Showing 36001 words to 39000 words out of 72825 words
faruwa a ɗakin Lubna, babu neman izini haka Leemcy ta afka cikin ɗakin, abunda taga
Lubna nayi ya sa ta tsorata tayo baya zata fice a ɗakin, sai dai kafin ta kai ga fita ƙofar ce ta
rufe kanta ji kake garam!....
*MEEN@RT...✍*
[8/9, 3:53 PM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*PAGE 2️⃣8️⃣__2️⃣9️⃣*
...Hajiya Murja da tayi mutuwar tsaye kasa motsi tayi domin tasan yau tana cikin wani mugun
yanayi, sake kafe murjar dake cikin ɗakin tayi tare da nuna ta da yatsa.
Tuntsurewa da dariya jabun Murja tayi tare da mika hannunta Luuuw yaje ya fizgo ainahin Murja
ta gaskitaya cikin ɗakin tare da dire ta a gaban jabun murja.
"Kina mamaki yadda na koma sak irin ki ko? To wannan kaɗan daga cikin aikina ne, batun yau
ba nasha gaya maki keda nutsuwar ruhi har abada sai kin za6i ki mutu a maimakon halin da
kike ciki."
Jabun Murja ta ƙarasa maganar tare da kife Murja ta ainahi da wani wawan mari.
Zafin marin sai da ya haddasa mata katantanwa ta kife ƙasa, Jabun Hajiya Murja ce ta sanya
hannu ta shaƙe Murja ta ainahi ta ɗage ta sama ƙafafu na harbe_harbe.
Tsabar azaba Hajiya Murja ta ainahi Sumewa tayi, jabun Murja kuwa rikiɗewa tayi tare da
komawa sak Hibba.
Tintsirewa da dariya tayi tare da kallon mahaifiyar tata dake kwance a sume, "wannan duk
somin tabi ne kika fara gani muje zuwa in dai nice."
Hibba ta ƙarasa maganar tare da bacewa 6at.
Sanyin ruwan da aka zuba mata ne yasa ta miƙewa a rikice tana dube_dube ganin Abban
Hibba kusa da ita yasa jero mata sannu domin a yanayin daya isketa ya tabbatar ba lafiya.
"Umman Hibba."
Mahaifin Hibba ya kira sunanta.
A hankali ta ɗago da fuskarta dake zubar da hawaye.
"Yau ina so muyi magana ta gaskiya, ki faɗa mani miye ainahin damuwar ki nayi maki alkawarin
nema maki magani aduk inda yake a fadin duniyar nan domin na lura kamar matsalar ki naso
ta fara tabo kwalwar ki."
Abban Hibba ya ƙarasa maganar tare da kafe ta da ido.
"Mi kake so in ce maka? Ya kake so inyi da rayuwata, kana ɗauka ta a matsayin maƙaryaciya
mai yima ɗiyar ka ƙage, ka kasa fahimtar irin azabar da nike sha a cikin gidan nan, irin azabar
da Hibba ke gallaza mani a gidan nan na fara tunanin anya Hibba mutum ce domim tunda tazo
duniya har yau cikin cin azabar ta nike."
"Ya isheki!."
Mahaifin Hibba ya kwatsa mata tsawa.
"Shin Murja sau nawa nike maki gargadi akan canfa mani ɗiya da kike yi, to wannan ya zama
na ƙarshe in ba haka ma Murja zani ɗauki mummunan mataki a kanki."
Abban Hibba ya ƙarasa maganar a matuƙar fusace.
"Kayi duk abinda zakayi wallahi na gaji da abinda kake mani a cikin gidan nan, kasani cewa
nima uwace kuma ni na haifi Hibba bani taba yi mata ƙage ko kuma sharri, amma tunda haka
kace Ubangiji yasan ya ta juyo kanka ta riƙa azabtar da ruhinka kamar yadda take azabtar da
nawa." Hajiya murja ta karasa maganar cikin zallar bacin rai tayi daki da gudu tana mai fashewa da
kuka.
Galala! Ya saki baki yana kallon Murja da tunda take ko cacar bako bata iya yi dashi amma yau
ita ce ke gaya ma shi maganganu haka, anya bazai yarda da maganar Murja ba kuwa."
Wata zuciyar ce tayi saurin kwabar shi.
"Ɗiyar ka mutum ce kada ka sake wasu camfe_canfen Hausawa susa ka fara zargin yar lelen
ka.
Watsar da zancen yayi tare da nufar ɗakin Hibba domin tunda ya dawo bai haɗa ido da ita ba.
Kofar ya tura tare da kutsakai cikin ɗakin amma wayam babu Hibba, Toilet ya tura nan ma
wayam, mamaki yahau yi ina Hibba zata je har haka basu sani ba? Maganar shi ce ta maƙale
sakamakon hango hibba da yayi kwance bisa gadon ta tamai ƙure da ido, wata firgita da kuma
rikicewa yayi ganin ai yanzu ya bincike ɗakin amma ba Hibba, to ta ina ta shigo? tsabar
mamakin da yake ne ya hanashi magana.
"Ni fa Abba kana shiga gona ta da yawa, yanzu daka iske ni a yana yin rikiɗa da kwanan ka sun
ƙare."
Cewar hibba cikin tsawa_tsawa.
"Kinci gidanku Hibba bani son sakarci daga ina kike."
Cewar Abbanta.
"Daga sama nike ko akwai abinda Zanyi maka ne."?
"Daga sama kuma Hibba."?
Abban ta ya tambaya.
"Bani son tambayoyi , kaga dai bani shiga gonarka a gidan nan to wallahi kada kayi kuskuren
shiga gonata bani son tambayoyi, ina ɗaga maka ne a gidan nan saboda babu hannunta ga
abinda aka aikata mani tun kafin in zo duniya."
Ta karasa maganar tare da juyama Abban nata baya.
Ganin waɗan nan maganganu da take ma shi sam ya kasa gane inda suka dosa fitowa yayi
daga ɗakin jiki a sanyaye.
"Mi Hibba ke Nufi da batun babu hannuna acikinn abinda akayi mata, to mi aka yima Hibba da
ta kasa yafewa."
Nan fa zuciyar shi ta shiga yi mashi saƙe_saƙen abubuwa da dama.
Watsar da maganar yayi tare da kama aikin dake gabanshi wato na rarrashin Hajiya Murja
domin yasan yau yakai maƙura wurin bata mata rai.
Da kyar ya shawo kanta tare da alƙawarin ya dena mata magana makamanciyar wannan.
Yau Abban Hibba ne maganar Hibba ta tsaya mawa a zuciya harta hana shi bacci sai juyi yake ,
shawara ya yanke kawai yaje ɗakin Hibba yaga mi take 6oyewa.
Cikin sanɗa yake takawa har ya kusa shiga ɗakin sai wata zuciya tace kada ya shiga, amma irin
zakuwar da yayi na ganin mi yar lelen tashi ke boyewa, cikin sa'a yana tura ƙofar yaji ta buɗe
kanta.
Ida shigewa kawai yayi, caraf idanun shi suka sauka akan abinda ya sanya shi sakin wani
guntun fitsari a firgice yayi baya zai gudu,amma kafin ya kai ga aikata haka ji yayi an fizgoshi an
watsa cikin ɗakin, ƙofar ta rufe kanta da ƙarfi...
_______________________________
...Rikewa Leemcy tayi tare da nufar ƙofar tana bugu tare da ƙoƙarin buɗe ta amma sam ta kasa
bude ta.
Lubna kuwa wani Kurnani kawai take ta Na harbe_harbe tana ƙoƙarin miƙewa tsaye, tamkar
yunwataccen zaki haka Lubna tayo kan Leemcy tare da kwaso ƙafafunta ta shiga buga ta da
ƙasa, ihu Leemcy take domin ko azabar da Uwar Aljanu ta bata bata taba basu irin wannan ba,
jefata tayi jikin bango ji kake ƙum!
Wani wahalallen ihu ta saki tana ƙoƙarin miƙewa ta gudu amma kafin ta kai ga aikata haka
Lubna ta shaƙeta tare da kaimata yakushi da ɗayan hannun, tsabar azaba Leemcy idanunta
kakkafewa suka yi ta sume, sakin ta Lubna tayi tare da nufar ƙofa tana wami gurnani tare da
ficewa a guje.
Turus! Lubna ta tsaya bata kaiga ficewa ba sakamakon Uwar Garke data gani zaune cikin falon.
Tamkar guguwa haka Uwar Garke ta bayya gaban Lubna.
"Hatsabibi mai matuƙar haɗari, a tunaninka zani taba bari ka gudu da Lubna ne."
Cewar Uwar Garke tana mai watsa ma shi mugun kallo.
Wata mahaukaciyar dariya mai kama da saukar aradu Lubna ta 6arke da ita, lokaci ɗaya kuma
ta turbune fuska.
"Haƙiƙa Kina shiga sabgar da ba taki ba, shin kin manta waye ni ko kin manta zalincin da akayi
mani har na dawwama jikin Lubna to ki sani yau zani gudu da Lubna a gaban idonki kuma
kikayi kuskuren hanani nayi maki alƙawarin shayar dake mamaki."
Hibba ta faɗa a cikin Muryar maza.
Kyalkyacewa da dariya Uwar Garke tayi har tana faduwa kasa tana mulmula tamkar kwallo kafin
ta miƙe tare da Nuna Hibba da yatsa.
"Ruwa ba sa'ar kwando bane haka ko kura ta lalace ta fi ƙarfin karunuka su kawo mata raini,
batun yau ba ka sanni nasan ka, a baya ma Ni ce nayi sake ka shiga jikin yarinyar nan dan
haka yanzu ƙaryar ka tasha ƙarya bazaka sake taku ɗaya ba da gangar jikin Lubna."
Cewar Uwar Garke.
"Ni ruwa ne in na taho babu mai tare mani hanka koda ace ka tare mani hanya tabbas zani bi ta
kanka in wuce, saboda haka yanzu a gaban idonki zan tafi da Lubna tafiya ta har abada babu
bil'adam ɗin da zai sake ganinta idan kina gani ke hatsabibiya ce ki hanani barin gidan nan da
Lubna."
Uwar Garke kuwa ganin da Gaske Zai iya guduwa da Lubna ya sa ta saurin shammatar shi ta
danƙi kanshi tare da sanya mashi wani farin hayaƙi, kururuwa Lubna ta hauyi sannan ta sulale
ƙasa.
Daf da kanta Uwar Garke ta matso tare da kallon Lubna dake kwance cikin halin suma.
"Rayuwar ki ta fara ne da ƙalubale tun daga ranar da kika shigo duniya a yanzu ke ba mallakar
mutum bace ke mallakin hatsabibin Aljani ce, amma nayi maki alƙawari zani taimakeki duk da
addininmu bai kasance ɗaya ba ni mai bada rayuwata ce domin taki, nayi maki alƙawari komi ya
kusa zuwa ƙarshe." Tana ƙarasa maganar ta sungumi Lubna ta kwantar da ita bisa gadon ta, Uwar Garke ɗakin ta
kalla ganin yadda Lubma ta farfasa glass nuni Uwar Garke tayi da hannun ta sai ga komi yana
komawa yadda yake hatta waɗan da suka farfashe sai gasu suna haɗewa su koma yadda suke.
Sai yanzu Uwar Garke ta lura da Leemcy dake gefen gado a yashe, kecewa da dariya tayi
domin tasan koba komi yau Leemcy ta daku a hannun Lubna.
Wani wawan Mari Uwar Garke ta sauke ma Leemcy dake kwance, a gigice Leemcy ta miƙe
tana dube_dube domin a zaton ta Lubna ce ke sake jibgar ta.
Jariri ta gani gefen ta ya wangale baki yana mata dariya, wata iriyar zabura Leemcy tayi tare da
miƙewa zata gudu, caraf taji Jinjirin ya riƙe mata kafa.
"Uwata ina zaki baki ɗauki ɗanki ba."
Jaririn ya faɗa yana 6angara dariya.
"Na shiga tara ni Halimatu ina na samo jariri da ganinshi ɗan Aljanune."
Ƙoƙarin yakice jinjirin take amma ta kasa.
Fashewa tayi da kuka ganin wannan azaba biyu da aka haɗe mata lokaci ɗaya ga zafin dukan
da ta sha hannun Lubna ga kuma wannan nataccen jinjiri dake kiranta Uwata.
"Dan uwar ka dan Ubanka ka sake ni ni duk lalacewa ta bantaba yadda na haihu ba , yau ni ina
ganin lalataccen Aljani."
Falau_falau aka shiga ɗauke Leemcy da mari dama da haggu.
Wata mahaukaciyar tsawa aka daka mata, a zarane ta juyo amma wayam bata ga kowa ba.
"Zaki ɗauke ni ko sai an saba maki kamanni."
Jinjirin ya faɗa.
A gigice Leemcy ta rarumi yaron ta buga da bango, memakon jinjirin ya tarwatse koya karairaye
sai ma gani Leemcy tayi ya miƙe da ƙafafunshi tare da zabgowa da gudu zuwa inda take, a
firgice ta bar dakin aguje jinjirin na take mata baya.
Ƙofar ɗakinta ta mai do ta rufe da ƙarfi tare da nufar gado ta faɗa, halbar da ita taji anji tayo
ƙasa babu shiri.
Uwar Garke ce ta miƙe daga saman gadon tana mai yin miƙa, mutuwar tsaye Leemcy tayi
domin tasan yau jikinta sai ya dare saboda dukan da zata sha.
"Eyye! Uwar Gantali daga ina kike kika tafi kika bar ɗaki tun ɗazu."
Uwar Garke ta faɗa tana mai bayyana a gaban Leemcy.
"Uwa mai daraja tuba nike daga ɗakin yar uwata Lubna nike."
Leemcy ta faɗa jiki na kyarma.
Kecewa da dariya Uwar Garke tayi.
"Ƙarya kike ce mani zakiyi kinje ganij kwaf, daga yau ko ƙofar ɗakinta kika sake shiga sai kinji a
jikin ki, yanzu ma ba kyaleki zanyi ba, kin ta6a yima ƙadangare tawai."?
Uwar Garke ta jefama Leemcy tambayar.
"Yau ni na lalace, wallahi ko a tatsuniya bantaba ganin wanda yayima ƙadangare tawaii ba."
Leemcy ta fada hawaye nabin fuskar ta.
"Yau kuwa zaki ga yadda ake ma shi, maza ɗauki wancan Ƙadangare kiyi mashi tawaii in ba
haka ba zaki yima zaki brush yanzu."
Leemcy jin wannan jawabi na Uwar Garke yasa ta kai hannu tare da ɗaukar danƙareren
Jankwataki ta fara mashi tawaii.
Ihu take tana rufe idon ta domin Ƙadangaren lafta mata cizo yake a hannu gashi kuma Uwar
Garke tayi mata kashedin indai ta bari Ƙadangaren ya faɗi jikinta ne zai gaya mata.
Leemcy taga rayuwa, domin tasha cizo ba kaɗan ba ga azabar Uwar Garke dake gefe.
Sai gaf da magriba Uwar Garke tabar ɗakin Leemcy.
Fashewa da kuka Leemcy tayi.
"Allah ya tsine maki Lubna ashe ke dangin Aljanu ce , yau anyi mani bugun da tunda nike babu
wanda ya taba yiman irin shi, wayyo baya na zai karye.
Shigowar Al'ameen gidan ce ta sanya Leemcy haɗiye kukan ta domin Uwar Garke tayi mata
worning in ta sake wani ya gane halin da take ciki sai jikin ta ya gaya mata.
"Lafiya Leemcy nike jiyo kukan ki tun daga falo."
Cewar Al'ameen dake gefe kaɗan da ita.
"Ba kuka bane dariya ce ni haka nike."
Cewar Leemcy dake danne kwallan dake ƙoƙarin kufce mata.
Galala Ya saki baki yana kallonta.
"Ni kike gayama baƙar magana, in jiyo kukan ki kice kuma wai dariya kike."
"Dan Allah ka rabu dani bani son jaraba."
Leemcy ta karasa maganar tare da ɗan gyasa ƙafar ta kamar gurguwa zata shiga Toilet, ta6arr!
Leemcy ta gurɗe ƙafa ta faɗi.
Mi Al'ameen zai yi ba dariya ba,Leemcy kuwa a fusace ta rarrafa ta shige Toilet ɗin.
Al'ameen samun kanshi yayi dason ganin halin da Lubna ke ciki domin in basu tare yafi jin wani
abu a kanta amma muddun ya ganta ji yake kamar ya kashe ta, miƙewa yayi tare da nufar ɗakin
Lubna.
Buɗe yaga ƙofar dan haka afkawa yayi ɗakin.
Wani ƙamshi wanda bai ta6a shaƙar irin shi bane ya daki hancin shi ba shiri ya karasa shigewa
cikin ɗakin.
( Niko nace gyaran ɗakin Aljanu daban dana bil'adama, duk mai buƙatar irin wagga gyaran
ɗaki tazo muyi ciniki Uwar Garke kullum a online take tana jira)
Ƙare mata kallo yake tsaf sai yanzu ya fahimci wani abu, Lubna tafi Leemcy jiki mai kyau ga
kuma diri mai ɗaukar hankali, wani tsoki yaja daya tuna Lubna baƙar fata ce.
Zama yayi gefen Gadon tare da kafe Lubna da kallo, ji yati babu abinda yake da buƙatar gani
kamar Rabin fuskar Lubna dake Lullube kullu yau'mun, a hankali ya fara janye gyalen da ta rufe
fuskar ta dashi, cikin bacci Lubna taga wannan namijin daya saba zuwar mata yana gyalgyata
dariya tare da faɗar. "Muddun kika bari Al'ameen yaga fuskar nan bazai ƙara ko minti daya a raye ba."
A firgice ta farka tare da fizge gyalenta tana me ƙara boye fuskar ta.
Wani kallo ya watsa mata.
"Kee! Ni tsaran wasan ki ne, wannan munafukar fuskar da kike 6oyewa ita nike son gani yau."
A firgice ta kalle shi.
"ba zani bari ka mutu ba, in kaga fuskata mutuwa zaka yi."
Ta ƙarasa maganar tare da ƙoƙarin barin ɗakin.
A matuƙar fusace Al'ameen ya miƙe tare da fizgo....
Shin mi Al'ameen ya fizgo?
Zai mutu ko kuma Lubna ce zata mutu?
Muje zuwa♀️♀️♀️
*MEEN@T...✍*
[8/13, 6:34 PM] Meenat A Yandoma: *RUWA BIYU!!*
_Free book_
Labari/Rubutawa
Meenat A yandoma
```MANAZARTA WRITERS ASSOCATION``` ️
*M.W.A*
*Kungiya d'aya tamkar da dubu, Masu Nazari da aiki da ilimi, burin 'kungiyar a ko yaushe shine
ta fad'akar ta Kuma Nishad'antar da Masoyan ta.*
https://www.facebook.com/107980080946102?referrer=whatsa
____________________________
*PAGE 3️⃣0️⃣__3️⃣1️⃣*
....Buguwar da Mahaifin Hibba yayi ce ta haddasa mashi dafe kanshi dake ƙoƙarin tarwatsewa.
Dishi_dishi idanunshi suka fara gani, da kyar ya miƙe yana laluben hanyar fita domin tseratar da
rayuwar shi.
"Kada ma kayi ƙoƙarin guduwa Abba, yau abinda ka jima kana ƙaryatawa gashi a zahiri zaka
gane ma idonka, abinda kake kira camfi yau zaka gane zahiri ne ba camfi ba ne."
Cewar Hibba tana ƙoƙari shaƙar wuyan mahaifin nata.
Jikn shi ne ya fara kyarma lokaci ɗaya wani gumi ya shiga wanke mashi jiki.
"Hibba! Nasan bake bace canza mani Hibbata akayi dan Allah ki fiddo mani ɗiyata kada ki cutar
mani da Hibba."
Mahaifin Hibba ya ƙarasa maganar jiki na mazari.
Tuntsirewa tayi da mahaukaciyar dariya
"Kayi kuskuren shigowa ɗakina a dai_dai wannan lokacin zani raga maka ne saboda kai babu
hannunka a cikin cutar dani da akayi, amma duk da haka yau sai ka yaba ma aya zaƙin ta daga
yau ba zaka sake ƙaryatawa akwai aljani ba."
Hibba ta ƙarasa maganar tare da dage mahaifinta sama yana wutsilniya.
Ihu ya shiga zabgawa yana kururuwa ko Hajiya zata jishi ta kawo mashi ɗauki amma shuru
kake ji.
Sakin shi tayi ya faɗo ƙasa tim tumbinshi ya bugu da tyles ɗis dake cikin ɗakin.
"Na rantse da Allah daga yau bani sake ƙaryatawa akwai Aljani Hibba kiyi mani rai nifa
mahaifinki ne, wayyo tumbina."
Ya ƙarasa maganar tare da dafe cikin shi.
"Yi mani shuru! Daga yau in ka ƙara shiga harka ta sai jikinka ya gaya maka ba zaka ji da sauƙi
ba ka daina gani ka na matsayin mahaifina ba wuya in murɗe maka kai sai dai a