare da ƙanƙame shi, "Wallahi i ta ce, kashe ni zatayi Hibba ce, wayyo Allah na
nikam na shiga ukkuna."
Ta karasa maganar tare da sakin kuka.
"Ki natsu wace ce zata kashe ki."?
"HIBBA ce ita ce zata kashe ni ka taimake ni."
Sakaka ya tsaya yana kallon ta.
"Ya isheki."
Ya daka mata tsawa.
"Shin sau nawa zan gargaɗeki da ki ƙara jifan ɗiyata da wannan kalmar, shin kodai kwalwarki ta
samu matsala ne, wani Aljani wani surutai can Hausawa ku kuka sanshi, mu maleriya muka
sani kuma nasan ita ce ke damun ki, ga likita nan zai zo ya dubaki, ina mai kara gargaɗinki da
kidai na jifar jinina da wannan kalmar can kuka san wasu aljanu." Ya barta nan sake da baki.
Wasu sabbin hawaye taji suna bin fuskar ta.
"Yau ta fahimci abinda mahaifiyar ta ke nuna mata tun lokacin da mutane biyu suka fito neman
auren ta, marigayiya mahaifiyar ta taso ta auri Bashir wanda ya kasance mai addini amma
baida kuɗi, in da murja ta nace ita sai Alhaji abdallah, ashe dama irin wannan ranar mahaifiyar
ta ke hasko mata gashinan yama ki yadda akwai wata halitta wai ita alaja." Ganin batada wata mafita yasa ta sauko daga saman gadon tare da fadawa toilet tayo alwalla
tare da kabbara sallar asuba.
Gama Sallar tata keda wuya likita ya karaso har cikin ɗakin likitan ya shugo ya duba ta tare da
yi mata VP nan yaga jinin ta ya hau.
Magunguna ya rubuta da za'a sawo mata tare da fatan samun lafiya, shigowar HIBBA ɗakin
yasa Hajiya Murja daburbucewa ta rasa mike mata daɗi.
"Umma ya jikin."?
"Da..dada.. Da sauƙi."
Ta amsa murya na kyarma.
Ɗago kanda zata yi idanunsu suka haɗu, da sauri ta kauda kanta ganin HIBBA na mata
murmushi ga wasu haƙora masu matuƙar tsini sun bayyana a bakinta.
Duk Hajiya Murja ta rasa sukuninta, ganin an kwana biyu babu abinda ya faru yasa ta fara sakin
jiki da HIBBA.
Zaune take bakin gado tana char da wata babbar aminiyar ta, saman screen ɗinta ta kalla nan
taga biyar da rabi na yamma lokacin sham maganinta yayi, lalace ya hanata motsawa ta ɗauki
maganin dake bisa bedside, HIBBA ta fara ƙwalama kira tazo ta ɗauko mata.
"HIBBA zoki miƙo mani maganina lokaci yayi."
"To Umma taji an amsa mata."
Shigowa tayi sanye da wata bakar riga kai babu kallabi.
"Umma gani."
HIBBA ta faɗa.
"Ke bake Umma ke kira ba dani take."
Wata Hibba Sak tafito daga Toilet ɗin Hajiya Murja ta faɗa.
Wayar dake hannun Hajiya Murja Su6ucewa tayi cike da tashin hankali take kallon HIBBA data
rabu gida biyu suna tsaye gaban ta.
"Aa duk ƙarya kuke nice nan Umma ke kira."
HIBBA cikon ta Ukku dake ƙokarin shigowa ɗakin ta faɗa.
Su duka HIBBA da suka rabu gida Uku garda suka farayi kowa na cewa ita ake kira.
Hibba ta farko cr tace
"Ku jira mu duka UMMA ke kira dan haka mu karasa wurin ta."
Gaba daya ukkun kecewa suka yi da dariya suka yi a tare suka haɗa baki "UMMA gamuuu...
_________________________________
...Tun bayan shigowar shi gidan har kawo yanzu da duhu ya fara baiga LUBNA ba.
"GAJE! ina yarinyar nan take har magriba tayi banga gilmawar ta ba."
Cewar Mahaifin su LUBNA.
Sai da tayi kamar ba zata tanka ba sannan ta buɗe baki a wulaƙance da nuna baka isa ba tace.
"Nifa kada ka isheni da tambaye_tambaye LUBNA na aiketa debo ruwa saboda tsabar ita ɗin
shegiya ce har yanzu bata dawo ba."
"Ya isheki GAJE."
Ya fada a tsawa ce, duk da shi mutum ne mai matuƙar haƙuri amma yau Gaje ta kawo shi wuya.
"Allah wadarai hali irin naki, kina bani mamaki ɗiyar cikin ki kike kira shegiya, wa'iyazubillah,
badan a gabana kika haifa su LUBNA ba tabbas da bazani yarda kece mahaifiyar ta ba, kin
tsani diyar da ta kasan ce ta cikin kinki, halittar da tazo duniya da ita bayin kanta bane lokacin
da zata zo duniya ba zabin halitta aka bata ba Allah shiya yi ta a haka amma kin kasa ganewa
mutanen unguwa su nuna mata tsana da ƙiyayya kema ki nuna mata Gaje kiji tsoron Allah."
"Kaga in wa'azi kaje ji kaje gidan redio amna ni GAJE na tsani LUBNA na tsani in ganta a kusa
dani, kai in takai ce maka magana so nike inga LUBNA tana wulaƙanta a rayuwa."
Tsabar bacin rai kasa magana yayi, face wani tuƙuƙi na bacin rai dake taso mashi.
Rikica! Sukaji faduwar wani abu, a guje yayo bakin ƙofar ganin LUBNA cikin wani hali zube a
ƙasa.
"Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un GAJE kinga abinda kika jaza mana ko ciwon ta ya tashi, kizo mu
samu a sata ɗaki kafin ta rikice."
"Wallahi ta mutu bani da matsala, ke Kulu tashi muje ɗaki mu kulle in ta gama haukanta mu
dawo."
Ɗaki suka shige suka kulle suka bar malam nan rike da LUBNA.
Idon ta na bangaren mace ne ya fara rufewa, a galabaice ta buɗe baki.
"Baba kai ma ka gudu ka sake ni kada in cutar dakai, dan Allah Baba ka gudu."
Ta fada bangaren fuskarta na namijin na fara canza launi.
"Ba zani barki ba, bani iya barin ki har abada koda zaki zama sanadin mutuwa ta, LUBNA ina
tare dake nafiso duk wahalar da zakisha musha tare, Ina sonki a duk yadda kike."
Ya karasa maganar hawaye nabin fuskar shi.
Jikin tane ya saki lokaci ɗaya ta fara wata kyarma, facewa da kuka Baba yayi tare da kara
ƙanƙame LUBNA tamkar za'a kwace mashi ita.
Farautan ta dake zaƙo_zako suka fara tsayi jikinta na malƙwashewa, ƙafafun ta kuwa
harbe_harbe kawai take take ƙasar wurin ta hau tashi.
Miƙewa tayi zaune tare da far kartar mahaifin nata da akaifunta da suka yi zaƙo_zaƙo tana
ƙoƙarin kwacewa.
Jiyo ihun LUBNA da makwafta keyi ya sasu shigewa gidaje tare da kullewa.
Jifa tayi da mahaifin nata kanshi ya bugu da wani bokiti, azabar da yake ji a jikin shi sam lokacin
bata ita yake ba, fatan shi shine kada ta yi nasarar ficewa daga gidan nan.
Tana kubcewa kururuwa ta hauyi tare da fatali da duk wani abu da taci karo dashi tana ƙokarin
barin gidan.
Da sauri ya tarbeta bakin shi dauke da addu'a ya samu ya riƙeta, wahalar duniya kuwa ya shata
ranar jikinshi duk ciwukan da LUBNA ta ji mashi ne.
Addu'a takobin mumine cikin ikon Allah ji yayi LUBNA tayi laƙwas a jikin shi ta sume.
Hawaye yaji sun kubce mashi lokacin da ya haɗa ido ds bangaren fuskar ts namiji dake aika
mashi da mugun kallo, addu'a ya tofa mashi tare da rufe mata rabin fuskarta ya ɗauketa ya
kaita ɗaki.
Gefen ta yake sai lokacin ya lura da ciwukan da LUBNA taji mashi da kuma jinin da ke fita a
jikinshi, "Ubangiji ga LUBNA nan kai ne mafi sani akan abinda ka boye na tattare da ita, Allah ka
zama gatan ta aduk inda ta tsinci kanta."
Baiyi bacci ba domin gata dai bacci take amma sai dai yaji ta kece da dariya tana ƙoƙarin tashi,
addu'a yake babu ƙaƙƙautawa.
Hatta sallar asuba yau cikin gida yayita kasan cewar jikin shi babu kwari.
Makwaftan su yaji sun fara ihun, fitowar da zai yi yaga an baje gawar su Goga da kuma Ɗan
Taure wuyan su a karye idanu sun firfito waje....
*MEEN@RT...✍*
[7/19, 3:17 PM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*PAGE 5️⃣__6️⃣*
...maganar da bokan ya faɗa mashi ce ta sanya wani gumi wanke mashi fuska babu shiri ya
cire hular dake saman kamshi ya hau firfita da ita.
Kallon garsaƙeƙen ƙaton bokan dake gaban shi yayi, "Boka a taimaka, wallahi ko labari ban
tabajin yarinya mai irin wannan halittar ba dan Allah a taimaka."
"Rufe mani baki!."
Bokan ya daka mashi tsawa da wata mummunar murya.
"In kasan da Allah miya kawoka wurin, radda duk ka ƙara ambatar Allah a gabana, kodai jinin ka
aljanu su tsotse shi ko kuma daga ranar ba zaka sake gani da idanun ka ba har abada."
Tamkar zai ma Bokan sujada haka ya durƙusa jiki na kyarma ya furta.
"Tuba nike."
"Maganar samo yarinya mai wannan halittar kuma, kada ka kuskura zabe ya taho ba tare da ka
samota ba, muddun ka bari akayi shiga satin zabe bamu gudanar da aikin mu ba to ba shakka
kana cikin matsala, bace mani da gani kada in sake ganin ka har sai an samo ta."
Da gudu_gudu Alhaji Lamaru ya baro bukkar Bokan, kafin ya kai inda ya baro security nashi sai
da ya sha baƙar wahala.
Yana shiga Motar ya Umurci driver ya wuce dashi gidan Alhaji Sufyan.
Yayi sa'a domin kuwa ya tarar dashi gida bai fita ba, nan aka gaisa irin ta abokan da suka daɗe
basu haɗu ba.
"Yadai! Duk na ganka a rikice, lafiya kuwa."?
Cewar Alhaji Sufyan.
"Za6e ya taho ya kuwa ba zaka ganni a rikice ba, kai fa kaji daɗin ka kayi gwamnan garin nan
ba tare da ka sha wahala ba ka gama yanzu kuma kana bisa kujerar ɗan majalisa, ka huta
bokan ka ya iya aiki, ni yanzu daga wurin Jikan oduduwa nike, ya umurce ni da samo abinda ko
a mafarki ban taba ganin shi ba kai a duniyar nan ma babu shi."
Murmushin takaici mahaifin AL'AMEEN yayi, domin ya lura har yau LAMARU bai yarda kuma ya
dogara ga Allah ba.
"Har gobe ina ƙara yi maka tuni, tunda nike ban taba zuwa gaban boka ko kuma malami ba
dumin biyan wata buƙata ina kai kuka na ne ga Allah shike share mani hawaye na a koda
yaushe, ashe har yau baka bar wannan mummunar ɗabi'ar taka ba tabin bokaye."
"Ai biyu na raba kafa ina sa malamai suyi addu'a ga kuma ta ƙarƙashin ƙasa da nike bi, kasan
abun biyu ake rabawa."
Murmushi kawai Alhaji Sufyan yayi, domin yasan Alhaji Lamaru yayi nisa bai jin kira.
AL'AMEEN da dawowar shi kenan gaida mahaifan nashi yayi tare da nufar cikin gidan, yana sa
kafarshi cikin falon yaci karo da Fadila dake zaune ta ɗora ƙafa ɗaya bisa daya tana kallon wani
series, kasan cewar Falon gidan guda ɗaya ne sai kabi ta cikin shi kafin ka isa zuwa ga
ɗakunan ta gaban ta yabi domin karasawa ɗakin shi.
"Mtsw! Su Balamu anyi asarar kunnuwa, wani kam yayi faɗuwar bakar tasa."
Maganar da Fadila ta fada ce ta dakatar dashi tare da juyowa.
"Kee! Dawa kike."
Ya fada rai a 6ace domin bai shiga harkar kowa cikin gidan.
"Da wanda ya tsargu nike, wai shin ni tsarar kace da zaka zo bisa kai na kana mani wasu
banzayen tambayoyin ka."
Fadila ta ƙarasa maganar cike da rashin kunya.
Duk da kasan cewar ta i ta ce babba hakan bai hana AL'AMEEN daga hannu ya tsinka mata
mari.
A fusace ta mike tare da dafe kumci tana masifa.
"Uwar ka ka mara, ka mari Salima, Allah ya isa na kuma wallahi banga abinda zai hana ni
haɗaka da yan sanda ba."
Zafin Zagin da tayi mashi ne bai san lokacin da ya cire Belt ya shiga zuba mata shi ta ko ina.
Ihun Fadila ne ke tashi cikin gidan tana neman taimako, a guje su Hajiya suka fado cikin falon,
ganin irin bugun da AL'AMEEN ke yima yayar shi yasa Hajiya Mariya yin kukan kura ta tinkari
AL'AMEEN, da kyar suka kwaci fadila da yayi ma lilis.
"Kin haifi Annoba gashi nan ya addabi kowa, to wallahi bai daki banza ma domin yau shima a
cell zai kwana, wama ya sani ko shaye_shayen shi yaje yayi ya zo ya sauke haukanshi kan diya
ta, to ba zata sa6uba."
Hajiya Mariya ta karasa maganar cike da masifa.
Fashewa da kuka Mahaifiyar AL'AMEEN tayi tare da fizgo kwalar rigar shi ta dauke shi da wasu
tagwayen maruka.
"kaga abinda ka ja mana ko."?
Ta karasa maganar cikin kuka mai tsuma zuciya.
Har tsakiyar kwalwarshi yaji marukan da tayi mashi, a fusace yayi boll wani jug nan take ya
tarwatse, da ƙarfi ya fizgi ƙofar falon ya fice tare da shigewa mota yabar gidan cike da zallar
bacin rai...
______________________________
...Ganin HIBBA da suka rabu gida uku suna tun karo ta yasa ta mikewa a guje tayi falo, tare da
kulle ƙofar falon tana sauke ajiyar zuciya.
Dafa kafaɗar ta taji anyi da wasu dogayen yan yatsu, jiki na ciri ta juyo domin ganin wane sabon
bala'in ne ta tarar.
Hibba ce tsaye ta wage baki tana kyalkyata dariya, "kin ɗauka zaki guje mana ne? To ni na
tarbe mana falo yadda in kin gudo in tarbe ki, kai ku shigo gata na tare."
HIBBA ta fada da ƙarfi.
Bango sauran HIBBA suka ratsa sai gasu cikin falon sun hade da cikon ta huɗun, kyalkyacewa
sukayi da dariyar a tare cikin wata irin ƙazamar murya.
"Ba zaki iya guje mana ba."
Suka fada a tare.
Nan fa suka fara kasuwa kashi_kashi suna cika falon tare da nuna ta da hannu suna kecewa da
dariya.
Ganin wannan bala'i
Jiki na kyarma ta nuna ta da yatsa "HIB...BAH."
tare da sulalewa kasa.
6at ta bace komi ya koma yadda yake.
Hasken daya kashe mata ido ne yasa tayi saurin maida idon ta ta rufe, a hankali duban ta yakai
ga drip ɗin da aka sanya mata, DADDYN Hibba ne