Showing 18001 words to 21000 words out of 46393 words
Chapter 7 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf
da karfin ran ta. Kullum jarumta ta ke ta nuna cewa lafiyar ta kalau, amma a zahirin
gaskiya ba ta da lafiya.
Muhsin da ya zo weekend don yanzu ya tattara ya koma hostel ya takura mata kan ta je asibiti, ta dage ita
lafiyarta kalau, amma kuma kullum a kwance ta ke wuni a daki, ko falo ba ta iya fitowa. Al-Qasim ma ya yi
ya yi a je asibiti, amma Addah ta ki.
Ciwo sosai ya ci karfin Addah wanda aka rasa gane kansa da gindin sa, ya zamana ko sallah ba ta iya yi sai
a zaune. Al-Qasim ne ya dauko likita mace ya kawo har gida don ta duba ta.
Likitar ta dudduba ta, sannan ta dauki jinin ta ta ce akwai gwaje-gwajen da za ta yi a asibiti kafin ta san
hakikanin me ke damunta. Ta takurawa Addah aka wuce da ita asibiti don cikin ta da za a yi wa scanning
sabida kukan ciwon ciki da ta soma yi.
Kafin result din gwaje-gwajen Addah ya fito Addah ta daina shaida wanda ke kanta. Daga ni har Muhsin
da Al-Qasim mun kasance cikin madaukakin tashin hankali. Hankalin mu bai kara tashi ba sai da
sakamakon gwajin ya fito inda suka sanar da mu Addah na fama da ciwon koda ne. Akwai bukatar a yi
gaggawar yi mata aiki a cire stones daga cikin kodar ta.
https://www.arewabooks.com/book?id=6329c8029b3e7782f077921d
Na kwantar da kaina jikin gadon da Adda ke kwance ba ta san wanda ke kanta ba. Shesshekar kuka nake
yi a hankali cikin rauni da karaya nake fadin, “Adda, Allah ya tashi kafadun ki, Allah ya ba ki lafiya
Addah… Ba ni da kowa sai Allah da ya halicce ni, sai ke…”
Kuka nake yi mai motsa zuciyar duk wani mai saurare da muryar da ke nuna maraici na. Alamun zaman
mutum na ji a kujerar da ke kusa da tawa, hanci na ya surnano min wani lallausar kamshi na turaren
obsession (by CK).
Hannu ya kai a hankali ya kama hannun Addah wanda babu karin ruwa a jiki. A hankali na dago ina bin
shi da kallo, kallon da a sannu yake sauya kala yana komawa na kiyayya… na tsane shi, na tsane shi don
na san duk matsalolin da Addah ke fama da su na hawan jini da yawan bacin rai shi ne sila. He is very
selfish… kansa kawai ya sani da shaidaniyar matar sa.
Ko kusa bai zame wa Addah sanyin idaniya ba, haihuwar sa ba ta kare ta da komai ba sai tulin bacin rai.
Ta dauki soyayyar sa da damuwa da lamarin sa ta aza a ranta har ya yi mata illah. Rabon da mu ganshi
yau watanni bakwai ke nan, sai yanzu da ya ji an ce Addar na gargarar mutuwa shi ne ya wani kwaso jiki
ya zo. To me ya zo ya yi mata? Ko ya zo ne don bakin cikin sa ya karasar da ita zuwa kushewar ta?
Ban san sanda na saki wani mugun tsaki ba. Na ji na tsani Yaya Maccido sakamakon treatment din sa ga
Addah. Tsana mai yawa, wadda ta cire min burgenin da yake a baya.
Na mike zan bar wajen, kallon mamaki Yaya Maccido ya bi ni da shi, na san tantama ya ke kan tsakin da
ya ji, da shi nake ko da wa? To in ba da shi nake ba da wa nake? Mu biyu ne kacal a dakin, sai Adda da ke
kwance rai kwakwai-mutu-kwakwai.
Wannan ba lokacin da zai tsaya yana tantance Ma’u ta yi masa tsaki ba ne ko a'ah. Ya zo ne da
kyakkyawar niyya ta YI WA KAN SA HISABI tsakanin sa da Addar sa, tare da yin repenting manyan
kura-kuran sa. Repenting din da zai baiwa kowa mamaki. Ya kuma wanke zuciyar kowa nasa. Ya amincewa
kansa bai kasance Da mai farantawa mahaifiyar sa ba. Ya kasance cikin wani irin ajizanci na lokaci mai
tsawo. Amma yanzu jin kan sa yake kamar wanda aka tasa daga nannauyan barci. Ya yarda tunda ya auri
Lubabatu ya canza akalar rayuwar sa bakidaya. A yanzu kam ya yarda Lubabatu ba ta jan shi ga hanyar da zai samu rahmar Allah. Ya tabbata Addah ta yi
hakuri a kansa hakurin da iyaye da yawa ba za su yi shi ba a kan ‘ya’yan da suka haifa. Yana rokon Allah ya
ara masa dama ya gyara kuskuren sa, ta hanyar da ba wanda yayi tsammani, ko da wannan shi ne abu na
karshe da zai aiwatar a duniya.
Hannun Adda ya kama ya rike gam! Hawaye na fita daga idanun sa. Daidai lokacin da likita da nurse suka
murdo kofar suka shigo, ni kuma ina bayan su. Na je ne na kira su don su cire mata karin ruwan da ya
kare su daura mata wani. Kallo daya na yi wa Yaya Maccido na fahimci kuka yake yi. Na kyabe baki a raina
ina fadin,
“Daga baya ke nan!” ....wai sadaka da bazawara.
Ko ganinsa idanuna ba sa son yi, saboda yadda tsanar sa ta lullube min zuciya, har cikin kokon raina.
Gefen gadon Addah na koma na tsaya na harde hannaye na a kirji, na kuma tokare kafata daya a jikin
bango. Ko kallon inda yake bana yi, addu’a kawai nake wa Addah cikin raina. Ina ji yana magana da likitan
kan ya tattara masa bayanan komai na Adda, nan da kwana uku zai fita da ita Jeddah - Saudi-Arabia a yi
mata aikin a can. A raina na ce,
‘Ta baya ta rago’.
Bayan fitar likitan ya dan saci kallon inda nake tsaye. Cikin taushin murya ya ce,
“Ba kwa bukatar wani abu? Zan je gida in dawo”.
Na zumburi baki, “Ba abin da muke bukata, in ma akwai Muhsin zai kawo idan zai zo”.
Ya dan tsura min ido kamar mai son tantance tone din murya ta mai alamun akwai fusata a ciki.
Kyabe baki ya yi, ya mike ya fice a ransa yana fadin, ko me na yi masa shi ya ja wa kansa da ya kula ni,
bayan ya lura yau fizga nake kamar mai bugun aljannu.
Yana komawa gida sashen sa ya nufa, ya yi wanka, ya yi sallah ya canza kaya marasa nauyi ya kishingida a
sofa bed. Wayarsa ya dauka ya kira Aunty Nabeelah. Sun dade suna magana wata irin doguwar magana
mai kama da doguwar jayayya, daga karshe Nabeelah kuka ta koma yi masa a wayar tana sanya mishi
albarka.
Ta ce, komai dare ya tafi Dogondaji, ita kuma za ta kira Bebeji.
Washegari Al-Qasim Yaya ya sa ya dauke ni muka tafi immigration don yin fasfo, don Yaya ya ce da ni za a
tafi Jeddan. Cikin kwana daya fasfo ya fito aka shigar da neman visa na Addah kuma aka sabunta shi.
Ranar da za mu tafi tun dare na hada duk abin da zan bukata, washegari ambulance ce ta dauki Adda
zuwa filin jirgi. Ni da Yaya kuma muna motar Al-Qasim, bai koma gida ba sai da ya tabbatar jirgin da muka
shiga na emirate mai zuwa Saudi-Arabia ya bar kasa.
Yau sai na ga Al-Qasim ya zame min kalar tausayi, he look pale. Na nemi Muhsin na rasa tun jiya, ba inda
ban duba ba ban ganshi ba, a jiya da safe dai ya ce min zai dan yi balaguro, amma ba jimawa zai yi ba sai
dai har mu tafi wata kilan ba za mu hadu ba. Aunty Nabeelah ta kira ni ta wayar Yaya ba da son ransa ba
ya ba ni wayar muna gab da tashi ta ce, “Ki ce alhamdulillah, subhanallah sau uku”.
Na yi yadda ta ce. A daidai lokacin dana gama fadar hakan ne naji gabana ya tsinke ya yi mugun faduwa,
dai-dai lokacin da daqiqar agogon hannu na ta nuna karfe sha daya na safe, kirji na ya hau yin wani
balli-balli har sau uku. Sai ta ce cikin sautin murmushi.
“Safe journey my lovely Sis, ki kula da kan ki, ki kula da Addah, zan iske ku a Jeddah next week Insha
Allah!"
******
JEDDAH, SAUDI-ARABIA
Yau ni Ma’un Nene ce a filin jirgin saman Sarki Abdul’aziz dake birnin Jeddah. Duk da jinya ce ta kawo ni,
na yi farin cikin kasancewa ta a kasa mai tsarki. Daga filin jirgi motar asibitin Doctoor Sulyman Faqeeh ce
ta kwashe mu zuwa asibiti, inda likitoci suka rufu a kan Addah suka ba mu daki V.I.P kamar yadda Yaya
Maccido ya zaba.
Kyawun dakin ya isa, kamar kana gidan ka. Ba abinda babu. Har da ciki da falo, talabijin, A.C, firji, da duk
abin da dan Adam zai bukata. Tunda aka shigo da mu dakin ban kara ganin Yaya Maccido ba, yana can
wajen management din asibitin. Haka tunda muka taho wata kalma ba ta hada ni da shi ba. Sai in na
samu faraga in harare shi son raina in dauke kai. Aka ce aikin banza wai harara a duhu, don Maccido bai
san ina yi ba, don kuwa ban ishe shi kallo ba. Duk da cewa ga kujera ta ga tasa, har kafadun mu na gugar
na juna. Earpiece ya sa a kunnen sa yana sauraron kira’ar Abdurrahman Sudaith, daga baya ban san me
yake yi ba sakamakon bacci da ya dauke ni bayan mun ci abinci.
Har muka sauka a Jeddah ina barci. Na gane an zo ne ta hanyar hannun Yaya da na ji ya zagaye ni yana
unfastening belt dina. Saura kadan numfashi na ya dauke sakamakon dumin numfashin sa da ya sauka a
wuya na. Na galla masa harara, a raina na ce ko ina ruwansa da ni? Oho! Meye business din sa da saka
belt dina da cirewa? Bai san na yi ba, don kuwa bai ma kalle ni ba.
Na nisa daga zuzzurfan tunanin da na fada, daidai lokacin da aka turo kofar dakin namu aka shigo. Yaya
ne, hannun sa rike da ledojin da na fahimci abinci ne ya sayo. A take akuyar ciki na ta motsa, don kuwa
rabo na da abinci tun na cikin jirgi.
Zama ya yi a kujera ya ja karamin tebir gaban sa ya daura ya bude ya soma cin kentucky fried chicken din
da ya shigo da ita, yana yi yana korawa da lemon Pepsi mai sanyi.
Na saci kallon sa tare da hadiyar yawu, mukut! Ko ya tuna da ni ya miko min dayar ledar, amma mutumin
nan ban ishe shi kallo ba. Ya cinye kazar sa tas! Ya fiddo waya ya kira inda daga sunan Sweetie na fahimci
shi da matar sa ne. Sauran hirarrakin kasa sauraro na yi, don ban saba jin irin su a rayuwa ta ba, sai na
mike na sa silifas da zummar barin dakin. A raina ina ta mamakin Yaya, ashe da ma yana magana haka?
Na ce a raina, bari in fita in dan zaga ko zan samu abin da zan saya in ci. Na tuna ko sisi ba ni da shi. Idona
ya cicciko da kwalla, na fita jikin barandar dakin na tsaya ina kallon shige da ficen motoci, a lokaci guda
ina share siraran hawaye daga idona. Ni ban san kaddarar da ta jefa ni hada tafiya irin wannan da Yaya
Maccido ba. Mutumin da uwar sa ma ba ta dame shi ba, wace ce ni da hakki na zai dada shi da kasa?
Wani balarabe ne ya zo inda nake ya tsaya ganin ina kuka yake tambayata cikin larabci ko akwai taimakon
da nake nema? Daga ni har shi ba mu ga sanda Yaya ya fito ba, sai jin hannun sa na yi cikin nawa yana yi
wa Balaraben godiya, ya ja ni muka koma daki.
A kujera ya dangwarar da ni, ya tsaya a kaina. Kallo yake kare min daga sama har kasa, kafin cikin kaushin
murya ya magantu da cewa.
“What’s wrong with you?”
Girgiza kai na yi hawaye na bilbilowa daga ido na, hawayen da bansan yadda zanyi in tsayar da su ba, me
yake so in ce masa? Horon yunwa da ya fara yi min ne ba zan iya dauka ba? Ko kuwa bana son jin ni da
shi mun kadaice a wuri guda irin haka, babu mutum na uku a tsakanin mu ban saba ba?
Hawaye na suka kara yawa. Murmushi ya yi, ya dauko ledar KFC ya aje a gabana, da kansa ya bude min ya
bincire min hancin gwangwanin fanta.
Ya ce, “In kin yi hakuri ai ba zan ci in hana ki ba, ina magana da Madam dina ne, daga yau kada ki kara fita
waje ba tare da ni ba, larabawan nan ba hankali ne da su ba”.
Na kasa cin komai sabida ya tsaya min a ka. Ya gane hakan, amma ya ki matsawa, kallo na yake daga sama
har kasa, ka ar yau ya soma gani na a gaban sa, kallon da na tabbatar Yaya Maccido bai taba yi min
kwatankwancin sa ba tunda aka haife ni, bai taba yi min kallo na biyu ba, amma yau kallon da yake yi min
har ya zarce ka’idar musulunci.
Yanke shawara na yi a raina, gara in shige toilet, don in kubutar da kaina daga wadannan mayatattun
idanun na Maccido. Ina mikewa na yi taku biyu sai ji na yi ya fizgo ni na fada jikin sa. Kadan ya rage in saki
fitsari sabida razana da tsabar firgita.
Rungume ni sosai Maccido ya yi yana sakin wata irin ajiyar zuciya, abin da ya dauke ni ya shilla wata
duniya da ban taba ziyarta ba ke nan. Duniyar da ta fi kama da ta yawo a kan gajimare, domin har bayana
yake bubbugawa da hannunsa daya, yayin da ya sarke na hagun cikin nawa. Tunda nake ban taba jin
lallausar hannu irin na Maccido ba.
Ganin komai nake kamar cikin mafarki, amma nan take kwakwalwata ta koma cikin hankalin ta. Adda ta
sha gaya min, duk namijin da zai nemi taba jiki na, to dan iska ne, kuma ba mutuin kirki ba ne, in guje shi
kuma in zo in gaya mata.
Da karfin gaske na janye jiki na daga cikin na Maccido na zura toilet a guje na banko kofar.
A jikin sink na tsaya ina regaining consciousness tare da hango abin da ya faru cikin dakikar da ba ta wuce
goma ba. Ni ce rungume jikin Yaya Maccido ba mafarki na yi ba, al’amarin mai kama da almara ya faru da
gaske. Kamshin turaren da jiki na ya koma yi na obsession (by CK) ya kara tabbatar min da hakan.
“Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un”. Na ambata har sau uku. Da ma malamin islamiyyar mu ya ce, “Idan
mace da namiji suka kebe, to tabbas shaidan ne na ukun su”. Wato don ya ga babu idon kowa a kan mu
shi ne zai aikata wannan zaluncin a gare ni? Zan kuwa ba shi mamaki, duk girman sa da ke idanuna
wanda da ma yanzu rawa yake, sabida tsanar dana yi masa akan laifuffukan sa ga Addah zan yakice shi in
nuna masa na san abin da nake yi, kuma na san mutuncin kaina. Ina masa kallon mutumin kirki ashe shi
ma in ya samu faraga dan duniya ne? Ina jin bude kofar sa da fitar sa, na wanke fuskata a sink na fito. Kazar na dauka na gyara zama na afka
mata babu sassauci. Addah na wani daki na musamman suna kula da ita, sai dare suka turo ta bisa gado
zuwa dakin mu suka kwantar da ita a kan gado. Da alama ta sha alluran barci don barci ta ke yi sadidan.
Ban kara ganin Yaya Maccido ba sai karfe tara na dare agogonsu na can. Ya canza kayan jikin sa, da alama
wanka ya yi. Ina daidai kan Addah rike da hannun ta sanda ya shigo, ledojin hannun sa ya ajiye ya karaso
inda muke. Na kuwa tattare fuska na hade girar sama da ta kasa.
“Ba ta tashi ba?” Ya tambaye ni.
Juyar da fuska na yi wani gefen ban ce masa komai ba.
Ya ja kujera ya zauna a gaban Addah yana karanto addu’o’i yana tofa mata.
“Ga abinci can ki je ki ci”.
“Na koshi”. Na yi saurin bada amsa.
Ya daga fararen idanunsa ya kalle ni, kallon sakan biyu, kafin ya ce cikin muryar bada umarni.
“Asma’u, na ce ki je ki ci abinci”.
Sai na samu kaina da kasa musawa wannan karon, domin ya murde fuska ya koma Maccidon sa da na
sani.
Shinkafa ce da gasasshiyar qibdah (hanta), na zauna na soma ci ba don yunwa ba, sai don bana son wata
magana kowace iri ce ta sake hada ni da Maccido.
Wayar sa ce ta yi kara, sai ya dauka ya yi magana, sai na ga ya kalle ni ya wani bata rai, kafin ya ce, “Zo ki
karba”.
Na tsame hannuna daga cikin abincin na je na amshi wayar na kara a kunnena. Aunty Nabeelah ce.
“Hello Ma’u, ya ku ka sauka, ya kuma jikin Addah?”
Na ce, “Aunty lafiya kalau. Addah dai tunda muka zo suke mata allurar barci wai sai jibi za a yi aikin”.
Ta ce, “Ina nan ina shirin tahowa, sai nan da kwana shidda. Ki yi hakuri da Maccido kin ji?”
Dan murmushi na yi, na ce, “Aunty ke ma kin san ba wani shiri muke ba, me ya sa aka hado ni da shi,
bayan ga Muhsin?”
Aunty Nabeelah ta yi ajiyar zuciyar da na jiyo ta, ta ce, “Sabida shi ne babba. Abin da zai yi Muhsin ba zai
iya ba. Sannan kin ga yana so ya yi amfani da damar ya yi repenting kurakuran sa ne. Ya kula da
mahaifiyar sa. Alhamdulillah tunda mun samu Allah ya juyo mana da hankalin sa sai mu ba shi dama. Shi
ma ya samu ladan mahaifiyar sa da yake ta batawa.