Showing 45001 words to 46393 words out of 46393 words
Chapter 16 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf
ta’.
Tausayin Yaya ya kama ni, na sani tun fil’azal shi ba mai son tashin hankali ba ne. Na soma kissing dinsa
lightly duk dai don in mantar da shi bacin ran da yake ciki. Daga nan muka manta komai sai hanyar da za
mu faranta ran juna. Kullum ya zo gare ni tamfar ba mu taba kusantar juna ba haka muke komawa.
Soyayyar kamar ana mata ban ruwa, tana dada yin yado da rassa.
A hankali zuciyata ta gama macewa a son mijina Attahir, wani irin so da ban san iyakar sa ba. Yaya ya tafi
ya bar Ihsan da Ahsan tare da mu, sosai nake kula da yaran, kwana biyu suka ware suka saki jiki da mu,
Muhsin na fita da su in ya dawo ya sawo musu ice-cream, ai kuwa nan da nan suka makale masa, su ce
min Aunty su ce wa Adda Granny kamar yadda Muhsin ya koyar da su.
Al-Qaseem ya zo ya gaya wa Addah ya samu matar aure, za a je masa tambaya, ‘yar garin Zamfara ce,
Addah ta ce in an fidda ranar zuwan ya sanar da ita za ta je insha Allahu.
A gajiye Attahir ya iso gida, falmaran din suit din jikin sa a hannu da jakar macbook din sa ya fito daga
mota ya rufe ya taka zuwa cikin gida.
Tun jiya da daddare da ya dawo ba su hadu da uwargidan ba, sanda ya dawo ba ta sani ba sannan da
sassafe kafin ta fito ya wuce ofis. Yana shigowa da ita ya fara tozali zaune a tsakiyar three seater.
Kallo daya ya yi mata ya kauda kai yana mamakin wai wannan matar sa ‘yar kwalisa wanke hannu ka taba
Lubabatu ce, ta koma kamar wadda aka kwanto daga turu, ta yi baki ta rame kamar ba ita ba. Kayan
jikinta ya gane tun wadanda ya ganta da su ne ranar da zai tafi Sokoto. Lokaci na farko da tausayinta ya
dan tsirga masa, ya sa kafa ya wuce ta zuwa dakin sa ba tare da ya ce da ita komai ba.
Yana shiga dakin ya tsaya jikin gado ya soma loosing tie din wuyan shi. Bankado kofar dakin ta yi ta fado
kamar an jefo ta. A firgice ya juya suka yi ido hudu. Cikin kakkausar murya ta ce.
“Attahir ina ka kai min ‘ya’ya na?”
Ya juyo tare da dan kura mata ido, sannan ya juya ya ci gaba da abin da yake yi. Hakan ya kara fusata ta,
wato ma bai san tana magana ba. Takowa ta yi har gabansa ta kama kwalar rigarsa ta girgiza shi cikin
yanayin fita hayyaci.
“Wallahi ko ka ba ni ‘ya’yana ko shari’a ta raba mu”.
Trying hard to control his temper ya ce “Sake ni Lubabatu tun muna shaida juna, bana so tsautsayi ya sa
na kara kai hannu a jikin ki, in har ba arziki ne ya kawo ki ba kar ki kuma gigin shigo min daki”.
Lubabatu ta sake shi ganin yadda idanun sa ke mata kallon da ta tabbatar yana nufin abin da yake cewa.
Ta sulale a gaban shi ta fasa wani irin gigitaccen kuka, ta ce,
“Tsakani na da kai yau ke nan Tahir, sabida ka auri ‘yar gidan ku? Duk soyayyar da na shayar da kai ka
manta? Duk wahalar da na yi maka ta daukar ciki da haihuwa sakamako na ke nan? Me ka gano a jikin
wannan yarinyar wanda ba ni da wanda ya fi shi? Shin soyayya ta gare ka tun ba ka da komai ta cancanci
wannan butulcin? Me na yi maka a rayuwa banda so da kauna da za ka yi min wannan sakayyar?”
Ta ci gaba da kuka mai nuna komai ya fara kare mata, dabara, izza, masifar da bala’in gabadaya sun kare
mata. Saboda wannan Tahir din da ke gabanta ta tabbata sabon Attahir ne ba wanda ta danne shekaru
biyar yana mata biyayya da bauta ba.
An ce tsakanin mace da miji sai Allah. Sai ya samu kansa da jin tausayin ta. Ya san Lubabatu na son sa,
kuma son ne yake take duk abin da ta ke yi, wanda a haukanta shi zai dawo mata da abin da ta rasa a
Tahir din. Yana son Lubabatu domin soyayyar ce ta sa ya aure ta, amma in ya tuna yadda ta shiga tsakanin
sa da kowa nasa tunda ya aure ta, sai ta yi bakikkirin a idanun sa.
Hannunta ya kama ya mikar da ita, ya ja ta suka zauna tare a bakin gado. Wani tsami-tsami da
bashi-bashi da ke tashi daga jikin ta ya naushi hancin sa. Da kyar ya hadiye miyau, ya ce, “Lubabatu ke ce
kuwa? Yaushe rabon ki da wanka? Now, ba ni da magana da ke sai kin je kin yi wanka, ki fesa turare
sannan ki zo mu tattauna. Amma ki sa a ranki Asma’u ta riga ta zama wani bangare nawa, dole ki karbi
wannan gaskiyar, idan har kina so mu yi magana ta fahimta ni da ke”.
Maganganun sa ba karamin tunzura Lubabatu suka kara yi ba, wai yau ita Attahir ke cewa tana wari,
sabida ya auri 'yar cikin sa, har me wannan bagidajiyar zata gaya mata? Kodayake ta san da gaske tana
bashin, rabon ta da wanka har ta manta.
Jiki ba kwari ta mike ta bi umarnin sa. Tana fita ya zaro wayarsa daga aljihun wandonsa. Bugu daya na
daga ya ce,
“Asma’u ko ki neme ni ki ji ya na iso gida ko?”
Na yi kasa da murya na ce, “Ayya Yayana. Wayar tawa ce Ahsan ya tsoma min a bokitin ruwa, wai zai
wanke min. Da kyar Muhsin ya samu aka gyaro ta yanzu. Amma ka san kana raina ko? Kuma addu’ata a
kowacce sallar farillahta ita ce Allah ya kare min kai a duk inda ka ke”.
Attahir ya lumshe ido, muryata na kara kashe masa jiki, ya ce, “na gode da wannan addu’a taki Asma’u
na, hope my soldier is kicking very well, kuma Ahsan da Ihsan ba sa damunsa? I’m missing you terribly…
idan na ce kewa ina nufin ta komai…”.
Murmushi na yi na ce, “Yaya na gode, kai ma ka san in na ce I LOVE YOU is not enough to express the
feelings…”.
Maccido sai daga kai ya yi ya ga Lubabatu a kansa tana huci kamar mesa. Kafin ya yi aune ta fizge wayar
daga hannunsa ta rotsa ta da kasa. Har ga Allah ya so ya yi sulhu da ita a wannan daren don ta samu
sanyi a zuciyar ta ko ya ya ne, amma abin da ta yi din nan ba karamin fusata shi ya yi ba. Ya daga hannu
zai kai mata mari, ya yi maza ya taro hannun nasa. Ya rike hannun da zai kai marin da hannun hagunsa ya
koma gefen gadon sa ya zauna.
“Fice min daga daki, kafin ki sa a kwashe ki a wheel-borrow yanzun nan, tunda ba tare muka hada kudi
muka gina dakin ba”.
Wani dogon tsaki ta ja, sannan ta juya tana fadin, “Aikin banza. An dai ji kunya wallahi, kanwar da aka
gama yi wa muzurai shekara da shekaru, rana daya ake ce wa I love you don yada girma da bunsuranci.
Yarinyar da ko fasali babu, ‘yar cin arziki kawai. Wallahi Attahir ka fadi babu nauyi".
Ganin ya taso zai cimmata ta kara da gudu ta bar dakin, ta shige nata ta banko kofa.
Rayuwar Yaya da Lubabatun sa ke nan. Sai abubuwa sun yi kamar za su gyaru sai ya kuntuka mata abin da
zai sa ta kara birkicewa. Duk abin da yake yi akan Asmau ba yana yi don ya tsokane ta bane sai don shi
kansa bai san ya ya aka yi yake zama Romeo ba in dai yana tare da Asma’u a waya. Ita kuma gata da labe,
kalaman da Lubabatu ba ta iya jure wa jin su, kuma ta kasa daina yi masa labe ga duk wayar da zai yi ko
da ba Asma’u ya kira ba.
Mamaki yake, sau tari ya ce "Lubabatu ashe haka ki ke? Ashe iblishiya ce ban sani ba? Shin a kanki aka
fara kishiya? To sai dai ki kashe kanki, kuma Asma’u ta shigo gidan. Amma masifar ki, jidalin ki, bala’in ki,
haukan ki da rashin hankalin ki ba abin da zai sa, ba abin da zai hana”.