Showing 9001 words to 12000 words out of 46393 words

Chapter 4 - YIWA KAI HISABI COMPLETE NOVELS BY TAKORI .pdf

hannunta.
Muna ganin sanda aka zuge labulen falon aka tabbatar akwai bakuwar mota a kofar gidan, kafin entrance
door din ta bude. Yaya Maccido ya fito sanye da jallabiyya fara kal mai gajeren hannu, kafarsa slippers ne
mai kalar fari shi ma. Ido na kura wa Yaya Maccido, yana karasowa inda muke.
Zuciyata na ji tana bugawa da sauri-sauri (at a speedy level) sakamakon ganin wata irin rama da baki da
ya yi. A lokacin da ya iso gaban motar mu ba zan iya ci gaba da kallon shi ba, runtse idanuna na yi na
sunkuyar da kaina ina tambayar kaina, wace irin rashin lafiya ya yi haka?
Ita kanta Aunty Nabeelah jikin ta ya yi sanyi, ta yi saurin balle murfin motar ta fito ta rufe ta jingina jikin
motar tare da harde hannayenta a kirji tana kallon shi yana doso ta.
Muhsin ma ya fito, amma ni sai na gyara zamana ina kallonsu daya bayan daya. Ya iso gaban Nabeelah
kamar za su hade don kusancin da ke tsakanin su, ya ce,
“Baki haka unexpected?”
Duk wani tanadi da Nabeelah ta yi na cin mutuncin Attahir ta neme shi ta rasa. Duk wasu muggan kalami
da ta shirya fada masa sun subuce daga bakin ta. Kallon sa kawai ta ke kafin ta kai hannu ta dafa kafadar
sa.
“Maccido!” Ta fada a hankali.

Dan murmushi ya yi kafin ya ce, “Nabeelah, ya ya za ku taso tun daga Sokoto amma ki kasa kira na ki fada
min?”
Ta lumshe idon ta a hankali ta ce, “Saboda ba ma so ka san za mu zo. It is a surprize visit”.
Kama hannayenta biyu ya yi ya ce, "I appreciate. How is ADDAH?”
Cikin raunin murya Nabeelah ta ce, “Do you still remember her? Ba ka neman ta ko a waya Maccido!”
Maccido ya girgiza kai idanun sa sun kada, ya ce, “She is always in mind, na zama busy ne kwana biyu.
Shekaran jiya muka dawo daga Egypt na kai Lubabatu ganin likita”.
Aunty Nabeelah ta gyada kai, “Ya yi kyau, mu karasa ciki ko? Don a gajiye muke”.
Juyawa ya yi kadan yana kallon falon nasa kamar mai tsoron ko ana kallon su, kafin ya ce, “Ku jira in sanar
da matar gidan, bai kamata ta gan ku katsahan ba”.
Ya juya da saurin sa, Nabeelah ta girgiza kai tana bin sa da kallon tsoro da mamaki, a ranta tana kakabin
al’amarin nan mai kama da mafarki. To tsoron matar tasa ya ke yi ko me? Ta gaza fahimtar komai, wai
Maccido ne wannan? Kanin ta vibrant and energetic? Gabadaya ya zabge kamar an zabtare shi, ya yi
sanyi kamar ba shi ba. Muhsin kam ai bai jira an dawo daga yi masa ison ba ya bude booth ya fiddo
jakunkunan mu ya cicciba ya yi gaba da su yana fadin,
“Ma’u fito kin ji! In mun shiga ba izni a koro mu”.
Na zunkuda goyona sannan na fito.
Daga matar har mijin sai ganin mu suka yi mun murdo kofa muna shigowa, kowannen mu dauke da
sallama a bakin sa. Cirko-cirko muka same su shi da Lubabatun kamar zakaru, da alama ko ma me suke
cewa ba cikin dadin rai ba ne.
Wani kallo ta yi mana kamar ta ga kashi, sannan ta juya ta yi masa kallon za mu gamu ne, ta yunkura da
kyar da tirtsetsen cikinta ta bar falon zuwa dakin ta. Ko kallon Aunty Nabeelah dake shigowa bata tsaya yi
ba.
A rayuwar Attahir Atiku Dogondaji, bai taba jin ya muzanta a gaban Yayar shi da kannen shi irin yau ba. Ni
dai ina daga gefe sai faman jijjiga Aasim da ke goye a baya na nake. An ce namiji har kullum namiji ne, shi
ya sa Yaya Maccido ya sunkuya ya dauki jakar Aunty da tawa ya ce mu biyo shi, yayin da baby bag din
Aasim ke hannuna.
Wani daki ya bude a falon ya ce mu shigo. Daki ne mai tsananin kyau ya sha furnitures na alfarma da
shimfidar gado mai laushi. Ya juya cikin jin nauyi ya ce da Aunty Nabeelah.
“Zan je na kai Muhsin hotel na samo muku abin da za ku ci, babu dakin da zai iya sauka a nan”.
Aunty ta ce, “A gaskiya ni bana cin abincin sayarwa sai wanda aka sarrafa a gida”.

Ya jefar da kai gefe, ya ce, “To ba mu yi ba, ko ba kya ganin ta yi nauyi ne, yaushe za ta shiga kitchen ta yi
muku wani girki a daren nab?”
Aunty ta kyabe baki, ta ce, “ba matsala, in dai akwai kayan girkin, yanzun nan Ma’u za ta dafa mana”.
Shi sai a lokacin ma ya lura da ni da ke gefe ina fama da baby. Ya dan dube ni na ‘yan sakanni a ran sa ya
ce, “Ta yi tsawo, ta kara girma”.
“Ba ki gaji ba za ki iya girki?” Ya fada yana kallon bangaren da nake.
“Babu komai, zan iya”. Na bada amsa cikin girmamawa.
“Okey, mu je in nuna miki komai”.
Na mika wa Aunty Aasim, na bi bayan shi muka fita.
Wani rantsattsen kitchen ya kai ni, komai tafiyayye kuma rantsattse, sai dai tsaftar kitchen din da sauki.
Ya nuna min freezer da fridge ya ce, “Komai ki ke nema za ki samu”. Sannan ya bude wani labule da ya
raba kitchen din biyu. Kayan abinci ne katan-katan da abincin gwangwani nau’i-nau’i, ya nuna min
bangaren spices da maggi, sannan ya dago ya dube ni by mistake muka hada ido.
“Ki dafa har da ni”.
Kai na gyada, ya fita ya bar min madafin.
Samun kaina na yi da bin bayan sa da kallo, wani irin kallo na tausayi da kaunar ‘yan uwantaka. Masculine
turaren sa mai sanyi har zuwa lokacin bai bar kicin din ba. Ajiyar zuciya na yi bayan fitar sa, na dau
madaidaiciyar tukunya na aza bisa wuta. A raina ina cewa, jallop din cous-cous zan yi da farfesun kifi
kawai ya fi sauri.
Na zo shigowa dakin don in tambayi Aunty ko zaben da na yi mana ya yi mata? Na ji tashin muryar ta a
bakin kofa cikin bacin rai tana fadin.
“Yanzu a matsayi na na Yayar ka uwa daya uba daya, tarbar da matar ka za ta yi min ke nan? Ta yi min
kallon banza ta shige daki, to me na tare mata? Ko zuwana ne ya bata mata rai, ko kuwa ba ka gaya mata
ko ni din wace ce dinka ba?
In ba ta so a rabe ta kaima sai ta hana ka rabar kowa naka? Uwar da ta haife ka Maccido tunda ka yi aure
ta daina ganin ka? No wonder na ga duk ka fige kamar kazar mayu, to ko dai ita mayya ce ta ke lashe ka
ba ta so a ankara sai ta gama cinye ka tas? Ta kaiwa uwarka kasusuwan ka? Attahir let me tell you what
you forgot… Addah ba ta da kowa sai mu, ba ta bukatar komai a wannan stage din na rayuwar ta sai mu
da kulawar mu. Idan ka biye wa wannan annamimiyar wuta za ta kai ka billahillazee… Na gama fahimtar
babu mutunci da imani cikin al’amarin ta. Bari ka ji in gaya maka, in ma asiri ta ke maka, ko tsoron ta ka ke ji da ka watsar da kowa naka ka kamata,
to mu zuba mu da ita shege ka fasa! Ta zo gidan da ba a san asiri ba, amma an iya dungura goshi a yi
sujjadah. Tunda ka zabe ta a kan mahaifiyar ka ka je mun yafe mata kai, amma zamu kai kara wajen Allah.

Dadin abun ba kai kadai Adda ta haifa ba… Allah ya kai mu gobe za mu yi asubanci mu koma inda muka
fito, in yaso ta yi gunduwa-gunduwa da kai ta sa a tukunya ta dafa ta cinye…”.
Ta fashe da matsanancin kuka, wanda ya sa ni saurin ja da baya na koma kitchen gabana na faduwa. Ban
taba jin Nabeelah na magana cikin zafin rai irin yau ba. Jikina har rawa ya ke yi in na tuna babban mutum
irin Yaya Maccido take yi wa wannan fadan.

**SUMAYYAH ABDULKADIR TAKORI* 07030137870
*










~HISABIN NAFS~




((5)). Har na gama girkin na dauko shi zuwa daki suna nan a yadda na bar su. Kai da ganin Yaya Maccido
ka ga wanda damuwar duniya ta yi wa rubdugu. Yana zaune gaban Aunty kan sa a sunkuye. Ban san dai
me ya ke gaya mata ba, amma na ga alamun ta sauko daga fushin ta sun koma magana ta fahimta.
Ta ce, “To wannan bakin da ramar da ka ke yi na mene ne? Matar taka ba ta ba ka abinci ne ko mene
ne?”

Ganin shigwa ta ya sa bai ba ta amsa ba. Ta maido dubanta gare ni, ta ce.
“Kawo abincin nan Asma’u”.
Na karasa gabanta na ajiye katon tray din ta ce, “Sannu kin ji, Allah ya yi miki albarka”.
Ta dau plate da serving spoon ta yi serving Yaya, ta loda masa abincin sosai ta tura masa, sannan ta zuba
wa Muhsin, ni da ita kuma ta hada mana a faranti daya.
Tunda Yaya Maccido ya soma cin abinci bai dago kansa ba. Kafin ka ce me ye wannan ya tashi da farantin.
Aunty na kallonsa ta kasan ido cike da tausayi, ta ce.
“Ko a kara maka?”
Ya ce, “I’m okey, zuba dai in kai wa Lubabatu ita ma ba ta ci abincin dare ba”.
Wani kallon banza Aunty ta yi masa, ta ce, “An hana, ba za a bayar ba, na karfi ne ku zo ku kwata”.
Murmushi Maccido ya yi, wanda ke kara masa kyau a duk sanda ya yi shi, ya mike yana fadin.
“Bari in bar ku ku huta, inda abin da ku ke so da babu a gidan ku fada da safe sai a sayo”.
Suka fita shi da Muhsin, kowanne jiki ba kwari.
Aunty ta dauka da safe Lubabatu za ta shigo ta gaishe ta, amma shiru ka ke ji ba ita ba karin kumallon
mu. Shi ma maigidan ba mu gan shi ba.
Bayan na yi wa Aasim wanka, na shirya shi ta ce in shiga madafi in sama mana abin da za mu ci. Ran
Aunty Nabeelah a matukar bace yake, ban taba ganin ta cikin fushi haka ba. Na shiga kicin ina tunanin
abin da zan sama mana mai dan sauki, na jona ruwan tea a kettle na debi dankali na soma ferewa. Ina
cikin aikin na ji taku an nufo madafin. Kafin matar gidan ta bayyana cikin kwalliya ta kasaita, kamshin
turaren ta duk ya bade kicin din. Ta yi min wani sakaren kallo ta ce.
“Ke kuma wace ce haka za ki shigo min kitchen babu neman izni babu komai? Ko haka ake yi a kauyen
ku?”
Na sunkuyar da kai rike da dankali a hannu.
Ta nuna min hanya, “Wuce ki ba ni waje gayyar na ayya kawai”.
Ba musu na ajiye wuka da dankali na fice.
Aunty na gyaran kayan mu lokacin da na shiga, ta daga ido ta dube ni, ta ce,
“Har kin gama?”
Kaina a kasa na ce, “Ta koro ni”.

Kafin in rufe baki sai gata ta shigo daga bakin kofa ta tsaya tana taunar cingam rakakas! Rakakas! Ta ce da
Aunty, “Sannun ku da zuwa, jiya kun zo ina jin barci, kuma zuwan naku ba notice”.
Aunty ta daga ido tana kallon ta kawai”.
Ta ce, “Mai aiki za ta zo yanzu sai ta dafa muku abincin, wannan yarinyar ta fiya gidadanci ko kunna gass
ba ta iya ba”.
Ba ta jira cewar Aunty Nabeelah ba, wadda ta daga kai a fusace zata mayar mata, amma nan da nan
gargadin Adda ya shigo cikin kan ta, Lubabatu ta yi wucewar ta.
Abinka da cikin jego, Aunty yunwa ta ke ji sosai, amma haka ta yi juriya. Yaya Maccido ya shigo ya sha
wanka ya dauki walwali cikin shadda getzner. Da na kalle shi sau daya, ban kara marmarin maimaitawa
ba, sakamakon cewa kwarjini, haiba da kamalar sa masu cika idanu ne. Ba kowacce mace ce zata iya jurar
hada idanu da Maccido ba.
Ko gama gaisawa da Aunty ba su yi ba, a gurguje ya ce, “Zan kai Lubabatu asibiti, wai tun jiya ba ta ji
motsin baby ba”.
Aunty ta hadiye malolon bacin ranta ta ce,
“Hakan yana da kyau, sai kun dawo”.

Sai bayan wajen awa daya da fitar su wajejen karfe goma na safe muka ji motsin ana share-share. Zuwa
lokacin yunwa ta ci ta cinye mu. Har karfe sha daya na safe ba breakfast din da aka ce ‘yar aiki za ta zo ta
ba mu. Yunwa ta ci mu ta cinye don mu a gida karfe takwas mun karya kumallo.
Aunty na kwance tana bai wa Aasim nono, ni kuma na yi wanka ina shiryawa. Ta dau wayarta ta kira
Muhsin.
“Muhsin, kana ina ne?”
Ya ce, “Aunty ina hotel din da Yaya ya kai ni, na shirya yanzu zan taho”.
Ta ce, “To don Allah ka tsaya ka samar mana wani abu a hanya, har yanzu ba mu karya ba”.
Bai tsaya bincike ba, ya ce,
“To, in sha Allahu”.
Muhsin ya iso mana da takeaway muka zauna muka ci mu duka uku. Shiru-shiru babu masu gidan har
bayan azahar. Aunty ta ce da Muhsin ya tashi mu kama hanya, ita ba za ta kuma kwanan gidan Maccido
ba. Muhsin ya yi ta tausar ta, ya ce, yanzu in mun tafi tafiyar dare za mu yi, ta yi hakuri goben da muka yi
da Addah za mu koma mu yi asubanci mu kama hanya.

Masu gidan ba su shigo ba sai karfe hudu na rana. Yaya Maccido rike da manyan ledoji, Lubabatu ta biyo
bayansa ta kalli Aunty da murmushin keta ta ce,
“Sannun ku fah!”
Aunty ba ta amsa mata ba, ta ce, “Mun biya gidan friend dita ne daga asibitin, ina fatan Rose ta ba ku
abinci?”
Daga ni har Aunty babu wanda ya amsa ganin haka ya sa ta tura katon cikin ta ta yi gaba tana yi wa Yaya
wani shu’umin kallo.
“Dear ina jiran ka in kun gama, ka tausa min kafafun nan, ka ga duk sun kumbura”.
Ta wuce ba tare da ta kara kallon kowa ba. Shi kuma kunyar Aunty ta hana shi amsawa.
Ya ajiye ledojin hannun sa ya zauna kusa da ‘yar uwar sa, sannan ya janyo su ya soma bubbudewa.
Sayayya ce ya yo mana har da ta banza, kowa ledar sa daban. Sannan ya mika wa Aunty ledar takeaway
din gasassun kaji da fresh milk, ya ce,
“Ku ci da hakuri, Lubabatu ta ce ba ta so Asma’u na shigar mata kitchen jiya ta lalata mata abubuwa”.
Aunty ba ta san sanda ta kira sunansa da karfi.
“Attahir!”
Da sauri ya dube ta, ta ce, “Kicin din nata ya ci abu kazan-kazan uban sa! Ma’u ba faqiriya ba ce, ba ta
kuma fito daga fatararren gida ba. Bar ganin dazu ta kira ta bagidajiya ta kuma kore ta daga kitchen na yi
shiru, to ba tsoro ba ne, gudun magana ne, gidan ku kuma yanzu za mu bar muku shi ba sai anjima ba.
Insha Allahu wani cikinmu bai sake takowa gidan ka Maccido, mun bar wa Lubabatu! Sannan ina mai
shawartar ka da ka dage a kan ibadah, ka gyara ibadar ka. Akwai gyara a cikin mu’amalarka da Ubangijin
ka. Wallahi Maccido ba kalau matar nan ta barka ba.
Gidanka kuma yanzu za mu bar shi ba sai an jima ba, ko kai ka saura da wa Addah, daga yau ta yafe ka,
mu uku mun ishe ta za mu yi mata komai. Sai dai ka kasance cikin kokonton hanyar shigar ka aljannah”.
Aunty ta mike ta sunkuci Aasim tana hawaye. Muhsin ya ce, “Aunty don Allah ki yi hakuri da yau da
goben duk daya ne, ki dauki abubuwa da sauki, abin duk bai kai ga haka ba”.
Yaya Maccido kansa na kasa bai ce komai ba. Ya rasa abin da yake masa dadi, ya rasa me suke yi shi da
Lubabatu wanda yake fusata Aunty haka. Shi bai ga laifin Lubabatu ba tunda gidan ta suka zo suka same
ta babu sanarwa. Ya san Lubabatu ba ta karbar wasu baki in ba nata ba, ai ta yi kokari ma da karbar da ta
yi musun, a dai halinta da ya sani.
“Ku yi hakuri, abun bai kai haka ba, Lubabatu fa ta yi kokari da har ta bar ku kuka kwana gidan nan, ita
bata karbar baki in ba ita ta gayyato su ba.”.

Yaya Maccido ya fada cikin sanyin murya.

Aunty zama ta yi a kasa tana kuka riris, fuskar ta cikin kafafun ta. Bayan ta dangwara min Aasim akan
cinya ta. Tausayin Maccido kawai ta ke ji. Kafin a samu mutumin kirki mai son ‘yan uwan sa da karrama
al'amarin su a baya irin Maccido abun mai wuya ne. Kafin a samu mutum mai kula da mahaifiya da
tsantseni cikin mu’amalarsa da ita irin Attahir sai an yi sa’ar gaske. Rana daya daga yin aure ya zubar da
duka wadannan halayen nasa. Mace ta canja shi, canjin da ta kasa ganewa.
Jikin Maccido ya yi mugun sanyi, shi ma nasa idon suka cicciko da kwallah. Amma kokari ya ke ya maida
su. Rokon Aunty ya soma yi a kan ta yi hakuri, idan ya bata mata rai, bai yi da gangan ba.
Ba zan iya jure kallon wannan abun tausayi ba, babban mutum kaman Yaya Maccido na hawaye a
gabana. Don haka na mike tsam na yi toilet dauke da Aasim ba tare da sun ankara da tashina ba. Zama na
yi a gefen kwamin wanka ina hawaye ni ma rungume da yaron, na tausaya wa halin da suka samu kan su.
Ban san yaya suka yi suka ciwo kan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login