Showing 24001 words to 27000 words out of 46393 words
Chapter 9 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf
Ya kara matsowa gabana saura kadan ya hade space din da ke tsakanin mu. Ya ce, “What are you afraid of
(me ki ke tsoro)?”
Shiru na yi na kasa amsawa, ni kaina ban san me nake tsoron ba, kawai dai na san bai kamata ba mu
zauna daki daya ni da shi. Hatta wannan closeness din da ya assasa a tsakanin mu na san mun keta
hurumin Ubangiji.
Jin na yi shiru ban amsa ba ya kai hannu ya dafa kafaduna guda biyu, murya can kasa, ya ce, “Asma’u. I’m
your brother ba zan cutar da ke ba. Ina so ki sa a ran ki cewa, kina cikin amanata. Na dauko ki ne cikin
amana, kuma cikin amanar zan mayar da ke hannun Addar ki. Idan har kin amince da hakan ki bude ido ki
dube ni”.
Dole kowa Yaya Maccido ke wa magana da wannan muryar tasa ya yi masa abin da yake so. Wata irin
kasala muryar tasa ta saukar min, hadi da faman murza yatsu na da yake yi su suka taru suka birkita ni.
Ko’ina a jikina rawa yake yi, amma a hakan na yi kokarin na bude ido na dube shi don dai ya yarda na
amince ba zai cutar da ni din ba. Abin da na hango cikin idanun sa mai girma da zurfi ne da ya shallake
tunanin mu. Ai ba shiri na maida idon nawa na lumshe su, shi kuma da wata irin azama ya rungume ni
kam-kam a jikin shi. “Hasbunallahu wa ni’imal wakeel...”. Na furta da karfin da ya sa ba shiri Yaya ya sake ni. Sai na durkushe a
wurin na soma kuka. Kukan da ban san dalilin yin sa ba. Na dai san Yaya ya sa mun yi abin da bai dace ba,
ya keta alfarmar Ubangiji sabida sakacin sa da gangan. Ina ga mun kwana a daki daya? Ni gabadaya ma ya
canza min, kamar ba Maccidon da na sani ba, handsome, giant, mijin Lubabatu. Wannan ya koma Tahir
mai shekaru ashirin da biyar ba wanda ya ajiye ‘ya’ya biyu ba.
Ganin kukan ba zai kai ni ko’ina ba, don Yaya barin gabana ya yi ya shiga jona kettle zai dafa
(gahwah-Al-arabiyyah), bai kara bi ta kaina ba. Jakunkuna na guda biyu na jawo na durfafi kofa, gara in je
ko kofar dakin da Addah ke kwance ne in dinga kwana, amma ba da ni za a yi wannan katobarar ba.
Tunda dai na rike sunan asibitin magana ta kare.
Na murda kofa na sake murdawa, amma ko gezau! Ta ki buduwa. Ban san sanda ya isa ya murza mata
mukulli ya zare ba. A jikin kofar na sulale na zauna ina kuka. Kukan da na tabbatar in har da imani a
zuciyar sa dole ya tausaya wa halin da na ke ciki.
Ilai kuwa kukan nawa ya dame shi. Ya hana shi nutsuwa. Ya ce, “Asma’u ki yi min shiru. Ki bar ganin ina
lallaba ki. To me ki ke tunanin zan yi miki in mun kwana daki daya? Ko kuwa kina so ne ki ce min kin san
akwai wata mu’amala tsakanin mace da namiji wanda ni ban san shi ba?”
Kukana ya makale jin abin da ya ce, in ma ban sani ba ai yau ga shi ya nuna min akwai din.
Ya taso ya baro gahwah din da yake sha zuwa inda nake, har yanzu singlet dinsa ce fara kal a jikin shi da
dogon wandon kayan da ya cire. Hannu ya miko min ina daga zaune.
“Hold my hand and get up!". Ya fada da muryar da na kasa amincewa ta Yaya Maccido ce. Maccidon nan
Ma’abocin izza da kasaita a cikin kannen sa, wanda tsakani na da shi sai hange daga nesa.
Sai na kasa resisting wannan lallashin nasa. A hankali na sanya hannuna cikin nasa. Ya mikar da ni tsaye
ya ja ni zuwa three seater din da ya taso, muka zauna kusa da juna. Shayin gahwah din da ya hada a dan
kankanin kofin tangaran din Larabawa ya nufo baki na da shi. Juyar da kai na yi alamar ba zan sha ba. Ci
gaba ya yi da shan abin sa, sai da ya gama ya ce.
“Now, listen, mu yi magana ta fahimta irin ta Yaya da kanwar sa. Ki lissafo min duk abubuwan da ba kya
so a zaman mu, na yi miki alkawarin zan kiyaye. Don gaskiya aljihuna ya yi kasa sosai, ba ni da kudin da
zan kama miki wani dakin”.
Shiru na yi ina nazarin kalaman sa, babu alamun wasa a fuskar sa, ko da ma can shi ba ma’abocin wasan
ba ne. Sai dai na san ya fada ne kawai don ya ji dadin bakin sa, da kuma wani dalili nasa na daban amma
ba don bashi da kudin kama min daki ba. Amma da hankalin sa saboda Allah me ya sa zai yi haka? Me ya
sa ya san tun farko bai shiryawa tafiyar ba ya dauko ni? Ni ina duba ya kamata ne, ko da nake karama
ashe na fi shi hankali. Don dai ni ban taba jin irin wannan katobarar ba.
“Ke nake sauraro, ina so zan kwanta”.
“Kada ka kuma zuwa kusa da ni, kada ka kara taba ko farce na even by mistake”.
Ban san sanda na fadi hakan ba, na manta ko da wa nake magana, tsabar bacin rai yasa na manta
wanene Maccido.
Ga mamakina murmushi ya yi, ya ce,
“Su ke nan sharuddan naki?”
Kai na gyada masa. Na ce.
“Sauran matsalolin zan san yadda zan yi da kaya na. Ubangiji ya sani ba ni da laifi”.
“Consider it done. Don haka kwantar da hankalin ki. I will not dare touch you again. Yanzu mu yi shirin
kwanciya kaina ya fara ciwo, kin sa ni magana da yawa”.
To amma kwanciyar Yaya za'a yi ta? Gadon dakin guda daya ne. Karasawa na yi na dauki pillow daya na
jefa a kan three seater na kwanta, ko kayan jikina ban canza ba. Rana ta farko ke nan tunda na yi wayo da
na kwana ba da kayan barci ba. Ina kallon shi ta kasan ido na ya je closet ya canza kayan jikin shi zuwa
pajamas bayan ya rage wutar dakin ya bar dim light.
“Amma da kin koma gadon ko? Kin bar min nan din wuyan ki zai yi ciwo”.
Na dan bude ido na kalli saitin da yake ina auna yadda tsayin shi zai yi occupying three seater, ai kuwa sai
dai ya yi ciwon baya.
“Na ci kankanta, na bar maka”.
Murmushi ya yi mai sauti ya dauko quilt din gadon ya rufa mini. Sannan ya karasa gadon ya kwanta.
Da asubah shi ya tashe ni da alama shi har ya dauro alwalla, na je na dauro na zo na same shi bai tayar ba
yana jira na. Shi ya ja mu sallar muka yi jam’i cikin daki. Yana gaba na ina bayan sa bayan mun idar. Wata
irin nutsuwa da gamsuwa na ji a rai na irin wanda ban taba ji ba a rayuwata, a lokacin da na gabatar da
ibadah. Sai na daga hannuwa ina kwararo addu’a na nemawa Addah lafiya dauwamammiya, sannan na yi
wa kai na ta gama wa da duniya lafiya.
Bayan wannan ba ni da wani buri don ni a rayuwata ban taba hango wa kaina AURE ba, na san ina son
yara, amma na mutane, don ni kam ma bana lissafa kaina a sahun mata. Ni din ba kowa ba ce face
Asma’u ‘yar Addah, kanwar Nabeelah Maman Aasim, autar Nene Zainabu. Kamar akwai wani exception
tsakani na da sauran mata (ni din ban cika mace ba) watakila da na cika mace da wani da namiji ya taba
cewa yana sona, bakin jini na kam ya wuce misali. Yau da na kasance kusa da Maccido, cikin wani
kyakkyawan yanayi, sai zuciya ta ta karkace, ta zarme, ta soma son kwatanta ni da mata ‘yan uwana,
musamman wadanda ke gidan aure, ashe contentment din da suke samu ke nan in suna tare da mazajen
su?
Gari ya soma haske, ni da Yaya babu wanda ya motsa, muna nan zaune a inda muka yi sallah kowa da irin
tunanin da yake yi a zuciyarsa. Wani yanayi ne na nutsuwa da ban san yadda zan kwatantashi ba ban
kuma taba tsintar kaina a ciki ba. Bana so ko kuda ya gifta ta gabana don kada ya katse min bakin
abubuwan da nake ji a raina. Don kada Yaya ya tashi daga gabana, ji na yi tamkar ya zame min garkuwa
daga duk abin da zai iya cutar da ni.
Yaya ne ya fara tashi, sabida lokaci ya ja sosai. Toilet ya wuce kai tsaye. Wanka ya shiga, yayin da na soma
tattare kayan da suke watse a kasa, na maida dakin neat. Ya fito sanye da rigar tawul ta wanka ya daure
igiyar daga tsakiyar cikinsa. Kallo daya na yi masa ban kara marmarin maimaitawa ba domin kuwa kirjinsa
na hango wanda ke rufe luf! Cikin lallausar suma baka sidik. Shi ma dai me ya sa yake saka irin wadannan
kayan a gabana? Ai bai kamata ba. Ko da yake na dade da fahimtar shi bai san ya kamata ba. Tun da ya
farlanta mana zaman daki guda din, da sai ya dau kayan sa a hannu ya shiga toilet ya canza tunda ya ce
zaman namu tare ya zama dole.
Dan gajeren tsaki na yi hadi da zunburo baki, wanda ban san cewa ya shiga kunnen Yaya ba. Na juya na
ba shi baya ganin ya fiddo kaya zai saka.
“Are you pouting at me (ni ki ke zumburo wa baki)?”
Na yi saurin girgiza kai tare da cewa cikin karkarwar murya,
“Amma Yaya sai na ga zai fi dacewa ka dinga saka kaya a toilet”.
Ina jin sautin murmushin sa, ya ce, “gashi ni ban iya takura wa kaina ba, ko ba komai na san daga ni sai
kanwata a dakin”.
Kamar in ce masa, ai ni ba Nabeelah ba ce, sai na yi tunanin zai ja zancen zuwa wata ma’anar daban, don
haka na ja baki na na yi shiru.
Sai goma na safe muka gama breakfast, wanda aka shigo mana da shi daga hotel din. Yaya ya isa ga
madubin dogon yaro yana murza hula a kansa, sai da ya tabbatar ta zauna sosai, sannan ya dauki
turarukansa biyu yana fesawa (obsession da oud abyad) da ya saya a nan Jeddah. Ya gama ya juyo inda
nake na yi tagumi, domin haka kawai nake fama da yawan faduwar gaba da kasala.
“Zan je asibiti Asma’u, daga nan zan je wajen wani abokina a King Abdul-Aziz University, sai wajen azahar
zan dawo. Za su shigo miki da abincin rana”.
Na marairaice, “Yaya don Allah zan bika, in son sanin halin da Addah ke ciki”.
“Ko mun je ba za su bari mu ganta ba, ki yi hakuri ki yi zaman ki. Idan Nabeelah ta zo sai ku dinga zuwa
duk inda ku ke so tare.
Ba da son raina ba na hakura, na ce, “To ka sayo min KFC”.
“Ita kadai?”
“Eh”.
“To sai na dawo, take care”.
Wani irin dadi na ji a raina, ashe haka mata ke ji idan suka samu kulawa ko da ta fatar baki ce daga mazan
su?
Sai azahar din kuwa ya dawo, ya kawo min KFC mai zafi da Laban mai sanyi. Daga nan ya kara ficewa bai
dawo ba sai dare.
Yau ma irin kwanjiyar jiya muka yi, ina kan kujera yana tsakiyar gado, ina jin shi yana ta kiraye-kirayen
waya da daddare. Ya kira matarsa sun sha hira, amma bai zurfafa hirar ba, sannan ya sassauta kalaman
sa.
Duk da haka sai na samu kaina da matukar jin haushin Lubabatu, bayan a zahiri ita ya kamata ta ji haushi
na ina nan ina more mata miji, har da kwana daki daya da shi babu sidi ba sadada. Idan har ta san muna
taren ke nan, na fi kyautata zaton bai gaya mata da ni aka yi tafiyar ba ma, don lafiya-lafiya suke hirarsu.
Washegari ya ce min zai je cikin jami’a wajen Musbahu abokinsa, lakcara ne a can. Rokon sa na yi ta yi a
kan zan bi shi har dai ya yarda, amma ya ce sai na sa niqaab. Ina ta zumburar baki na sa niqab din muka
jera ni da Yaya muka fito.
Mai Ajrah ya shigar da mu har cikin King Abdul-Aziz University, daga nan muka taka zuwa ofis din abokin
nasa. Mai fara’a da shi, baki mai zubin Mallawa.
Ya ce da Yaya, “Maccido yau ba kai ne bakona ba, Madam ce, don haka ita zan fara yi wa barka da zuwa”.
Yaya ya ce, “Musbahu ka ki aure ko? Har mun tara yara kana nan a tuzurun ka”.
Murmushi ya yi, ya ce, “In za ka ba ni kanwar nan taka me zai hana in biya sadaki kafin ku koma Nigeria?”
(Na dage niqaab dina sama don in sha iska shi ne har Musbahu ya ga fuskata). Na juya na kalli Yaya sai na
ga duk annurin fuskar sa ya kau, kuma bai bi ta kan zancen Musbahu ba. Tun daga nan in muka hada ido
sai ya yi ta dalla min harara. A karshe ma hirar ta ki dadi, ya ce da Musbahu za mu koma, yana so ya shiga
asibiti.
Tunda muka hawo ajrah Yaya ya soma fada, fada yake yi tamkar ya kai hannun shi jiki na.
“Na ce ba za ki biyo ni ba ki ka kafe min kahon naci, ashe don ki zo ki tallata wa maza fuskar ki ne. In ba
haka ba me ye na cire niqaabin a gaban maza? Ko an ce da ke in kin yi hakuri har gida Allah ba zai kawo
miki mijin aure ba?”
Fadan yaya sai ya koma ba ni dariya, amma na san ko giyar wake na sha ban isa na yi ta ba a yadda yake
matukar fusacen nan. Kadan ya rage ya kai min mari. Saboda Allah ina ruwana da wani niqaabi ni ba
matar kowa ba, ba ‘yar takari ba? Na hadiye dariya ta ban yi ta ba, don na lura ba karamin fusata ya yi ba.
Yau ko ‘yar KFC din bai saya mana ba, tunda na bata masa rai. Ya rantse ya sake rantsewa ba zai kuma
zuwa ko'ina da ni ba, in dankare a dakin hotel.
A hankali cikin ‘yan kwanakin da muka yi tare nake ta fahimtar wane ne Attahir (Maccido)? Sanin da
tunda aka haife ni nake zuwa gidan su har rasuwar iyaye na da dawowata gidan su gabadaya ban taba yi
masa ba. Na lakance shi, wata irin lakanta da bana jin ko matar shi da ya kwashe shekaru biyar tare da ita
ta yi masa irin ta. Na san irin abubuwan amfanin sa kama daga suttura, turare, bath kit (kayan wanka)
kayan askinsa (shaving kit) na Arganavita. Na san duk irin abincin da ya fi so da abin shan sa, na san likes
and dislikes din sa. Na gane halayen sa ciki da ba. Na lakance shi karshen lakanta, ta yadda na tabbata
ranar komawar mu gida tabbas zan kasance cikin kewar sa.
A baya ina masa kallon wani mutum mai izza da girman kai, ina masa kallon mai wasu irin baudaddun
halaye da suka sha bamban da na mutane. A dan zaman nan namu cikin birnin Jeddah sai na gane Yaya
Attahir Maccido yana daga cikin kariman mutane; wato mutane ma’abota kirki da karamci ga duk wanda
zama ya hada su da shi na dan lokaci mai tsawo.
Babban abin da ke burge ni da Yayan namu shi ne; tsaftarsa, ba ya kwanciya sai ya yi wanka, haka in ya
fita ya dawo sai ya yi, in ya sa kaya sau daya ba ya maimaita su sai an wanke an goge. Bai cika sanya
kananan kaya ba sai in a gida zai zauna. Kusan kullum cikin shaddoji, voile da yaddidikan filtex masu
karshen tsada da aka yi wa dinki tazarce yake rayuwar sa. Dinkunan sa kullum simple, ba'a cika su da ado,
amma in ka duba links dinsu za ka samu masu daraja ne sosai.
Zan iya kwana in wuni ina fasalta muku wane ne Maccido? Don haka na bar wa mai karatu sauran, ya
gane cewa Attahir is classique, perfect, decent and genius. Ta yadda in na zauna sai in yi ta kintace da
hasashen Lubabatu wace irin sa’ar zuwa duniya ta yi?
Gobe ne Aunty Nabeelah za ta sauka a Jeddah, kuma a gobe ne za a bar mu mu ga Addah, don haka don
zumudi yau barci na ragagge ne. Yaya Maccido ko barcin sa ya shaka har da minshari.
Tun asubah bayan mun idar da sallah na fada wanka, ganin rawar jikin da nake yau sai ya shiga bata lokaci
yana yi min yanga yadda yake so, na ce mu fita tun bakwai sabida Nabeelah sha daya na safe za ta sauka.
Tunda akwai tazara tsakanin cikin gari da airport. Yaya Maccido ya ce, tabdi ai shi bacci ma zai koma,
sannan sai ya tashi zai yi wanka. Ya shige cikin quilt ya bar ni a zaune kamar na fashe da kuka.
Haka na daure na kyale shi na zauna ban da aikin duba agogo ba abinda nake yi. Karfe tara na kure karar
talabijin don dai ta tashe shi.
Ya tashi yana yamutsa fuska ya shige toilet. Nan ma sai da ya ci rabin awa ya fito ya shiga shiryawa
lakakai-lakakai. Na shige cikin duvet yadda nake yi duk lokacin da na fahimci zai canza kaya, tunda shi
hakan ba damuwar sa ba ne.
Ya dau turare yana fesawa na mike na rataya jaka ta na nufi kofa zan saka takalmi. Amma sai Yaya ya ce,
wai shi sai ya karya kumallo. Hawayen da ke makale tun dazu na bari suka zubo kawai.
Ya kama baki yana min dariya, wai Nabeelah ko uwata ce sai haka.
Ganin na ki zama na babbake a bakin kofa ina ta