Showing 60001 words to 63000 words out of 72825 words
mahaifiyarta da
aka kashe har take wannan iƙirarin, wani zazzafan mari mutumin ya ɗauke ta dashi.
"Sakarar banza mara kishin ɗan uwan mu, kina bani hanya ko se munbi ta samanki mun wuce."
ƙanin mamacin ya fada rai a matuƙar bace.
Haka suka riƙe mahaifin Lubna dake ƙoƙarin haka su cimma burin su gefe guda shida Saro
suka tunkari Lubna da ta gama jibgar Gaje.
Uwar Garke kuwa wani murmushin mugunta tayi domin tasan yau tabbas zata yi ƙeta irin
wadda bata taba yi ba, mutumin dake ƙoƙarin fizgo Lubna yana gaf da isa gare ta wata
mahaukaciyar guguwa me matuƙar Ƙarfi ta turniƙe gidab lokaci ɗaya aka kece da mahaukaciyar
dariya...
Babu yawa mu haɗe gobe in shaa Allah.
*MEEN@RT...✍*
08133562798
[8/31, 6:47 PM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*PAGE 5️⃣0️⃣__5️⃣1️⃣*
...Guguwar nan haka ta turniƙe gidan ko tafin hannun ka baka iya gani, sannu a hankali ihun
mutane ya fara cika dodon kunnen su Malam Sule.
Bulalai ne suka bayyana ba tare da kaga ne bugun ka ba sedai kawai kaji saukar su ta ko ina,
nan fa maza suka fara kururuwar neman temako makaman dake hannuwan su duk suka zube
nan suka fara neman hanyar guduwa cike da nadamar shigowa gidan su Lubna domin basu yi
tunanin hatsabibancin ta ya kai haka ba.
Uwar Garke nan ta shiga laftarsu suna zabga ihu, an ɗauki lokaci me tsayi kafin ƙurar guguwar
ta fara lafawa sannu a hankali aka fara hango mutanen dake yunƙurin kashe Lubna baje a ƙasa
suna mai da numfashin wahala, da dai suka ga guguwar ta lafa a guje suka riƙa ficewa a gidan
ɗaya bayan ɗaya.
Tun daga ranar mutane ke matuƙar tsoron Lubna domin sun ji lokacin da take laftar mutanen
nan suna ihu, Gaje kuwa ta ɗauki lokaci tana shakkar Lubna kafin ta manta abinda ya faru ta
koma baƙin halin ta, abinda zai baka mamaki shine koda wasa yan uwan mamacin basu tada
zancen bugun da akai masu ba balle kuma wani yayi ƙoƙarin ɗaukar mataki.
Tsagaitawa Malam Sule yayi tare da kallon su Malam Saif da suka tsura ma shi ido cike da
zallar mamakin wannan al'amari gami da tausayin rayuwar Lubna, ruwa aka bashi ya kora tare
da ci gaba da bada labarin.
"Tun daga ranar mutanen garin da kuma makwafta da sunji ciwon Lubna ya tashi haka suke
kulle gidajen su ba tare da ansa mu mai ƙarfin imanin da zai kawo mana ɗauki ba, nasha
tunkarar Malamai da dama da batun ciwon Lubna amma da sunji labarin abinda ya faru da
ɗayan malamin nan kai tsaye suke bijirewa su ƙi taimako na, nasha baƙar wahala akan Lubna
wadda badan na jajirce da addu'a ba da tuni na rasa rayuwa ta, ni ne kaɗai wanda Lubna zata
raba taji sanyi a zuciyar ta amna banda Gaje ko alama batasan miye soyayyar Uwa ba, ta rayu
cikin kaɗai ci da zallar damuwa, A wannan rana a dai_dai wannan lokaci na sauke nauyin dake
kai na, na faɗar gaskiyar lamari, Lubna waɗan nan sune iyayenki na ainahi."
Malam Sule ya ƙarasa maganar hawaye nabin fuskar shi na rabuwa da wadda yana ji a jikin shi
zai iya sadaukar da rayuwar shi saboda ita.
Wuri yayi shuru bakaji sautin komi sai shasshekar kukan Murja da kuma Gaje, Hajiya Salima
kuwa a ranar tayi kukan da bata ta6ayin irin shi ba, domin tunda take bata ta6a jin labari me
matuƙar ban tausayi ba kamar wannan, tabbas Lubna abar tausayi ce tun tana jinjira rayuwar ta
ke cikin garari.
Al'ameen kuwa ji yake ina ma zai samu dama kuma ace kisa ba haram bane, da kuwa tabbas
babu abinda zai hanashi kashe Gaje domin ko a tarihi bai taba ganin marar imani kamar ta ba,
wani irin tausayi haɗi da ƙaunar Lubna ne yaji suna ƙara baibaye zuciyar shi,alƙawali ya ɗauka
na kulawa da Lubna tare da rayuwa da ita koda ace fuskarta ba zata dawo dai_dai ba, Baƙar
mace face kuma kai baka son baƙar mace."
Wani sashe na zuciyar shi ya tunatar dashi, wani tsoki yaja domin sai yanzu ya fuskanci baƙar
mace ba abar wulaƙantawa bace, baƙar mace tana ɗauke da wani kyau da baiwa ba kowa ke
fahimtar shi ba.
Alhaji Jadda kuwa jin yadda jinin jikinshi tayi rayuwa cikin ƙunci da kuma zallar baƙin cike bata
san miye gatan uwa ba, ji yayi zuciyar shi tayi baƙiƙirin a matuƙar fusace ya dubi Hajiya Murja.
"Kin cutar dani cutarwa mafi muni, Murja Jini na ɗiyar dana haifa ku ka salwantar saboda cikar
burin ku, Murja kije keda Allah bazan taba yafe maki ba har abada, kije na sake ki saki biyu."
Alhaji Jadda ya ƙarasa maganar cike da bacin rai
Kaurewa mutanen wurin suka yi da salati cike da muwar jim abinda mahaifin Hibba ya furta.
"Subhanallah! Malam Jadda bai kamata ace kayi saurin ɗaukar mataki cikin fushi ba, kowa
yasanan cutar dakai amma haƙuri shi ya kamata kayi komi da kaga ya samu bawa da sanin
Allah, Murja ta tafka babban kuskure wanda tunda nike bantaba jin in da Uwa ta ɗauki ɗiyar da
ta haifa jiM kaɗan bayan haihuwarta ta bada ta kyauta domin cikar wani burin su, babban
abinda ke bani mamaki shine yadda murja ta reni Aljana ba tare da ta sani ba, domin kowa ya
sani mutum bai iya haihuwar ɗan Aljani."
Cewar Malam ya me maida duban shi ga Murja da take darzar kukan nadamar sakin da mijin ta
yayi mata, yanzu da wani ido Lubna zata kalle ta, anya ta yima Lubna adalci kuwa?anya Lubna
zata kalleta a matsayin mahaifiya a gare ta.
Mahaifin Murja kuwa tsabar rikicewa miƙewa yayi tare da fara sabbatu domin tuni sakamakon
abinda ya aikata ya fara samunshi.
Hibba dake Kusa da Lubna ce ta fara magana kamar haka;
"Kada kayi mamakin jin na rayu a gidan Murja ba tare da an gane ni, tun bayan rabani da mijina
da suka yi na wanzu cikin baƙin ciki da zallar damuwar wannan cuta da akayi mana da rana
tsaka sun ɗauke mani mijina tare da sanya shi aikin da bai da yadda zai yi domin su haɗa shi
da babban Bokan da ko a ƙasar Indiya yayi fice, da rana tsaka suka raba soyayyar dake
tsakanin mata da miji tare da bari na ni ɗaya ina rayuwa tamkar bani da kowa, bincike na fara
domin gano waɗan da suka aikata mani wannan zalumci amma duk binciken da nayi ban garo
in da aka kai mani miji ba domin bokan yayi aikin da koda zani zagaye duniya ina neman shi
bazan taba ganin shi ba sai da na gano waɗan da suka aikata mani haka wato Murja da
mahaifinta, ina shirin baro indiya ne na samu labarin saukar su Murja ƙasar indiya, nayi farin ciki
domin ko ba komi aikin da nike burin aiwatarwa zai zo mani da sauƙi.
Shiri nayi na musamman tare da shammatar Bokan da yayi aikin naga bayan shi domin
alƙawari ne nayi tunda aka raba ni da farin cikina nima sai na raba kowa da farin cikin shi, kai
tsaye hotel ɗin da su Murja suka sauka na nufa cike da farin ciki na ɗaukar fansar da zanyi a
kanta, cikin ƙanƙanin lokaci nayi nasarar shiga jikin Murja tare da burin hallaka abinda ta haifa
ni kuma in maye gurbin shi, ranar da Murja ta tashi da naƙuda a ranar na ha shaƙe wuyan
abinda ta haifa tun kafin ya iso duniya, na shammaci malam asibiti tare da maye Gurbin ɗiyar
da murja ta haifa da ni, tun ranar nayi ma Murja illa domin na lalata mahaifarta ta yadda har
abada ba zata sake haihuwa ba sai dai taga haihuwa wurin wasu, ganin yadda Murja ke masifar
son abinda ta haifa nan naji lallai na samu hanyar da zani azabtar da rayuwar ta kamar yadda
suka cutar da tawa rayuwar, na ɗauki lokaci mai tsayi ina cutar da Murja tare da bata tsoro
domin nasan kota sanar da mahaifina bazai yarda ba, na kashe mutane da dama domin duk
wanda naga yana ƙoƙarin tona mani asiri kauda shi nike, kai ne malami na farko da ya katse
mani aiki ba tare da na ɗauki wani mataki ba, ka dakatar dani daga kashe Murja da nike niyyar
yi domin badan kazo da wuri ba da tuni Murja ta baƙunci lahira."
Hibba ta ƙarasa maganar tare da jifar Murja da wani kallo me wuyar fassaruwa.
Malam Saif ne ya fara magana.
"Duk da an cutar dake amma kema kin cutar da waɗan da basu ji basu gani ba, Murja ita ce
wadda tayi maki laifi shin ina za kije da Haƙƙin Alhaji Jadda da bai ji ba bai gani ba amma kina
kashe mashi ɗiya, in Murja tayi maku laifin Shin miye laifi Jadda da kuma mutanen da kika riƙa
karkashewa."? Cewar Malam Saif cike da jimamin wannan lamari.
"Ko mi ya faru Murja da Mahaifin ta sune sanadi, bil'adama basu da tausayi suna da mugun hali
yate da shiga gonar da ba tasu ba, ko yanzu da miji na ya bayyana ban fidda rai da sai naga
bayan Murja."
Murmushi Uwar Garke tayi domin tasan wace ce Gul hatsabibiyar Aljana da ta zarta mijin ta
hatsabibanci.
Aljanin jikin Lubna ne ya fara magana.
"Koda baku buƙata ba zani bar Jikin Lubna amma dole ne ina fita jikin ta Mamman zai haukace
ba za'a jima ba zai mutu domin wannan shine sharaɗin da aka gindaya mashi kafin biyan
buƙatar shi."
Aljani Gullam ya faɗa.
Wata zabura Hajiya Murja tayi jin abinda Aljanin ya faɗa
"Ni Murja na cuci kai na, na cutar da Mijina da kuma ɗiyata duk dan saboda cikar wani buri
namu na duniya."
Murja ta ƙarasa maganar tare da fashewa da kuka.
Babu wanda yabi takan Murja domin kowa yasan abinda suka shuka ne zasu girba.
Malam Saif dubar Aljanin Lubna yayi.
"Ka cutar da jinjirar da bata ji ba bata gani ba, kuma bayan haka ka nakasa mata fuska ta koma
rabi ta na miji shin fuskar ta da ka lalata zata iya dawowa dai_dai."
Cewar Malam Saif.
"Tabbas Fuskarta zata dawo dai_dai domin nayi haka ne bada son rai na ba a yadda akayi
yarjejeniya dani Lubna a matsayin mallaki na take, Malam kai Mutum ne me matuƙar adalci dan
haka zani fita daga jikin baiwar Allah nan ba tare dana cutar da ita ba jikin ta zai dawo tamkar
yadda na ko wace mace yake, sannan kuma nida mata ta zamu amshi addinin ku."
"Allahu Akhbar!"
Mutanen cikin falon suka yi kabbara a tare.
"Na matuƙar jin dadin wannan al'amari Godiya ta tabbata ga Ubangijin mu me rayawa da kuma
kashewa Haƙiƙa Allah gafurun rahimun ne ku musulumta da kyakkyawar niyya Ubangiji me
gafara ne zai gafarta maku dukkan wasu zunuban da kuka aikata madamar kuka musulumta da
niyyar ba zaku sake aikata abinda kuka aikata a baya ba, kuyi tuba ta haƙiƙa."
"Malam ni na aikata kisa da dama shin Ubangijin ku zai gafarta mani."?
Hibba ta faɗa.
"Ubangiji Me gafara ne madamar kika yi taubatunnasuha Allah zai yafe maki."
Uwar Garke ce ta fara magana ita ma.
"Malam a baya nima ina kallon musulmai ne da baƙin fentin da su Alhaji Mamman suka shafa
masu, amma a yanzu na fahimci a cikin ko wace al'umma akwai mutanen banza da kuma na
kirki, ina so in shiga addininku domin ya jima yana burgeni."
Murna farin ciki sune suka saka Malam Saif hawayen farin ciki, domin bai manta hadisin
Manzon Allah da yake cewa wa mutum ɗaya ya musulumta ta dalilinka ya fi alkhairi da abaka
jayen raƙuma.
A tare ya laƙana masu kalmar shahada suka me me ta, suna ya buƙaci kowanen su daya zaba
inda Hibba ta zabi Aisha mijin ta kuma ya zabi musa, uwar garke kuwa shuru tayi domin ita har
ga Allah tana son sunan ta.
"Shin malama musulumce suna na za'a iya ci gaba da kirana dashi ba tare da an sauya mani
ba."?
Murmushi Malam Saif yayi.
"Eh to amma mafi aa la ki zabi wani sunan duk da dai sunanki bai da aibu amma mu in kakaji
ance Uwar garke ana nufin kodai kana da wani garken dabbobi to babbar cikin su ita ake kira
uwar Garke."
Malam Saif ya faɗa.
"Na za6i LUBNA domin ina ƙaunar sunan kamar yadda nike ƙaunar me sunan."
Babu musu nan aka laƙana mata Lubna.
Aisha da Musa kuwa nasiha malam Saif yayi masu dasu nemi Malami a cikin Aljannu ƴan
uwansu su nemi ilimi a wurin shi, haka suka yi godiya tare da neman gafata wurin Alhaji Jadda
yafe masu yayi nan suka bace daga wurin.
Lubna kuwa Wani bacci ne yayi awon gaba da ita.
A yadda Malam Sule keji yau babu wanda ya kai shi murna da farin cikin samun lafiya da
Lubnar shi tayi.
Ƙofar falon ce aka banko da ƙarfi tamkar za'a karya ta, duk mutanen dake cikin falon duban su
ne ya koma ga masu ƙoƙarin shigowa.
Mahaifan Leemcy ne rirriƙe da Leemcy da kallo ɗaya zaka yi mata ka tabbatar bata cikin
gayyacin ta, Dariyar gefen baki Uwar Garke tay domin tasan yau asirin abinda suke boyewa zai
tonu....
*MEEN@RT...✍*[9/2, 12:01 PM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*PAGE 5️⃣2️⃣__5️⃣3️⃣*
...Cike da mamaki suke kallon Mahaifan Leemcy da ke ƙoƙarin kwantar da ita bisa ɗaya daga
cikin kujerun falon, ganin yadda ido ya dawo kansu yasa Mahaifiyar Leemcy fashewa da kuka.
"Dan Allah ku ceci rayuwar ɗiya ta, yau kimanin kwanaki biyu kenan da shigarta wannan hali
duk wani magani da zamu yi mata a banza domin yadda take ko motsi bata yi."
Mahaifiyar Leemcy ta ƙarasa maganar ta mai share hawayen fuskarta.
Hajiya Salima kallon su tayi cike da matuƙar mamaki domin ita sam tama manta da cewa
Al'ameen ɗinta na da wata mata bayan Lubna, to mi ya samu Leemcy ta dawo haka tamkar
gawa."?
Al'ameen kuwa tsabar takaicin ganin Leemcy yake ji, kallo ɗaya yayi mata yaji wata iriyar
tsanarta ta ɗarsu a zuciyar shi, to mi ma ya kai shi ya auri Leemcy yarinyar da ta gama zubar da
mutumcin ta a kwalta."?
Ya hau tambayar kanshi.
Malam Saif kuwa Kallon ta yayi cike da mamakin domin da gani kasan Aljannu ne suka bugeta.
"Mi ye musammabin abinda ya faru da ɗiyar ku har ta samu kanta cikin wannan halin."?
Malam Saif ya jefa ma Mahaifin Leemcy tambayar.
"Ranar wanka dai ba'a 6oyon cibi, ka haifi Ɗa amma baka haifi halinshi ba, tun bayan auren
Halimatu bamu sake sanin halin da take ciki ba domin muna ganin yanzu kaf nauyin ta yana ga
mijin ta, mun ɗauka har cikin ranmu cewa Aure ya kimtsa Halimatu ashe abun ba haka yake ba,
sam bata bar mugayen halayen da take yi ba, da yammacin marecen jiya ne aka kiramu da
Number Halimatu cewa muzo wani babban hotel na garin nan ɗiyar mu na cikin wani hali, a
gigice muka kwasa nida mahaifiyarta muka nufi Hotel ɗin, a yanayin da muka iske Halima yayi
matuƙar muni domin batasan wanda ke kanta ba mimmiƙe kamar Gawa muka iske ta, tambayar
ma'aikatan wurin muke me ya same ta yaushe tazo hotel ɗin, nan suke sanar damu ita da wani
sauratin ta ne suka kama ɗakin a ƙalla sunyi kimanin mako guda a Hotel ɗin, yau da safe ne
wanda ya kama ɗakin yaje ya biya mu kuɗin zaman da yayi a ɗakin abun mamaki muna zuwa
ɗakin sai muka iske wannan baiwar Allah tamkar gawa bata san wanda ke kanta ba, faɗin
tashin hankalin da muka shiga a wannan lokacin 6ata lokaci ne, Mahaifiyar ta kuka ta fashe
dashi domin tasan wannan na daga cikin abinda take gudu ma shagwa6a Halima da nayi, cike
da takaicin cin amanar aure da Halima tayi muka kwasheta muka nufi asibiti amma a banza Ƙin
amsarta suka yi domin sun lura ba ciwon asibiti bane, duk wani malami da muka kira a banza
domin kuwa babu abinda ya sauya, munyi yun ƙurin sanar da Al'ameen halin da ake ciki amma
muna tsoron irin hukuncin da zai ɗauka na jin matar shi na tarayya da wani a can hotel, munje
gidan Al'ameen bamu same shi ba shine muka yanke shawarar kawo ta nan gidan domin muna
da tabbacin Al'ameen na nan." Mahaifin Leemcy ya ƙarasa maganar cike da jimamin wannan al'amari.
Shuru kake ji falon yayi domin wannan al'amari ya zama ruwan dare mace ta riƙa cin amanar
auren ta saboda rashin tsoron Allah.
Cike da zallar mamakin hali irin na Leemcy Hajiya Salima ke kallon ta "kenan shi yasa da ta
kirata ta sanar da ita halin da Al'ameen ke ciki ko zuwa bata yi ba, ashe tana can tana sheƙe
ayar ta, Ubangiji ka ƙara shirya mana zuri'a."
Hajiya Salima ta ƙarasa maganar zucin.
Al'ameen Kuwa wani malolon baƙin ciki ne ya tokare